Showing 153001 words to 156000 words out of 209154 words
Bamu buk’atar maganinta..”
Musaddiq ya katsesa da fad’in “Babu yana zataje.. Sabida ita mutumiyar kirki ce.. Kuma Aunty Nuratu tana buk’atar maganinta..!”
Aunty Shemau ta zaro idanu waje tana kame k’irji, mai Musaddiq yake nufi da cewa Nuratu tana buk’atar maganin yarinyar.. Kodai Musaddiq yasan shirinsu ne itada mahaifiyarsa..? Muryar Mu’azzam ne ya kaste mata tunanin nata.
Ganin yanda yake amsa masa magana yasa ya kuma karkatowa yana duban Musaddiq d’in “Are you high..?” Mu’azzam ya tambaya yana tsare Musaddiq d’in da idanu.
Tambayar da Mu’azzam yai masa na k’arshe ya mugun tunzirasa, lokaci guda ya soma fad’in “Kana tunanin kai kad’ai ne mutumin Kirki a nan.. Well let me remind you.. You are not a saint Mu’azzam Gamji.. And you need to learn that you can’t control the lives of the people around you.. And yes like it or not Babu yanda Ajidde zataje.. Tana nan a gidan nan..!”
Wann karon cikin tsananin mamaki Mu’azzam ya girgiza kai kad’an yana duban Musaddiq d’in “Have you lost your mind.?” Ya furta a hankali yana duban Musaddiq d’in.
Inne tai saurin rik’o Musaddiq tana k’ok’arin janyosa baya yayinda Mama Hindu ta janye Ajidde suka fice daga wajen. Shemau kuwa gyara tsayuwarta tai tana kallon show d’in dake wakana.
Inne tana janye Musaddiq take fad’in “Ya isa haka abi komai a sannu..”
Musaddiq cikin d’aga murya yace “No Inne.. who does he think he is da dole kowa Sai ya bi abinda yake so.. Ajidde bazata bar gidan nan ba.. Kuma zata dawo zama cikin gidan nan na har abada..!”
Yaci gaba da sakin huci yana nufo Mu’azzam d’in, saida ya tsaya kaman k’irjinsa zai bangaji na Mu’azzam kafin yaci gaba da fad’in “And do you know Why is that Mu’azzam Gamji..? Because I love her..! Yes I love her.. And I’m going to marry her.. Kai baka isa ka koreta ba Mu’azzam Gamji..!”
K’iris ya rage Shemau bata kifa k’asa ba.. Daga Inne har Mu’azzam Cak suka tsaya suna duban Musaddiq dake ci gaba da sakin huci kaman zai kaiwa Mu’azzam d’in naushi.
Mu’azzam yai k’ok’arin calming kansa dan ya lura kaman Musaddiq d’in a sama yake.. K’ila yasha wani kayan mayen nasa.
Inne zatai magana Mu’azzam ya dakatar da ita yana fad’in “Kar ki damu Inne I’ll take care of this..”
Lokaci guda ya mik’a hannunsa yana k’ok’arin kamo Musaddiq d’in yake fad’in “Brother calm down.”
Fuzga Musaddiq yai yana ci gaba da sakin huci yake nuna Mu’azzam d’un da yatsa “Don’t you dare.. Don’t you dare come near me.!” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige cikin huci.
Inne tai saurin taresa cikin tsananin b’acin rai take fad’in “Baka da hankali ne kake d’agawa D’anuwanka murya haka.. Kodai ka koma shan kayan mayen Naka ne..?!”
