Showing 78001 words to 81000 words out of 209154 words

Chapter 27 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3063

yana fad’in “Yallab’ai hoto aka maku d’azu kaida Madam baku Sani ba.. Yayi kyau sosai bud’e ka gani..”

A hankali Mu’azzam yasa hannu ya amshi envelope d’in.. Lokaci guda ya soma zaro hoton kaman mai tsoron ganin hoton.. Fuskokinsu ya gani su duka biyun suna murmushi sanda yake ce mata ta nastu tayi acting d’inta da kyau idan tana son komawa gidansu..
Sunyi kyau sosai like a real couple.. Kud’in hoton ya zaro ya mik’a wa mutumin kafin ya saki tsaki a hankali ya tura hoton cikin aljihunsa.. Ya kaindubansa ga Sadiya dake zaune cikin Mota ta kifa kanta da alamun kuka take. Ya d’auke kansa yana sakin gajeren tsaki.. Lokaci guda ya shige cikin motar ya tada suka tafi.. Sam baiji dad’I ba dan babu wani abinda suka samu gameda Su Danger ko masu bibiyan Sadiya.

Suna isowa gida tai shigewarta tana matsan k’walla.

“My jacket.” Ya fad’i yana dubanta.

Babu musu ta cire ta mik’a masa abunsa kafin tai shigewarta. Shima shigewar yai nasa d’akin dan yin wanka dan duk a jik’e suke.

Yana cikin rage kayan jikinsa yaga hoton da akai masu a park.. Ya jima yana duban hoton, lokaci guda ya k’arasa dustbin zai disposing sai kuma ya tsaya kaman wanda ya tina wani abu.. Drawer ya janyo ya jefa hoton ciki kafin yai shigewarsa bathroom..

Yana fitowa daga wanka yaga kiran Assad na shigo masa.

Daga d’aya b’angaren Assad ke sanar dashi Sun sami wani clue regarding the search for Danger..

“Are you serious Assad.. Did you find his whereabout..?”

“No not really... But mun samu abinda zai iya leading namu to his hideout..” Assad yace yana juya flash drive d’in dake hannunsa. Lokaci guda yaci gaba da fad’in “I’ll tell you about the details idan muka had’u.. Yanzu dai ya kamata muyi aiki akaine.. Ina zamu had’u..?”

“Let’s meet up here at my place..” Mu’azzam yace yana k’arasa shiryawa.

Assad yace “Alright zamu taho tareda Yusuf dan d’aya location d’in shi yaje yai spying mana..”

“Alright sai Kun k’araso..” Daga haka sallama sukai kafin ya ida shiri a gurguje ya fito ya nufi masallaci dan kiraye kirayen sallar magrib ake.

Yana dawowa daga masallaci d’akinta ya nufa ya tadda Ta ida sallah kenan tana k’ok’arin linke darduman.

Bata ko dubi yanda yake ba taci gaba da abinda take.

“My friends are coming over tonight, kar ki damu ba masu kud’i bane balle kice zaki samu wani attajirin cikinsu.. ‘Yansanda ne irina masu fafutuka.. So karki kuskura ki sauk’o downstairs har sai Sun bar gidan nan...” Daga haka Sa kai yai ya juya ya fice a d’akin..

Ta girgiza kai ba tareda tace komai ba. Zama tai nan saman carpet tana tinanin abinyi.. Take taji ya kamata Ta karanta Alk’ur’ani dan zuciya da karatun alk’urani ne kawai take samun nastuwa.. A hankali cikin tsanaki ta soma rero karatun ta cikin suratu Maryam daka dan dama ta haddace suran.


Bayan su Assad da Yusuf sun iso tuni sukai connecting na’urar aikinsu a nan parlorn gidan. Mu’azzam yai masu offering coffee da tea Assad yace “Tab Inaa wannan ai sai ku turawa.. ni wllhi yunwa nakeji.. Idan zan samu something solid I’ll be glad..” Bai kai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “The kitchen is right there Sai ka shiga ka girka dan dai nikam k’asan ban iya girki ba.”

“Toh matar gidan fah.. Haba Malam Officer gidan Amarya fah muka zo.. Ni wllhi kafin a fara aikin nan sai an bani abinci idan ba haka ba bazaku tab’a gane kaina ba..”

Mu’azzam ya aika masa mugun kallo yasan da gangan Assad yai maganar nan kawai dan dai ya had’asa magana da yarinyar ne..

