Showing 195001 words to 198000 words out of 209154 words
tinda Mommy tana Abuja ne.. Ita dai Shemaun ita ake aike.
Cikin tsananin k’unan rai Shemau ke fad’in “Amma Hajara Bakida kirki.. Bakida imani.. Juya min baya zakiyi..?”
Mommy ta dara tace “Iya ruwa ke fidda kai.. Kowa ya biya allonsa sai ya wanke.”
“Ban gama dake ba Hajara. Akwai last card d’ina da zanyi amfani dashi akanki.. ‘Yarki Safeenah..!”
Mommy ta tsaya Cak tana sauraron Shemau. Yayinda Shemaun taci gaba da fad’in “Zan tona mata asiri wajen Mu’azzam cewa itace Ta bani umarni na kawo wa matarsa Sadiya kwarto.”
Katseta Mommy tai cikin k’yalk’yalewa da dariya “Amma kin tabbata shashasha Shemau. Yo a d’akin waye aka kama Kwarto. D’akin Mijinki ne ko kuwa D’akin matar Mu’azzam.?”
Shiru Shemau bata bata amsa ba sai hawaye dake k’ok’arin ciko idanunta.
Mommy ta kuma murmusawa kafin tace “Bakida wata hujja akanmu daga ni har ‘yata.. Babu wanda zai yarda dake Shemau b’ata ma kanki lokaci kawai kike..” Ta kuma murmusawa kafin tace “Sai ki tattari k’wararen da aka kawoki dasu maza a koma ruga.. Dan idan ban mance ba da k’waraye uku kawai aka kawoki, na wayar dake na gogar dake na nuna miki duniya shine bari ki min tijara har ni kike ma barazana.. Go ahead Shemau.. Kije ki fad’a ma duk wanda zaki fad’i kiga ko akwai mai yarda dake..” Daga haka D’if Mommy ta kashe wayar.
Aka bar Shemau rik’e da waya tana jinjina lamarin duniya. Wato duk tarayyar da ba’a ginata dan Allah ba da tsiya take watsewa.. Wasu irin k’walla ne na nadama Shemau taji suna ciko idanunta.. Shin dama ita rayuwar duniya haka take..? Shin dama da gaske ne hausar nan da ake cewa idan ka so wa mutane alkhairi kaima ka tsammaci alkhairi a matsayin tukwicin duniya.. Haka idan Kaso wa mutane sharri kaima sai ka tsammaci sharri a matsayin tukwicin duniya.. Bata ida tunanin nata na ta sinkayo muryar mijin Boddo daga parlor yana ci gaba da sababi “Ni gaskiya ta fice ta bar mun gida.. Ba yanda za’a yi matar nan ta k’ara kwana a gidan nan.. Wllhi kinji na rantse miki idan baki sallami bak’uwarki a gidan nan ba zan had’a harda ke na sallameku dan ni babu masauk’inta a gidana.. Matar da labari ya gama karad’e gari cewa maza take kaiwa cikin gidan mijinta.. Ke barin fad’a miki.. Daga yau.. Daga rana mai kamar ta yau na yanke alak’arki da ita.. Babu ita Babu ke kinji na fad’a miki.”
Boddo ta marairaice fuska tace “Haba Abban Huzaifa Shemau batada majingini ne dan Allah ka tausaya mata.. Wllhi akasi aka samu amma ba halinta bane biye biyen maza.. Ni zanyi wann shaidar.”
Banda uwar harara baya aikata mata komai “Wann kuma matsalarku ce can abinda naji a gari dashi zanyi amfani. Ko mutuwa kai shaidar da aka maka shi zai bika dan haka wann watsattsiyar batada masauk’i gidana.. Toh ma Wai batada iyaye ne.. Ubanta ne ni da za’a koreta Ta kwaso k’afa tazo mun gida.. Ki fice a idanuna fah Boddo..” Ya k’arashe yana nunata da yatsa.
Boddo ya sauk’e ajiyan zuciya Ta mik’e Jiki babu k’wari.
Shemau dake rakub’e d’aki tana sauraron tattaunawar mijin Boddo da Boddon sai taji wasu k’wallan na kuma ciko idanunta “Na shiga uku ni Shemau Ina zan saka kaina..!” Ta k’arashe tana d’aura hannayenta biyu aka.
A haka Boddo ta shigo ta taddata.
Shemau na hawaye take fad’in “Baddo naji komai. Kuma wllhi nasan Kinyi iya k’ok’arinki.. Na gode matuk’a K’awata... Zan tafi dan bazanso Kema na lalata miki naki auren ba.. Kaman yanda na lalata nawa..”