Bai daina sakin huci ba yake duban Inne “Go ahead and take his side.. Dama abinda kuka iya kenan.. Baya laifi a idonku.. Bani ya kamata ki tambaya ko na koma shan kayan maye ba.. Shi ya kamata ki tambaya tinda har zai tare k’aramar yarinyar nan yace ta masa sata bayan bata sata masa komai ba.. Idan bai gode wa d’awainiyar da takeda mahaifiyarsa wanda bazai iya biyanta kwatankwacin abinda tai ba bazai k’ala mata sharrin sata har yace zai koreta a gidan nan ba.. Kuma kunji abinda na fad’a I love that girl.. Ina sonta.. Ina sonta sosai kuma zan aureta.. Idan zaku koreta a gidan nan sabida shalele Mu’azzam yace a koreta Toh definitely zaku had’a dani dan nima zan tafi kuma bazaku sake ganina ba..!” Daga haka ya fice fuu yana sakin huci.
Inne tai mutuwar tsaye tana duban Musaddiq har ya fice. Aunty Shemau dake lab’e bayan parlorn itama kallo tabi Musaddiq d’in dashi tana jinjina lamarin cikin zuciyarta har yazo ya shigeta ya fice a parlorn.
Mu’azzam ya k’araso ya rik’e Inne ya zaunarta a hankali saman kujera.
Duban Mu’azzam tai tace “Kaga yanda yake d’aga mana murya..? Anya yana cikin hankalinsa..?”
Mu’azzam ya fuzar da fuci kad’an yace “Zan same shi Inne.. Zan mishi magana.. Zanji meke damunsa.. Tabbas akwai abinda ke damun D’anuwana.. Koda ya sha abubuwansa ba haka yake ba.. Something is off with him..”
Inne dai shiru tai tana jinjina abubuwan dake faruwa da ahalinsu. Safeenah tayi harbi da bindiga. Auren Mu’azzam da Safeenar ya k’are yanzu ga Musaddiq ya bijiro da wani irin hali da basu saba ganinsa ciki ba dukda ya kasance mai gagara. A hankali Ta maida kanta cikin kujera tana ambaton Allah tareda rok’onsa ya tsare mata ahalinta.
Basu kuma ganin Musaddiq a gidan ba har dare. Sannan a daren Inne da tsiraru cikin dangi sukaima Sadiya rakiya zuwa b’angaren da tin kwanaki Innen Tasa aka gyarawa Mu’azzam da Safeenah.
**
Bugu biyu Mommy ta d’aga wayan Shemau, ko gaisawa basuyi ba tace “Ina sauraronki Shemau, fad’a mun meke faruwa.. Kun raka Karuwar Mu’azzam d’akinta ko k’ak’a..?”
Aunty Shemau ta nusa tace “Idan nice ke Aunty Hajara ba wann zan tambaya ba..”
Shaye da mamaki Mommy tace “Yo mai zan tambaya..? Ko Nuratu ce ta mutu kike shirin bani albishir..?”
Aunty Shemau ta nusa tace “Wann ai ba albishir zan miki ba.. Abin tashin hankali zan sanar dake.”
Wann karon mik’ewa tsaye Mommy tai tana girgiza kai take fad’in “A’a Shemau.. Na gaji da jin labarai marassa dad’i.. Kar dai kice mun nakasashiyar matar Marwan warkewa tayi..?!”
Aunty Shemau tace “Duk ba’a kansu bane..”
Cikeda k’osawa Mommy tace “Shemau ki daina tsinkar min da gaba ki sanar dani meke faruwa.. Marwan ne ya sake yo mun kishiya kokuwa..?”
Shemau tace “Duk ba’a kansu bane. Kan d’anki Musaddiq ne..”
Mommy Ta dafe k’irji tace “Na shiga uku ni Hajara mai ya sami Musaddiq..”
Aunty Shemau Ta murmusa tace “Babu abinda ya sami Musaddiq amma kiyi shirin biki dan Musaddiq ya sami mata a nan..”
Mommy ta girgiza kai tace “Ban fahimceki ba Shemau.”
Aunty Shemau tace fillanci kike so na miki sai kifi fahimta da kyau. Toh d’anki Musaddiq ya fad’a soyayya da mahaukaciyar yarinyar dake kawowa Nuratu magani..”