Car keys d’insa ya d’auka yana fad’in “Barin sayo maka a nearby eatery..”

“A’a wllhi.. No gaskiya bazanci na restaurant ba na Amarya nake so idan kuma ba rowar abincin gidanka zaka mana ba.. Ko ya kace Yusuf..?” Ya k’arashe yana duban Yusuf wanda tinda suka fara tattaunawar murmushi kurum yake yana k’ok’arin connecting computer.

Fuzar da huci yai kad’an yana aikama Assad mugun kallo “Damn you..!”Ya fad’i yana hayewa upstairs.

“Oho dai naji koma menene..” Assad yace yana darawa kad’an.


Mu’azzam na hayewa ya tadda karatu take. Ya d’an tsaya jikin k’ofa yana sauraronta. K’amshin nan nasa da taji ya tabbatar mata yana tsaye wajen. Ta dasa aya ma k’aratun nata kafin ta juyo a hankali. Cikin zuciyarta tai tsaki tace mutum kaman goyon maguzawa Sai ya ringa shiga waje babu sallama.

“Abokaina suna jin yunwa.. I told them ba’a dafa abinci a gidan nan amma sunk’i amincewa.. Can you cook something simple for them..?”

Jin bata amsasa ba ya sanyasa fad’in “Nasan kin San matsayin girman miji a wajen matarsa. So idan har kinada karatun addini kaman dai yanda naji kina karatun nan zakiyi abinda mijinki ya umarceki.. Idan kuma Bakiyi ba Kinsan mai hakan yake nufi.. And please do not embarrass me.”

Daga haka ficewa yai ya barta nan zaune ba tareda ta tankasa ba. Watau yanzu kuma da Ubangijinta zai had’ata bayan ya gama mata barazana da mission. Taji wasu k’walla masu zafi suna zuwa mata... Tasha jin ana cewa ko Wanne gidan Aure da nasa k’alubalen wata nata dangin miji ne wata uwar miji ne nata k’alubalen wata kuwa shi mijin kansa ne k’alubalen kaman dai yanda nata ya kasance dikda kuwa Auren nata ba mai d’aurewa bane. Tina cewa da tai koda auren na d’an lokaci ne shid’in mijinta ne kuma umarni yake bata ya sanyata mik’ewa ba dan taso ba. Ta nufo wardrobe d’in tana duba mai zata rufa akanta.. Wani shud’in mayafi ta d’auko yalwatacce ta rufa akanta kafin ta nufo k’asa ta shige kitchen d’in.. Tana jin hayaniyar su shida abokan nasa har tana mamaki ashe dama ana jin muryar sa haka.. Wata zuciya tace ai indai bincike yake kam tsaf zakiji muryarsa.. Ta tab’e baki kad’an kafin Ta nufi kitchen d’in.

Store ta soma dubawa taga store d’in shak’e da kayan abinci. Ga dangin su pasta da couscous.. Tai tinanin dafa masu abinci mai sauk’i kaman yanda yace. Couscous d’in ta d’auko ta dawo kitchen d’in ta bud’e fridge ta duba groceries nan taga gasu veggies sealed cikin leda irin yanda ake saidawa a super markets harda minced meat dasu sausage dik Suma sealed... Minced meat d’in ta d’auko kafin ta dafa white couscous tai garnishing d’insa da veggies sannan tai soma had’a masu sauce d’in minced meat d’in wanda za’aci white couscous d’in dashi..


Suna zaune parlor suna aikinsu k’amshi ke dakan k’ofofin hancinsu. Assad yace “Kai wannan k’amshi ai sai ya cika mana ciki kafin muci.. Gaskiya da alama Amarya ta iya girki..”

Gajeren tsaki Mu’azzam yai ya kuma duban Yusuf dake k’ok’arin saka flash jikin computer yace “Ina sauraranka Yusuf go ahead.”

Yusuf yaci gaba da fad’in “Kaman yanda na fad’a maku shi wannan footage d’in wajen security d’in da suke kula da restaurant d’in na samu bayan na shafe kwana biyu ina bincike ina tambaya people around the area ko sun tab’a ganin mai kama da Danger wajen.. Toh shine na samu har mutum uku suka ce Sun tab’a ganinsa sau kusan uku yana zuwa wannan restaurant d’in yana sayan abinci.. Da alama Danger yana son abincin wannan restaurant d’in.. Toh sai na tambayi CCTV Footage daga wajen securities bayan na sanar dasu matsayina da binciken da nake.. Bari mu gani gaba d’aya mu tabbatar..”