Boddo ta k’araso ta dafa Shemau tace “Kiyi hak’uri Shemau wllhi babu yanda na iya ne.. Tinda Abban Huzaifa yace haka nasan bazai kuma sauk’owa ba.. Amma da ace zaiyi hak’uri ya barki ki zauna a nan wllhi da bazan bari ki tafi ba.. Kiyi hak’uri k’awata.”
Rungumeta Shemau tai tana kuka tana girgiza kai “Dole na tafi Boddo dan kar Kema na jaza miki.. Abinda na shuka ne Tabbas nake girba.. Duniya makaranta ce dama.. Yau ta kuma biya mun wani karatu.. Mutanen da nayi tarayya dasu wajen aikata muggan laifuka duk sun juya mun baya.. Sun barni a rana tsaka babu rumfa babu majingini.. Ga Salman har umarni yai ma securities na Companyn su cewa ko mai kamannina suka sake gani k’ofar wajen Su koreta..” Ta saka bayan hannunta tana goge hawayenta kafin taci gaba da jinjina kai tana fad’in “Banida zab’i da ya wuce na koma ruga can wajen su Inna Fini da Baffah.. Boddo zan koma rayuwar da na baro a baya.. Rayuwar da Allah ya cireni a ciki ni kuma nayi butulci... Na butulce wa Rahamar Ubangijina... Bani da zab’i da ya wuce na fuskanci wann rayuwar a halin yanzu..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.
Tausayinta ya cika Boddo. Tabbas Shemau ta bata tausayi dukda cewa kuskure Ta riga da Ta tapka.. Tana rok’on Allah yasa wann karatu da duniya ta biya mata ya shiga kanta.. Sann masu d’abi’a irin na Shemau su hankalta su gane..
Boddo Ta k’arasa Ta d’auki ‘yar jakanta Ta ciro ‘yan kud’ad’e riban Kunun ayanta Ta bawa Shemau tace tai kud’in mota.. Harda ‘yan tufafi Ta had’awa Shemau. Shemau na hawaye Boddo na hawaye haka sukai sallama.
Rayuwa kenan. Idan Allah yayi maka baiwa da wani rahama toh ka gode masa sai ya k’ara maka da wani.. Idan ka zab’i butulce masa Toh ka sani shine mai jujjuya al’amara a lokacin da yaso.. Cikin k’ank’anin lokaci zai canza labarin rayuwarka ka koma tamkar baka tab’a jin wann dad’in ba. Ka ribaci abu uku a GIDAN ARO kafin a amsheta daga wajenka. Ka ribaci lafiya tun kafin rashin lafiya ya sameka, ka ribaci K’uruciya tun kafin tsufa ya taddaka, ka ribaci rayuwa kafin mutuwa ya taddaka.. Allah kasa mu dace duniya da lahira Ameen.!
**
Zaune suke su biyu shida Assad a parlorn laptop aje gabansu suna gudanar da bincike.
Kana ganinsa zaka fahimci gaba d’aya ma hankalinsa bayaga abinda suke. Har Sadiya tai sallama ta aje masu ruwan shayi bai kula da hakan ba.. Yadai ki gaisuwan da suke itada Assad har Assad na jefo mata ‘yan zolaya. Ita kanta Sadiyar ta kula yau d’in mijin nata ba k’alau yake ba. Ta k’agu su keb’e taji meke damunsa.
Bayan Ta koma ciki Assad ya dubesa cikeda kulawa, ya d’an gyara zamansa kafin yace “Wai har yanzu tunanin abin kake ne..?”
Mu’azzam ya furzar da huci kad’an yace “Assad it’s Safeenah we are talking about... She’s not mentally stable sann ga gudan jinina a cikinta.. Ta yaya abin bazai dameni ba..”
Assad ya d’an murmusa kad’an kafin yace “Tanada hankalinta sann Tana son D’anta, bazata yi abinda cikin zai sami wani matsala ba..Ko mahaukaci yasan abinda yake nasa Mu’azzam..”
Ya d’an girgiza kai kad’an yace “Kana magana kaman bakasan wacece Safeenah ba.”
Assa ya d’an Ka kwantar da hankalinka in sha Allah babu abinda zai sami D’anka... Toh amma ni a nawa tunanin mai zai hana ka maida Safeenah tunda gashi har rabo ya tsaga..”
D’an duban Assad yai kad’an ba tareda yace komai ba. Ya kuma d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ule waje guda “I’m still not sure idan Safeenah tanada gurbi cikin rayuwa na.. Amma abinda na sani shine D’ah na ko ‘Yata bazan bari su girma gaban wani ba ni ba matuk’a Ina raye.”
