Showing 165001 words to 168000 words out of 209154 words

Chapter 56 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3042

mamaki d’in nan kafin yace “Shattima are you aware of what you’re saying.?”

Assad ya had’iyi throat d’insa ya jinjina kai “Yes Chief.. I’m their accomplice.. Ni nake masu aiki a nan CID..”

D’agowa Chief yai ya dubi Mu’azzam dake tsaye “Inspector Gamji.. Did you hear that..?”

Mu’azzam bai cewa komai ba sai duban Assad kurum da yake cikin rashin yarda.

Chief ya k’ara kiran sunan Mu’azzam “Inspector Gamji, are you going to interrogate him..?”

Nan ma Mu’azzam bai iya furta komai ba Sai duban Assad d’in kurum da yake.

Chief ya dubi Yusuf yace “Take him away.. Jail him

Yusuf ya jinjina kai da k’yar had’ida sarawa Chief kafin ya janyo Assad.

Mu’azzam kam tamkar wanda ruwa ya shanye haka ya koma har aka shige da Assad.

Muryar Chief ya sinkayo bayan ofishin ya rage saura su biyu. Chief yana tsiyaya ruwan a gora cikin cup yake fad’in “So unfortunate mutumin da ka aminta dashi yaci amanarka. Who would’ve ever thought Shattima zai zamto traitor..” Ya k’arashe yana kurb’e ruwansa dake cikin cup.

Mu’azzam ya tako gabansa yana dubansa, ya jinjina kansa a hankali yana murmushi, lokaci guda yake waina d’an k’aramin metal clock da aka k’awata table d’in da yatsun hannunsa “My friend is not a rat.. He’s not a criminal.. I’m pretty certain wani ne ya tilasta masa yin hakan because I know exactly how things work here.. And believe me, who so ever did this to my friend.. that person is going to pay.. Zan kama shi ko shi wanene.. And I’ll clear my friend’s name.. Ka rubuta hakan ka ajiye, Chief.!” Yana ida fad’in haka ya fice yana shafe fuskarsa cikin tsananin damuwa da tashin hankali.

Da mugun kallo Chief ya rakasa yanaji kaman ya damk’o wuyarsa ya gama dashi once and for all.


Wani kujera dake waje ya samu ya zauna, ya kifa kansa a k’asa yana jin k’irjinsa na masa nauyi. Statement d’in Assad kurum yake saurarowa. Ya fuzar da fuci kad’an yana shafe fuskarsa..

Maleeka data hangosa zaune shi kad’ai cikin sauri ta k’arasa garesa, tana isowa ta kifa kanta kad’an kafin ta k’arasa d’aya kujeran ta zauna. Lokaci guda tai gyaran murya kad’an “It so painful.. I never thought mole d’in nan zai kasance daga cikin team d’inmu.. Na kasa gano wanene ke mana zagon k’asa Ina can inata cincike cikin Department d’inmu ashe yana nan kusa damu... Detective Assad of all people.. Kai hak’uri idan ban ida assignment d’in da ka bani on time ba.. Kamo mutum irin Assad abu ne mai matuk’ar wahala idan ba shi yai confessing d’in ba.”

D’agowa Mu’azzam yai yana dubanta na d’an lokaci kafin yace “Get out of my sight.!”

Maleeka tai rau rau da idanu tana dubansa.

Ya kuma furta “Ki b’ace mun daga gani before I lose control..”

Zumbur ta mik’e ganin yanayin da Yai maganar ta bar wajen tana waigowa tana dubansa.

Mik’ewa yai shima yana kiran wayan Yusuf.

Yusuf ya k’araso suka keb’e.

Lokaci guda Yusuf ke girgiza kai “Ban yarda ba nima akwai wata a k’asa.. From the way he talks zaka fahimci akwai wata a k’asa.. Wann abun shiryawa akai.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Na sani Yusuf.. Shiryawa sukai don su b’atar da Assad sabida wata manufa nasu.. But bazamu bari hakan ya kasance ba.. Among the three of us Assad yafi saurin yarda da mutane.. I’m quite certain taking advantage kindness d’insa sukai..”

Yusuf ya girgiza kai yace “But Maiyasa zasu sa Assad ya D’auki laifin nan.. What could be their motive.”

“It’s pretty obvious so suke su rabamu sai suka b’ullo ta wann hanyar.. But believe me bazan tab’a bari hakan Ta kasance ba.”

“Kana tunanin Jaja ne yai haka..?”

