Showing 207001 words to 209154 words out of 209154 words
ya girgiza kai yace “You are so stubborn Marwan.. Yanzu ya zamuyi da yarinyar nan.. Ko asibiti muka kaita mai zamuce.. Babu police report.? Yarinyar da ko sunanta bamu sani ba.. Balle musan daga wace Nahiyar ta fito..” Yana maganar yana k’ok’arin taimakawa Marwan suka rik’eta su biyun.
“I don’t know Yaya.. Amma Iyakacin abinda na sani shine bazamu tafi ba tareda ita ba..”
Abubakar ya jinjina kai yace “Shikenan muje.. Allah Sa kar ‘yansanda su ganmu da mutum haka su tuhumemu..”
Marwan ya amsa da “Babu ma abinda zai faru in sha Allah.. Allah yaga niyya mu na taimako.. Muje..”Ya k’arashe suna masu ficewa tallafe da Budurwar.
Kasancewar yamma ne lis yasa kowa nasa sauri sauri yake ya yada zango.. Babu wanda ya kula dasu da tsintuwarsu abinka da birni mai yawan Al’umma.. Wani asibtin kud’i suka kaita kasancewarsu yaran attajiri tuni Likita ya amsheta.. Sai kuma likitan ya tambayesu mai ya sameta sann wacece ita..
Suka dubi juna a tare cikin rashin sanin mai zasuce..
Marwan yai saurin cewa “‘Yaruwarmu ce had’arin mota ta samu..”
Likitan ya dubesu da mamaki yana kuma dubanta dan ga alamun bruises kad’an jikinta alamun dai had’arin tai.
“Toh ina iyayenku kuka kawota ku kad’ai..” Likitan ya kuma tambaya.
Wann karon Abubakar yai saurin cewa “Makaranta muke a nan gaba d’ayamu iyayenmu basa nan.. Dr please save our sister.”
Dr ya jinjina kai kafin aka soma attending ‘yar uwar tasu.
Likitan ya kuma tambaya “Ya sunata..?”
Cikin rashin sanin mai zasuce suka dubi juna, sai kuma Marwan yai saurin fad’in “Nur.. Sunanta Nuratu..”
Abubakar ya dubesa sai kuma ya dubi likitan ya jinjina kansa.
Daga nan aka soma kula da ita, barin garin da Abubakar baiyi ba a ranan, koda Ta farfad’o Likita ya tabbatar masu cewa ‘yar uwarsu Ta samu matsalan shafewar tunani.. Bazata iya tuna komai ba, bata kuma San ita wacece ba.. Watak’ila sai gaba tunaninta ya iya dawowa..
Saida Abubakar ya kuma shafe Sati a garin yana dubata a asibti kafin aka sallameta.
Marwan da Abubakar sukai zaune suna dubanta daga yanda take zaune, Abubakar ya girgiza kai yace “Yanzu ya zamuyi da ita.. Mai zamu sanar da Inne da kuma Baffah..? Kasan yanda Baffah yakeda tsauri.”
Marwan yace “Tsintar ta mukai, batasan kowa a nan ba, batada kowa.. Na tabbata Inne da Baffah zasu rik’eta amana, Nidai kawai kasan mai zaka sanar da iyayenmu tinda suna jin maganarka..” Yana maganar yana dubanta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.
Lokaci guda ya kuma kamo hannayen Abubakar yana fad’in “Kamin wann taimakon Yaya.. Ka kaita wa Inne da Baffah.. Su rik’e mun Ita har na ida karatuna na dawo..”
Abubakar ya tsaresa da idanu sai kuma ya murmusa yace “Da alama addu’ana ya kama D’anuwana ka samo masu Inne sirka a Lagos..”
Murmushi Shima Marwan d’in yai had’ida sadda kansa kad’an “Kallo d’aya nai mata hasken fuskarta ya haskaka zuciyata... Shiyasa na ambaceta da suna Nuratu.. Noor... Haske..”
Abubakar ya murmusa kad’an kafin ya dafa D’anuwan nasa yace “Zanyi duk abinda kace, zan kuma kaita ma Inne da Baffah.. Zan tabbatar nayi convincing d’insu, Zasu rik’e maka Nuratu har dai ka dawo.. D’anuwana..”
