Showing 147001 words to 150000 words out of 209154 words
mak’oshi ya mana banga banga..” Ya kuma murmusawa yana fad’in “Good job Officer.. Kinsan aikinki.. Dole BAT ya baki kyauta na musamman bisa jajircewa da kikai..”
Ta murmusa kad’an kafin tace “Na gode da yabo Sir.. Amma Sir Ina son sanin wanene asalin BAT.. Shin menene had’insa da case din nan..?”
Murmusawa Chief yai kafin yace “Zai fi miki idan kika tsaya a nan ba tareda Kin kuma kutsawa ciki ba..”
Maleeka ta d’an girgiza kai kad’an kafin tace “Har yanzu baku gama yarda dani bane.. Chief ina son sanin Wanene BAT.. Ina son sanin ma wa nake aiki..?”
Chief ya murmusa kafin yace “Har yanzu dai zan k’ara shawartanki kar ki nemi sanin wanene Jemage domin kuwa bakinksa baya banbance abu mai kyau da najasa, komai ta baki yake. harta najasa ta baki yake fitarwa.. Jemage baida gaba sai baya..!” Ya k’arashe cikin tsoratarwa.
Maleeka ta d’anyi jim kafin tace “Chief kana nufin BAT wai Jemage kake nufi ba abbreviation na sunan wani bane..?”
Murmusawa Chief yai kafin yace “You love asking crucial questions Maleeka and you never give up akan bincike.. Ked’in material ce Babba.. Zakiyi amfani ma CID sosai da ace zaki zamto mutumiyar k’warai...” Daga haka katse kiran yai ya barta tana tinani.. Ta fuzar da fuci kad’an tana nanata kalmar Jemage.
**
FUFORE..
Su Inne dasu Aunty Shemau gaba d’aya suka fito tarbansu, duk wanda ke cikin gidan ma saida Inne ta sanyasa fitowa domin a tarbi kishiyarta amaryar Mu’azzam d’inta.
Ajidde ce kawai bata a wajen amma har su Mama Hindu duk sun fito.
Gaban Sadiya Sai fad’uwa yake sanda suka soma fitowa daga motar. Ita da Mu’azzam ne a baya sai ko Musaddiq da driver a gaba.
Tana fitowa ta hango Dattijuwar sai sakin murmushi take idanunta tarau akanta sauran mutanen na lale lale.
A hankali Sadiya ta sadda idanunta k’asa sanda taji hannun Mu’azzam saman nata. Tai k’ok’arin zame hannunta amma yak’i saki.. Ta d’an d’ago idanunta ta dubesa kaman mai shirin kuka alamun ya sakar mata hannu.. Bai sakar matan ba sai ma d’auke kansa da yai alamun ta daina b’atawa kanta lokaci dan bazai cire hannunta cikin nasa ba.
Babu yanda ta iya ta maida kanta k’asa.
Musaddiq ya tafi da sauri ya rungume Dattijuwan yana fad’in yayi kewarta wanda Sadiya keda tabbacin cewa itace Inne.
Inne ta d’an dunguri k’eyarsa tana fad’in “Toh maza kayar dani sai kaji dad’i.. Fitananne..”
Musaddiq ya d’an shafi kansa yace “Haba mana Inne tarban da zaki min kenan..”
Ta tsaresa da idanu tana karantar k’wayan idanunsa ko da ya tafi Abuja ya koma shan wasu abubuwan.. “Shige ka jirani zanzo na bincike ka..” Ta fad’i tana turasa kad’an.
Daidai lokacin Mu’azzam da Sadiya suka k’araso.. Mu’azzam ya bawa Inne light hug yana fad’in “Nayi kewarki Inne na..” Murmushi itama tai kafin ta d’an turasa tana fad’in “Ka dank’aro mun kishiyoyi dole kace haka.. Bani waje na fara gaisawa da kishiyan tawa kafin kai.” Ta k’arashe tana mai nufo Sadiya.
