Showing 150001 words to 153000 words out of 209154 words
hakan.
Inne ta dubi Sadiya tace “Tashi maza kije koh.. Idan kina son wani abin ki fad’awa Hindu kinji koh.. Ki saki jikinki nan gida ne kinji koh..”
Sadiya ta sadda kanta tana mai amsawa da “Toh Inne..”
Tana tafe yana binta da Kallo har ta b’acewa ganinsa. Inne na hankalce dashi.
Ganin Inne shi take duba ya d’an sanyashi sosa kai kad’an.
“Mu’azzam..”
“Na’am Inne..” Ya amsa yana dubanta dan tinda yaji batace Modibbo ba ta kirasa da sunansa kai tsaye yasan magana ce mai girma zata masa.
Inne ta juya ta nufi parlor tana fad’in “Biyo ni muyi magana.”
Babu musu ya mik’e yabi bayanta.
A nan parlorn Aunty Nuratun suka zauna, Inne ta tsaresa da idanu.
Ya d’an sadda kansa kad’an ba tareda yace komai ba.
“Magana nake so muyi kan Safeenah..”
Yanajin ta ambaci Safeenah a ransa yace anzo wajen.
Inne taci gaba da fad’in “Safeenah ta kirani tana kuka.. Kasan bana d’aukan shashashancin Safeenah amma abinda ta sanar dani cikin waya ya matuk’ar d’aga mun hankali had’ida bani mamaki.. Mu’azzam kana cikin hankalinka zaka furta kalmar saki wa matarka kuma ‘yaruwarka a cikin gidan Mahaifinta.. Gaban mahaifiyarta da kowa nata dan kawai kayi sabon aure..? Babu wanda zai hanaka aure kuma babu wanda zai hanaka d’aukar matarka ka tafi da Ita yanda kake so.. Amma Safeenah tace mun kan kawai tace itama sai ta biyoka shine ka furta cewa ka saketa saikace wata ‘yar tsana.. Haba Mu’azzam saki fah ba k’aramin abu bane.. Ba’a wasa da saki.. Cikin gidan nan kaf wa kaga ya taso yana haka.. Mu ba’a mana wannan shaida ba. Mata hak’uri ake dasu, sabida Kai namiji ne tinanin ka da nasu ba zaizo d’aya ba. Sannan koda mace ta buk’aci saki bazaka biye mata ba.. Dan idan aka biye na mata sai a sakesu sau d’ari musamman idan akan kishiya ce.. Modibbo kishi nada matuk’ar zafi wanda ba Don Allah ne ya hukunta hakan ba kanajin akwai macen da zata amince mijinta ya zauna da wata ce.. A al’amari irin na aure dole a kula da irin haka musamman duba da yanda Kayowa Safeenar wata mata a tsakanin k’ank’anin lokaci.. Banji dad’in abinda ka aikata ba kuma ban amince ka aikata hakan ba saida nasa Safeenah ta bani Hajara a waya ta sanar dani K’warai anyi haka dan kasan bana yarda da wautan Safeenah..” Ta k’arashe cikin b’acin rai.
Tinda ta fara magana kansa ke a k’asa. Saida ya bari ta ida kafin ya d’ago yace “Inne kiyi hak’uri.. Nasan bakiji dad’i ba kuma banso Labarin ya riskeki a irin haka ba.. kiyi hak’uri Inne..” Ya k’arashe cikin kwantar da murya.
Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Inne basu sanar dake gaskiyar abinda ya faru ba.. Quite alright na saki Safeenah amma basu sanar dake yanda al’amarin ya kasance ba..”
Inne ta dubesa a d’an karkace kafin tace “Watau dai da gaske dai kayi sakin..”
Mu’azzam ya jinjina kai a hankali kafin yace “Nayi amma ba wancan dalilin da Safeenah ta sanar dake bane ya sanyani yin sakin.. Inne ban saki Safeenah dan nayi wani aure ba sann ban saketa dan zan d’auko Sadiya na taho da ita nan ba..”
