Showing 186001 words to 189000 words out of 209154 words
ta yasar shi.. Shikenan Ta rasa abinda yai mata saura na bayanta. A hankali ta koma ta zauna tana girgiza kai hawaye na k’ok’arin ciko idanunta “A’a a’a bazan rasa wann sisin kwabon ba.. Shine kad’ai saura mun.. Zanci gaba da nemansa cikin kaya har Allah yasa na samu.. Nasan yana nan mak’ale wani wajen.. Zanci gaba da dubawa sannu a hankali har na sameshi..” Ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka gangaro mata.
**
Ta yanda Mommy take shiga bata nan take fita ba “Sabida bakida hankali ke shahshasha ce wacce ta rako mata duniya koh.. Shine kika d’ibi k’afafu kika tafi gidansa kikaje kina haukar nan naki da bazaki daina ba koh.?!”
Safeenah ta turo baki tana jin zuciyarta na tashi kaman zata amayo da cikinta. Yamutsa fuska tai tace “Mommy dan girman Allah ki barni naji da abinda ke damuna.. Ni wllhi ganin matar Mu’azzam da nai ya haifar mun da tashin zuciya.. I already have headache dan Allah ki k’yaleni haka nan Mommy, Please..!” Ta k’arashe tana mai d’ago wa mahaifiyar nata hannu.
Cikeda takaici Mommy tace “Ai idan baki cire wann jarababben cikin zuciyarki ba haka nan zaki k’are da wahala.. Jarababbiyar banza ‘yar wahala.”
“Mommy idan dai akan my Halal ne ki kirani da sunan da kikaga dama wllhi wllhi babu abinda zai rabani da mijina.. Ko shi Mu’azzam d’in bai isa ya raba aurenmu ba.. So ki daina bama kanki wahala kan My Halal.”
Throw pillow dake gefenta ta jifawa Safeenar dan takaici “Kinci ubanki keda Halal d’in.!” Hakan yai daidai da mik’ewar Safeenah a guje ta nufi guest toilet tana k’waza amai..
Mommy ta bita da kallo baki sake ita ta ma mance Safeenah ciki gareta.
Sallaman Mu’azzam ya dawo da hankalin Mommy..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*58*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Zabura Mommy tai babu shiri ta nufo k’ofar tana k’ok’arin taresa take fad’in “Mai ya kawoka gidan nan.. Kai yanzu idan kanada kunya sai ka kuma tako k’afarka cikin gidan nan bayan dik kalan rashin mutuncin da ka fesa mana.. Idan gaisuwa ce ya kawoka ni Hajara na yafe bani buk’ata a k’ara gaba ehe.. Idan kuma k’anina mahaifinka kazo gaidawa shima kasan yanda zaka samesa.. Kaje can company ka samesa amma ba gidana ba.. Sann Idan tak’amarka shine nan d’in gidan mijin mahaifiyarka ne Toh itama bata a nan gidan balle kace zakake shigowa kanka tsaye duk sanda kaga dama.!” Ta k’arashe tana huci tayi famkam famkam Ta cike k’ofar gaba d’aya.
Mu’azzam baice mata komai ba Sai dubanta da yake cikeda mamaki. Wai Mommy ke masa duka wad’ann abubuwan. Matar da a baya bata nuna masu komai ba face zallan k’auna.. Abubuwan da take masa shi gani yake yayi yawa ace duk kawai kan laifinsa k’wara d’aya take hukuntasa haka. Ya fara shakkun k’aunar da Ta nuna masu a baya shida ‘yaruwarsa da mahaifiyarsu.
Musaddiq ya k’araso yana girgiza kai ganin ko damuwa da cewa gidan akwai ma’aikata sann ga k’annensa Mommy batayi.. Ita kawai damuwarta ta tozarta Mu’azzam.
“Mommy dan girman Allah wann wane irin abu ne.. Mommy will you please..”
Dakatar dashi Mu’azzam yai ta hanyar d’aga hannu kafin ya dubi Mommy na d’an lokaci kaman mai karantarta. Sai jijjiga take nan bakin k’ofar tana addu’a cikin zuciyarta Allah hana Safeenah fitowa daga band’akin nan a yanayin da take.
Ya d’an d’ibi dak’ik’ai a haka kafin ya jefa hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ba tareda ya furta komai ba ya juya ya fice daga parlorn.
Musaddiq ya dubi Mommy kawai had’ida girgiza kai kafin yasa kai ya shige.