Duban Yusuf yai kad’an kafin yace “Not only Jaja.. Ai sabida Nasan akwai wanda ke ratting information a team d’inmu shiyasa nai assigning Maleeka Ta kamo mana Rat d’in.. Wann yarinyar inada tabbacin tana aiki dasu Jaja.. Kasancewar banida cikakken shaida a hannuna shiyasa nai assigning nata ta zamto cat d’in sann tayo mana farautan Rat d’in.. You know banida ikon da zanyi accusing nasu koda inada tabbaci akansu har sai inada tangible evidence. That’s why I assigned her to catch that rat. idan ta rufta ciki ni kuma sai nai amfani da damar na kamata redhanded daga nan kaga zata fito da accomplices d’inta.”

Yusuf ya jinjina kai yace “Yanzu miye abin yi..?”

Mu’azzam ya nusa kad’an yace “We need to clear his name Kafin a gabatar dashi gabansu DIG, kafin a gudanar da wani zama akansa we have to make sure yayi retracting statement d’insa.”

Yusuf ya jinjina kai yace “Fad’a mun nawa part d’in zan kula dashi..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Akwai wani asibiti da Nayi DNA test na B.A.T ban yarda da sakamakon gwajin ba. Ina so kaje wann asibitin ka gudanar da bincike na sirri ka gano idan anyi tempering wann result d’in ne..” Ya k’arashe yana mai ciro wayarsa ya nuna masa asibitin.

Yusuf ya jinjina kai yace “I’ll investigate kar ka samu damuwa..”

Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya dafa kafad’an Yusuf yace “Thank you.”

Yusuf ya jinjina masa kai suka nufo building d’in a tare.

Cell d’in da aka aje Assad ya nufa. Yai tsaye yana duban Assad d’in daga can nesa yanda yai zaune ya had’e k’afafunsa waje guda kansa kife a k’asa.

Cikin tsanaki ya tako ya k’araso k’ofan cell d’in.

Assad ya d’ago ya dubesa kad’an yana jin zuciyarsa na masa nauyi. Sai kuma ya kauda kansa kad’an.

“Did they threaten you..? Did they force you to take the blame..?” Mu’azzam ya tambaya yana duban Assad d’in.

Murmushi mai ciwo Assad yai kafin yace “I don’t know what you are talking about Inspector.. Na riga da na bada statement d’ina.. Mai kuma kake nema..?”

“Tell me mai sukai amfani dashi sukai threatening naka..?” Mu’azzam ya kuma jefo masa tambayar.

Idanun Assad naga wani b’angaren yake fad’in “Is that how you interrogate a criminal Inspector..?”

Mu’azzam ya tsaresa da idanu yana fuzar da fuci kad’an. Lokaci guda yake jinjina kai still yana duban Assad d’in “Ka mance cewa We might have different personalities but we have the same profession.. We both know ba gaskiya kake fad’i ba Assad.. Dani da kai duk munsan haka.. Zaifi kyau idan ka sanar dani gaskiyar komai.”

Wann karon mik’ewa Assad yai yana sakin huci ya k’araso jikin k’arafunan cell d’in. Ya rik’esu suna duban juna shida Mu’azzam d’in. Lokaci guda yake jinjina kai idanunsa akan Mu’azzam d’in “Idan har ka yarda munada profession d’aya then you are abusing your profession.. Baka San aikin ka ba.. Idan har kana tunanin akwai yarda mai k’arfi tsakaninmu wanda zaisa bazan iya cutar dakai ba.!”

“Shut up Assad.!” Ya katsesa da fad’in haka kafin yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “You’ll retract your statement Tun kafin ya isa sama.. Did you hear me..”

Murmushi mai zafi Assad yai kafin yace “Who do you think you are Mu’azzam Gamji. Kai dole kowa Sai ya yarda dakai yabi abinda kake so.. Well you are mistaken wann karon bazanbi ra’ayinka ba.. Wnn shine gaskiyar ka yarda ko kar ka yarda.. Ni ne nan B.A.T d’in da kake nema..!” Ya k’arashe idanunsa na kad’awa.

Mu’azzam bai kuma cewa komai ba Sai duban Assad d’in da yakeyi.. Ya jima yana dubansa Assad d’in wanda tuni ya koma mazauninsa ya zauna.