Inne ta katsesa da fad’in “Kana nufin k’arya sukai maka kenan..?”
“Kusan haka Inne..”
Inne ta girgiza kai tace “Wai meke faruwa ne Modibbo..?”
Mu’azzam ya gyara zamansa kad’an yana fad’in “Ni banso kiji wann labarin ba.. Dan nasan zai tada miki hankali ne kawai.. Amma tinda ita Safeenar ita ta kiraki ta sanar dake, kuma hakan na nufin ita ta zab’i kiji, zan sanar dake duk abinda ya faru Inne..”
Inne ta gyara zama tana saurarensa.
Tiryan tiryan Mu’azzam ke karanto mata dik abinda ya faru.. Tin daga kulle masa k’ofa da Safeenah tai wanda hakan ya hanasa shiga ya sanar mata tafiyar nasa balle yai mata sallama, har d’auko bindigarsa da tai taima Sadiya barazana da rayuwarta harde da munanan kalaman da ta dinga ambatonsa dashi har dai zuwa harba bindigar jikin garu da Safeenah tai zuwa zab’i data basa tsakaninta da Sadiya.. Ko abu guda bai b’oyewa Inne ba sai zuwan Mommy gidansa da tai tace sai ya saki Safeenah shine kawai bai sanar da Inne ba dan har wannan lokaci Kallon Uwa yakewa Mommy dan yasan ko mai Mommy zata masa bazai tab’a biyan d’awainiyar da sukai masu ba daga ita har Daddy musamman akan mahaifiyarsa. Sam baijin zai iya tozarta Mommy koda mai zata masa.
Inne da take jin abun, shaye da mamaki take dubansa “Safeenah tace da bindiga zata harbi mutum..?”
Mu’azzam yai shiru baici komai ba dan dama ba’a sanar da Innen ba lokacin da aka kama Safeenah ta zama suspect na mutuwar Ikram.
Inne taci gaba da fad’in “Ikon Allah.. Abu kaman a cikin shirin wasan kwaikwayo... Kuma waima duk Ina shi Marwan d’in ake wann rashin hankalin cikin gidansa..?”
Mu’azzam ya girgiza kai yace “Daddy baya gida shima dawowa yai ya tadda al’amarin..”
Inne ta jinjina kai tace “Yanzu a gidan Marwan ake wannan rashin hankalin.. Ita Safeenah ba’a wauta ta tsaya kawai ba abin nata harda hauka ne..? Wann ai Ba abin yin shiru bane abin a nema mata magani ne dan batada hankali bamu San mai zata aikata gaba ba..”
Mu’azzam ya girgiza kai yace “Inne da hankalinta tasan abinda take.. Attention take nema as always.”
Inne ta jinjina kai tace “Eh Lallai.. Safeenah da harba bindiga..?” Tai maganar tana kuma jinjina lamarin.
Sauk’e ajiyan zuciya yai kafin yace “Inne ki kwantar da hankalinki komai ya shige.. Safeenah bazata sake barazana ma wani da bindiga ba.”
Tsegege take dubansa kafin tace “Idan aka barta gaba sakewa zatai, zan kira shi Marwan d’in naji wani mataki ya d’auka kan haukar Safeenah.. Asibitin mahaukata zai kaita ko ajeta zai a gidansa.. Dan idan a gidansa zai barta gwara ya kawo mun ita nan a sakata a mari da turu ehe..!”
Girgiza kai Mu’azzam yai yace “A’a Inne kar ki kira Daddy please, nasan yanzu haka bayan abinda Safeenah tai gaba d’aya hankalinsa ba’a kwance bane.. Banso hankalin Daddy ya kuma tashi.”
Ta tsaresa da idanu kafin ta murmusa kad’an tace “Kai da Marwan kuna matuk’ar son juna.. Ina Farin ciki da matuk’ar alfahari da hakan.. Badon bansan mai ke rufe cikin zuciya ba da Sai nace kai kafi soyuwa a gareshi sama da nasa yaran.”