Tabi bayansu da kallo tana jinjina kai “Ba yanzu ba Mu’azzam.. Bazan bari kasan cewa akwai gudan jininka kwance cikin Safeenah ba sai zuwa lokacin da na tsara.. Shiri na musamman nake maka my dear stepson or should I call you my dear Son-in-law.” Tana gama fad’i Ta murmusa a hankali kafin Ta juyo tana duban k’ofan bathroom d’in da Safeenah ta turo ta fito dik a galabaice. Fuskarta ya kuma yin haske na musamman, kana ganinta kaga mai k’aramin ciki.
Dikda jiwa dake k’ok’arin d’aukanta bai hanata nufan k’ofa tana fad’in “My Halal.. Mommy kaman naga My Halal yazo..!”
Janyota Mommy tai a fusace ta zaunar saman kujera “Zauna dan Ubanki babu yanda zakije.. Mahaukaciyar banza.”
Safeenah ta turo baki tana duban Mommy “Mommy Nifa bazaki min wann fir’aunanci na d’auka ba ehe.. 21st century fah muke.. Da a k’asashen waje ne nayi imani da na makaki kotu.. Saidai kawai kiga sammaci..”
Mommy ta saki baki “Ni kike ce zaki maka Kotu kan wancan watsettsen.? Eh lallai Safeenah yayi.. Wato Ina karb’ar miki ‘yanci baki gani.. Toh maza tashi tashi ki bisa d’in kiji bak’ak’e.. Matarsa ta kwance miki Karnuka shi kuma saidai ya kwance maki mari masuji da lafiya.. Idan ke shashasha ce ki tashi kije..!”
D’an lumshe idanunta Safeenah tai tana dafe kanta dake d’an sara mata. Ga k’amshin turaren wutan dake tashi a parlorn sam bai mata dad’i ba. Batabi takan Mommy ba ta shiga kiran ma’aikatan gidan tana tambayarsu wane irin turare suka saka yau a gidan. Dik suka ce wanda aka saba sakawa ne.
Tsaki tai ta shiga masu masifa tana fad’in kar su sake saka wann turare mai warin a gidan. Ma’aikatan wann ya dubi wann wancan ya dubi wancan. Da gani zaka fahimci akwai zance a bakunansu.
Mommy tai masu izinin tafiya tana fad’in su canza turaren.
Haka suka wuce suna ‘yar k’us k’us anya ba ciki ne da Safeenah ba. ‘Yar dattijuwar cikinsu tana fad’in ai da ganinta kaga mai ciki, d’ayar fad’i take da safe ta kai mata tea d’in data saba sha dik safiya Ta watsar tace is too concentrated kar Ta sake kawo mata.
Dattijuwar ta murmusa tace “Allah yasa wann rabo yasa a maida Safeenah d’akinta.”
‘Yanmatan tab’e baki sukai ba tareda sun amsa da Ameen ba dan dama haushi take basu.
Suna tsaka da zancen sai ganin Mommy sukai k’ofan kitchen d’in tana aika masu firgitaccen kallo. Gaba d’aya suka natsu suka shige taitayinsu.
Mommy ta tako cikin kitchen d’in cikeda isa da mulki tana dubansu d’add’aya “Naji duk abubuwan da kuke cewa munafukai.. Aikin da kuka iya kenan dama. Toh wllhi kunji na rantse maku idan kuka kuskura naji zancen nan ya fita kaf zan koreku na canza ma’aikata.. Ko Safeenah ce ban yarda ku sanar da ita abinda gulmanku ya raya maku ba balle wani cikin gidan nan.. Dik abinda take so ku girka ku bata bakinku alekum.. Idan kuka sake naji zancen nan wani waje kunsan sauran.!” Ta k’arashe tana mai gyad’a kanta alamun jaddada kalamanta kafin tasa kai ta fice.
**
Mu’azzam kaw suna ficewa shida Musaddiq ‘yar nasiha yaima Musaddiq d’in kan hak’uri da iyaye especially Mommy.
