Showing 183001 words to 186000 words out of 209154 words
girl.. Itace mai mana zagon k’asa.. Yusuf make sure baka barta ta fice ba.. Gani nan Ina tafe na nufo headquarters.”
Yusuf ya sanar da Mu’azzam duk yanda sukai da Maleeka. Take yace ya turo masa address d’in gidan Maleekan sai su had’u a can d’in. Yana kashe wayar kuwa sak’on ya shigo wayarsa Yusuf ya turo masa address d’in gidan Maleeka. Sai sauri yake yana fuzgan mota yana ganin kaman bazai isa ba.
**
Tana kwance Sun ida waya da Inne kenan ta soma jiyo hayaniya daga gate. Tai saurin mik’ewa zaune tana jin hayaniyar na k’ara yawa. Babu shiri ta mik’e ta nufi upstairs ta zira doguwar riga a jikinta had’ida tura sumarta cikin hula. Sauri sauri ta sauk’o k’asa ta bud’e k’ofar parlorn tana hangen abinda ke faruwa. Tuni Safeenah ta bangaje Patrick tana fad’in shi bai isa ya hanata shiga gidanta ba. Ko Boss d’in nasa ne bai isa ya mata iyaka da wann gidan ba.. Gidanta ne da sunanta aka gina bataga mahaluk’in da yakai ya mata iyaka da wann gidan ba. Ta nufo cikin gidan tana huci Patrick na biye da ita yana rok’onta tazo ta fice abinda takeyi na iya shafan aikinsa.
Sadiya kaw tana hangosu Ta maida k’ofa ta rufe tai zamanta.
Safeenah na k’arasowa ta shiga bugun k’ofar tana fad’in “Munafuka kizo ki bud’e mana.. Da kika ganni shine kika shige kika b’uya.. K’aramar maras kunya.. Kinyi sa’a wancan karon harsashin bai sameki ba.. Ki bar murna dan kin tsallake tuggun da na had’a miki.. Idan sunana Safeenah Gamji wllhi sai kin bar gidan nan.. Gidan nan nawa ne, mai gidan shima nawa ne ke Kinyi kad’an to come between us nida my Halal.. Kizo ki bud’e nace.!” Ta k’arashe tana mai waige waige tana neman abinda zata daki glass d’in window dashi.. Bata sami komai ba ta cire dogon talakalmin dake k’affunta.. Ta shiga bugun glass d’in window da tsinin takalminta “Zan shigo na taddaki na fitar dake daga cikin gidan da k’arfi.. Come out now.. Ki fito nace..!” Tanayi tana dukan glass da tsinin talkalminta.
Idan Patrick ya nufota tayo kansa da takalmin nata tana fad’in sai ta rapza masa.
Ana haka Sadiya ta bud’e k’ofar. Patrick ya k’araso da sauri yana fad’in “Ma’am Maiyasa kika bud’e k’ofar gashi nan ina kiran Oga amma baya d’agawa.. But I think I’ll just call the cops..”
Safeenah tace “Go ahead and call them.. Ka kirasu nida kai sai muga waye za’a tafi dashi.”
Sadiya ta dubi Patrick tace “K’yaleta Patrick. Jeka abinka I can handle her.”
But yace “But Ma’am wann fah ba mai lafiya bace.. What if Ta miki wani abun..?”
“Uwarka ce batada lafiya..” Safeenah ta basa amsa da fad’in haka.
Patrick yace “Ma’am kinaji koh.”
Sadiya ta jinjina kai tace “Naji Patrick.. Ni kam Karnukan nan yai ka fita dasu morning exercise.?”
Patrick ya girgiza kai yace “A’a Ma’am tun jiya baa fita dasu ba.”
Ta jinjina kai tace “Ka bud’esu susha iska zasu buk’aci hakan..” Tana ida fad’in haka ta maida k’ofa ta rufe.
Safeenah ta shiga tura k’ofar tana fad’in ta bud’e mata. Patrick kaw tuni ya shige bud’e Karnuka.
Safeenah sai kururuwa take tana fad’in Sadiya ta bud’e mata k’ofa.. Ganin bazata bud’e ba ga Karnuka Patrick na shirin kwance su babu shiri Safeenah ta rik’o takalamanta a hannu ta nufi gate a guje tana kuma tsinema Sadiya.
Ta window Sadiya ke lek’en gudun Safeenah sai dariya take har Safeenar ta fice tattare da rigarta takalma a hannu.
Patrick ma dariya ya dingayi yana fad’in lallai Ma’am ta basa satan amsa wann mahaukaciyar tana zuwa nan gaba abinda zai mata kenan ya k’yaleta Ta shiga ya kwance mata Karnuka tinda tana tsoronsu.