Musaddiq dake k’ok’arin shigowa parlorn fasa shiga yai sakamakon abinda ya sinkayo Inne na fad’i.. Tabbas gaskiya ne. Daddy yafi son Mu’azzam sama dasu.. Jiki a sanyaye Musaddiq ya koma da baya ya fasa shiga.
D’aki Musaddiq ya koma yana duban kansa jikin mirror lokaci guda yake furta “You are a monster Musaddiq.. Dole Daddy yafi son Mu’azzam.. Dole kowa yafi son Mu’azzam.. Sabida kai ba komai bane face Monster.. Monster.. Monster..!” Ya dinga nanatawa yana duban kansa cikin madubi. A hankali ya silale ya zauna saman gado zuciyarsa na masa tsananin k’una.
**
Sadiya da Ajidde ne zasu kwana wajen Mamy dan dama Mama Hindu ke kwana da ita, yau da Ajidde zata kwana sann ga Sadiya ma ta nuna kwad’ayin kwana wajen Aunty Nuratun Sai Mama Hindu ta k’yalesu su kwana wajen Aunty Nuratun.
Mu’azzam baisan Ajidde na gidan ba, baima San zata kwana gidan ba.. Yadai san matarsa Sadiya zata taya mahaifiyarsa kwana na ranan. Hakan yasa ya saci k’afa ya nufi d’akin Mamy.
Da wayarsa ya haska ya ganota kwance gefen k’afafun Mamy idanunta a lumshe. Duk’awa gefenta yai yana hura mata iska kad’an a kunne.
Ta Ware idanunta a d’an firgice kaman mai shirin kurma ihu. Saurin rufe mata baki yai da hannunsa guda kafin yace cikin sigan rad’a “Hey it’s just me.”
Ta d’an ture hannunsa kafin tai sauri ta kunna side lamp da bai cika Haske ba.
Ta saci kallon Mamy kafin tai k’asa da murya tace “What are you doing here..?”
“Isn’t it obvious.. D’aukan ki nazo nayi..”
Ta girgiza kai kad’an kafin tace “Ka mance yau da Mamy zan kwana tashi ka fice before Mamy opens her eyes..” Tai maganar tana k’ok’arin turasa.
“Hey relax bazata tashi ba.. Beside zan dawo dake.. Hira kawai zamuje ki tayani.. I’m bored I couldn’t sleep..”
Ta girgiza kai tana fad’in “Nak’i wayon.. Dan Allah ka tashi ka fice kafin wani ya ganka.. What if Inne ta shigo taga bana nan..!” Tana maganar k’asa k’asa tana turasa.
D’aukanta yai Cak cikin hannunsa yana fad’in “I promise Zan dawo dake kafin Inne tai noticing baki nan..”
Bai Kai aya ba sukaji an bud’e k’ofar bathroom, shaff Sadiya tama mance tare da Ajidde suke a d’akin toilet ta shige kafin Mu’azzam ya shigo d’akin.
Wani irin razannan k’ara Ajidde ta saki ganin alamun mutum tsaye sabida hasken dim night lamp dake kunne. Tana iya ganin alamun mutum tsaye.
Ajidde ta shiga ihu tana tsalle tana fad’in “Wayyo mun shiga uku b’arawo b’arawo..!”
Cak yai tsaye yana dubanta ba tareda ya ije Sadiya dake cikin hannunsa ba yana mamakin mai wann mahaukaciyar yarinyar take d’akin mahaifiyarsa.
Ai kuwa kan kace mai Inne dake sallah ta jiyo ihun Ajidde dake neman d’auki.. Mama Hindu ma da baccinta bai nisa ba ta jiyo ihun Ajidde daga d’akin Aunty Nuratu.. Kai kan kace mai Ajidde ta tada gidan da ihunta..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*48*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Inne ce ta soma shigowa Mama Hindu na biye da ita, har lokacin Ajidde bata daina tsalle tana ihun b’arawo ba.