Mommy ta dafe k’irji tace “Na shiga uku ni Hajara.. Kiyi istigifari Shemau domin kuwa Ina raye Musaddiq bazai auri dangin bokaye da ‘yan bori ba.. Toh banda bak’in jaraba mai ya gani tattare da ita ya tsallake duk matan dake sonsa a nan Abuja.”
Shemau ta tab’e baki tace “Yo ina na sani.. Shawarin da zan baki Aunty Hajara tun wuri ki d’auke Musaddiq daga garin nan ya daina ganin yarinyar ta haka ne kawai za’a iya rabasu.”
Mommy na safa da marwa cikin d’aki take fad’in “Ta yaya zanyi haka Shemau bayan Kinsan halin wannan jarababbiyar tsohuwa..”
Aunty Shemau tace “Tun wuri ki nemowa kanki hanya, kiyi duk yanda zakiyi ki tabbata kin rabasu.. Dan ni duk bama wann ba muddin Musaddiq zai soyayya da yarinyar nan asirinmu tonuwa zai.. Ni babban tashin hankali na kenan..”
Mommy tace “Yo da na had’a iri da zuri’ar bokaye da bori ai gwara asirinmu ya tonu..”
Shemau tace “Lallai baki San abinda kike fad’i ba Hajara.. Wllhi wllhi bazan bari asirina ya tonu Mu’azzam ya jefani kurkuku ba.. Koda wasa kar d’anki ya mun sanadi.. Ni ba damuwata bace idan ma Jikanyar ifiritu zai aura.. Ni damuwata shine kar asirina ya tonu ehe.. Tun wuri kisan yanda zakiyi ki d’auke d’anki daga garin nan Ni zanji da yarinyar..!” Daga haka Shemau ta katse wayar a fusace.
Mommy tana kiran sunan Shemau ko tsayawa sauraronta batai ba ta datse kiran.
Hannu biyu Mommy Ta d’aura aka tana fad’in “Na shiga uku ni Hajara Musaddiq zai karni a tsaye.!” Cikin sauri ta shiga neman layin Musaddiq saidai bata shiga.
**
A b’angaren Sadiya kaw tinda akai mata rakiya zuwa b’angaren bata sanya angon nata a idanunta ba, har dare ya soma ja, Ta mik’e ta gabatar da sallar isha da batayi ba.
Tana nan zaune saman darduma taji alamun shigowarsa dan taji kaman tab’a k’ofar parlorn. Gabanta ya fad’i, bugun zuciyarta na k’aruwa.
Bata tashi saman darduman ba saima tsintar kanta da tai tana kuma gyara zaman tahiyar nata kaman dai bata sallame sallar ba.
Tanajin alamun bud’e d’aya k’ofar d’akin da yayi dan dama d’akuna biyu ne sai parlor da kitchen a section d’in.
Ya b’ata lokaci a d’aya d’akin tana nan zaune tamkar wacce aka dasata.
Jim kad’an taji alamun ana tab’a handle d’in d’ajin da take, bugun zuciyarta ya k’aru.. Sai k’irga yatsun hannunta take kai kace tasbihi take a zahiri alhali ita kanta bazatace ga tak’amaimen abinda take ba.
K’amshinsa shi ya rigayi muryarsa mata sallama. Ta lumshe idanunta a hankali tana mai amsar sallamar nasa can k’asa dan ba lallai bane ma idan yaji.
K’arasowa yai ya zauna bayanta yana jira Ta sallame.
Ita kaw tinda taji alamun ya zauna sai ta k’asa katab’us taci gaba da motsa ‘yan yatsunta da take.
Sosai suka d’auki lokaci haka, k’arshe gyaran murya yai kad’an yace “Madam a rage sauran addu’an mana muma mu samu..”
Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmusawa.