Sadiya tai saurin duk’awa da niyyan gaida Inne.. Saidai Inne bata bari ta isa k’asa ba ta kamota tana fad’in “A’a na yafeki.. Tashi abinki ni k’awarki ce ba kishiya ba..” Tai maganar tana mai rungumar Sadiyar.
Ita kaw Sadiya daketa sakin murmushi sanne kanta tai da mayafinta jikin Inne dan kunya..
A haka Inne na rik’eda Ita suka nufi cikin gidan.
Shemau ta rakasu da idanu kafin ta jinjina kai tace a cikin zuciyarta. Tirk’ashi Lallai Safeenah kinada jan aiki.. Lokaci guda ta soma dialing layin Mommy tana mai barin wajen.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*47*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A d’akin Inne aka soma mata masauk’i a cewar Inne sai Washe gari su kaita b’angarenta suyi mata rakiya kaman yanda akeyi a al’ada. Ba haka Mu’azzam yaso ba, saidai babu yanda ya iya tinda haka Inne tace. Tai wanka nan band’akin Inne Ta kuma sauya shiga cikin tufafi masu sauk’i.. Sai nan da Ita Inne take, gaba d’aya Sadiya ta gaza sakewa Dikda cewa da Innen take ta saki jikinta gida take.
Mama Hindu ce ta shimfid’a mata abin sallah sanda ta ida shirin nata.. Nan Mama Hindu Ta nuna mata gabas, itama sai nan nan da ita take.
Sadiya tai mata godiya cikeda risinawa kafin ta tada sallar isha.
Ruwan sama na kuma b’arkewa kaman da bakin k’warya.
Mama Hindu ta fito ta nufi d’akin Aunty Nuratu tana fad’in yau Ajidde batai mata sallama ba ta tafi..
Kicib’is sukai da Ajidde ta fito daga waje ruwa ya jik’ata shakaf rungume da gwaiba cikin hijabinta.
Mama Hindu ta saki baki tana duban Ajidde da tsananin mamaki “Ke Ajidde Wai dama baki tafi gida ba.. Toh ina kika tsaya..? Jibi yanda ruwa ya miki lilis..” Tai shiru tana duban Ajidde dake rawan d’ari.. Sai kuma ta girgiza kai tana duban ‘ya’yan gwaiba data jido.
Mama Hindu Ta girgiza kai tace “Yanzu tsayawa tsinkar gwaiba kikayi a ruwan nan ga duhun dare Ajidde.. Kar dai ma bishiya kika d’ale a daren nan..?”
Ajidde tana tura ‘ya’yan gwaibanta jaka take fad’in “Yo ai ba tsinka nayi ba a k’asa na gansu sun zurzubo.. Kuma ai Inne tace ko mai nake so na tainka kayana wanda bazan iya ba nace a tsinkar min..”
Mama Hindu ta girgiza kai tace “Toh amma kinji ruwan da ake tsulawa kuwa.. Waima ya akai yau kika makara ne..?”
Ajidde ta dubeta sai kuma ta lek’a waje tana ganin ruwa na kuma zuwa kaman da bakin k’warya.
K’arasawa tai Ta zauna dirshan a wajen ta fara sunbatu kaman na mai kuka “Ni wllhi bansan dare yayi haka ba.. Kuma wllhi gwaiban sunada yawa a k’asa ne shisa na bisu d’aya bayan d’ayan ina tsintarsu.. Wllhi su suka jamin.. Na shiga uku Mama Hindu dan Allah ki kaini gida..”
Mama Hindu ta girgiza kai tana jinjina shiriritar Ajidde.. Daidai lokacin Inne ta k’araso an Ta jiyo kaman kukan Ajidden.
“A’a Ajidde lafiya.. Ya na ganki haka..? Meke faruwa..?”
Cikin kuka take fad’in “Inne ai ke kika ce duk bishiyar da nake so na tsinka.. Shine na kad’o gwaiban nan suka zubo da yawa dama tin da ake hadari suke zubowa a k’asa shine na bisu ina tsintarsu ashe Wai dare yayi kuma anata ruwa...” Ta k’arashe tana goge hawayenta.