Tinda Sadiya taji shigowar su Inne tai saurin zame jikinta ta silale saman gado Ta lumshe idanunta tamkar mai bacci.
Babu halin ya fice gasu Inne sun shigo sun tare k’ofa.
Inne tace “Lafiya Ajidde meke faruwa..?”
Ajidde taci gaba da tsalle tana nuna mata alamun mutum da ta gani tsaye kusan gadon Aunty Nuratu. Tana fad’in “Inne kin gansa can lab’e wllhi b’arawo ne.”
Cikin sauri Inne ta danna switch na wuta, Haske ya gauraye cikin d’akin.. Mu’azzam suka hango yasha mur sosai yana aikawa Ajidde wani irin razannan kallo.
Ajidde ta zaro idanu waje had’ida kame baki. Tana nanata ta shiga uku cikin zuciyarta.
Mama Hindu ta girgiza kai kafin ta janyo Ajidde tana fad’in “Shige muje..” Ai babu musu Ajidde Ta bita kaman rak’umi da akala.
Sadiya kaw da idanunta ke lumshe sai danne dariyarta take.
Aka bar Mu’azzam da Inne tsaye nan wajen. Inne ta girgiza kai tace “Kar kace min komai.. Zo ka shige..” Ta k’arashe tana nuna masa k’ofa.
K’wafa yai kad’an cikin zuciyarsa yana furta sai ya taka yarinyar nan kafin ta daina shiga hidimarsa.
Suna fitowa parlor Inne ta tsaresa da idanu, tauna leb’en bakinsa na k’asa yai kad’an kafin ya soma fad’in “Inne yarinyar nan fah ba mai hankali bane.. Kan mai za’a barta Ta kwana da Mamy.. Yaushe ma ta fara kwana gidan nan.. What if haukarta ya tashi taje taiwa Mamy wani abin..”
“Rufe mun baki.. Kai mai ya kaika d’akin..?” Inne ta tambaya tana tsaresa da idanu.
Shafa kansa yai kad’an kafin yace ya soma ‘yan kame kame.
Girgiza kai kad’an Inne tai kafin tace “Zo ka fice Allah ya bamu alkhairi.. Gobe in sha Allah za’a kai maka ita..” Tana ida fad’in haka ta janyosa ta turasa waje had’ida janyo k’ofar ta rufe.
A b’angaren Ajidde kaw suna zuwa d’aki Mama Hindu ta sanyata gaba da fad’a “Ke Wai bazaki natsu na sai kin ja ma kanki wahala koh.. Kin masa na farko ya janye idanu bai miki komaiba, baki daddara ba shine yanzu ma kika sake tara masa jama’a a karo na biyu koh..?”
Ajidde Ta girgiza kai tace “Wllhi Mama Hindu Allah shine shaidata ban San shi bane tsaye wajen.. Kuma Ai ko kece kiga mutum haka dole ki razana.” Ta k’arashe kaman zatai kuka.
Mama Hindu ta girgiza kai tace “Allah dai ya yaye miki wann shiririta naki Ajidde.. Mijinki nada jan aiki.. Maza nemi waje ki kwanta a nan..” Ta k’arashe tana mai nuna mata wajen kwanciya.
Jiki a sanyaye Ajidde ta kwanta tana tunanin gamuwarsu da Mu’azzam dan tasan wnn karon irin kallon da taga ya mata Allah ne kawai zai ceceta.
**
Washe gari kaw sassafe ta fito zata je gida tazo da magani. Tana tafe tana sand’a kaman b’arauniya sai waige waige take.. Kaman daga sama taji ance “Ke.!” Tai saurin juyowa a razane tana duban yanda ta jiyo muryar.
Zuciyarta yai wani irin yankewa sakamakon hangosa da tai tsaye bayanta yana sanye da tracksuit alamun morning jugging ya fito.
Jikinta ya d’auki rawa ganin yanda ya had’e rai sosai yasha mur.
