Showing 162001 words to 165000 words out of 209154 words

Chapter 55 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3061

ba, Assad d’in yasan bazai saurari hakan tinda yace zai dawo zai dawo d’in..

Zama Assad yai yana mai fad’awa cikin kujera k’irjinsa na masa nauyi. Ya dafe kansa yana fad’in “What have you done Assad..?” Lumshe idanunsa ya kuma yi kansa na masa wani irin nauyi.

A hankali ya jinjina kai yana furta “Our job however, required us to put our minds over our fears. I must do this.. I have to do this..!”
**

Misalin k’arfe 9:00pm suna zaune parlor, kanta saman cinyarsa tayi matashi da cinyar nasa hannunsa saman sumarta yana shafawa a hankali yayinda Sadiyar ke ci gaba da labarta masa barkwancin Ajidde da yanda take jin dad’in labarunta. Nan dai taga kaman hankalinsa baya wajen.

Ta d’an mirgino tana dubansa “Are you alright..?” Ta tambaya tana dubansa.

Ya saki miskilin murmushi a hankali yana mai jan hancinta kad’an da yatsun hannunsa “Why wouldn’t I bayan kina taredani.. Ga kuma Mamy na a nan ga Inne.. Mataye guda uku da sukeda matuk’ar mahimmanci a rayuwata..”

Ta murmusa kad’an jikinta na kuma yin sanyi jin bai ambato Safeenah ba, ko maganarta bai tab’a yi ba tinda sukazo garin.

Ta d’an gyara kwanciyarta sosai tana kuma dubansa “Safeenah fah..? Dan Allah bazakayi hak’uri haka nan ka maidata ba.. Kaga fah babu abinda ya faru babu wanda ta harba.. Dan Allah ka mata afuwa haka nan..”

K’uri yai mata yana dubanta, sai kuma ya d’auke kansa kad’an “Kar ki sake mun zancen Safeenah..!” Abinda ya fad’i kawai kenan cikin tsananin tsimewa wanda har saida ya koma mata tamkar Mu’azzam d’in da ta soma sani.

Jikinta ya d’anyi sanyi, ta maida kanta Ta kwantar, sai kuma ta dubesa kad’an ganin yanda ransa ya b’aci sosai. A hankali ta furta “Kai hak’uri bazan sake ba.”

Bai ce mata komai ba Sai k’urama waje guda idanu da yai, al’amarin Musaddiq da Assad na kuma Yawo a kwanyarsa. Tun bayan data masa maganar Safeenah ta lura walwalarsa ya d’auke.. A nata zaton kan maganar Safeenah da tai ne ya maidasa haka saidai batasan cewa abubuwa ne da dama k’unshe cikin zuciyar mijin nata ba. Har wajajen k’arfe 11pm bai shigo ya kwanta ba, tana nan kwance k’walla tab idanunta tana tinanin kodai fushi ne yayi da ita..? Maiyasa bai shigo ba..? Can taji shigowarsa yana waya wanda takeda tabbacin da mutanesa na wajen aiki ne.

“Alright Yusuf.. Eh gobe in sha Allah ina nan tafe.. Thanks for the update, Sai munyi magana..” Daga haka katse kiran yai ya k’araso saman gadon ya zauna yana kuma shafa wayar tasa.

Sadiya tana jin haka ta rintse idanunta a hankali hawaye na gangaro mata, kar dai tafiya zaiyi.? Kardai fushin da yai da ita har ya kai wann matakin kan kawai Ta masa maganar Safeenah.. Kukan da take ta k’ok’arin dannewa ya soma fin k’arfinta.

Ya daina abinda yake ya karkato kad’an yana dubanta. A hankali ya migrino kusanta nan saman gadon. Tana jin alamun k’arasowarsa kukanta ya k’aru.

Bai furta komai ba Sai janyota dai cikin jikinsa, kaman wanda yace ta k’ara. Tana nan cikin jikinsa bai hanata kukan ba har dai kukan nata ya soma lafawa a hankali.

Ya d’an d’ago fuskarta yana duba had’ida saka tafin hannunsa guda yana share mata hawayen “Tell me.. What happened why are you crying..?” Ya tambaya yana share mata hawayen.

Ta d’an dubesa sai kuma ta girgiza masa kai.

Ya gyara zamansa cikin gadon yana mai mata matashi da b’angaren jikinsa. Ya kamo yatsun hannunta guda yana murzasu cikin tafin hannunsa a hankali.

“Tafiya zakayi ka barni..?” Ta tambaya cikeda rauni.