Suka rungume juna kyakkyawan murmushi saman fuskokinsu..
Marwan yace “Allah ya kiyaye maku hanya.. Ka kula D’anuwa.”
Abubakar ya jinjina masa kai suna waiving ma juna kafin ya k’araso yanda Nuratu take.
Bata um bata um um tinda ta farfad’o, dama Likita yace zata d’auki lokaci mai d’an tsawo kafin Ta soma magana.
A haka suka d’auki hanyar Adamawa Abubakar da kuma Nuratu.
Koda suka iso gida Inne da Baffah sunsha mamakin ganin D’an nasu da bak’uwar fuska.. Baffah ya tsaresa da tambayar Ina ya samo yarinya budurwa gashi bata um bata um um..
Abubakar ya sanar da Iyayen nasa komai cewa tsintarta sukai batada kowa kuma batasan daga yanda take ba. Hasalima tinaninta ya shafe magana ma bata fara ba tukuna.
Tausayinta ya lullub’e Inne da Baffah, saidai da fari Baffah ya dage kan a bincika ko za’a sami iyayenta, amma yin hakan ba abu bane mai sauk’i musamman a wancan lokacin da akeda k’arancin ci gaba. ga k’aunar Yarinyar da ya shige zuciyar Inne lokaci guda kasancewar basu tab’a haihuwar d’iya mace ba. Ji take Allah ne ya azurtasu da samun d’iya mace bayan yara maza har guda uku da Allah ya albarkacesu dasu. Tuni Nuratu ta zamto d’iyar Inne, k’aunarta ya dabaibaye Zuciyar Inne, Ta samu d’iyar da bata tab’a samu ba, ga biyayya ga saurin shiga zuciya.. Sannu a hankali ta soma magana saidai har lokacin bata iya tuna ko ita wacece da kuma yanda ta fito.. Nuratu ta shiga Zuciyar su Inne harma da Baffa musamman duba da yanda takeda biyayya da kuma hankali, yarinya ce natsatsiya wacce kowa zai alfaharin ace ita d’in d’iyarsa ce. A haka take zaune da Iyayen Abubakar da kuma Marwan suna nuna tsananin k’aunarsu gareta yayinda ita kuma take nuna biyayya garesu. Ta d’auki Abubakar tamkar babban Yaya, takan kirasa Hammana shi kuma ya kirata Nurie ‘yar k’aramar k’anwata, Yakan koya mata karatu boko da Islama har ya zamto tamkar malaminta, akasarin lokuta suna tare musamman da shike ya kammala karatun Jami’arsa, ya kuma fara kula da Gidan Gonarsu, abu kaman wasa iyayen suka kula kaman soyayya ce take neman k’ulluwa tsakanin Abubakar da Nuratu.. Sukam hakan yayi masu domin kuwa koda basu haifi Nuratu ba sunyi Na’am da hankalinta da kuma Tarbiyarta. Baffah shi ya yanke shawarin had’a auren Nuratu da kuma Abubakar wanda Inne ma ta goyi bayan hakan dan sosai take k’aunar Nuratu kaman ita ta haifeta.
Koda Baffah ya sanar da Abubakar da Nuratu k’udirinsu na had’a aurensu Nuratu sanne kai tai cikeda kunya dan Allah ya gani sosai take k’aunar Hamman nata koda bata furta ba. Sabo da shak’uwarsu shi ya haifar da Soyayya tsakaninsu, saidai a b’angaren Abubakar zuciyarsa ta raunana, Tabbas bai tab’a tsintar kansa cikin soyayya da wata mace ba face Nuratu budurwar da yaima D’anuwansa Alk’awarin zai dawo ya isketa.. Bazai iya musu wa Baffah ba dan bai tab’a bijire ma umarnin mahaifansa ba.. Hakan yasa koda Baffah ya sanar dashi ga k’udirinsu bai masa musu ba bai kuma ce a’a ba.. Saidai ya shiga rud’ani na rashin sanin wanne abu zai aiwatar.. A zuciyarsa yana matuk’ar son Nuratu sann wani b’angare na Zuciyar ya kasa natsuwa, gani yake kaman amanan D’anuwansa zaici idan har ya amince da auren Nuratu.. Tuni an soma shirye shiryen biki har lokacin Abubakar baisan mai zai aiwatar ba.