Suka jinjina kai a tare sanda Yusuf ya soma playin videos d’in har kashi Uku wanda yake tabbatar da cewa Danger ne yake zuwa Restaurant d’in sayan abinci dikda yana saka rigar sanyi mai hood dan kar a ganesa.

Sanda akazo daidai fuskar mutumin Mu’azzam yace “Stop. Yi zooming muga.” Yusuf yai kaman yanda yace d’in.

Jinjina kai yai yace “It’s him.. Danger ne.. So Ta tabbata yana zuwa wannan restaurant d’in tinda har yaje sau uku..”

Yusuf ya jinjina kai kafin Assad y ciro wani flash drive d’in yace “Wannan kuma wani super market ne da aka ga wani mai kama dashi once.. But nima I’m not sure idan shi d’in ne domin wannan kaman yafi Danger girman jiki saidai kuma idan camera ce ta k’ara masa girman jikin.. Footage d’in na k’ofar super market d’in ne wanda fuskarsa ta d’an fito amma is not that clear..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Saka mu gani..”

Lokaci guda Assad ya saka ya soma playing..

“Wait.” Mu’azzam ya dakatar dashi yace masa yai zooming.. Lokaci guda ya k’ura ma lambar motar da mutumin zai shiga idanu a nan k’ofar super market d’in..Lambar motar tayi daidai da motar da aka basu bayanan cewa itace motar data buge Baban Sadiya.

Mu’azzam ya shiga jinjina kai yana fad’in “That Scumbag.! Shi ne.. Shine ya kad’e Babanta.. Danger ne ya kad’e mahaifin Sadiya..!”

Ya shafa sumarsa a hankali yana jin zuciyarsa na masa zogi.. Cikin sauri Yusuf ya shiga d’aukan plate number d’in motar dan suyi comparing da wancan...

Assad yace “Yanzu ya tabbata Danger yana nan cikin garin nan yana hunting dik wani wanda yakeda alak’a da case d’in nan.. By all means yake so ya rufe bakin kowa.”

Ya dubi Mu’azzam yace “Surely Danger will come after your wife..!”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “I’ll kill him if he attacks her..” Yai maganar yana murza hannunsa a hankali.

“What’s plan now.?” Assad ya tambaya yana duban Mu’azzam d’in.

Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya soma fad’in “Yanzu dole mu rabu muje wuraren da muke tsammanin Danger na zuwa. Kunga ni bazai yuwu na tafi aiki under NPF ba since I’m still on my suspension.. Naji ASUU sunyi calling off warning strike d’in da suka tafi.. So Sadiya zataje makaranta gobe.. Ni zan kaita dan nasan Maybe Danger yai tinanin attacking nata idan ta fita makaranta.. Kai kuma Assad kaje wannan Super market d’in.. Kai kuma Yusuf ka tafi wannan location d’in.. Restaurant d’in sai muga ina danger zai fara zuwa.. We should all stay alerted wanda dik ya soma ganin Danger cikinmu Sai muyi alerting juna mu nemi backup..”

Gaba d’aya suka jinjina masa kai suna fad’in “Yes sir..!”

Daidai nan Sadiya ta fito daga kitchen rik’eda plates ta nufi dining table.. Tin daga nesa Assad ke zolayarta ta cika masu ciki da k’amshi.


Mu’azzam sai satan kallanta yake cikin zuciyarsa yana addu’an Allah yasa kar Ta basa kunya.

Saidai ganinta da yai sanye da tufafin da ya zuba mata a wardrobe yasa hankalinsa d’an kwanciya. K’ila bazata basa kunya ba.

Daga can yanda take tsaye ta d’an duk’a ta gaidasu Assad gajeren murmushi saman fuskarta jin yanda Assad ke Zolayarta ta cika masu ciki da k’amshi had’ida yi mata godiya.

Ko duban yanda Mu’azzam ke zaune bataiba tai juyawarta kitchen ta kawo masu sauran abincin. Harda pineapple drink Ta had’a masu.. Sai dubanta yake cikeda mamaki. Ita kaw yi tai kaman batasan yana parlorn ba, tana gama jera komai tai hayewarta sama. Yabi bayanta da kallo har Ta b’ace ma ganinsa..


Muryar Assad da tuni ya nufi dining area ya soma bud’e warmers d’in shi ya dawo da hankalin Mu’azzam.