Ya d’aura hannunsa guda saman sumarta yana shafasu a hankali “Kan wann kike kuka kike mu nasaran hawayenki masu tsada..? Kiyi hak’uri tafiyar ne ta taso min babu shiri. Naso na zauna mu k’arashi hutun mu tare but babu yanda na iya akwai ayyuka da suka taso mun.. And akwai wasu adjustments da nakeson yi kafin ki koma.. As soon as everything is done zan turo a d’aukeki..”

Ta d’an dubesa kafin ta jinjina kai a hankali “Bakayi fushi dani ba..?”

Murmusawa yai yana dubanta kafin ya d’an ja hancinta kad’an Sai ya kuma janyota jikinsa yana fad’in “Come here.” Ya mak’aleta cikin jikinsa ya matseta sosai yana shak’an k’amshinta. Idanunsa a lumshe yake fad’in “I’ll miss you Beautiful..”

Tai kwance cikin jikinsa yana narkar da ita da kalolin k’aunarsa. Jin zancen ya soma canzawa ne ya sanyata saki masa kuka. Cikeda tsoron yanda tasha wahala first time.
Kansa na nan saman k’irjinta, idanunsa a lumshe yake furta “It’s almost a week fah.. Nayi k’ok’ari ai.. Please ki barni muyi sallama..”

Kuka ta kuma fashe masa dashi tana fad’in ita dai tsoro take.

“Babu abinda zai faru I promise..” Ya fad’i yana kuma rikitata.

Ta d’an turasa kad’an cikin dabara tace “Nifa bana sallah ma ashe.” Tai maganar duk a tsorace.

Ya d’ago yana dubanta da mamaki kafin ya murmusa yace “Haba yarinya ma wa zakiyi wann wayon.. Ance miki bansan date d’inki bane..”

Ta d’an waro idanu tace “Yaushe ka sani..?”

Ya murmusa yana mai kuma janyota jikinsa “The very first time dana soma had’uwa dake.. A ranan kika sanar dani date d’inki..” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda.

Ta murmusa tana rufe fuskarta da tafukan hannunta, sai kuma ta d’an Ware idanun ta narkar da murya kad’an tace “Kai Inspector ni dai gaskiya bansan yaushe akai hakan ba..”

Ya d’an janyota yana fad’in “Kin mance da mai kika jifeni first had’uwarmu..”

Sai lokacin take recalling abubuwan da suka faru. Ta zaro idanu cikeda kunya sai kuma ta kifa kanta saman cinyarsa cikeda kunya tana fad’in “Na shiga uku Wai dama a kai nai jifan nan.. Innalillahi..!” Ta kuma danne kanta cikeda kunya tana maganar tamkar zata sakar masa kuka. Shiko sai k’ok’arin d’agota yake yana murmusawa.
Sai wann lokacin take tuna abi.da Safeenah tai mata data tura mata sanitary napkin a baki tace sai ta cinye,. Weto ashe Inspector ta jifa dashi ya tafi gida da abin har Safeenah watak’ila Ta gani..Kunya y` kuma daaibayeta.

“Dama asan bakisan Kinyi haka ba. But ni tun a lokacin na rik’e date d’in nasan bazaki shige wann range d’in ba.. So }ou don’t have any excuse idan kuma ba rowa zaki min ba.>”

Ta marairaice fuska kaman zata saki kuka “Nydai tsoro nakeji..”

Shima marairaice mata fuskar yai yace “Matar Inspector bata tsoron mission.. I promise yoT baxai kai wancan ba.. Trust me..” Ya c’arashe cikin nuna mata salon k’aunarsa.

Iya juriya da dauriyakam tayi shi, saidai keman yanda yace d’in bai Kai keron farko ba saiea k’ok’arin maida masa Martanin k’aunar lasa gareta da take. Albarka ya dinga saka mata ya mat{eta tsam cikin jikinsa yana0fal’in irin kewarta da zaiyi. Komai tare sukai itada Inspector d’in nata.. Kama daga wanka zuwa shiryawa dukda cewa da k’yar ta bari hakan ta kasance 3abida kunya. Zallan k’auna mai tsafta had’ida tsayawa a rai yake nuna mava. Pabbas sunyi sallama mai tsayawa a rai da zai sakasu kewar juna matuk’a.

Kafin Mu’azzam xa tafi sida ya bar mata amana kanta da kuma Mamynsa. Sann ya sake dank’awa Inne amanar Sadiyar tasa. Kuka da shagwab’a kaw haka ta dinga narka$masa da k’yar ya samu sukai sallama da k’udirin zata riyosa nan bada jimawa ba cikin yardar Ubangiji. Dan ra don aikin dake gabansa ba da k’afarsa k’afarta bazai tafi ya barta ba Amma babu yanda ya iya abubuwa suna nemaO fiva out of hand tinda ya taho.