Inne ta murmusa tace “Daina kukan toh.. Goge hawayenki zan saka Shemau ta kira min Innan taki a waya sai na sanar da ita ruwa ya tare ki zaki Kwana nan..” Ta dubi Mama Hindu tace “Ta canza kayan nan nata ya jik’e gaba d’aya.”
Mama Hindu Ta jinjina kai tace “Shirirtar Ajidde nada yawa ai Hajiya.. Yo ni gidan nan ma bansan kayan waye zai mata ba..”
Sadiya dake tsaye gefe wacce itama kukan Ajidden ne ya fito da ita nan tace “Kayana zasu mata..” Tai maganar tana duban Ajidde wacce ta dakata da goge fuskarta tana duban Sadiyar. Murmushi saman fuskar Sadiya wacce duba guda tai ma Ajidden taji ta kwanta mata, dukda zancen shiriritar da taji tana yi.
Inne tace “‘Yar nan ayi haka daga zuwanki..”
Murmusawa Sadiya ta kumayi kafin ta girgiza kai tace “Babu komai Inne bara na d’auko mata.”
Inne Ta saki murmushi tana duban Sadiya da ta shige d’aukowa Ajidde kaya kanta a k’asa tana gyara zaman mayafinta.
Tana shiga d’akin Inne taji an janyota Ta fad’a jikin mutum.
Ware idanunta tai tana shirin kurma ihun itama. Nan ta gansa hasken k’wan wutan lantarki ya Haske masa FUSKA tarau.. Yayi wanka ya sauya shiga shima zuwa wasu tufafin ruwan toka, wando mai Laushi irin na sanyi mai kaman roba a k’asa sai rigar itama ruwan toka mai d’aukeda tambarin Adidas wacce itama ta sanyin ce mai dogon hannu saidai bata cika kauri ba. Sai ni’imtaccen scent d’in Blue De Chanel dake tashi jikinsa.
Tai narai narai da idanu tace “Inspector ka razane ni.”
Tsareta yai da rikitattun idanunsa yana duban shigar data sauya zuwa wata Maroon Dubai gown marar hayaniya mai laushin gaske wanda ya amshi fatarta, ta yane sumarta da mayafin kayan Wanda shima kalan Maroon ne. Ta masa kyau har ta gaji.. Shi data wanke kwalliyar ma sai yaga tafi masa kyau sosai.. Fatarta data sha gyara Sai k’yalli da sulb’i yake.
Janyota yai cikin jikinsa yana fad’in “You look beautiful..” Yai maganar murya a d’an dashe ba tare da ya janye idanunsa daga kanta ba.
Gabanta ya d’an fad’i, Ta soma k’ok’arin zame jikinta tana fad’in “In..Inspector.. Inne tana jirana.. Aike na akai..”
D’aya hannunsa yai amfani da ya kuma shigar da ita jikinsa kafin yace “Yaushe kika zama ‘yar gida da har aka fara aikenki..?”
Ta d’an rausayar da idanunta kafin Ta tab’e baki kad’an tace “Bakada labari Inne ta bani certificate na zama cikakkiyar ‘yar gida..” Ta k’arashe cikin dabara tana mai son zamewa daga rik’on da yai mata..
Wannan karan gajeren murmushi ya saki da gefen bakinsa still idanunsa akanta.. Bata ida zame jikin nata ba taji ya kuma juyar da ita ya rungumeta ta baya..
Bugun zuciyarta ya k’aru.. Ta lumshe idanunta a hankali.. Cikin rawar murya take fad’in “Dan Allah kayi hak’uri.. Aike na fah akai.. Yanzu idan aka shigo aka ganmu haka fah.? Tamkar zata fashe masa da kuka haka tai maganar.