Assad yai ma Yusuf tai baibi takan Mu’azzam ba. Suka soma cin abincin yayinda Mu’azzam ke ci gaba da duba footage d’in dikda kuwa sosai k’amshin ya cika masa ciki.





SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*





*27*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*







Haka su Assad sukaita santin abinci Mu’azzam bai tankasu ba. Sanda zasu tafi Assad harda cewa a kirawo Amarya suyi mata godiya.

Mu’azzam ya aika masa mugun kallo yace “Congratulations for ruining my evening Detective Assad.!”

Assad ya dara kad’an yace “Wait baka bani labari ba.. How did your mission go Inspector..? Ko da yake bari dai nai shiru, maybe everything is classified for now, but we’re not in a hurry. In due time zamu San komai..” Ya d’an kashe masa ido guda yana fad’i a hankali “Bari dai muga yaushe za’ayi accomplishing mission d’in.”

Fuzar da huci kad’an Mu’azzam yai kafin yace “Get out before I blow your brains out.”

Darawa ya kumayi kafin yace “Sai mun had’u goben.. At the meeting place.” Daga haka sallama sukai kafin Assad ya fito ya tadda Yusuf dake jiransa.

Mu’azzam kaw yana dawowa cikin gidan tsayuwa yai a dining area yana duban saman table d’in lokaci guda yana tunanin maganganun Assad..

Gajeren tsaki yai yana shafa sumarsa a hankali.. Lokaci guda idanunsa suka kan clean plate da spoon d’in dake aje wajen. Wato harda plate d’insa ta kawo da cup.. Kenan harda shi tai serving abincin. Gajeren tsaki yai kafin yasa kai zai shige.. Sai kuma ya dawo da baya kaman wanda ya tina wani abu..A hankali ya shiga bud’e warmers d’in yana d’an tab’e baki kad’an.. A ido abincin wasn’t that bad. Ya jinjina kai a hankali kafin ya janyo kujera d’aya ya zauna.. Lokaci guda ya soma serving kansa abincin.. Ya zuba kad’an saman plate kafin ya janyo jug d’in ya zuba drink.. A hankali ya soma sipping drink d’in kaman mai tsoron kar yaji taste maras dad’i.. Saidai drink d’in na shiga bakinsa yaji wani irin taste mai dad’i ya gauraye cikin bakin nasa har yana lumshe ido.. Saida ya kusan shanye glass d’in kafin ya aje ya janyo plate d’in ya soma cin abincin. A hankali yake jinjina kai cikin zuciyarsa yana fad’in not bad.
Wasa wasa saida ya cinye abincin tas, ya lumshe idanunsa yana tinanin yaushe rabon da ya k’oshi haka. Daga nan kitchen d’in ya nufa dan yaga wasu abubuwan girki ya kamata ya k’aro since she can cook like this. Ya shiga store yana dubawa.

Sadiya kaw sam batasan yana kitchen d’in ba, Ita a nata tunanin ma ya fice tareda abokansa. Ta d’an lek’a parlorn kafin ta tab’e baki ta nufo dining table d’in tana tattare plates d’in da suka ci abincin..
Sam batasan Mu’azzam na cikin store d’in ba Ta aje plates kenan aka d’auke wuta a daidai lokacin shi kuma ya fito daga store.. Lalume ta soma tana neman hanya tana fad’in “Oh no I’m scared of the dark..!” saidai kaman daga sama taji ta fad’a jikin mutum..

A razane ta bud’e murya tana sakin razannan k’ara.. Ya janyota sosai cikin jikinsa tana kiciniyar k’wacewa lokaci guda ya rufe bakinta da hannunsa guda.

“You scream over every little thing..!” Ya fad’i cikin sigan rad’a..Cizo ta gantsara masa a tafin hannunsa wanda ya sanyasa sakin bakin nata babu shiri..

“Malam ka sakeni na tafi..”

Bai saketa ba Sai yarfe hannunsa data ciza yake.
Daidai nan aka kawo wuta, hasken wutan lantarki dake kitchen d’in ya haske fuskokinsu.

Fuskar nan tasa a tsime yana duban nata fuskar Wanda itama babu wani walwala saima sakin huci da take.