**
Maleeka tai zaune a parlor sai murza tafin hannunta take tana jin zuciyarta na wane irin tsinkewa, tasan abinda take k’ok’arin yi abu ne mai matuk’ar had’ari amma nata da wani zab’in da ya shige ta fad’i gaskiya koda za’ayi arresting d’inta ne.. Ji tai bazata iya tafiya da hakkin kowa ba ba tareda ta sanar dasu gaskiyar Al’amari ba. Tana nan zaune tana aikin tunani taji ana knocking daga k’ofa. Ta mik’e tsaye tana tinanin su Mu’azzam ne suka iso.. Batai wata wata ba ta bud’e k’ofar.. Saidai tuni tai wani irin Daskarewa ganin ba Mu’azzam bane ba Yusuf bane.. Wani mutumi ne sanye da bak’ak’en tufafi ya rufe fuskarsa da bak’in mask. Bata iya ganin komai na jikinsa. Take ya soma nunata da k’aramar bindigarsa irin wacce sam ko anyi harbi da ita bazakaji sautin harbinba.
Ta soma jada baya tana fad’in “Please don’t kill me.. Dan Allah kar ka kasheni..” Tana maganar tana k’ok’arin k’arasawa yanda makaminta yake. Mutumin da yake all in black na kuma nufota.. Baka ganin komai nasa sanye yake cikin bak’aken tufafi fuskarsa rufe da bak’ar mask hannayensa rufe cikin bak’ak’en black hand gloves.
Abinka da wacce tasha training itama tsalle tai cikin k’warewa ta naushi hannun mutumin bindigar ya fad’i.. Take mutumin suka soma fad’a da Maleeka. Dukansu biyun cikin k’warewa suke attacking juna. Kai da gani kasan fad’an wad’anda suka sha training ne. Take Maleeka ta soma kokawan yaye hular mask d’in dake kan mutumin yana k’ok’arin hana faruwar hakan.
Maleeka bata gajiya ba taci gaba da kokawan zame hular tana fad’in “Who are you.. Just show yourself.. You coward.. Jaja ne ya turoka ko.. Toh zan kashe ka na kuma kai masa gawarka.. Asirinku ya tonu.!” Ta k’arashe tana mai funcuke hular fuskar mutumin ya bayyana..
Cikin tsananin shock Maleeka ke jada baya.. Ta shiga nunasa da yatsanta dake tsananin rawa tana fad’in “You..you..!!”
Su duka biyun suka tsaya suna duban juna. Maleeka na nunasa cikin tsananin rawar jiki yayinda mutumin yai tsalle ya d’auki bindigar. Aiko nan Maleeka tayo tsalle ta fad’o kansa itama tana kokawan k’wace bindigar.. A haka bindigar na tsakaninsu kowa na kokawar k’wacewa cikinsu.. Tau.! Harsashi ya tashi. Zasu iya cewa basusan waye harsashin ta d’ana ba cikin su biyun dan bindigar a tsakaninsu take. Maleeka takai dubanta zuwaga cikinta yanda harsashin ya sameta. A hankali take duk’awa saman gwiwoyinta har ta isa k’asa tana dafe da cikinta yanda ya harbeta jini na zubowa.
Ta d’ago a galabaice tana dubansa. Take ya k’ara mata harsashi guda. Kan kace mai Maleeka ta zube tana fidda numfashi da k’yar.
Ba tareda ya bar wani trace ba yai gaggawan ficewa daga wajen abinka da k’wararre.
Mu’azzam sai sauri yake yana kuma kiran layin Yusuf. Yusuf d’in ma nan ya sanar dashi ya kusan isa holdup ne ya rik’es.
Kusan tare tare Yusuf da Mu’azzam suka iso gidan. Gidan babu kowa da shike duk ma’aikata ne duk sun tafi aiki.. A bud’e suka sami k’ofa, suka dubi juna kafin suka k’arasa cikin gidan sauri sauri.
Kwance suka hangi Maleeka cikin jini ta gama galabaita tana bud’e idanu da k’yar.. Yusuf bai k’arasa kanta ba sai Mu’azzam da ya isa cikin sauri yana ambato sunanta.
Girgiza kai take tana dubansa... Tana so Tai magana ta kasa sabida ta gama jigata gab take da amsa kiran mahaliccinta “B..! BA.!! BA.. You...You....” Kalman da ta iya fad’i kenan cikin rarrabewar harrufa a hankali idanunta suka rufe.. Tana kwance cikin jini...