Hab’arsa ya d’aura kad’an saman kafad’arta guda yana kuma shak’an daddad’an k’amshin dake tasowa daga cikin jikinta, idanunsa a lumshe yake furta “This is my grandma’s room babu mai shigowa..”
“Toh idan Inne ta shigo fah..?” Ta kuma fad’i kaman zatai kuka.
Hannunsa taga ya mik’a saman switch na wuta ya kashe wutan d’akin.
Cikin tsoro take furta “Na shiga uku.. Inspector what are you doing..? Dan Allah ka barni naje zasu gaji da jirana..” Bai bari takai aya ba ya rufe bakinsa da nata.. Wata rayuwa ce da bata tab’a tsintar kanta ciki ba, tsantsan k’aunarsa yake nuna mata wanda bata tab’a koda hasasho su biyun a irin wannan duniyar ba. Saida ta sakar masa kuka kafin ya k’ok’arta ya saketa.
Ya kunna switch d’in wutan yana dubanta yanda take share hawayenta.
Hannayenta ya kuma janyowa kafin yace “Ke kikace kar a ganmu shisa na kashe miki wutan.. Kuma na mance you are afraid of the dark..”
Ta d’an dubesa kad’an kafin tasa kai zata shige.. Yai saurin kamota yana fad’in “Wait tsaya mana.. Kinyi fushi ne..? Idan kika fita haka Inne zata fahimci mai kika tsaya yi a d’akinta gwara ma ki sake wann fuskar taki..”
Ta mak’ale kafad’a ba tare tace komai ba still baki a ture.
Ya d’an kauda kai kad’an yana murmushi kafin ya maido da dubansa gareta “Ok tell me meye aikan sai na kaiwa Inne kar Ta ga fuskarki da hawaye..”
“Idan ma Ta gani zan fad’a mata abinda kayi ne.. Kuma ma ai ba kai ta aika ba..” Ta basa amsa kai tsaye.
Sosai ta basa dariya amma sai ya d’an gimtse yace “Ok shikenan.. D’auki aikan ki kai mata ina jiranki a nan zamu je ki gaisa da Mamy..” Ya k’arashe yana mai fitowa Parlorn Inne. Zama yai nan kan kujera yana jiranta.
Yayinda Sadiya ta k’arasa ma’ajiyan kayanta jiki a sanyaye jin yace zasuje ta gaisa da mahaifiyarsa.
Har Ta fita ta kaiwa Ajidde kayan yana nan zaune saman kujera yana duba wayarsa. K’afarsa d’aya bisa d’aya.
Sarai yaji dawowarta amma yai kaman baiji ba. Tai tsaye gefe tana jiran mai zaice, shiru baice komai ba.. Ta d’an Langab’e kai kad’an cikin zuciyarta tana fad’in mai hali baya canzawa.
Bata ida tinanin ba taga ya mik’e yana zira wayarsa a aljihu.
Ya d’ago yana dubanta sai ta sadda nata kan k’asa.
Hannunta guda ya kamo ba tareda ya furta komai ba, nan ta shiga bin bayansa kaman rak’umi da akala.
Tin daga k’ofar d’akin take jin bugun zuciyarta na ninkuwa.. Wani irin yanayi mai kaman tausayi had’ida rauni sun taru sun cika zuciyarta. Tasan mahaifiyarsa batada lafiya amma bata tab’a ganin yaya jikin mahaifiyar tasa yake ba.
A hanya suka had’u da Mama Hindu tana fitowa.. Suka gaisa da Mu’azzam yana tambayarsa mahaifiyar tasa.
Mama Hindu tace tana ciki yanzu ta ida mata shirin bacci.
Ya jinjina kai kafin ya kuma janyo hannun Sadiya suka shige.
Fuskar matar ta soma hangowa kwance saman gado, Fuskar tata tayi Haske sosai irin na wanda ya jima yana jinya.