Musaddiq ya d’an fuzar da fuci yace “Wai baka ganin Mommy Ta tsira abubuwan da batai ba a baya ba. Batayi wad’ann abubuwan zamanin k’uruciya ba sai yanzu da girmanta muma da girmanmu.. Haba Mu’azzam wann ai rashin dacewa ne.”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Na Sani Musaddiq. But still Mommy mahaifiyarka ce.. Kar kace zaka d’aga mata murya ko zaka mata tsawa.. Iyaye ko ba musulmai bane ba’a d’aga masu murya Musaddiq.. AlQura’ani mai girmama wajaje da dama yayi umarni da cewa a kyautata ma iyaye. Wann zai tabbatar maka iyaye ba abun wasa bane.. Girman hakkinsu ya shige abinda za’ayi wasa dashi.. Musamman uwa wacce takeda girman hakki akan D’anta kaso uku kafin uba wanda yake da guda d’aya kaman yanda yazo a hadisin Annabin rahama (S.A.W).” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko nasiha zakai ma iyaye kwantar da kai ake da lallami da kwantar da murya da lallashi.. Ba’a yima iyaye ihu Musaddiq.. Sai Mommy ta d’aga maka k’afa ka shiga Aljannah.. Kaje ka bata hak’uri anjima kuma ka lallasheta.. Ni nasan ba halinta bane kawai zafin abinda naima d’iyarta Safeenah ne yasa take duk wad’ann abubuwan.. But I believe Mommy tanada zuciya mai kyau tinda ta rik’emu bisa gaskiya da amana ta kuma d’auki tsawon shekaru tana jinyar mahaifiyata. Wacce duk zatai haka akwai goodness a cikin zuciyarta.”
Musaddiq ya d’an jinjina kai kad’an yana had’e fatun bakinsa “Shikenan zanyi yanda kace.. Zan bata hak’uri..”
Mu’azzam ya murmusa yana dubansa, Sai ya tuna sab’anin da suka samu a Gidan Gona. Ya kuma murmusawa yana jin dad’in yanda al’amra suka soma daidaituwa tsakaninsa da D’an uwan nasa. Ya d’an bubbuga kafad’ar Musaddiq d’in guda kafin suka soma tafiya suka nufi b’angaren Musaddiq d’in Mu’azzam na fad’in “muje mu buga PS mana na d’an lallasa maka kad’an.”
Video game din suka d’anyi tare wanda suka jima basuyi ba, Musaddiq d’in sosai yaji dad’in samun time da D’anuwansa da yayi wanda suka kwana biyu basuyi hakan ba.
Haka Musaddiq ya lallasa wa Mu’azzam a game d’in. Mu’azzam ya aje control pad d’in yana d’ago hannayesa biyu alamun surrender.
Musaddiq ya dara kad’an yana fad’in “Haba Officer ka bada gari kenan..?”
Mu’azzam ya tab’e baki kad’an yana d’aga kafad’unsa “Ni yanzu bayan bincike I guess babu abinda na iya.” Yai maganar yana mai mik’ewa tsaye.
Musaddiq na nan rik’e da control pad d’in yana ci gaba da darawa idanunsa kan TV. Mu’azzam ya d’an matsa gefe yana duban D’anuwan nasa. Take tunanin B.A.T ya fad’o masa. D’an kauda fuska yai yana k’ok’arin kauda tunanin. Kaman ance ya dubi saman kujerar dake bayansu ya hango hular Musaddiq mai d’aukeda B.A.T ya k’arasa a hankali ya d’auki hular yana juyata.
Musaddiq dake ci gaba da buga game d’insa d’an juyowa yai yana duban Mu’azzam rik’eda hularsa ya k’ura mata idanu.
Murmushi yai yana furta “Duk wanda ya sanni ya sanni da son wann hular.. Idan baka mance ba a wani Kanti muka saya a London nida kai wani rakiya da mukayi wa Aunty Nuratu.” Tin a shagon na d’auki hular sanyin na gwada akaina.. Kuma na kasa rabuwa da ita har yanzu.. Kwanaki da ban ganta ba har na soma tunanin ko na rasata ne ashe a laundry na saka.”
Mu’azzam ya murmusa kad’an yana mai jinjina kai kafin ya aje masa hular. Lokaci guda zuciyarsa tana tuhumarsa Maiyasa zai tunanin Musaddiq nada wata alak’a da Danger bayan hula ce kawai ya gani mai kamanceceniya data Musaddiq d’in.. Company zata iya yin dubanninsa.
Aje hular yai yana fad’in bari ya shiga nasa d’akin yana zuwa.
Musaddiq ya jinjina masa kai yana mai bin bayansa da kallo.. Aje control pad d’in shima yai kafin ya k’arasa ya d’auki hular yana juyata. Cikin sauri ya nufi d’aki hular tana nan dunk’ule cikin hannunsa.
Wardrobe ya bud’e ya turata can ciki yana mai shafe fusakrsa da duka tafukan hannayensa.
