Showing 129001 words to 132000 words out of 209154 words

Chapter 44 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3086

da k’unci..!” Yana ida fad’in haka yasa ya fice.

Daddy da ya rapka uban tagumi yabi bayansa da kallo har ya b’ace masa.. Meke shirin faruwa da ahalinsa ne..? Mene abubuwan da suke faruwa.. Yanzu Hajara saida ta bak’anta Mu’azzam wajen D’anuwansa Musaddiq.. Yau shine Musaddiq ke masa barazana har yana cewa zai sanar da Mu’azzam tattaunawar da yaji sunayi da Salman.. Lallai shaid’an ya shigo masa kan ahali.. Bazai bari ahalinsa ya tarwatse ba.. Jiki babu k’wari Daddy ya mik’e ya haura sama. Ya shirya tsaf kafin ya sauk’o ya nufi b’angaren Musaddiq.

Zaune ya tadda Musaddiq d’in hannunsa rik’eda pills yana k’ok’arin afawa bakinsa sai sakin huci yake.

Daddy ya k’arasa da sauri ya buge hannun Musaddiq k’wayan suka watse k’asa.

Cikeda tausayawa Daddy ke duban Musaddiq d’in.. Ya shiga girgiza kai yana duban yanda Musaddiq ke hawaye cikin tsananin k’unan rai.

Daddy ya girgiza kai yace “Akan abinda ya faru shine kake k’ok’arin maida kanka ruwa Musaddiq..? Maiyasa..? Akan na samu matsala da mahaifiyarka..?”

Musaddiq baice komai ba Sai hawayen dake ci gaba da fitowa daga idanunsa.

Daddy yaci gaba da fad’in “Musaddiq mahaifiyarka ce ta turoka ka rama mata abinda bai mata.. Shin Ita tace kazo kamin rashin kunya abinda ba d’abi’arka ba..?”

Musaddiq ya d’ago idanu masu zuban ruwa yana duban Daddy “Mahaifiyata ce Daddy.. Kuma dole nabi bayanta a lokacin da ahalin da take tink’aho dasu suka guje mata.. Daddy Menene matsalar Ahalin nan..? A koda yaushe matsalar guda d’aya ce shine Mu’azzam... Baga kai ba baga Inne ba.. Duk Kun d’auki son duniya Kun d’aura masa.. Shin Daddy mu ba ‘ya’ya bane.. Why always him..?” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.

Shiru ne ya d’an biyu tsakani kan Daddy a k’asa, kafin ya girgiza kai yace “Kar ka bari Shed’an ya sanya maka hassada cikin zuciyarka d’ah na.. Ba haka abun yake ba.. Banfi son Mu’azzam ba, dukanku Ina sonku daidai gwargwado.. Haka Inne ma na tabbata tana k’aunarku gaba d’aya.. Idan kaga anfi son wani ba shi d’in akafi so ba kyawawan mu’amalarsa da d’abi’unsa ake so.. Zuciya tana son abu mai kyau ne Musaddiq ba gurb’atacce ba.. Kai shaida ne lokacin da ka koma Fufore da yanzu ka duba Alak’arka da Inne kasan akwai banbanci.. Inne tana nuna maka asalin k’aunarta gareka a halin yanzu.. Ashe ba kaid’in bane bata k’auna.. A’a so take ka gyara d’abi’unka shiyasa take nuna tsauri akanka..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Musaddiq duk abinda nakeyi ba inayi bane don Mu’azzam.. A’a inayi ne domin ahalinmu.. Ko wani ahali sunada nasu k’alubale da suke fuskanta amma bana fata Allah ya jarabcemu da k’alubale na tarwatsewar ahali ko gaba mai muni ya shigo tsakani wanda wasu lokutan zaka samu ya shafi har ‘ya’ya da jikoki.. Musaddiq sabida wannan dalilin naketa k’ok’arin naga kan ahalinmu bai tarwatse ba.. Sannan na tabbata mahaifiyarka bata sanar dakai mai Ta aikata ba.. Amma naji dad’i da baka sani b, kuma bana so ka sani.. Sannan koda bakace naje na dawo da Hajara ba zanje na dawo da ita dukda cewa ita ta sallami kanta bani na sallameta ba..” Ya mik’e yana gyara tsayuwarsa still idanunsa kan Musaddiq d’in.