K’afafunta a mimmik’e gwanin ban tausayi.. Baka ganin komai a fuskar nata sai dogon hanci da kwarmin idanuwa alamun jinya Yaci rabonsa.. Ya Allah ka azurta majinyatanmu da lafiya ka k’ara mana lafiya da zaman lafiya a cikin al’umman musulmi.
Hawaye ne taji sun ciko idanunta tab.. Ta tina cewa wannan matar da take kwance babu abinda take nema face lafiya.. Da za’a ce ta bada komai nata dan ta sami lafiya zata bayar.. Ina kai da kake da arzikin lafiya shin mai ka aikata da wannan lafiya da Ubangijinka ya baka..? Shin ka tab’a tambayar kanka lafiyar nan zuwa wane lokaci aka ara maka..? Shin ka tab’a hisabi ma kanka cewa mai ka aikata da wannan ni’ima na lafiya da Ubangiji ya baka..? Shin kasan mutane nawa ne suke buri da fatan su sami lafiya irin naka domin Su bautawa mahaliccinsu da ita.. Allahu Akbar Tabbas Lafiya itace babbar arziki da Allah zaiyiwa Bawa, kuma babu arzikin da ya kaita.. Ina kake mai kukan Allah bai baka arzikin gidan duniya ba, ka sani idan Allah ya baka arzikin lafiya ya gama baka babban arziki wanda mutane da dama Sun saka arzikinsu domin su sameta kuma basu sameta ba. Ina kake mai burin tara abin duniya ka sani idan babu lafiya arzikin da ka taran ma bazaka ji dad’inta ba..Lafiya uwar jiki aka ce babu mai fushi dake.. Idan an d’auke maka ita jarabawa ne.. Haka idan aka Barka da ita duk cikin jarabawa ne.. Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci a rayuwa Ameen.
Muryar Mu’azzam Ta sinkayo yana furta “Queen Mother.. She’s my Mum.. My Mamy.. My sunshine.. My Happiness.. My everything..!”
Ya d’an sassauta muryarsa kafin yaci gaba da fad’in “Na rasa jin kalamanta masu taushi da dad’in sauraro sama da Shekaru goma sha biyar.. Kunnuwana sun d’auki lokaci mai tsawo basu jiyo albarkan da take saka ma rayuwata ba..” Ya d’an murmusa kad’an still idanunsa akan mahaifiyarsa kafin yace “Do you know, my Dad used to say she cooks the best food.. Sann tanada kalamai masu taushi da zak’i saman harshenta..” Muryarsa ya d’an sark’afe yana k’ok’arin maida k’wallan dake k’ok’arin ciko idanunsa.. “Nayi kewarta sosai.. In fact nayi kewar ahalinmu sosai.. It seems ni kad’ai nai saura cikinsu.. Babu Daddy babu Ikram.. And Mamy tana nan ne tamkar da bata nan.. tana kwance cikin jinyar da Batasan a yanda take ba shekaru goma shabiyar.. An gwada magunguna da dama amma Allah bai mufa za’a dace ba..But Alhamdulillah ala kulli halin shine abinda zamu ce.!” Ya k’arashe yana mai d’aura hannunsa guda saman na mahaifiyarsa.
Sadiya ta saka mayafinta ta goge hawayen da suka zubo mata cikeda tsananin tausayinsa. Tabbas idan kaga mutum kar kayi garajen yi masa hukunci dan baka San mai yake going through a rayuwa ba. Watak’ila matsalar da yake fuskanta bazaka iya d’aukan kwatankwacin sa ba idan aka aza maka.
Ji yai hannunta guda ya sauk’a saman nasa hannun dake d’aure kan na mahaifiyarsa.. Ya dubi hannayen nasu d’aya bisa d’aya. Nasa saman na mahaifiyarsa saiko na matarsa sadiya da ta aza saman nasa hannun. Ya d’ago yana duban fuskarta da hawaye ke gangarowa. A hankali ta soma fad’in “Allah baya d’aura ma rai abinda bazata iya ba. In sha Allah zata sami lafiya.. Kar ka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji kaji.. Da izinin Allah zata sami lafiya ta zamto Tamkar bata kwanta jinyar nan ba.. Muyi fatan jinya ya zamto mata kaffaran kura kurai kaji..!” Tana maganar hawaye na gangaro mata cikin yanayin muryar mai tsananin rauni.