Bai kuma cewa komai ba Sai ficewa da yai cikin tsananin sanyin jiki lokaci guda yana tuna sa’insansu da Musaddiq wanda yai shige da na Assad d’in.. His two best friends sun juya masa baya.. Maiyasa bazasuga abinda yake gani ba..? Maiyasa suke basa mummunan fassara.. He wants nothing but the best ma dukansu biyun.. Shin laifi ne hakan..? Ya dafe kansa kad’an yana zama saman kujera.
A hankali ya maida bayansa ya kwantar zuciyarsa na fad’i masa cikin tattausar Murya “Kyakkyawan aiki shine aikin da baka neman yarda ko amincewar wani sai na Allah.. Keep being you koda hakan zai masu zafi.. Da sannu zasu fahimci komai daki daki..” Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai sakin murmushi.. Tinanin da yai yanzu da lumshe idanun da yai ji yai tamkar kalamanta ne yakeji cikin kunnuwarsa cikin yanayin sautin ta mai dad’in sauraro.. A halin yanzu babu abinda yake so face ya kasance da ita.. A fili ya furta “My beautiful stubborn head.. I miss you so much.. And I need you so badly..” Ya k’arashe yana mai lumshe idanunsa. Mik’ewa yai. Daga nan bai zarce ko Ina ba sai Company wajen Daddy.

**
Assad kaw Mu’azzam na ficewa silalelewa yai ya zauna yana jin rauni na kuma taso masa. Ya lumshe idanunsa kad’an yana furtawa a hankali “I’m sorry Mu’azzam.. Kai hak’uri abokina.. Na fad’a tarkon mace.. Bazan iya Barin wann kayan tashin hankali ya riski d’iyata ba.. Idan Annabin Allah Annabi Yusuf (AS) zai tafi Kurkuku ya shafe shekaru sabida kaidin mace kan laifin da baiji ba Bai gani ba Toh ni wanene da bazan zab’i zaman kurkuku ba.. Kai hak’uri Mu’azzam nima na zab’i na tafi kurkuku akan mutuncina da na ahalina harma da d’iyata.. Kai hak’uri Abokina.. Na tabbata idan har banida laifi akwai ranan da Allah zai wanke ni kaman yanda ya wanke bayinsa na K’warai da aka masu k’age bayan tsawon shekarun da suka kwashe a kurkuku.!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa.

**

FUFORE


Zaune take gefen Aunty Nuratu tana yanke mata faratunta. Bayan Ajidde ta gama bata ruwan addu’a an shafe mata sauran a goshinta. Sadiya ta k’ura ma fuskarta ido tana kallon kaman tasan mai yanayin kamanninta saidai sabida rama na jinya da fuskar tai sai kuma tana Ganin k’ila dai ta tab’a ganin wata mai kamanninta ne.

Ta kuma d’ago nails d’insa da fingers d’in tana dubawa tana juyasu a hankali.. Itakam tanajin wani irin Al’amari gameda Mamy.. Kaman ta tab’a saninta a wani wajen na daban.. Sann tanajin comfort da wani natsuwa na musamman idan tana tareda ita.. Ta murmusa kad’an tana mai aje mata hannun nata cikin zuciyarta tana fad’in dole ma taji natsuwa a kusanta ko Dan kasancewarta mahaifiya ga mijinta abun k’aunarta. Mutumin data farà sanin menene so akansa.. Sai yanzu take yarda da zancen Sabeera cewa duk samarukan da tai a baya babu wanda ta tab’a so.. Kuma dan dai abin hannunsu take so shiyasa take ganin kaman babu wani kalma mai suna soyayya sai idan zaka sami abun Duniya.. Yanzu da Ta had’u da Mr Inspector ta yarda akwai soyayya sosyya irin wanda zaka so mutum kaji shid’in kake so koda bai mallaki wani abu na k’yale k’yalen duniya ba.. Sannan zaka iya kasancewa dashi a duk yanayin da ya tsinci kansa.. Irin wann soyayyar take ma Inspector. Ta murmusa kad’an tana mai gyarawa Mamy kwanciyarta.

Aunty Shemau dake tsaye bakin k’ofa tana karantarta jinjina kai tai a hankali kafin tasa kai ta shige.

D’aki ta koma ta soma tunanin ya kamata ta binciki Sadiya taji inane asalinsu.. Garinsu da danginsu muddin tana so hak’arsu ya cimma ruwa.. Batasan dalili ba amma ganinta tareda Nuratu yasa taga zubi da yanayin Ikram a tattareda yarinyar.. Idan har Nuratu zata sami wacce zata maye mata gurbin Ikram Tabbas hak’ar mijinta na mallakan dukiyar nan bazai cimma ruwa ba. Toh amma a halin yanzu ba Nuratu ce damuwar ba, yarinyar itace damuwar tinda da Safeenah zasuyi amfani ba da Mommy ba. Da wann tunanin ta mik’e tana zagaye d’akin tana tinanin Ta yanda Zata b’ullowa al’amarin.