“Ni sa’anki ne..?” Ya tambaya yana dubanta
Tai saurin girgiza kai alamun a’a. Sai kwantar da kai k’asa take tsaban tsoro.
Yai mata K’uri yana dubanta, take ya tuna farkon zuwansa da ita ya soma had’uwa har taso masa sata sai yanzu kamanninta na wancan ranan ya bayyana masa.. Wato Ta jima tana shiga huruminsa since day one.. Ya zama dole ya taka mata Burki ta yanda nan gaba hanyar da yabi cikin gidan saidai Ta kaucewa wann hanyar.
“D’ago kanki ki fad’a mun ni da ke waye b’arawo..!”
Tai saurin d’agowa a zabure jin abinda yace sai kuma ta girgiza kai da sauri alamun a’a.
Yace “Kinsan sarai mai nake nufi b’arauniya.!”
Ta kuma d’agowa a d’an tsorace tana kuma firfito da idanu.
“Daina kallo na da wann idanun naki..!” Ya daka mata tsawa da fad’in haka. Lokaci guda yai mata nuni da bishiyar mangoron da taso bud’e masa jaka a k’ark’ashinta “Kin tuna ko in tuna miki..?” Ya k’arashe yana zaro k’aramar piston cikin rigarsa.
Wane irin zabura Ajidde tai zata saki k’ara ya d’aura yatsarsa guda saman labb’ansa yace “Idan kika ce pit sai na fasa kanki da bindigar nan.”
Ta rik’e labb’anta Duka biyu da k’arfin gaske tana jin kuka gadan gadan na zuwa mata, lokaci guda take girgiza kai alamun ta tuba.
“Dama ni tin da na ganki na fahimci kinada suffar criminals.. Yau kwanakin ki ya k’are a gidan nan.. Shige muje..” Ya k’arashe yana nuna mata hanya.
Hawaye na zubo mata take tafe hannayenta duka biyu rik’e da labb’anta sabida tsananin tsoro shi kaw Mu’azzam na biye da ita rik’e da bindiga.
D’akin da ake aje manyan shanayen gidan gonar suka shiga. Kana ganin Ajidde zaka fahimci Ta tsunduma cikin tsananin tsoro wanda bata tab’a shiga irinsa ba.
Yasha mur sosai yana dubanta rik’eda bindiga. Jikinta sai rawa yake tana rik’eda labb’anta tana zuban hawaye.
Drum Babba da ake zuba ma shanu ruwa ya nuna mata yace “Ke danna kanki cikin ruwan nan..!”
Ajidde ta zaro idanu waje ta shiga girgiza kai, sai lokacin ta iya bud’e baki da muryarta dake tsananin rawa “Dan Allah na tuba.. Wllhi bazan sake ba.. Dan Allah kamin rai.”
Bindiga ya d’ana mata a k’eya yace “Idan baki danna kanki cikin ruwan nan ba sai na fasa kanki da bindigar nan..!”
Jiki na rawa Ajidde Ta rintse idanunta had’ida tura kanta cikin ruwan.. Ga Mu’azzam tsaye kanta da bindiga ba abun ta d’ago kanta ba.. Saida ya ta fara fiki fiki kaman kaman an jefa kaza cikin ruwa alamun galabaita kafin ya d’aga bindigar yace “D’ago kanki..”
Ajidde ta d’ago kanta tana shak’an numfashin azaba tana fitar da iska daga bakinta alamun ta jigata tana bud’e idanunta da suka jik’e da ruwa da k’yar.
Ya kuma danna mata bindigar a k’eya yace “Maida kanki..!”
Ta sake masa kuka tana rok’onsa dan Allah yai hak’uri ya k’yaleta.
“Ke ina wasa dake ne.. Idan baki maida kanki ba Sai na d’ana miki harsashin nan..!” Ya fad’i cikin kakkausar murya yana firfito da idanunsa.