Mu∙azzam ya tafi ya barta da tarin kewa.

**
Tinda Shemau ta sanar daSafeenah dawowar Mu’ezzam d’in ta k’udiri niyyan$komawa gidanta, {ann wancan ‘yariskar Wato Sadiya kenan ta fiva da fitar ta kaman yanda Aunty Nuratu ta fice daga gilan mahaifinta. Koda wasa bajati bari ‘yariskar can ta dawo mata cikin gida ba dan dama ta k’udiri alwashin gidanta tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta sai ta fice ta bar mata gida.

Da wann tinanin Safeenah ta shirya tsaf ta nufi gidan. Saidai tana isa ta tadda kayan tashin hankali domin kaw kaf kayan gidan Mu’azzam yasa anata fito dasu, daga gani ma’aikatan company ne masu aikin interior design. Sai zuba sabbin furniture ake ana sealing nata cikin manyan cartons ana shiryasu a cikin wata k’atuwar mota. K’irjin Safeenah yai wani irin tsinkewa.

A fujajan Ta nufi cikin gidan tana tambayan mutanen wanda ko kallo bata ishesu ba.

“Ina zaku kai mun kaya..? This is my house.. Who ordered you to do this..? Kai magana nake maku..!”

Bata kai aya ba taji sauk’an k’aton abu kusan k’afarta.

Tai tsaye tana duban hoton aurensu da ya fad’o kusan k’afarta wanda ko shakka babu jefosa akai.

Da mamaki ta d’ago tana duban Mu’azzam dake tsaye yana dubanta. Ta duk’a a hankali tana Shafa hoton auren nasu hawaye na gangaro mata.

Lokaci guda ta mik’e tana girgiza kai tana hawaye. Ta isa wajen Mu’azzam a guje tana kamosa “My Halal.. Zaka canza mana tsarin gidan ne.. Please kar ka cire hotonmu ko sabon hoto kake so muyi a manna.” Tana maganar tana murmushi hawaye na zubo mata.

“Safeenah, I’m not changing anything for you.. it’s over between us.. Kin fahimta..”

Kuka ta fashe dashi gadan gadan tana girgiza kai tana hawaye “No it’s not over.. You are mine Mu’azzam..! You are my Halal bazan tab’a k’yaleka ba.. Kai nawa ne ni kad’ai.. My Halal please don’t leave me kaji. Wllhi ina maka son da banayi ma kaina..” Ta k’arashe tana kamo arms d’insa had’ida jijjigasa.

“Enough Safeenah..!” Ya fad’i yana cire hannayenta daga jikinsa, yaci gaba da furta “This is not love Safeenah.. You don’t love me, you are just obsessed with me.. And.. And this is just a crazy feeling not love.. If you can point a gun at me mai kike tunani Safeenah.. zaki kira wann abun love.. Ba love bane it’s just an obsession.. Please Safeenah you need to accept this.. Kafin Azo ana danasani gwara ya tsaya a nan.. You are like a sister to me and I don’t want to hurt your feelings.. I don’t love you as a woman please..” Ya k’arashe cikin sigan kwantar da hankali.

Zabura tai tana mai kuma fashewa da kuka ta ciccib’i hoton nasu tana k’ok’arin maidasa Majinginansa “You are just lying.. I know you love me kawai wancan ‘yar iska karuwarce Ta karkatar maka da tunani.. Tambad’add’iya wacce ta gama watsewa a layi.. Ba dole ka mance kanka ba taje tana maka abubuwan da karuwai matan layi keyi Wanda ni bana maka irinsu koh..!”

Fincikar hoton yai ya kuma jifa dashi. Yana nunata da ‘yar yatsa cikin sakin huci “Don’t make me lose my mind Safeenah..! Kar ki sake kiran matata Karuwa.. Sabida matata sabuwa ce, first grade ce, fresh ce.. Sann ni ne mutum na farko da ya mallaki darajarta.. Idan akwai wacce za’a kira tambad’add’iya a nan wacce ta gama watsewarta a club da parties ba kowa bace face ke, kin zaci na yarda da labarin da kika bani ne cewa an miki fyad’e wajen party..?” Ya girgiza kai kafin yaci gaba da fad’in “I didn’t believe you one bit Safeenah.. Kar ki mance I’m a Detective na sani if someone is not telling the truth.. Na miki uziri ne na kauda kai sabida girman zumunci.. Amma kinata pushing d’ina, kinata yin wasu abubuwa baya albarka kike ci.. Zaman bazai yuwu ba Safeenah ya riga ya k’are.. Sann da Mommy take cewa kar na shafa miki cuta.. Ni ya kamata na guje ki dan kar ki Shafa min cutan da kike d’ebo wajen yawon parties da samaruka..!” Ya k’arashe idanunsa tar a kanta yayinda Safeenar tai tsaye tamkar wacce ruwa ya shanye tana zuban hawaye.