Zama tai saman gado wani b’angare na zuciyarta na tuhumarta “Shin mecece ribar ganin bayan wani..? Shin wace riba zaki samu a nan duniyar idan kika cutar da wani..? Duniyar da ba komai bace face GIDAN ARO..” K’ok’arin kauda tinanin tai da fad’in “Zan sami yarda da amincewar miji na..”

Da wann tinanin ta soma neman layin Safeenah saidai sam ba’a d’agawa.. Kiran duniya Aunty Shemau tayi baa d’aga wayar ba. Tai gajeren tsaki tana aje wayar gefe.

**

Mu’azzam na shigowa Company ya hangi Daddy ya nufo parking lot Sai sab’a babbar riga yake yana fad’in gashi nan tafe.

Ko sauraron driver baiba ya shige motar da kansa ya soma driving. Kai da ganin yanayin da Daddy ke ciki kasan babu lafia.

Cikin sauri shima Mu’azzam d’in ya karya kan mota yabi bayansu.

A hankali ya dinga bin bayan motar Daddy.. Saidai baisan ya akai ya nemi motar Daddy ya rasa a holdup ba. Ya fuzar da fuci yana tunanin ina Daddy ya nufa. Ya shafi goshinsa kad’an yana jin motar bayansa na masa horn. Daidai lokacin wayar Inne ya shigo masa.

Gaisawa sukai kafin daga d’aya b’angaren Inne tace “Shin bazaka turo ka d’auki matarka ba Modibbo.. Zaman ai ya isa haka nan.”

Ya d’an rage girman idanunsa kad’an kafin yace “Shigowata Company kenan ma, Zanyi magana da Daddy inaso a bani driver.. Idan yaso ko zuwa gobe sai ya taho jibi su dawo in sha Allah..”

Inne Ta jinjina kai tace “Hakan yayi, zan nemi ‘yar tayin zaman Mota a nan cikin ‘yanuwa sai ta mata rakiya..”

Ya jinjina kansa a hankali yace “Shikenan Inne gobe in sha Allah Adnan zai taho gobe in sha Allah.. Daddy ya fice van samu nayi magana dashi ba amma zan sameshi a gida ko zuwa dare.”

Inne Ta jinjina kai tace “Yayi.. Allah shi maku albarka..”

Daga haka katse sallama suka kafin Inne ta katse kiran. Haka dole ya canza hanya

Fuzar da fuci ya kumayi kafin ya soma tunanin tunanin zuwa gidan Daddy.

A k’ofar gidan ya had’u da Meema da Kiki na zaune gefenta an bud’e masu gate suna fitowa.

Suka taho zasu shige Meema ta sauk’e glass suna gaishesa.

“Ina zaku..?” Ya tambaya yana dubansu.

“Asibiti zamuje wajen Addah Feenah..” Meema Ta basa amsa da fad’in haka.

“Safeenah kuma..? Mai ya sameta..?”


Meema da Kiki suka dubi juna.

Mu’azzam ya katsesu da fad’in “Bakuji tambayar da na maku bane. mai ya sameta..?”

“Tasha poison ne Wai zata kashe kanta shine Mommy ta tsinceta a d’aki tana aman kumfa.” Cewar Kiki.

Yai shiru yana jinjina maganar kafin yace “Wani asibiti take.?”

Meema Ta fad’a masa asibitin.

JInjina kansa yai kafin ya basu hanya suka shige.

Kai tsaye shima hanyar asibitin ya d’auka.

Tare tare suka iso asibitin dasu Meema. Daidai lokacin motar Daddy ma ta shigo asibitin.

A fujajan Daddy ya nufi cikin asibitin bayan su Kiki sun Shige, hankulansu duk a tashe.

A natse ya fito daga nasa motar ya nufi cikin asibitin yanda ya hangosu carko carko k’ofar Emergency.

Mommy tana hangosa ta nufosa tana fad’in uban mai ya kawosa bayan shine silan shiga tashin hankalin da d’iyarta ke ciki. Ta rufe idanu ko tunanin asibiti ne batayi Ta yanda take shiga bata nan take fita ba saidai Mu’azzam ya fice daga asibitin.

Da k’yar Mommy ta daina borin da take saida Daddy ya kusan fice mata a giya.