Daddy ya d’an kuma gyaran murya kad’an kafin yace “Ya kamata ka koma Fufore, zamanka a nan bazai haifar maka da komai ba illa ya kuma maidaka cikin Rayuwar da ka riga ka baro a baya..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige.

Musaddiq yai saurin ambato sunansa.

Daddy ya juyo yana dubansa.

Ya k’araso yana sadda kansa k’asa, a hankali ya furta “Kai hak’uri Daddy ka yafe mun..”

Daddy ya saki murmushi kafin ya d’an buga kafad’an Musaddiq kad’an yace “Babu komai Abubakar Allah shi maku albarka gaba d’aya.” Daga haka Sa kai Daddy yai ya fice ya nufo k’asa ya shiga motarsa dan already driver d’insa ya tafi, da kansa ya tuk’a motar ya tafi d’auko matarsa dake gidan Hajiya Faty.

**

FUFORE


Aunty Shemau Ta dubi mijinta dake zaune gefen gado yana duba wasu takardu.. Lokaci guda ya d’ago mata takardun yace “Takardun irin wad’annan ne.. A gabana Yayana Abubakar ya saka hannu cewa baison k’wandala na Kampanin, kuma zaiyi resigning daga wannan ranan.. Zai nemi nasa daga scratch..”

Aunty Shemau Ta girgiza kai cikin rashin fahimta kafin yace “Amma Maiyasa zai haka bayan Dukiyar nan mahaifinku ne ya bar maku..”

Murmusawa Uncle Salman yai kafin yace “Bakisan kalan Zuciyar Yayana Abubakar ba, yana da matuk’ar zafin zuciya da gudun duk abinda zai kawo masa magana ko raini..Yanda kika ga D’ansa Mu’azzam haka yake.. Maganganun da nake jifansa dasu kan cewa yayi tsaye akan dukiyar mahaifinmu yana son ya handame komai shiyasa yak’i barina na girma a Kampanin wann kalaman su suka tunzurasa yace na basa takarda da alk’alami ya saka hannu cewa daga wannan ranan baya buk’atar ko k’wandala na daga abinda mahaifinmu ya bar mana sannan zai tashi ya nemi nasa bazai kuma dogaro da abinda aka bar mana ba.. Shemau wad’annan takardun nake nema wanda D’anuwana Marwan ne ya b’oyesu na tabbata.. Sabida bayan rasuwar Yayanmu da aka Zo ana maganar rabon Gado sai cewa yayi babu yanda za’ayi a cire iyalan Yaya cikin Company.. Ni kuma sai na sanar dashi ga abinda Yayanmu yayi ya rubuta cewa baya son k’wandala amma sai Marwan yace “Gado Allah ne ya riga ya raba abunsa.. Ko Yaya yana so ko baya so yanada gadon mahaifinmu tunda mahaifinmu ya rigarsa rasuwa, sannan kasonsa za’a dinga bawa Iyalansa koda basa so... Bazai tab’a yarda da wannan yarjejeniyar ba kuma bazai bari na raba mana kan ahali ba.. Kinga idan na samu takardun nan ni kuma zan kai Kotu na tabbatar cewa iyalan Yayanmu basuda gado dan mahaifinsu shi da kansa ya ciresu daga cikin gadon.. Harma yayi furuncin idan inason nasa kason na had’a gaba d’aya shida Iyalansa basa kwad’ayin wannan dukiyar.. Kinga kuwa ai Shemau baki shi ke yanka wuya.. Zafin ransa ya jawo yayi wannan rubutun ya cire iyalansa daga cikin Dukiyarmu.. A yau idan na sami takardan yajejeniyar nan zan tafi Kotu kuma dole a daina cire kason su Mu’azzam a cikin Company dan Ubansu da kansa ya ciresu.. Balle ma Mu’azzam idonsa baya kan dukiyar na tabbata Marwan shima amfani yai da wanann damar yake handame nasu kason dan har yau bai d’aura Mu’azzam a hidimar Company ba.. Sannan shi Mu’azzam d’in idanunsa baya kan dukiyar sam.. Dan da alama Mu’azzam bai rage wa mahaifinsa komai ba na rashin son abun Duniya..”