Yusuf ya k’araso yana dubanta sai kuma ya girgiza kai yana duban Mu’azzam “I think she’s gone..” Ya fad’i daga nan yanda yake duk’e.
Mu’azzam ya dafe kansa had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Ya lumshe idanunsa a hankali. Take Yusuf ya mik’e yana fad’in “Zan kira backup.”
Mu’azzam bai iya furta komai ba, Sai duban Maleeka da yake. Yasan zai matuk’ar wahala su bar Maleeka a raye tinda yasan yanda Al’amara ke gudana a wajensu.
Allah ya wanke Assad ya kuma kub’utar dashi. Saidai kuma Maleeka ta tafi bayan taso tayi abinda ya kamata a k’urarren lokaci.
Yusuf ya dubesa sanda aka kewaye gawan Maleeka da igiya ana ana d’aukan bayanai.
Yusuf ya k’urawa gawan Maleeka da ake bincike akai idanu. A fili yake furta “She was ready to confess.. Tayi nadama.. Taso ta bayyana gaskiya.. But unfortunately sun kasheta. Basu bata dama ta fad’i abinda ta sani ba.”
Mu’azzam ya kaikaito kad’an had’ida k’ura masa idanu. Baice komai ba sai maida idanunsa kan gawan Maleeka da yai zuciyarsa fal tinani. Duk wanda su Jaja sukai amfani dashi wajen kashe Maleeka wani ne wanda ya sansu in and out.. Sann yasan dik yanda zai bi yayi ta’addanci ba tareda ya bar wani trace ba. Wani ne da yake da ilimin abun.. But who could that person be.? Tambayar da yai ma kansa kenan. He needs to solve this puzzle.. Kalman da Maleeka taso fad’i shi ya tsaya masa a rai BA..
Ya Tsuguna a hankali yana duban yanda harsashi ya huda a jikinta. Lokaci guda yana karantar irin harbin da aka mata da kuma yanayin da gangan jikin nata yake a kwance.
Wani abu k’arami mai kaman toci mai tsananin Haske ya Ciro cikin aljihunsa yana haska k’asan wajen kaman yana neman wani abu. Dik wani abu mai kama da trace baiga alamunsa ba. Yai shiru yana examining wajen.
A hankali ya mik’e yana zira hannayensa cikin aljihu. Wanene makashin Maleeka..? Shine tambayar da ya tsaya masa a rai.
**
A k’ofan prison d’in suka tsaya jingine jikin mota shida Yusuf suna jiran fitowar Assad.
Can suka hangosa yana nufosu kwantattun k’walla cikin idanunsa.
Yana k’arasowa ya shige tsakankaninsu Yusuf da Mu’azzam sai kuma ya rungumesu yana jin hawaye na zuwa masa.
Sameena Aleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*57*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Murmushi yake yana dubansu, su d’inma murmushi ne saman fuskokinsu.
“Thank you both for not giving up on me.. Thank you for believing in me.. Na gode K’warai..” Assad yace yana dubansu.
Yusuf ya dafasa kad’an yace “You don’t need to thank us.. This is what brothers are for.. Na maka murna” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’arsa murmushi saman fuskarsa.
Mu’azzam baice masu komai ba har lokacin, kaman baya wajen haka ya b’ace shiru.
Yusuf yai gyaran murya kad’an ya dubi Mu’azzam d’in yace “I’ll be heading to the headquarters.. Suna jirana akwai report d’in da zan basu.”
Mu’azzam ya jinjina masa kai kurum yana dubansa. Assad ya masa fatan sauk’a lafia.
Wajen ya rage saura Mu’azzam da Assad.
Assad ya d’an dube mutumin nasa cikin ransa yana ayyana yanda zasu kwashe. Abubuwan da sukaita faruwa shi yake zuwa zuciyarsa. Yai gyaran murya kad’an “Na yarda ka fini gaskiya a akasarin lokuta.. Kuma kaid’in ka fini sanin makamar aikinka.. A akasarin lokuta nakan yi zaton ka tsaurara.. Nakan yi k’ok’arin dakatar dakai.. Like you said, we have same profession but our personalities differ.. Mu’azzam aikin da kayi zan iya cewa kaid’in k’aararre ne a sanin makamar aikinka.. You proved me wrong.. Tabbas ba ko yaushe ake yarda da mutane ba.. Na d’auki darasin rayuwa bayan abinda ya faru dani.”