Assad ya d’anyi jim sai kuma yace “Ko wane d’ah zaiso ya girma tareda iyayensa guda biyu musamman idan dukansu suna raye.. But unfortunately wasu lokutan akan dole iyaye suke rabuwa. Kaman yanda na rabu da Hanifa.. And hakan affects the children..” Ya k’arashe murya a hankali.
Mu’azzam ya dubesa kad’an sai kuma ya jinjina kai yace “Haka rayuwa ta gada.. Unfortunately we don’t choose our Destiny.” Ya k’arashe yana kurb’an shayin da Sadiya ta aje masu.
Assad ya jinjina kai yana furta “Haka ne, Allah yasa mu dace..” Ya k’arashe yana mai janyo computer d’in lokaci guda yana danna keyboard d’in alamun yana typing.
Black African Team shine kalaman da ya rubuta ya kuma danna search. Jim kad’an results suka bayyana masa. A tsanake ya dinga bi d’aya bayan d’aya yana karantawa yayinda Mu’azzam ya b’ace duniyar tunani kaman bashi a wajen. Tinanin juna biyu da Safeenah ke d’auke dashi sam ya hanasa sukuni.. Gani yake kaman Safeenah bazata iya kula da cikin jikinta ba, dan bata kula da kanta ba balle abinda ke cikinta. Tinda yasan wacece Safeenah da kuma kalar haukarta. Muryar Assad ya sinkayo yana fad’in “Look.. Duba nan kaga.”
Mu’azzam yai saurin karkatowa yana duban abinda Assad ke nuna masa.
A tare suka soma karanta shafin da Assad d’in ya bud’e.
Black African Team wata K’ungiya ce da shekarun baya suke fataucin mutane daga nahiyoyin Africa wato k’asashen bak’ak’en fata zuwa Nahiyar turai. Tun a wad’ancan shekarun akayi nasaran murk’ushe wann K’ungiyar a port na jirgin ruwa dake can jihar Lagos. Black African Team sukan d’auki mutane daga Nahiyoyin Africa sai su yaudaresu da cewa da anje Turai za’a sama masu rayuwa mai inganci sann zasu samu Dukiya da abunyi.. Alhali kuwa ba haka bane. Idan an kwashesu daga nan zuwa Turai tamkar bayi haka ake maidasu. Za’a basu wahala wasu ma a sayar da sassan jikinsu masu amfani irinsu K’oda da sauransu. Idan akwai ‘yanmata kyawawa sai a tilasta masu yin Karuwanci na dole domin su sama ma iyayen gidansu kud’i.. A tak’aice dai Wann K’ungiyar Human Trafficking Syndicate ne Wato K’ungiyar ‘yantadda ne da suke fataucin mutane a wancan lokacin kafin ayi nasaran murk’ushesu.
A tare Assad da Mu’azzam suka dubi juna bayan sun gama karancewa.
Assad ya girgiza kai yace “Human Trafficking Syndicate ne..”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Kenan Danger nada alak’a da wann Syndicate d’in.”
Assad ya d’anyi jim yace “Zai iya yuwa.. But shekarun sunada yawa, how’s this possible..?”
Mu’azzam yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Maiyasa na samu shaidar wann Syndicate d’in cikin kayan mahaifina..?” Yai maganar fuskarsa fal damuwa kafin ya kuma duban Assad yace “Babu abinda ya had’a mahaifina da wann Syndicate d’in right Assad.?” Yanda Yai maganar dole ya baka tausayi.
Assad ya jinjina kai yace “Don’t think like that Mu’azzam.. Babu abinda ya had’a Mahaifinka da wann Syndicate d’in..”
Ya katse Assad da fad’in “Toh Maiyasa na sami shaidar k’ungiyar cikin kayansa.. And why does it seem ahalina su Danger suke bibiya.. Maiyasa zasu kashe Ikram bayan sunyi kidnapping d’inta basu nemi Ransom ba.. Assad Wai meke faruwa ne.. I’m lost Assad.. I don’t know what to think anymore.. What is all this..?” Ya k’arashe cikin tsananin damuwa.
Assad ya d’an Dafasa kad’an yace “Kar damu Mu’azzam.. Zamu samo duka amsoshinmu sannu a hankali..”
Muryar Mu’azzam ya sinkayo yana fad’in “I need to catch Danger once and for all.. Yanada tambayoyi da dama da zai amsa min.”
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*61*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Sallama sukai da Assad bayan sun sami matsayar yanda zasu b’ullowa Al’amarin.