Aunty Shemau ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Tabbas Dukiya Itace mafi munin bala’i ga D’anadam a doron k’asa, za’ayi tsafi sabida a sameta, a kashe rai duk dan a sameta.. Za’ayi komai domin a tarata a GIDAN ARO.. Gidan da sam ba tabbata za’ayi ba balle a cinye abinda aka tara..”

Uncle Salman ya d’an dubeta yace “Mai kikace..?”

Ta d’an tab’e baki kad’an kafin tace “Toh ni meye role d’ina a wasan Naka daka sa na shiga jikin Hajara na samu yarda da amincewarta..?”

Uncle Salman ya murmusa kafin yace “Ai kaman yanda kikace Dukiya itace mafi munin fitina ga D’anAdam a GIDAN ARO.. Kin manta wani abu guda d’aya wanda tare suke tafiya kunnen doki suke..”

Aunty Shemau ta dubesa da mamaki kafin tace “Mai kenan kake nufi..?”

“Mata..!” Ya bata amsa kai tsaye.

Kafin yaci gaba da jinjina kai yana furta “Kud’i da mata tare suke tafiya.. Idan muka samu yardar matarsa Kinga mun samu kansa cikin sauk’i itace kawai wacce Ta hanyarta zamu iya samun wad’annan takardun..”

Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai tana tinanin yanzu idan bata samu takardun nan Ta wajen Mommy ba. Hardai Alhaji Marwan ya fahimci ta taimakawa Mommy Sun d’auko wa matarsa mai rufa ido da sunan mai gani shikenan kashinta ya bushe Ta tabbata Mu’azzam jefata zai gidan yari ya kulleta.. A b’angare guda Mommy zata gane da biyu Ta shiga jikinta kenan dan Ta cimma burin mijinta na samun wad’ann takardun masu mahimmanci.. Kenan fah Ita tayi b’atan b’akatantan fah kenan.. Babu nan babu can.. Lallai tun wuri gwara tasan alk’iblarta..

**

ABUJA


Yai tsaye yana duban yanda Safeenah Ta tak’ure cikin pillow tana bacci bayan ta gama cin kukanta. Ta zab’esa akan mahaifiyarta, shin wacce Ta zab’i zama dashi akan mahaifiyarta zata iya kashe masa ‘yaruwa..? Toh amma Maiyasa ahalinsa suketa shigowa cikin binciken nasa.. Kodai ahalin nasa ne zai bincika..? Kodai akwai abinda ke rufe cikin ahalin nasa bai sani ba..? Kai a’a wannan wasannin Danger ne.. Bazai tab’a zargan ahalinsa da aikata mummunan laifi irin wannan ba.. Toh amma...Zaici gaba da bincikensa daki daki har ya gano komai..

Ya k’arasa saman gadon nata ya zare pillow d’in yai mata matashi da k’irjinsa..

Safeenah da ba bacci take ba dama da taji shigowarsa ne Tai likimo kaman mai bacci nan ta saki ajiyan zuciya tana mai kuma shigewa jikinsa.. Plan d’inta yayi aiki dan tasan yanzu kam dole Mu’azzam ya koya ma kansa sonta koda bayayi tinda har Ta zab’esa akan mahaifiyarta.