A ranan d’aurin aurensu da Nuratu Marwan ya dawo daga makaranta. Yaga cincirindon mutane a k’ofar gidansu, koda ya tambaya sai sanar dashi akai auren Yayansa Abubakar da kuma Nuratu ake.
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Shine abinda Marwan ke iya nanatawa cikin zuciyarsa. Ya saki jakansa a hankali ya silale k’asa. Ya dawo da burin ya auri Nuratu.. Ya dawo da burin ya kasance da hasken zuciyarsa.. Saidai tuni ya iske wann labari na cewa Yayansa ya aure Nuratu..
Sukai tsaye suna duban juna shida Abubakar.
Abubakar ya sadda kansa k’asa ba tareda ya iya duban Marwan dake tsaye yana zuban hawaye ba.
“Maiyasa..? Ka sanar dani maiyasa..?”Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.
Abubakar na hawaye ya k’araso da zummar kamo hannun D’anuwan nasa.
Marwan ya kuma jada baya yana girgiza kai “I thought we were brothers..” Yaci gaba da jinjina kai yana hawaye “Kace zaka rik’e amana.. But what did you do.. You did the total opposite Hamma.. Kaci amana.. Ka yaudareni.. Ka rud’eni Yaya.. Ka rabani da Nuurr.. Ka rabani da hasken zuciyata.. How could you do this to your own brother..?” Ya k’arashe dafe da k’irjinsa yana hawaye.
Cikin kuka Abubakar ke Fad’in “Bayina bane Marwan.. Banso hakan Ta kasance ba D’anuwana.. Dan Allah ka yarda dani banci amanarka ba D’anuwana..”
Marwan na hawaye yake girgiza kai yana hawaye “Kaine D’anuwa mafi soyuwa a gareni amma ka zab’I kaci amanata.. Bansan mai zance maka ba.. Amma ka sani ka dab’awa zuciyata tabo da bazai tab’a warkewa ba.. Ka sani Nuratu zata rayu a gidanka ne tamkar tana a GIDAN ARO.. Ko ba dad’e ko ba jima zata dawo gareni..!”
Har ya soma tafiya ya juyo ya kuma dubansa da idanunsa masu zuban ruwa “From now on.. You are not my brother m.!”
Daga haka Sa kai yai ya shige d’aki yayinda Abubakar ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa.
‘Yanuwa masu k’aunan juna suka samu rashin jituwa, saidai Abubakar baiyi k’asa a gwiwa ba, bai bari iyayensu sun fahimci wann sab’ani da suka samu ba. Kullum cikin k’ok’ari yake yaga sun koma like before shida D’anuwansa.
Saidai tun ba’aje ko ina ba Marwan yai sadaukarwa mai girma, ya sadaukar da soyayyar Nuratu ga D’anuwansa Abubakar, sabida yaga yanda su biyun suke matuk’ar k’aunar juna. Sann idan Nuratu zata kasance cikin Farin ciki da D’anuwansa shima zaiyi Farin ciki da hakan, zaiyi k’ok’ari ya mance da Noor har abada.. Marwan ya karb’i k’addararsa... Ya samu mata Hajara a cikin garin Yola akai aurensu dikda ba wani sonta yake ba Sai dan yana so yai moving on ya kuma daina rayuwa in the past. Bai yarda ya sanar da kowa labarin ba, ya binne hakan a zuciyarsa dan Farin cikin Nuratu da kuma D’anuwansa Abubakar.
A haka rayuwa taci gaba da tafiya, Ko wannensu ya maida hankali kan ahalinsa da kuma kasuwancin ahalinsu dan tuni sun soma hayayyafa daga Duka b’angarori biyun. A haka suka bud’e dairy company bayan meat factory d’insu dake nan Fufore.. Daddy Sai ya rik’e ragamar Dairy Company ya koma Abuja da zama sann hakan yafi masa, yayinda Abubakar mahaifin Mu’azzam yake kula da Meat Factory da kuma gidan Gona, a haka Salman na makaranta yana tasowa shima.