Bayan Assad ya fice komawa yai cikin kujera yana jingina kansa tunanin wann Syndicate d’in bai k’yalesa ba wanda. Ba komai yafi tsaya masa a rai ba kaman shaidar K’ungiyar da ya samu cikin kayan mahaifinsa.. ‘What if mahaifinsa nada wata alak’a ne da wann K’ungiyar.?’ Cikin sauri ya shiga girgiza kai yana mai k’aryata zuciyarsa. Mahaifinsa bazai tab’a samun wata alak’a da wann K’ungiyar ‘Yantaddan ba. Yafi k’arfafa zaton Su Danger dai Sun jima suna bibiyan ahalinsa ne. A b’angare guda kuwa ga tinanin juna biyu da Safeenah ke d’auke dashi ya kasa barinsa.
Jiki babu wani kuzari ya mik’e ya kashe duk wani abinda ya danganci wutan lantarki dake parlorn kafin ya nufi upstairs.
Kai tsaye d’akinta ya nufa. Ya hangeta tsaye gaban dressing mirror d’aure da towel alamun fitowarta kenan daga wanka, hair dryer rik’e hannunta tana aikin busar da sumarta. Sautin k’arar dryer d’in ya hanata sauraron shigowarsa.
Yaci gaba da takowa a hankali har ya isa ya d’aura hannunsa saman dryer d’in. Ta juyo tana murmushi tana dubansa. Shid’inma kasaltacciyar murmushin ne saman fuskarsa.
Babu musu Ta sakar masa dryer d’in ya amsa cikin hannunsa, a nata zaton taimaka mata zai ya busar mata da sumar amma Sai gani tai ya kashe ya ajiye gefe. Ta baya ya rungumota yana shak’an k’amshin shower jell da shampoo da tai amfani dasu, idanunsa a lumshe yake fad’in “Why didn’t you wait for me bayan Kinsan tare muke shirin bacci.. And Meye ma na wahalan busar da suma bayan yanzu zaki sake jik’a shi..”
Ta gane mai yake nufi, tuni ta marairaice masa tana fad’in “Kai Mr Inspector yau fah akwai sanyi anyi ruwan sama fah.. Nidai sanyi nakeji..”
Ya d’an kuma shigar da ita jikinsa kad’an, fuskarsa saman wuyanta idanunsa a lumshe yake fad’in “Yeah I know.. Shiyasa nake so nai warming naki ..” Yana maganar yana rikitata da salon k’aunarsa.
K’ok’arin zillewa take kaman zata sakar masa kuka take fad’in “Nak’i wayon..” Amma sai taji ya fuzgota sun fad’a saman gado, yai mata rumfa suna duban juna. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake fad’in “It’s been a while since I heard you call me Mr Inspector.. You know a bakinki kawai nake jin sunan nan ya mun dad’i..”
Ta murmusa kad’an tana fad’in “Who would’ve ever thought That Tyrant Mr Inspector zai zama wann Prince Charming d’in da yayi rescuing Princess d’insa..” Tana maganar cikin dabaran zillewa daga jikinsa saiji tai ya mirginota Ta dawo samansa, ya saka hannayensa ya tallafi bayanta, still su duka biyun suna fuskantar juna. Saida suka kwashi d’an lokaci a haka yana dubanta cikeda kulawa, d’an Sauran ruwan dake cikin sumarta ya d’igo zuwa nasa goshin, ya lumshe idanunsa a hankali kafin ya furta “I love you.” Ya k’arashe yana mai ware idanun nasa a fuskarta.
Yanda yai maganar ya tabbatar mata tin daga zuciyarsa ya furta hakan ba wai a fatar baki bane kawai. K’wayar idanunsa da sautin fitar kalmar sun tabbatar da haka.
Ta murmusa kad’an tana share masa ruwan cikin sumarta da ya d’igo saman fuskarta da yatsarta guda “I know.. And I love you too.”
Ya kafeta da idanu sosai kafin yace
“Don’t ever leave me.!” Wann karon ma da gani kasan zuciyarsa ne ke furta hakan.
Tai masa K’uri tana dubansa kafin tace “I won’t leave you.. I’ll never leave you.. Zan rayu dakai kuma zan mutu da kai.”
Dubanta yake ba tareda yace komai ba cikin shauk’in k’aunarta, a hankali ya janyota ya had’e bakunansu waje guda.. Sunyi nisa sosai cikin wata duniya da basu gani kowa face su biyun wayar Mu’azzam dake gefensu ta soma ruri. Da k’yar ya iya mik’a hannunsa ya janyo wayar. Safeenah ce mai kira. Babu shiri ya mik’e zaune yana k’ara wayar a kunnensa.
Shafa kansa yai kad’an yace “Ina Musaddiq..? Ba kowa a gidan ne..?”