Turarrukan data shafe jikinta dasu wanda Aunty Shemau Ta bata sun taimaka sosai wajen kai Mu’azzam wata duniyar.. Dukda cewa idan ya rufe idanunsa ba Safeenar yake hangowa ba.. Sadiya yake hangowa suna raya wannan duniya mai tsafta tare.. Cak ya d’auki Safeenah suka nufi nasa d’akin yana nuna mata salon k’aunarsa wanda Ta jima tana mafarkin samu daga garesa.

A b’angaren Mu’azzam kaw tin daga hanya ya fahimci akwai banbanci da lokacinda ya tasamma kusantar Sadiya.. Tabbas ba d’aya suke ba.. Abinda zuciyarsa Ya raya masa kenan.. Toh mai hakan yake nufi..? Safeenah tasan maza ne Ta saba da maza kokuwa..? Amsar da ya gaza bama kansa har komai ya lafa.

Yai mata K’uri yana dubanta, duk sai tasha jinin jikinta dukda cewa bai furta mata komai ba..

Kukan da batayi tun daga farko ba shi ta fara bayan al’amra Sun lafa. Cikin kuka take furta “I’m sorry my Halal..”

Ya dubeta da mamaki kafin ya girgiza kai yace “Why are you apologizing.. Maiyasa kike bani hak’uri.?”

Safeenah Ta kuma sadda kanta kafin tace “Ko baka fad’a mun ba fuskarka ya nuna my Halal.. You are disappointed.. And believe me I feel ashamed..”


Mu’azzam ya kuma girgiza kai yace “I still don’t get you Safeenah.. Stop beating around the bush.. Ki fad’a mun menene..?”

Tasa bayan hannunta ta share hawayenta kafin tace “Lokacin ina Salford friend d’inmu Ta gayyacemu birthday party d’inta.. You know yanda parties suke kasancewa a k’asashen turawan nan.. Wllhi banyi niyyan zuwa ba friends d’inmu suka tak’ura man na bisu.. Shine boys d’in sukai drugging namu suka sanya mana k’waya cikin drinks sukai raping d’inmu.” Kuka ya kuma kufce mata tana fad’in “Amma wllhi daga ranan ban kuma zuwa parties ba koda birthday ne.. Please forgive me My Halal na kasa kare maka kaina.. Naje Party an k’eta mun haddi..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka.

Dukda cewa haka kurum baiji zuciyarsa ya aminta da zancen Safeenah ba Sai ya fuzar da fuci kad’an da yai, ya d’an kauda fuskarsa gefe na d’an lokaci kafin ya soma fad’in “Laifinki d’aya na zuwa Party da maza. Da bakije ba watak’ila da abinda ya sameki bai sameki ba.. Shi kamun kai ya shafi mutanen da kike mu’amala dasu, wajajen da kike halarta da kuma yanayin shigarki.. Yanda kikai appearing ma mutane haka zasuyi addressing naki.. Na tabbata abokan ku na wajen Partyn zasuyi tunanin kuma irinsu ne shiyasa kuka d’ibi k’afafu kukaje irin wann wajen hardai sukai abinda sukaga dama daku.. Allah ya ganar damu baki d’aya ya hanemu aikin danasani.”

Yana ida fad’in haka ya mik’e ya nufi bathroom ya bar Safeenah nannad’e cikin bedcover tana ci gaba da matsan k’walla nata wautan ita a dole yau tayi dabara ta tsara zance ba tareda taimakon Meema ba kuma Mu’azzam ya yarda.


Haka ya tsarkake jikinsa ya fito daga bathroom d’in tana nan kwance, duba d’aya yai mata yace Ta tashi taje tai wanka. Babu ko irin tarairayan nan da ake ma ko wacce amaryar da takai mutuncinta da Martabarta.