Mommy na hawaye take duban Mu’azzam lokaci guda take dubansa tana fad’in “Idan na rasa Safeenah bazan tab’a yafe maka ba..” Tana kuka take ci gaba da fad’in “Bayan duk abinda nai ma mahaifiyarka a rayuwa abinda zaka saka min dashi kenan Mu’azzam.. I spent half of my marriage life ina d’awaniya da jinyar mahaifiyarka.. Wllhi nayi imani da Allah idan na rasa Safeenah bazan tab’a yafe maka ba..” Ta k’arashe cikin kuka.

Daidai lokacin Dr ya k’araso yana fad’in Safeenah tayi regaining consciousness..

Gaba d’aya suka bi bayan Likitan idan ka d’auke Kiki da Meema wanda dama basa tsaye wajen.

Suna K’arasowa k’ofa Mommy tace atafau Mu’azzam bazai shiga ba. Bai forcing ba, ya dubi Daddy yaima Safeenah fatan samun lafiya kafin ya fice daga asibitin.

Suna shiga cikin d’akin da kuka Safeenah Ta fara masu tana ambato her Halal.

Mommy takaici kaman ta shak’o Safeenah dake saman gado tana kuka tana fad’in Ina her Halal yake.

Daddy ya k’arasa ya rungume kan Safeenah dake zaune saman gado cikin jikinsa. Lallashinta ya dinga yana k’ok’arin calming nata kafin ya zauna gefenta.

Cikin kuka Safeenah ke ci gaba da fad’in “Daddy I love him.. I can’t live without my Halal..”

Mommy dake gefe tsawa ta darara mata da fad’in “Kika sake ambato wani my Halal a nan sai na halarta ma tafin hanuna fuskarki.. Sai na shata miki mari Safeenah. Shashasha kawai wacce bata San yanda ke mata ciwo ba.”

Safeenah Ta kuma fashewa da kuka yayinda Daddy ya aikawa Mommy mugun kallo “Fita ki bamu waje Hajara.” Ya fad’I yana duban Mommyn.

Cika kurum Mommy take tana fuci kafin tai k’wafa tasa kai fuu ta fice.

A k’ofa Ta had’u da Dr rik’eda file d’in Safeenar.. Ta dubesa tace “Yaya..?”

Likita yace “Report d’in Safeenah ne..”

Mommy Ta nuna masa hanya tace “Muje ka sanar dani ni ce nan mahaifiyarta.”

Dr ya d’an dubeta sai yace “Mijinta fah.?”

Mommy tace “Sun rabu basa tare. Zaka iya sanar dani komai..”

Ya d’an jinjina kansa kad’an kafin ya nuna mata hanya yana fad’in “After you.”

Mommy tasa kai Dr ya take mata baya.

A cikin d’aki kaw yanda Safeenah ke kwance Daddy yaci gaba da mata nasiha da fad’in “What were you thinking Safeenah.. Shin Kinsan matsayin wanda duk ya kashe kansa a addini.. Kafuri fah ya mutu Safeenah.. Shij kinaso ki mutu kafura..? Mai zai sa ki hallak’a kanki kan soyayya. Kwanakin baya kin tasamma halak’a matar Mu’azzam yanzu kuma kina yunk’urin halak’a kanki.. Kan wani dalili Safeenah..!”

Cikin kuka take fad’in “Daddy tambayata kake kan wani dalili bayan kasan dalilin son Mu’azzam ne.. Ni dai Daddy gwara na mutu kan na rasasa..”

Daddy ya girgiza kai yace “Mu’azzam doesn’t love you Safeenah. Learn to accept this.”

Safeenah Ta kuma girgiza kai tana hawaye “My Halal loves me Daddy.. He loves me.. I know he does.. Kawai dai wancan muguwar ce ta rabamu.. Daddy you need to help me please.. Dan Allah ka masa magana Daddy.. Yana jin maganar ka.. Dan Allah Daddy kace ya maidani..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.

Daddy ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tura hularsa baya kad’an. Harga Allah ya soma gajiya da halin Safeenah akan Mu’azzam. Ya kula tana ma Mu’azzam son da bazata iya yakicesa cikin zuciyarta ba. Daga wnn sai wancan.

A can office d’in Dr kuwa da tsananin mamaki Mommy ke dubansa, ta d’an girgiza kai tace “Kace she’s 4 weeks pregnant.?”

Dr ya jinjina kai yace “Gwaji ne na jini wanda ko cikin Kwana guda ne jikinta zai nuna.

Mommy tai shiru tana jinjina kai tana tuna tarewar Safeenah gidan Mu’azzam wata guda kenan harda kwanaki. Muryar Dr ta sinkayo yana ci gaba da fad’in “Luckily cikin bai fice ba amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login