Ya d’anyi jim alamun yana sauraro daga d’aya b’angaren.
Jiki babu kuzari ya mik’e ya soma had’a botiran rigarsa still wayar manne kunnensa yana fad’in “Ya isa haka, gani nan tahowa.. Kar ki kuskura kice zakiyi driving.. Gani nan zuwa..” Ya k’arashe yana duban Sadiya data tsaresa da idanu alamun bata gane meke faruwa ba.
Peck ya manna mata a gefen kumatu yana mai matsar da bakinsa saitin kunnenta, cikin sigan rad’a ya furta “Wait for me right here kinji koh.” Yai maganar murya a dashe.
Ya mik’e yana duba agogon dake d’aure hannunsa ya nuna 10:30pm. Lokaci guda yake furta “Safeenah needs me now.. Zamuyi magana idan na dawo kinji koh.”
Bata iya amsa sa ba sai nanata abinda yace cikin zuciyarta take. Wai Safeenah ke buk’atarsa.. A cikin daren nan.? toh meke faruwa kenan.? Ji tai jikinta yayi mugun sanyi. A hankali ta kuma nitsewa cikin gadon tana janyo bargo Ta rufa akanta. Har lokacin zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Safeenah tana buk’atarsa cikin daren nan? Abinda fah ya fad’a mata kenan.. Sai nanata kalmar take cikin zuciyarta . Ta lumshe idanunta a hankali tana k’ok’arin nitsa zuciyarta. Har lokacin ta Kasa ficewa daga cikin gadon.
**
Yana isowa gidan ya tadda Safeenah ita kad’ai a parlor sai kuka take tana fad’in mararta da bayanta ciwo suke mata. Aiko tana ganin Mu’azzam ta kuma fashewa da wani irin kuka tana ciza labb’anta. Sai yarfe hannu take alamun tana jin jiki.
Ya k’araso cikin sauri ganin ita kad’aice a parlorn. Ya duk’o cikeda kulawa yana dubanta “Tun yaushe ne Bakida lafiya.. Kuma duk gidan nan a rasa mai kaiki asibiti.?”
Cikin yanayi na kuka take fad’in “Musaddiq Bai dawo gida ba.. Ba driver ko d’aya dake kwana a gidan nan yanzu. Meema kuma tun last week ta tafi sch a hostel take zama. (Meema ta samu gurbin karatu a Nile University dake birnin tarayya).
Safeenah taci gaba da kuka tana fad’in “And Mommy yanzu bata iya tuk’i musamman da dare.. Kuma Mommyn da Kiki duk sunyi bacci.. Ni kad’ai aka bari a nan, na tashi zan tafi d’aki naci marata da bayana sun rik’e ko tafiya bazan iya ba.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.
Ya d’an girgiza kansa kad’an yace “Tashi muje.. Zaki iya tashi..?”
Ta kuma fashe masa da kuka tana girgiza kai lokaci guda take furta “Bazan iya tashi ba.. Ciwo yake mun..”
D’an sunkuyowa yai yana k’ok’arin kai hannunsa jikinta, sai kuma yaji tana kuma sakin k’ara babu shiri ya tallafota yana fad’in suje.
Safeenah ta Kasa tafiya sai Sabon kukan da ta sakar masa tana kuma d’ingile k’afarta alamun bazata iya tafiya ba.
D’aukanta yai cak ya nufo downstairs da ita. Bai wata wata ba ya sakata a mota yana mata sannu ganin yanda taketa ciza baki tana dafe bayanta da cikinta.
Asibitin da Ta soma ganin Dr tai masa umarni suje.. Suna zuwa kaw Dr d’in yai attending nasu.. Ya duba Safeenah ya bata magunguna.. Mu’azzam ya tambayi ko Babyn na lafiya.. Dr yace yana lafiya amma a dinga kulawa, dama dole zata dinga jin irin wad’ann pains d’in lokaci zuwa lokaci musamman dake cikin k’arami ne ga kuma yanayin da yazo dashi na had’arin ficewa ko wani lokaci.. Abu k’ank’ani zai iya sa cikin ya salwanta.. Saidai a dinga kula.
Mu’azzam yai masa godiya yana jinjina kai ”Za’a kula in sha Allah Dr..”
Sukai masabaha had’ida sallama, Mu’azzam yai masa godiya.
Da k’yar Safeenah ta mik’e tana jan k’afarta, Mu’azzam na biye da ita dan gani yake kaman zata iya fad’uwa k’asa tsaban yanda take taka k’afarta da k’yar. A haka suka isa mota, Safeenah sai raki take tana kuma narke masa.