Safeenah Ta d’an turo baki tace “Gaskiya ni bacci nakeji zanyi da safe..”

Mu’azzam ya girgiza kai yace “A’a bazaki kwana mun a gado haka ba.. Saidai kuma idan zaki tafi naki d’akin..”

Badon taso ba ta mik’e tana ture turen baki Ta shige bathroom.

Bai kuma bi takanta ba yai kwanciyarsa zuciyarsa na muradin sake kasancewa da Sadiya.

**

Washe gari Safeenah batasan ficewarsa ba tanata sharan baccinta, tasan dai ya tada Ita sallar asuba. Tun kafin ya dawo daga masallaci ta kuma hayewa gado tai kwanciyarta. Ba ita ta farka ba sai wajajen k’arfe 8:30am. Ta shafa taji baya kan gadon Ta kuma lumewa cikin gadon tana mai canza position d’in kwanciyarta dan tasan definitely office ya tafi. Tasan sa da bama aikinsa mahimmanci.


Shiko Mu’azzam tinda ya fice asibiti ya soma biyasa ya duba jikin Assad kafin ya nufi foundation.

Sadiya na kitchen tana taya Aunty Larai da wasu ayyukan Ta sinkayo muryar Habeeb yana fad’in ga Uncle Cop.

Cak ta daina abinda take jin k’anina nata na shelan zuwan Mr Inspector.




SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*43*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*









Tana jinsu dasu Aunty Larai suna gaisawa Ta kasa fitowa daga kitchen d’in saima tambayar kanta da take “Toh mai yake a nan da sassafen nan..?” Bata kaiga nemo amsar ba Habeeb ya shigo rik’eda bindigar wasa ta roba yana fad’in “Aunty Sadiya Uncle Cop yace Wai yana kiranki.. Kinga bindigata da ya kawo mun.. Zanyi chasing bad guys nima..” Ya k’arashe yana saitata da bindigar.

Fuzar da huci tai kad’an kafin tace “Shida waye a parlorn.?”

“Shi kad’aine yace yana jiranki..” Ya bata amsa yana ci gaba da wasansa.

“Alright je ka kawo mun hijab d’ina..” Batakai aya ba Aunty Larai Ta shigo fuska fal fari’a tana fad’in Yauwa had’a ma mijin naki abin kari.. Yana parlor yana jiranki..”

Sadiya ta d’anyi rau rau da idanu ba tareda tace komai ba, ta lura wannan Matar tak’ura wa rayuwarta take son yi.. Akan dole tai abinda ta umarceta kafin tazo zata shige.

Aunty Larai ta tareta “Ina kuma zakije.?”

“Zan d’auko mayafi ne..” Ta bata amsa kai tsaye.

Murmushi Aunty Larai tai tace “Yo banda abinki Sadiya mai gida fah akace.. Yo wane irin mayafi..? Wa yafi cancanta yaga kwalliyarki sama dashi, ai ko mu bamu kaisa cancanta ba.. Jeki abinki haka ni bana San wani k’auyanci.”

Ta had’iyi miyau da k’yar kafin ta d’auki farantin tana mitan tak’ura mata da wannan matar tai cikin zuciyarta.

Yana zaune saman kujera kansa kife yana aikin shafa waya Ta hangesa.. Kaman yasan shi take kallo ya d’ago idanunsa, Ya jima yana dubanta yayinda ta sadda kai k’asa taci gaba da takowa sallama saman bakinta.

Murmushin da ba lallai ka fahimta ba saman fuskarsa yake dubanta har ta k’araso cikin parlorn. Ta dire tray d’in ba tareda tace komai ba.

“Good morning..” Ya fad’i yana dubanta.

Bata amsa ba sai k’ara masa sallama da tai cikin ranta tana fad’in mutum kaman goyon yahudu.

Ya amsa mata sallamar . Yana kasheta da wani irin kallo wanda gaba d’aya ya hanata sukuni.