“Zo ki fice mun a gida..!” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa.

Cikin tsananin sanyin jiki ta nufo k’ofar tamkar wacce ruwa ya shanye.

Saida ta kai k’ofa ya dakatar da ita. Hoton ya jifa mata bayan ya yage b’angaren nasa fuskar yace “You forgot this..”

Safeenah na hawaye Ta dubi hoton sai kuma ta d’aga ido ta hangi ma’aikatan daga can sun ciro wani sabon hoto cikin frame suna k’ok’arin mannawa a wajen. Kuka bai kuma zuwa mata ba saida ta hangi hoton Mu’azzam d’inta da wancan tsinanniyar ce da suka d’auka a park irin Wanda Ta k’eta kwanakin baya shine aka lik’a a wajen anyi enlargement an saka cikin k’atoton frame kaman ka kirasu su Zo.

A guje Ta fice daga gidan tana cazgan wane irin kuka tanaji kaman harda zuciyarta ne zai fito waje dan k’unci.. Banda tsanar Sadiya babu abinda ke ruruwa cikin zuciyarta. Bata da burin da ya wuce Sadiya Ta b’ace b’at daga rayuwarsu itada Halal d’inta. Ta shirya yin komai domin ta cire Sadiya daga cikin rayuwarsu. Ko menene kuwa matuk’a Sadiya zata zamto tarihi a garesu.

**
Washe gari yake shirin shiga Office, saida ya kirata suka sha firan soyayyarsu kafin ya nufi office d’in. Tin daga nesa Maleeka ta tsaresa da idanu tamkar Zata lashesa. D’an kwana biyu da yai baya nan sai taga ya k’ara mata gizo da wani kyau na musamman. K’warjininsa ya kuma bayyana, ya sake zama wani cikakken namiji mai cikeda Charisma. Wutan k’aunarsa Sai ya kuma ruruwa cikin zuciyarta. Hardai zata dinga ganin Inspector Gamji Tabbas k’aunarsa bazai ragu cikin zuciyarta ba. Take kuma zuciyarta yai wani irin yankewa tana tinanin kar ya tambayeta progress kan Assignment d’in da ya bata.

Tana jin sanda suke gaisawa da Yusuf, Yusuf na basa wasu updates d’in. Ta kifa kanta a k’asa zuciyarta naci gaba da tsinkewa.

Bak’ak’en covers d’insa ne idanunta suka sauk’a bisa alamun ya k’araso gabanta.

Ta d’ago da k’yar ta dubesa. Sai kuma ta sara masa tace “Sir, welcome back.!”

Ya tsareta da idanu ba tareda yace komai ba alamun yana examining nata. Zufa ne kurum ke karyo wa Maleeka dan gani take Inspector Gamji ya ganeta an gama.

“Have you found the mole..?” Ya tambaya a d’an tsare.

Zuciyar Maleeka ya kuma tsinkewa. Ta kasa furta koda kalma.

Ya kafeta da idanunsa masu rikitata had’ida bata tsoro. Cikin k’ok’arin had’o kalamai take furta “I.. I.. I’m still working on it.. Sir..”

“You know the mole.. Juts admit it..!” Ya fad’i cikin dakewa tareda k’ok’arin tsoratar da ita dan ya fito da gaskiya daga bakinta.

Ta shiga girgiza kai tana fad’in “Sir.. Sir I.. I swear I don’t know what you are talking about.!”

“You are their accomplice. You are the traitor here in our team.. You are the one betraying the CID...You are working with those criminals.. You are the one giving them information.. Just admit it now..!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa yana dunk’ule hannayensa tamkar zai damk’ota. Irin yanda sukeyi idan suna son tilasta mutum yai magana.

Maleeka Ta fashe da kuka tana girgiza kai. Jikinta na tsananin rawa sabida tsoro da tashin hankali.

Daidai lokacin Assad ya turo k’ofa ya shigo.

“Mu’azzam we need to talk now. There is something you need to know..!” Assad ya fad’I daga nan yanda yake tsaye.