Ya d’ago hannusa data ciza wanda har ya d’anyi ja yana nuna mata “Baki ciza banza zan rama kuma nasan a ina zan rama..” Ya k’arashe yana tallafota sosai.. Ta shiga turasa tana fad’in “What are you doing..? Just let me go.. Let go..” Batakai aya ba taji ya rufe bakinsa da nata.
Ta zaro idanu k’irjinta na wani irin bugawa.. Jikinta ya d’auki rawa ganin bak’on al’amarin dake faruwa da ita.. Ta soma kiciniyar k’watan kanta amma ta kasa.. Batasan sanda hawaye suka soma gangarowa daga idanunta ba.. Saida ya tabbata ya razanata sosai kafin ya cire bakinsa daga nata..
Saitin kunnenta yake rad’a mata “W’ll continue with our mission tomorrow, ki shirya da wuri Kinsan ban son jira..” Daga haka ficewa yai ya barta nan tsaye tana goge bakinta da duka hannayenta biyu kaman wacce zata cire bakin nata.

A guje ta nufi washing base ta bud’e famfo tana wanke bakinta still hawaye bai daina zuba mata ba.. A fili take furta “Allah ya isa mun mugu kawai..” Can k’arshen kitchen d’in Ta k’arasa ta durk’usa ta tak’ure waje guda hawaye na kuma gangaro mata.

Yana haurawa sama tsaki ya dingayi yana tinanin irin maganganun da ake fad’I akanta, Allah kad’ai yasan yawan mazan da tai mu’amala dasu dan Ta sami kud’i da abin duniya.. Kai tsaye bathroom ya shige ya soma brushing bakinsa kaman zai cire bakin yanajin zuciyarsa na masa k’una.
**

Koda Daddy ya koma gida babu yanda Mommy batai ba ya sanar da ita yanda sukaje shida Mu’azzam amma yak’i sanar da ita, abin sosai yake damunta.. Uwa uba rashin kwanan Mu’azzam a gidan, tana tsaka da tinanin Aunty Shemau Ta kirata. Taji yanayin Mommyn cikin damuwa nan Mommy take sanar da Ita abinda ke faruwa.

Shamau tace “Nifa zaman Safeenah a nan ma duk bata taso ba, gashi nan Inne ta saka anata gyara section d’in dake gefenmu tana cewa a nan Fufore zasu tare.. Aunty Hajara idan har muka bari Mu’azzam ya zauna kusa da uwarsa akwai damuwa.. Ya kamata Safeenah Ta dawo gida Ta tare gidanta.”

Mommy tace “Haka ne.. Nima nayi wannan tunanin.. Ni abinda nace ma kawai su Safeenah su tattara su dawo idan yaso sai ace wa Inne likitan gyaran K’ashi Safeenah zata gani a nan Abuja kuma visiting Dr ne daga k’asar waje ba ko yaushe ake samunsa ba.. Kinga idan so samu ne ma gobe gobe Ta dawo kawai ta tattara ta koma Gidanta.. Ni wllhi gantalin da take da aure bata tare ba ya soma damuna.. Ita ba matar aure ba ita ba bazawara ba.. Ni wasu lokutan Sai inke ganin anya ba abinda naima Nuratu bane yake bibiyata ta hanyar d’iyata Safeenah..?” Ta k’arashe cikeda tsoro.

Aunty Shemau tace “Haba Aunty Hajara, ki daina damun kanki.. Karma ki saka wannan tinanin a ranki, Safeenah zata tare gidanta tsaf. Abinda kikace d’in kawai shi za’ayi.. Yanzu zan samu Uncle Salman da maganar, shi Sai ya samu jarabebbiyar uwarsu ya sanar da ita.. Gobe idan Allah ya kaimu sai muyi fitowar sassafe idan yaso Muasaddiq sai yai driving bama sai an tsaya ana jiran wani driver ba.. Sassafe zamu fito dik tsiya dai zuwa yamma mun iso.. Ni zan taho da dik wani kayan buk’ata na gyaran Amarya saidai kawai a shirya Safeenah a kaita d’akinta idan yaso tai jinyar nata a can..”

Mommy Ta nusa tace “Shikenan ma kuwa.. Kai Shamau ni wllhi kin gama min komai.. Ko ciki guda muka fito iyakaci..”

Aunty Shemau tace “Haba Aunty Hajara ai yima kaine.. Ki daina wani min godiya.. Kawai ki zuba idanu ki jira isowarmu gobe in sha Allah..”

“Toh shikenan Shemau. Allah ya kaimu goben.”

Shemau ta amsa da Ameen kafin sukai sallama. Daga nan ta shiga ta tadda Safeenah da Meema da batun. Meema kam hakan yafi mata dan dama ta gaji gida take san komawa. Safeenah ce dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login