Mu’azzam ya d’an kauda kansa gefe kad’an yana zira hannayensa cikin aljihu “Ka zama mai bud’edd’en zuciya.. Ka yarda da mutanen da suka baka yarda.. It’s not a crime don ka zama mai sauk’in fahimta.. But it can be a crime idan ka zama wanda kowa zai d’ebo sharansa ya zuba..” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Kowa zai iya zama mai laifi.. Ban cire maka kowa ba.. Harta ni da kai zamu iya zama masu laifi.. People change, zuciya batada k’ashi.. Tsokace zalla da takeda tsananin rauni lokaci guda kuma takeda power a gangan jikin D’anadam.. Idan ka bata wann power d’in nan ne zata kaika Ta baro ka.. Amma idan ka barta da rauninta.. Sannu a hankali zata kasance a haka.. Sai ka samu power da zaka sarrafata..” Ya k’arashe yana juya coin d’in Black African Team dake rik’e cikin hannunsa.”
Assad ya kafe abokin nasa da idanu yana dubansa yana murmushi. Zuciyarsa fal jinjina ga abokin nasa.
Jinjina kai yai a hankali kafin ya gyara tsayuwarsa yace “Na gode da kalamanka... Na gode da bakai watsi dani ba.”
Kauda kansa gefe ya kumayi yana rage girman idanunsa kad’an. Dan bayan yaji statement d’in Assad a gaban Prosecutor yaji kalan tuggun da Maleeka taso k’ulla masa sam baiga laifin Assad na amsa laifin da bai aikata ba. Yayi ne to protect his reputation. Ko a shari’a idan aka maka barazana da b’ata suna bakai laifi ba don ka amsa laifin da ba Naka ba ka zab’i tafiya gidan kaso.
“Let’s get going Detective. Akwai aiki sosai gabanmu.” Mu’azzam ya fad’i yana bud’e marfin mota.
Assad ya d’an tsaresa da idanu kad’an yana duban Mu’azzam d’in, gajeren murmushi yai kafin ya jinjina kai yace “Yes Inspector.!” Yai maganar yana sara masa.
Girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin yaja motar suka shige bayan Assad ya shige cikin motar.
Suna tafe labarin mutuwar Maleeka ya kuma zuwa ma Assad “Dukda ta mun laifi naji zafin yanda mutuwarta ya kasance. Hak’ik’a ta zab’i turba maras d’aurewa.. Tanada k’wazo da sanin kan aikinta.. But still ta zab’i tabi hanya wanda babu komai cikinta face k’arya da tsananin duhuwa. I’m quite sure silencing nata sukai..”
Shiru Mu’azzam baice masa komai ba saima ci gaba da tuk’a motar da yake, idanunsa naga kwalta.
Assad yaci gaba da fad’in “So sad.. Sun kasheta bayan ta zab’i tai abinda ya kamata.. Na yafeki Maleeka..! Kuma ina fata ki samu rangwame wajen Ubangiji.. Allah yasa masu hali irin naki su hankalta su gyara.”
Sai lokacin Mu’azzam ya amsa da Ameen yana mai duban window d’in dake side d’insa.
Suna tafe Assad yaga ya d’auki hanyar Lafiya.
Da mamaki yake duban Mu’azzam d’in kafin yace “I thought kace aiki na jiranmu.”
Mu’azzam bai amsa sa ba yaci gaba da driving.
Assad ya d’an murmusa kad’an had’ida girgiza kai, yasan bazai amsa shin bane.
Suna isowa k’ofar gidansu Assad yaja yai parking.
“Hajiya ce tafi cancanta ta soma ganinka fiyeda Chief Jaja..” Yai maganar cikeda barkwanci wanda zaka iya cewa kaman ma ba daga bakinsa ya fito ba.
Assad ya kuma murmusawa yana girgiza kai yana duban abokin nasa lokaci guda yana bud’e marfin motar.
A tare suka jera suka nufi cikin gidan yayinda suka soma had’uwa da Shamsu zai fice shago dan dama yanada shago a d’an k’asa dasu kad’an.
Cikin sauri Shamsu ya k’araso ya rungume D’anuwansa cikeda jin dad’in ganinsa yana masa Barka da fitowa.
Ya k’araso yana gaisawa da Mu’azzam had’ida sake masa godiya kan d’awainiyar Assad d’in da yai. Assad kam tuni ya shige ciki yana ambato Hajiyarsa.
Hajiya harda hawayen murnan sake ganin D’an nata tai. Allah sarki D’ah da mahaifiya kenan. Yanda Assad da Hajiya suka rungume juna suna hawaye ya karya Zuciyar Mu’azzam. Tausayin kansa ya rufesa.. Allah sarki, rabonsa da yayi haka da tasa mahaifiyar shekaru ak’alla goma sha biyar. Ina ma shida Mamynsa zasu rungume juna wata Rana suna hawayen Farin ciki irin haka. Ya d’an sadda kansa k’asa yana k’ok’arin barin wajen.