D’akinsa na samartaka ya shige abubuwa cunkushe cikin zuciyarsa, ya rasa Wanne tunani zaiyi. Drawers ya soma k’ok’arin dubawa ko zaiga yanda ya aje wann coin mai kamanceceniya da wanda ya samu hannun k’anin Sadiya wanda yakeda tabbacin su Danger sunada alak’a da wann coin d’in. Sann idan haka d’in ne zasu iya zama sunada alak’a da mutuwar mahaifinsa. Toh amma tin mahaifinsa nada rai ya tab’a samun coin d’in cikin stuff d’in mahaifin nasa.. Toh kodai akwai abinda wad’ann kalaman na jikin coin d’in suke nufi ne..? Ko maybe wata K’ungiya ce da ta shafi su Danger.. Mahaifinsa was a successful business man. Watak’ila su Danger da Association d’insu sun jima suna bibiyan ahalinsa.. Watak’ila akwai dalilin da yasa suka sace Ikram..
Yai shiru hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ulesu waje guda yana tunani.
A hankali ya mik’e had’ida tura hannayensa cikin aljihu yana taka d’akin yana nazari.
Mai Maleeka take son sanar dashi.? Take zuciyarsa ta basa amsa da fad’in “So take ta sanar dakai ga makashinka.”
Ya k’ara jefo tambaya ma kansa “Wanene Makashin Maleekar.?”
Zuciyarsa ta kuma basa amsa “Ka bud’e kalaman da Maleeka ta sanar dakai a dunk’ule zaka iya fahimta.”
Ya d’an shafe hab’arsa kad’an kafin yana mai k’arasawa jikin window. Sai yaji kaman mostin mutum ya fice daga bayansa. Ya d’an waigo yana dubawa baiga kowa ba. Shafe fuskarsa ya kumayi yana jin duk tunaninsa ya k’are.
Bai samu coin d’in ba hakan yasa ya fito yai sallama da Musaddiq. Bai tsaya jiran Daddy ba ya nufi gida dan yanada abubuwan yi da yawa. Bincike ne da yake so yayi kan mutuwar Maleeka wanda baya so yai involving kowa ciki harda abokan aikinsa.
**
Ta gama jera komai saman dining table tana jiran zuwansa. Saida ta k’ara tsala wanka ta shirya cikin wata riga off neck ruwan d’aurawa wanda ta tsaya daidai cinyarta. Tayi kyau sosai kaman ka sure ka gudu. Ta k’araso kan kujera tai kwanciyarta tana bud’e shafukan zumunta dake cikin wayar nata. Facebook taje ta duba account d’in k’awarta Sabeera ko zataga ta amsa mata sak’on da ta tura mata tun kwanaki amma shiru bata amsa ba ga wayar Sabeeran sam ya daina shiga. Ta lumshe idanunta tana addu’an Allah yasa da rabon su sake had’uwa da Sabeera.
Tana nan a kwance taji k’aran bud’e masa k’ofa. Ta mik’e da sauri ta k’arasa jikin window tana lek’ensa. Murmushi saman fuskarsa take dubansa. Har ya ida rufe motar nasa waya mak’ale kunnensa na hagu.
A ranta tace sarkin waya ba, shi ko gajjiya bayayi.. Gashi a zahiri baida hayaniya baida yawan magana amma idan abinda ya shafi aiki ne tana tsammanin zai iya kwana yana waya.
Ya turo k’ofar ya shigo yana mai k’are mata kallo dan Ta masa kyau sosai. Sauri sauri yai rounding wayar nasa kafin ya bud’e mata hannaye alamun ta taho. Aiko nan ta taho a guje Ta haye cikin jikinsa. Cak ya d’agata kaman wata baby yana juyi da ita. Ya mak’aleta tsam cikin jikinsa yana fad’in tayi kyau.
Ta d’an rufe idanunta da tafukan hannayenta tana murmushi.
Hannayensa yasa ya cire nata hannayen daga saman fuskarta yana kuma tsareta da rikitattun idanunsa.
Hannayenta cikin nasa suna fuskantar juna yake fad’in “Beautiful bazaki daina rikirkita mun lissafi a gidan nan ba. Naga alama yanzu ke kike bani Assignments d’in ba ni nake baki ba.. Duka missions d’in naki ne yanzu kam.”
Ta d’anyi fari da idanu kaman zatai kuka tace “Kai Handsome, ni kuma mai nayi yanzu..? Kaga muje ka fara yin wanka sai ka sauk’o kaci abinci.” Tana maganar tana warware masa necktie d’insa. Yayinda ya kasa janye idanu daga barin dubanta. Ya d’an janyota cikin jikinsa yana kwanto da fuskarsa kusan nata yake furtawa a hankali “I think I’ll start with you first before abinci..” Ya fad’i yana kashe mata idanu guda. Kafin tai wani aune ya sureta cikin hannunsa ya nufi upstairs da ita yana nuna mata kalolin k’aunarsa. Itama dai saida ya b’ata mata nata wankan suka kuma shiryowa tare suka nufo downstairs mak’ale da juna. Haka yaita santin abincin Su duka biyu suna cike da nishad’i kaman rayuwa ta dawamma masu a haka ba tareda wani iftila’i ko tashin hankali ya ratsa tsakani ba.