Mu’azzam ya d’ago yana duban Assad d’in da yanayinsa.



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*



*51*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Cak Mu’azzam ya mik’e yana duban Assad dake shigowa cikin room d’in. Ya tsaresa da idanu sosai yana jiran yaji abinda zaice. Suma Maleeka da Yusuf kallo suka bisa dashi suna jiran jin meke tafe dashi babu kaman Maleeka wacce tai masa K’uri zuciyarta na tsinkewa.

Assad yai tsaye gaban Mu’azzam su duka biyun suna duban juna.

Idanun Assad suka sauk’a kan handcuff dake aje saman table.. Lokaci guda ya mik’a hannunsa ya d’auko handcuffs d’in kana ya d’aga sama yana nunawa daidai fuskar Mu’azzam.

Mu’azzam ya girgiza kai kad’an cikin rashin fahimtar abokin nasa.

Assad ya jinjina kai kafin yace “Handcuff me..” Yai maganar yana mik’awa Mu’azzam handcuffs d’in.

D’an murmusawa Mu’azzam yai irin murmushin da yake idan Assad yana wasu shirirtarsa a cewarsa.

“Yau kuma da irin wann wasan kazo...?”

Girgiza kai Assad yai cikin tsananin dakewa “I’m serious Mu’azzam.. You need to arrest me.. I’m here to confess.. I’m here to turn myself in..!” Ya k’arashe yana mik’o hannayensa duka biyu wa Mu’azzam d’in.

Maleeka da Yusuf suka dubi juna cikeda mamaki yayinda Mu’azzam d’in ya kasa janye idanunsa daga duban Assad.

A hankali yaji fatan bakinsa yana furta “What are you doing Assad..? What is all this..?”

Assad ya bud’e murya yace “This is nothing but the truth, Mu’azzam.. Arrest me now.. Just do it..!” Ya k’arashe yana kuma d’ago hannayensa yana mik’awa Mu’azzam d’in.

“Have you gone mad.? Ka kuwa San abinda kake fad’I? Maiyasa Zanyi arresting d’inka .. What’s wrong with you Assad.. Wannan ba wasa bane kafi kowa sanin hakan..!”

Cikin fad’a fad’a Shima Assad d’in ke fad’in “Na sani.. K’warai na sani.. Kuma nima ba k’arya nake maka ba.. Ba wasa nake ba.. Gaskiyar kenan Mu’azzam.. I’m the rat in our group.. I’m working with Danger.. I’m his accomplice.. Ni ne nan nake cin dunduniyarka Mu’azzam..! Ni nake maka zagon k’asa.. Arrest me now..!” Ya k’arashe hawaye na fitowa daga idanunsa.

Girgiza kai kurum Mu’azzam yake yana jin bugun zuciyarsa na ninkuwa cikin dak’ik’a.. Lokaci guda yake girgiza kai alamun a’a ba haka bane. A hankali bakinsa ke furta “No.. That’s not true.. It can never be true.. You are just joking around kaman dai yanda ka saba..” Ya k’arashe murmushi mai ciwo saman fuskarsa.

Duban Yusuf Assad yai kafin yace “Takedown my statement now.. Take it down..!”

Yusuf yai pause yana duban ikon Allah.. Yayinda Mu’azzam wanda ya koma tamkar ruwa ya shanye yaci gaba da duban Assad d’in cikin rashin yarda.

Kafin Yusuf ya soma rubutu Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in “Don’t write anything down Yusuf.. He’s gone crazy.. Ina ganin hakan daga k’wayar idanunsa.. He’s just lying.. Baya aiki da Danger.. I know my brother can never do such a thing..!”

Murmushi mai ciwo Assad ya saki yana jinjina kai yake duban Mu’azzam d’in kafin yace “You don’t want to believe me right.. Then zan tafi wajen Chief and confess everything to him..!” Yana ida fad’in haka ya fice gumi gauraye da hawaye saman fuskarsa.

Cikin tsananin tashin hankali Mu’azzam yabi bayansa yayinda Yusuf ya take masu baya shima hankali tashe.

Suna ficewa Maleeka Ta goge hawayen idanunta, tana mai sakin murmushi ta zauna saman kujera tana juyi a hankali zuciyarta wasai “Good.. Good job Detective Assad.. Lallai kayi tunani mai kyau.”

Kafin su Mu’azzam su cimmasa ya isa Ofishin Chief ya soma confessing cewa shine spy d’in Su Danger.

Mu’azzam yaja ya tsaya Cak yana duban Assad da Chief.

Chief ya girgiza kai irin yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login