Hajiya ta dakatar dashi tana kuma masa godiya.
Ya murmusa kad’an yace “Babu komai Hajiya.. Nida Assad ‘yanuwan juna ne.”
Hajiya ta murmusa tana goge k’wallanta “Allah yasa amincinku ya d’aure har Aljannah.. Allah ya rabaku da sharrin mak’iya na b’oye da na zahiri a dik yanda kuka kasance. Allah shi maku albarka.”
Daga Assad d’in har Mu’azzam Ameen suketa amsawa dashi cikeda jin dad’in addu’o’in Hajiyar a garesu.
Assad yace bari yai ma Mu’azzam rakiya.
Har mota ya rakosa. Ya saluting nasa yana fad’in “Idan Inspector yace kar nai reporting back to work Sai nan da sati ma bazance komai ba.”
Gajeren murmushi yai da gefen bakinsa kafin yace “I thought prison did change you..” Yana maganar yana shigewa mota.
“Sai munyi magana.” Mu’azzam ya k’ara da fad’in haka.
Assad na murmushi yake jinjina kai “Alright shikenan.. Da Allah ka bani update fah.”
Bai amsa sa ba sai key da yaima motar. Yasan ba lallai ya amsa d’in ba.
“Zan kira Yusuf kawai naji komai.. Drive safe.” Ya k’arashe yana d’an saluting nasa kad’an wanda kaman d’abi’ar aikinsu ne.
Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai masa horn alamun sallama.
Yana tafe saman kwalta yana tuna kalaman Maleeka na k’arshe “BA.. You..” Ya furta a hankali kafin ya fuzar da huci kad’an.
Kai tsaye gidan Maleeka ya kuma komawa yaci gaba da examining gidan yanda abun ya faru.
Tin daga k’ofa yake karanta. Ya d’aga kai yana duban yanda wasu frames irin mai guda biyar d’in nan Babba da k’ana... Nan yaga babu guda d’aya.. Ga wajen da yake makal’e harda alamun k’usa amma babu.. Take ya soma tinanin Maiyasa babu guda d’aya. “Garin kokawa ya fad’i glass d’in ya fashe.. Wanda yai kisan sai share komai kaman dai Babu abinda ya fashe.. Kenan Maleeka tayi fad’a da mutumin da ya kasheta kafin ya cimma kashetan.” Zuciyarsa ce take wann zancen. Yanayi yana kamanta yanda Maleeka sukai bata kashi da makashin nata. Hoton abubuwan na zuwa cikin k’wayan idanunsa.
K’aramar torchlight d’in ya ciro cikin suit pocket d’insa ya shiga haska k’asan wajen. A hankali ya duk’a yana kuma haska wajen nan ya hango k’anan broken glass alamun dai tinaninsa ka iya zama gaskiya, akwai k’aramar frame d’in a wajen garin kokawa Ta fad’i ta fashe. Yai shiru kaman mai nazari. Gefe kad’an ya haska nan ya hango shatin alamun k’asan takalmi saman farar tile d’in. Cikin tsanaki ya zaro Balck marker dake cikin aljihunsa. Take ya soma tracing shatin k’afan takalmin cikin tsanaki da k’warewa. Saida ya zana tsaf suffar shatin k’asan takalmin ya bayyana. Ya jinjina kai a hankali yake duban zanen tracing k’asar takalmin da yai. Wayarsa ya ciro yai hoton zanen k’asan takalmin da yai kafin ya mik’e yana kuma k’are ma gidan kallo yana karantar ko Ina a tsanake.
Dik iya binciken da yai gidan bai samu abinda zai linking Maleeka da Chief ba. Koda shike yasan hakan abu ne mai matuk’ar wahala, bazasu yarda su bar wani abu da zai nuna sunada wata alak’a ba. A fili yake furta “Sannu sannu bata hana zuwa Chief Jaja.. Da sannu zaka iso hannu.”
Daga nan ficewa yai daga gidan ya nufi gidan Daddy.
**
Umma tai zaune tana tinanin ina ta yar da sisin kobon. Wann sisin kwabon shi kad’ai ne abinda yake tuna mata bayanta. Bazataso ta rasa sa ba. Mik’ewa tai ta janyo akwatin da suka tara kayayyakinsu na wancan gidan. Addu’a kurum take Allah yasa yana ciki. Ta shiga bincikawa tana duba cikin akwatin.. Babu wann sisin kwabon babu alamunsa. Tai zaune tana tinani.. Watak’ila a Suleja