Ta lura ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta. Alla alla take ta tashi ta bar wajen. Ta warware d’ankwalin dake kanta ta d’an yafa zuwa kafad’arta tana fad’in “Emm.. Aunty Larai tace na kawo maka breakfast..” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa.

“Wait..” Ya dakatar da ita da fad’in haka kafin yaci gaba da fad’in “Shikenan kuma sai ki tashi ki tafi.. Haka akeyi a garinku.. You haven’t even served me”

Ba tareda ta kuma cewa komai ba Ta dawo da baya ta duk’a ta zuba masa abincin.

“Don’t go until I say so..” Ya fad’i yana zuba sugar cubes a cikin tea.

Ya tsareta da idanu kafin ya d’auki mug na tea yana kurb’a. Wane b’angaren take duba ba shi d’in ba.

“You look good..” Ya fad’i yana dubanta.

“Thank you..” Ta basa amsa cikeda k’osawa murmushin da za’a iya kiransa da yak’e saman fuskarta. Lokaci guda ta kuma d’aure fuskar tana mai duban wani b’angaren.

Ya d’auki fork kafin ya janyo chips da liver sauce dake cikin bowl ya soma ci a hankali still idanunsa akanta “This food is delicious.. You made it..?”

D’an gyara murya tai kafin tace “Well, actually yes.. But only the sauce.”

Jinjina kai yai kad’an kafin yace “So you can cook like this..? I thought zama a gaban motar samari kawai kika iya..” Yai maganar yana cin abincin ba tareda ya dubeta.

Ta had’iyi maganar nasa tana mai kauda fusk. Saidai ba shid’inba bazai zauna bai yab’a mata magana ba. Wai ya zaci zama gaban motar samari kawai ta iya tsaban wulak’anci. Babu wanda ya kuma tanka kowa cikinsu saima cin abincinsa da yake peacefully.

Ya d’anci da yawa kafin ya d’auki tissue yana goge bakinsa.. Daidai lokacin wayarsa Ta soma ruri.

Ya d’aga yana murmushi ganin Inne ce mai kira. Saidya tanaji yanda yake fira gwanin ban sha’awa da Kakarsa.. Tanata mamakinsa dan Ita sam batai zaton na magana haka ba.. Koda yake Ta lura da selected people yakeyi dan ta kula sosai sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu shida Habeeb. Tana tsaka da tinanin ta sinkayo Muryarsa yana fad’in “Alright Inne.. Zan fad’a mata cewa kina gaisheta..” Ya kuma murmusawa kafin yace “Soon zan kawo maki ita in sha Allah..” Daga haka sallama sukai kafin ya dubi Sadiya da Ta b’ace shiru tamkar bata a wajen.

“Inne tace tana gaisheki.. And she wants to meet you soon..”

“Inne..?” Ta fad’i tana dubansa.

Jinjina mata kai yai yace “She’s my Grandmother.. Tace inada sa’a nayo mata kishiyoyi har biyu lokaci guda.” Yai maganar kaman ba daga bakinsa barkwancin ya fito ba.

Murmushi ne ya kufce mata wanda yafi kama da yak’e kafin tace “Amma ka mance baka fad’a ma Inne ba.. Cewa you create your own luck yourself.. And aurenmu na mission ne.. Ba mai d’orewa bane..”

Shiru yai yana dubanta kafin ya gyara zamansa yace “Look here.. Kalleni..” Ya fad’i yana tsareta da idanu.

Dukda gabanta dake tsananin fad’i hakan bai hanata k’ok’artawa Ta juyo tana dubansa ba. Sai kuma ta sadda idanunta a hankali tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa.

“Sadiya..” D’agowa tai tana dubansa for the first da taji ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da zata ce Ta tsinci kanta cikin yanayi mai wuyan fasaltuwa.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “We’ve been wearing each other out for quite some time now.. I don’t want to have another stressful conversation with you..I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login