Suka k’arashe yininsu suna nuna ma juna zallan k’auna. Sallah ce kawai ke fitar dashi. Kafin su kwanta bacci ma saida sukai shafa’i da wutiri tare sukai addu’o’insu suka kai koke kokensu wa Rabbil Izza wanda shine majib’icin lamuransu.
Kallo ya saka masu a laptop d’insa, yai mata matashi da k’irjinsa, ya rage wutan d’akin yabar dim-night popcorn gabansu suna kishingid’e saman gadon suna kallon wanda da gani zaka fahimci sabida ita kawai ya saka kallon ba wai dan yanada lokacin kallon ba. Babu ma film cikin computer d’in, downloading yai a Netflix kawai sabida ita, dan ya bata lokacinta a matsayinta na matarsa tinda yasan yanda yanayin aikinsa yake, shi kansa gani yake kaman lokacin na kasa masa.
Kasancewar horror film ne haka yasa duk abin tsoro da aka nuno sai ta cukukuye cikin jikinsa. Shiko da biyu ya saka horror film d’in. Dan idan taji tsoro idanunta suka firfito waje cikeda shagwab’a mugun kyau take masa. Yaita sakin murmushi yana kallonta har bacci yai awon gaba da ita nan cikin k’irjinsa.
Ya gyara mata kwanciyarta a hankali ya rufa mata bedcover d’in, ya shafa mata addu’a had’ida manna mata peck a cheek d’inta kafin ya kashe kallon.
Cak ya d’auki computer d’in ya sauk’o parlor. Dining area ya zauna yana nazarin abinda ke gabansa wato binciken mutuwar Maleeka.
Cikin laptop d’in nasa ya soma binciken abinda ke rubuce jikin coin d’in nan Wato Black African Team. Results da dama ne suka bayyana masa wanda baiga wani tak’aimammen abu guda da zaice yayi kamanni da ta’addanci ba. Hasalima results d’in akasari associations na bak’ak’en fata ya dinga nuno masa wasu na schools a k’asashen waje wasu ma a nahiyoyin Africa d’in amma bai samu tak’aimammen abinda zaice gashi ya had’a Su Danger ko nasa ahalin da wad’ann kalmomi ba.
Yai shiru yana kuma duba net. Babu abinda ya samu hakan yasa ya d’an tura computer d’in gefe yana dafe kansa kad’an.
Mik’ewa yai ya d’auko paper da pen ya dawo ya zauna yana k’ok’arin rubuta kalaman da Maleeka taso sanar dashi.
BA.. You... Ya rubuta saman takardan.
Kafin ya sauk’o k’asa kad’an ya rubuta Black African Team.
B zai iya zama yana nufin Black. A zai iya zama yana nufin Africa.. To kodai BAT taso sanar dashi..? Kodai taso tai abbreviating kalmomin ne. Sai su zamto BAT a sauk’ak’e.. Kenan BAT d’in da Ta so sanar dashi sunan k’ungyar su Danger ne? Maybe You d’in da tace taso tace “BAT.. You need to find BAT..” Maybe kenan haka Maleeka taso fad’a masa “BAT.. You need to find BAT..” Ya nanata a hankali yana bubbuga pen d’in saman takardan.
Tagumi yai kad’an yana kuma wani tunanin. What if Maleeka BAD taso ambata tinda an masa text kwanaki da sunan BAD..who could be BAD.. Take ya bama ma kansa amsa da fad’in “Barrister Ameer Dikko..” Ya kuma canza position d’in taguminsa yana fad’i a fili “What if Ba da tace Barrister Ameer take son fad’i.?” Ya kuma nanatawa kaman haka “Ba.. You need to find Barrister Ameer..” What if BA d’in da Maleeka take nufi kenan..?”
Ya d’an shafe bakinsa a hankali yana fuzar da huci. Amma makashin Maleeka k’wararre ne kuma yayi fad’a da Maleeka kafin ya samu galaban kasheta.. And Ameer is not that well trained da zaiyi fad’a da Maleeka irin haka.. Could it be Danger ne ya kashe Maleeka..?’
Ya kuma gyara zamansa yana ci gaba da tunanin yanda zai solving wann puzzle d’in. ‘Amma Maleeka tasan Danger.. Da da