Shima d’in murmushin ne saman fuskara ya mik’e ya k’araso gabanta, ya zauna ya nad’e k’afafunsa irin zaman cin abinci. Lokaci guda ya mik’a hannayensa ya janye nata hannayen da ta rufe fuskarta dasu.
Da k’yar ta iya d’ago k’wayan idanunta tana dubansa. Yana sanye cikin jallabiya fara k’al irinta Larabawa. Shid’inma ita yake duba kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.
Sai kuma ta dad’a Murmusawa tana maida nata idanun k’asa.
“Mrs Mu’azzam Gamji.!” Ya fad’i yana dubanta still murmushin ne saman fuskarsa.
Bata amsa ba sann bata d’ago ta dubesa ba saima sakin kyakkyawan murmushi da take.
“D’ago ki kalleni. Ba wani bane ni ne nan Mr Inspector.. And we are going to push through with our mission right this moment..!” Ya d’an k’arashe a dake.
Ai bata San sanda ta d’ago tana dubansa a d’an tsorace jin yanda Yai maganar. Taga ya tsime yana dubanta, ya koma mata Mr Inspector data soma sani. Take tsoro ya wanzu saman fuskarta.
Ganin haka ya sanyashi sakin murmushi kad’an dan dama reaction d’inta yake son gani.
“Kar ki damu I promise you.. This will be the best mission ever.” Ya fad’i yana rik’o hannayenta cikin nasa.
“Tashi muyi sallah..” Ya k’arashe yana mai mik’ar dasu tsaye gaba d’aya.
Ta d’an d’ago ta dubesa kad’an a d’an shagwab’e tace “Ni fah nayi sallah..”
Ya jinjina kai yace “I know.. Zamu sake wani ne..” Ta sadda kanta kad’an sanda ya shige gaba dan yi masu limanci.
A natse ya daidaita tsayuwarsa ya tada kabbaran harama dan sallar nafila ba’a mata ik’ama kaman sallar farilla.
Cikin natsuwa ya jasu sallar suka sallaci raka’a biyu kaman yanda yazo a sunnah.
Bayan sun ida ya d’aura hannunsa na dama saman goshinta ya karanto addu’an neman alkhairi da tsari daga sharri.
Ya d’anyi gyaran murya kafin ya ambato sunanta cikin wane irin siga wanda ya kuma kashe mata jiki had’ida haifar mata da rauni.
Mu’azzam yaci gaba da fad’in “I have a lot to tell you wanda ba lallai daren nan ya ishemu ba.. Amma kafin nan Ina so kije wancan d’aki mai kallon wann akwai abinda zaki d’auko min cikin d’akin..”
Ta d’an dubesa kaman tana son rambayarsa mai zata d’auko masa sai kuma ta tuna jawabin Aunty Larai cewa kar Ta tab’a masa gardama kan abinda bai sab’awa shari’a ba. Ta yuwu wann assignment ya bata ba tareda ya fayyace mata ga abinda zata d’auko masa ba. Idan tana son cin assignment d’in Toh tayi abinda yace d’in without asking questions..
Kai tsaye ta jinina masa kai kafin ta nufi k’ofa kanta a k’asa. Zuciyarta sai tsinkewa yake tana tinanin mai zataje d’aukowa ba tareda ance ga abinda zaki d’auko ba.. Wann wane irin aike ne.
Sanda ta iso k’ofar d’akin tai k’ok’arin saita kanta kafin ta kama handle d’in ta murd’a da bassamalla. Saida tayi sallama kafin ta tura k’ofan d’akin.
Ga tsananin mamakinta takarda ta soma tuntub’e dashi an linke. Saman takardan an rubuta mission number 1.
A hankali ta duk’a ta d’auki takardan ta warware “I’m sorry.. Please forgive me.!” Murmushi tai kafin ta girgiza kai kad’an tana lumshe idanu.