Ya jinjina mata kai a hankali yana mai sakin murmushi “In sha Allah..!” Ya furta yana duban idanunta kafin ya d’ago d’aya hannunsa ya shiga goge mata hawayenta.
Yana goge mata hawayen yake fad’in “Kinsan cewa itace sanadiyar had’uwarmu..?”
D’an duban fuskarsa tai tana mai son Ganin k’wayar idanunsa.
“Kace Itace sanadiyar had’uwarmu.?” Sadiya ta tambaya tana dubansa dikda cewa shid’in ba cikin idanunta yake duba ba fuskarta yanda yatsun hannunsa ke sauk’a yana goge mata hawayen nan yake duba.
A hankali ya jinjina mata kai kafin yace “Nayi alk’awari wa Mamy cewa matuk’a Ina aikin D’ansanda zan zak’ulo wanda duk ya kashe mata d’iyarta Ikram da izinin Allah.. A ta dalilin binciken mutuwar Ikram na had’u dake har ta kaimu ga aure.. Kinga Mamy tana cikin sanadi.” Ya k’arashe yana mai sauk’e k’wayar idanunsa cikin nata.
Ta janye nata idanunta daga barin duban nasa tana mai sakin murmushi a hankal.
Murmushin shima yasaki kafin ya maido da dubansa ga mahaifiyarsa.
Ya kuma rik’e hannun mahaifiyar tasa dake bacci cikin nasa kafin ya soma fad’in “Mamy.. Ga d’iyarki na kawo miki ku gaisa..” Sai ya d’anyi fasali ya karkato yana duban Sadiya. Lokaci guda yaci gaba da furta “Although She’s the most stubborn person I’ve ever met.. Ko cikin mutanen da nake gwagwarmaya dasu a interrogation room, ban tab’a cin karo da stubborn person irinta ba..” Ji yai ta mintsili hannunsa dake cikin nata.
Ya d’an saki k’ara yana dubanta yanda ta firfito da idanu waje.
Lokaci guda take girgiza masa kai kafin tace “That’s not true..” Ta fad’i kaman zatai kuka.
“Ok nayi shiru kar na fad’a..? Baki so Mamy taji halin ‘yar nata ne..?”
Tai narai narai da idanu had’ida mak’e masa kafad’a alamun a’a.
Yai intertwining yatsun hannayensu kafin yace “Bribe me idan baki so na fad’a mata..”
Ta zaro ido waje tace “D’an sanda da karb’an cin hanci da rashawa..?” Tai maganar a hankali kaman mai tsoron kar Mamayn ta jita.
Ya kashe murya kad’an shima kafin yace “Believe me this one is allowed..” Ya fad’i yana kashe mata ido guda. Hakan yayi daidai da shigowar Inne sallama saman bakinta.
Suka amsa mata sallamar Sadiya na cire hannunta daga nasa. Ta gyara zamanta sosai daga nan yanda take zaune gaban gadon Mamy.
Inne ta k’araso tana tambayarsu ko Mamyn tayi bacci.
Mu’azzam ya bata amsa da fad’in tayi bacci ai.
Inne ta jinjina kai kafin ta dubi Sadiya da ta sadda kanta k’asa lullub’e da mayafi sai kuma ta dubi Mu’azzam tace “Zata kwana wajena gobe idan Allah ya kaimu da yammaci a kaita d’akinta kaman yanda aka saba a al’ada.. Ba wani taro za’ai ba duba da yanayin jikin Nuratu.. ‘Yan uwa k’alilan ne zasu mata rakiya zuwa d’akinta kaji koh..”
A hankali ya furta “Toh Inne..” Kana jin yanda ya amsa kasan a dole ya amsa