Babu shiri Ajidde tana kuma maida kanta cikin ruwan a jigace.. Haka ya dinga mata saida ya tabbata Ta jigata sosai. Kafin ya nuna mata gefe yace “Tsuguna..!” Babu musu ta tsuguna jiki har na rawa tana kuma matsan hawaye ga kanta da fuskarta sharkaf a jik’e.
Ya gyara tsayuwarsa yana maida bindigarsa cikin aljihu “Kinsan sunan wann horon..?”
Tai saurin girgiza kai tana hawaye.
“Wann horon irinshi ake ma b’arayi irinki a police station.. Tashi muje ki fad’a masu wacece ke kafin a dangana dake ofishin ‘yansanda a kulleki..”
Ajidde Ta mik’e tana kuka tana fad’in “Wllhi ni ba b’arauniya bace dan Allah kayi hak’uri.. Na rantse da Allah ni ba b’arauniya bace.”
“Shut up..!” Ya daka mata tsawa wanda ya kuma sanyata had’iye kukanta. Ya nuna mata k’ofa yace “Shige muje kafin na fasa idanuwankin nan..!”
Cikin sauri had’ida rawan d’ari ta fice sabon kuka na zuwa mata.
Ta window Shemau ta hango Ajidde biyeda Mu’azzam sun nufi sashen Inne. Babu shiri ta mik’e ta nufo bayansu.
Tin daga hanya Inne ta hango Ajidde Mu’azzam na biye da ita, daga yanayin data hangosu ta fahimci ba lafiya ba. Aiko suna shigowa parlorn Inne ta mik’e tana tambayarsu lafiya.
Mu’azzam ya nuna mata k’asa yace “Tsuguna a nan..!”
Babu musu Ajidde ta duk’a tana kuka.
Inne ta tsaresa da idanu tana jiran ba’asi.
Mu’azzam ya dubi Inne yace “Da alama baku San wa kuka kawo gidan nan kuka ajiye ba Inne.. Wannan yarinyar b’arauniya ce ba mai magani ba.. Dama ni tun farko ban yarda da ita ba..” Ya dubi Ajidde dake duk’e wajen tana hawaye ya daka mata tsawa da fad’in “Ke.! bud’e bakinki ki fad’i cewa ke b’arauniya ce.!”
Inne ta dakatar dashi da fad’in “Haba Modibbo.. Wane irin abu ne zaka saka ‘yar talikan nan gaba kana tuhumarta da sata.. Awho dan Ta maka ihun b’arawo jiya shine yau kaima bari ka kirata b’arauniya.. Ko dan kaga tufafin matarka jikinta.?”
Mu’azzam dake faman aikawa Ajidde mugun kallo daga nan yana take duk’a tana hawaye yace “Inne yarinyar nan b’arauniya ce.. Itace yarinyar da ta tasamma min sata kwanakin baya Ran da nazo gidan nan..” Ya kaikaito ya dubi Ajidde yace “Ke.. Ki fad’a mata cewa ke b’arauniya ce.” Ya daka ma Ajidde tsawa da fad’in haka.
Kafin Ajidde takai ga basa amsa suka sinkayo muryar Musaddiq ya doso wajen yana fad’in “Ita ba b’arauniya bace..!”
Gaba d’aya suka juyo suna duban Musaddiq dake nufosu cikin tsananin dakewa.
Mu’azzam ya d’an tsaresa da idanu kafin yace “You don’t know anything Musaddiq.. Just stay out of this..”
Musaddiq dake sakin huci dab kusan Mu’azzam d’in ya tsaya suna fuskantar juna lokaci guda yake furta “I told you she’s not a thief.!”
Yanda yake maganar da zafin rai yasa Mu’azzam tsaresa da idanu yana dubansa, ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “Are you alright..?”
“Garau nake..! Na fad’a maka ita ba b’arauniya bace.. Or did she steal from you..?!” Yai maganar yana duban cikin idanun Mu’azzam.
Mu’azzam ya girgiza kai yace “She didn’t amma tayi kusa.. And for that zata bar gidan nan dan bamu San wace irin criminal bace ita..