Ta d’an k’ara gaba kad’an taji Ta taka wani takardan, Ta duk’a kad’an ta d’auka an rubuta mission no2 “Look up there.”
A hankali ta d’aga kanta tana duban center cikin d’akin. Nan taga an zagaye ginin da red roses k’anana tsakiya an rubuta I LOVE YOU. Hannayenta ta d’aura saman bakinta tana karanta kalaman a hankali cikin zuciyarta da kwanyarta. Tana nan tsaye tana kallon kalaman tana sakin murmushi siraran hawaye na gangaro mata taji sauk’an hannayensa saman kunkuminta zuwa cikinta. Ya rank’wafo da kansa saitin b’angaren kunnenta na dama kafin ya furta a hankali “Do you like my surprise..? Are you ready for mission number3..?” Yai maganar yana mai karkatota suka fuskanci juna.
Sai lokacin ta kula da sauran abubuwan da ya shirya cikin d’akin.
Saman gadon an jera red roses an zana tambarin heart dasu. Gefe kuma kujeru ne guda biyu k’aramar table a tsakiya kaman d’ai coffee chairs. Saman table d’in harda candles maimakon champagne kwalin fresh milk ne sai glass cups guda biyu saiko faranti mai d’aukeda gasasshiyar kaza.
Ta saki murmushi kad’an kafin ta saci kallonsa tace “You did all this..?”
Ya jinjina mata kai yana mai dubanta “For my Beautiful Queen.” Ya bata amsa yana mai kuma rik’o hannayenta cikin nasa.
Ta d’an rausayar da idanunta kafin tace “Inspector.. Are we on a date..?”
Janyota yai cikin jikinsa idanunsa tar akanta “We are on a mission..” Yai maganar yana mata wasu salo masu kashe mata gabb’an jikinta. Ta soma k’ok’arin zamewa daga nasa jikin.
Ya saki murmushi a hankali yana dubanta kafin ya rage hasken d’akin sai hasken candles dake saman table d’in kake iya gani.
Ta d’an zaro idanu waje alamun tsoro. K’arasowa yai ya kuma kamota kafin ya rad’a mata “I’m with you Babu abinda zai sameki.. Nasan kina tsoron duhu..”
Ta saki murmushi a hankali kalan k’aunarsa na kasheta. Ta mance komai bata gani komai sann bata ganin kowa a duniyar sai su biyu.
Hannunta ya kamo suka k’araso wajen table d’in. Yai saurin janyo mata kujera yana fad’in “Allow me..” Ta saki murmushi kad’an tana kashesa da wane irin kallo kafin ta k’arasa ta zauna.
Zama shima yai ba tareda ya janye idanunsa daga kanta ba.
Ya soma zuba mata fresh milk d’in a cup yana fad’in “Allow me to take care of you tonight.” Ya k’arashe yana mai mik’o mata cup d’in kusan bakinta.
D’an rau rau tai da idanu had’ida langab’e kai “Inspector nifa na k’oshi..”
Ya tsareta da idanu yace “Do you want to fail this mission tin kafin ki fara..?”
Ta kuma marairaice masa fuska.
Cikin sigan lallashi ya d’aura hannunsa guda saman nata yana kuma kai cup d’in kusan bakinta yana fad’in “Yi hak’uri kad’an zaki sha.. You know you can’t go to bed without eating anything... Oya drink it now..!” Ya k’arashe yana shafa tafin hannunta a hankali alamun lallashi. Nan ko tasha ya kuma bata naman ma Ta d’anci kad’an. Zallan k’aunarsa yake nuna mata.
Daga bisani ya mik’e tsaye ya mik’a mata hannu guda yace “May I have this dance.?” Yai maganar yana mai d’an rank’wafowa kad’an.
Ta d’an marairaice idanu kad’an tana dubansa “But I don’t know how to dance Inspector.”
Ya saki miskilin murmushi kafin yace “I don’t know either.. I guess I just want to have my first dance in history with you..”