Saidai tinda Salman ya gama karatu sai ya d’aura idanunsa kan Meat Factory Kampanin da mahaifin Mu’azzam ke kula dashi, baida buri da ya wuce ya zamto shine mai kula da wajen dikda cewa an sama masa gurbin aiki a ma’aikatan bayan kammala karatunsa, saida fah shi hakan bai masa ba, yafi so ya zama shine shugaba a wann Ma’aikatan, musamman da yaga yanda mahaifinsu ke matuk’ar son Abubakar sabida k’wazonsa wajen aiki da kuma tabbatar da had’in kan ahalinsu. hakan yasa sam Salman bai jituwa da D’anuwansa Abubakar.. A haka kasuwancin ahalinsu na bunk’asa har Allah ya amshe rayuwar mahaifinsu Jauro Gamji suka ci gaba da kula da kasuwancin ahalin kaman yanda mahaifinsu ya d’aurasu akai.
Wannan kenan.
_CI GABAN LABARI_
A hankali Daddy ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya, ya sumbaci hannun Nuratu guda yana hawaye “Bansan furucin da nayi zai zamto gaskiya ba, bansan cewa D’anuwana zai tafi ya barki ba.. Ko da wasa ban tab’a kawowa zaki zamto matata a duniyar nan ba.. Nuratu na jima da cireki cikin zuciyata.. Ban zaci zan rasa D’anuwana har mu kasance tare ba nida ke...” Muryarsa yaci gaba da rawa sosai yana kuma kifa kansa gefenta, cikin rawar murya yaci gaba da furt “Noor ke kad’ai ce macen da na tab’a so a rayuwata.. Kuma Ked’in ke kad’ai ce.. Har abada ke kad’ai zaki kasance babu wacce zata maye gurbinki..” Ya k’arashe wasu hawayen na gangaro masa.
Ya d’an b’ata lokaci kafin ya manna mata kiss a goshi yana dubanta, murmushi gauraye da hawaye saman fuskarsa yake furta “Mu’azzam ya girma ya zama babban mutum harda iyali, sann yana kan bincike dan gano makashin Ikram, bazai huta ba har Sai ya gano azzalumin da ya rabamu da Ikram.. And justice will be served..” Ya k’arashe yana jinjina kansa alamun tabbatarwa.
Hannunta ya kuma rik’owa cikin nasa ya sumbata kafin yace “Zan tafi gobe Noorie, but next time in sha Allah tare zamu tafi.. Akan k’afafunki.. Zaki koma gidanki da kika baro akan k’afafunki da yardar Ubangiji... Kaman yanda nai alk’awari ma D’anuwana.. Zan kula da bayansa.. Zan kular masa daku..!” Ya k’arashe hannunta cikin nasa yana murzasu a hankali, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa mai gauraye da hawaye. A hankali ya gyara mata kwanciyarta kafin ya kuma sumbatar goshinta ya sa kai ya fice.
Yana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idanunta.
**
ABUJA...
Tinda Ta shigo gidan gaisuwa kawai sukai ta k’ule a d’aki tana aikin kuka.
A haka Aunty Larai ta shigo ta sameta, juyin duniya Aunty Larai tayi ta fad’i meke damunta meke faruwa tak’i fad’i sai kuka take.
Aunty Larai ta kuma lek’a waje ko zata hango motar Mu’azzam amma shiru bataga kowa ba.
Ta dawo d’akin ta dafa Sadiyar.
“Sadiya.. Wai meke faruwa ne..? Wani abu ne ya sami Mu’azzam d’in.. Kinzo kin kulle kanki a nan Kina kuka.. Idan Umma ta ganki haka ai sai ki d’aga mata hankali.”
Maimakon ta amsa mata sai kuka da kuma fashewa dashi mai d’an sauri wann karon.
Aunty Larai ta girgiza kai kafin ta dubi Ashiru da shigowarsa kenan d’akin tace “Kai Asheer d’auko min wayata a parlor, idan bazaki fad’i ba shi Mu’azzam d’in ai zai fad’i ai..”
Wani kuka Ta kuma fashewa dashi ta rik’o Aunty Larai tana girgiza kai take fad’in “A’a Aunty nidai kar ki kirasa dan Allah.. Kawai nayi kewarku ne shine nazo..” Ta k’arashe tana goge hawayenta..
Aunty Larai Ta dawo da baya ta zauna “Ina sauraronki.. Meke faruwa..?”
SameenaAleeyou📚