Ta murmusa kad’an kafin ta mik’a masa hannunta ya d’agota.
Hannunta guda cikin nasa ya kuma kamo d’aya hannun nata ya d’aura saman chest d’insa yanda heart d’insa yake kafin ya sakalo kunkuminta da d’aya hannun nasa. A hankali yake motsasu yana kallon fuskarta yayinda Sadiya ke duban k’irjinsa yanda hannunta guda ke bisa. Tana iya jin bugun zuciyarsa na ratsa tafin hannunta zuwa jijiyoyin jikinta.
Gaba d’aya ji tai Ta gaza sakewa, a hankali ta kwantar da kanta saman k’irjinsa had’ida lumshe idanunta.
Muryarsa Ta sinkayo yana fad’in “Something is missing..”
Bata iya d’agowa ba bata iya furta koda kalma ba sabida yanda tai Lami cikin k’irjinsa tamkar wacce aka zare ma laka.
Ya d’an kwanto da kansa saitin kunnenta yace “Sing a song for us..”
Kaman wacce aka mintsila Ta bud’e idanunta, sai kuma ta girgiza kai tace “Ban iya ba fah.”
“Gashi nima ban iya ba, ya kenan za’ayi..? Wait kece yarinya.. Ke kika iya wak’ok’in zamani. Oya sing one for us.”
Ta marairaice fuska tace “Da gaske ban iya ba, saidai kai kayi..”
Ya d’an murmusa kad’an yana mai kuma kwantarta cikin jikinsa “Ai ban iya na zamani ba.. Saidai outdated ones na zamaninmu..”
Ta murmusa kad’an kafin tace “Inaso naji na zamaninka..”
Ya kuma murmusawa kafin yace “Come here..” Ya kwantar da kanta saman k’irjinsa, suka d’ibi lokaci a haka kafin can ya soma furta
_”If our love was a fairy tale
I would charge in and rescue you
On a yacht, Baby, we would sail
To an island where we’d say I do_
-And if we had babies they would look like you
It would be so beautiful if that came true
You don’t even know how very special you are_
Muryarta ya sinkayo daga nan yanda kanta ke bisa k’irjinsa tana furta
_You leave me Breathless
You’re everything good in my life
You leave me Breathless_
Ya saka hannunsa guda ya d’ago hab’arta kafin ya furta
_I still can’t believe that you are mine._ lokaci guda ya manna mata light kiss saman lips d’inta.
Ya tsareta da idanu yace “Ina kika iya wak’ar..?”
Ta murmusa kad’an cikeda kunya tana tura kanta cikin k’irjinsa.
Shauk’in k’aunarta na fuzgansa ya kuma kamo hab’arta ya tsareta da idanu yace “Did you mean what you said.. That I’m everything good in your life..?”
Ta d’ago a hankali tana dubansa kafin ta jinjina masa kai alamun eh.
Rungumeta yai cikin jikinsa yana fad’in “Allow me to show you how much you mean to me please Saady..” Yai maganar yana kuma rikitata. Daga yanda yake jin yanayinta ya fahimci tsananin tsoron yanayin da ta tsinta kanta ciki. Murya can k’asa yake furta “I promise I’ll be gentle.. And this mission will be the best of my all missions..” Yana ida fad’in haka ya rufe bakinta da nasa cikin nuna shauk’I na k’auna.
Tabbas wann mission d’in yasha banban da ko wanne, kaman yanda yace he’d be gentle bashi ya hanata jin jiki hannunsa ba.. Inspector bai farga da aika aikan da yai cikin mission d’in nasa ba saida ya maida stubborn head d’insa cikakkiyar mace. Kuka da raki kam yashasa wann daren. Haka ya dinga aikin lallama da lallashi kaman ya d’auketa ya goyata bayansa haka yakeji. Duk wani gyara da Aunty Larai tai mata saida Inspector ya