Showing 45001 words to 48000 words out of 209154 words

Chapter 16 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3080

tareda ta iya juyowa ba, jikinta sai rawa yake. Ta nemi layar zana da kyallu ta bata ta rasa. Tana cikin dibi dibin ta sinkayo muryar mutumin da ya shigo d’akin yana fad’in “Who are you.? What are you doing in here.?”

A slow motion Ajidde ke juyowa. Musaddiq ya ware idanu yana duban yanda ta zaro k’wayar idanunta, dikda babu janbaki da jagiran data zana wancan lokaci tsaf ya ganeta dan bazai mance wannan k’wayar idanun nata masu tsananin haske da kyau ba “You again.?” Ya furta yana nunata.

Daidai lokacin aka soma tab’a k’ofar bathroom alamun mutumin dake ciki zai fito.

Ajidde ta rikice ta rasa wanne zatai dan tuni Mu’azzam ya fito d’aureda towel, rufin asirin Allah hannunsa na rik’e da k’aramar yana goge fuskarsa zuwa sumarsa sam bai an kare ba balle ya gane da mutane cikin d’akin.

Cikin azama Musaddiq ya finciko hannun Ajidde da ta saki baki da hanci tana duban Mu’azzam ya turata cikin wardrobe.

K’aran rufe wardrobe Mu’azzam yaji ya d’ago fuskarsa yana duban Musaddiq dake tsaye wajen cikin wani irin yanayi na daburcewa.

“Hey are you with someone.? Ina wanka kaman naji murya..” Mu’azzam yace yana k’arasowa.

Musaddiq da gaba d’aya yake a rikice sabida Ajidde dake b’oye cikin wardrobe saurin girgiza kai yai yace “Me. A’a no.. Yanzu shigowarta.. Mu’azzam you need to come, wani mutumi ne naga ya dirk’o ta Katanga shine nazo kiranka.. You need to hurry kafin ya b’ace mana..”

Yanda duk yake a birkice yasa Mu’azzam zuba masa idanu yana karantarsa “Musaddiq will you calm down please..”

“Wane irin calm down kake magana. Inace maka b’arawo ne kaman naga ya shigo kana ce min calm down.. I know you’re a Corp shisa nazo wajenka direct.. Please you need to hurry..” Ya k’arashe yana mai janyo Mu’azzam d’in suka nufi k’ofa.

“Wait Musaddiq.. I need to get dressed first.” Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in haka.

Sai sannan Musaddiq ya tina towel ne jikin Mu’azzam d’in.

Mu’azzam ya d’an girgiza kai yana k’ok’arin nufan wardrobe.
‘Oh shitt.. He can’t see her in there.’ Musaddiq ya fad’i cikin zuciyarsa. Kafin Mu’azzam d’in ya bud’e wardrobe d’in wanda tuni Ajidde dake dubansa ta d’an tsakanin da bai ida rufuwa ba ta sadak’ar kawai ya kamata dan har toshe bakinta tai ta rintse idanunta tana jiran mai afkuwa ya afku. Kwatsam Musaddiq ya k’araso ya damk’o hannunsa ya hanasa bud’e wardrobe d’in lokaci guda yake fad’in “Dan Allah kazo muje kar ya gudu.. Zo ka gansa ta window..” Ya k’arasa da Mu’azzam jikin window yana yaye curtains yake nuna masa “Look look duba tacan ka gani..”

Girgiza kai Mu’azzam yai cikeda k’osawa yace “Musaddiq I can’t see anything..”

“Ok wait muje wajen ka gani..”

Ya d’an fuzar da fuci hannayensa saman kunkumi “Bani jallabiyata cikin wardrobe I just hang it there.”

Cikin sauri Musaddiq ya jinjina kai yayinda Mu’azzam d’in ya d’an girgiza kai yana mai fuzar da fuci.

Musaddiq na bud’e wardrobe d’in sukai ido hud’u da Ajidde da k’iris ya rage bata saki fitsari ba dan tsoro.. Ya aika mata mugun kallo kafin ya zaro jallabiyar dake lank’aye jikin hanger. Ya maida wardrobe d’in ya rufe kafin ya kawo wa Mu’azzam jallabiyar ya zira. Lokaci guda Mu’azzam d’in ya nufi waje ba tareda ya kuma bi takan Musaddiq ba.. Mu’azzam na ficewa ya dawo ya bud’e Ajidde yace “Kina jina kar ki sake ya ganki dan idan ya kamaki kashinki ya bushe.” Cikin sauri Ajidde da tuni Ta had’a gumi take jinjina kai alamun taji. Sauri sauri ta fice ta nufi d’akin Aunty Nurah tana sauk’e nannuyan ajiyan zuciya.

Tana shiga ta tadda Hindu ta kawo mata abin kari. Hindu ta dubeta tace “Ina kika fito ga abin kari na kawo miki tuntuni..”

Murmushin yak’e Ajidde tai tace “Oh wllhi makewayi na fita inata nema ai.”

Hindu ta murmusa tace “Banda abinki Ajidde ai da tambaya kikayi muje na kaiki.”

Ajidde tai saurin girgiza kai tace “A’a ki barshi kawai ai yanzu ma zan tafi bana so nayi rana.”

Hindu Ta d’an tab’e baki tace “Toh shikenan.. Abincin fah..?”

Ajidde ta juya taga kayan dad’in da aka kawo mata. Sai kuma ta dubi Hindu tana wage baki alamun tanaso taci.
Hindu ta murmusa tace “Ki zauna kici abincinki kafin ki tafi..”

Aiko Hindu na ficewa Ajidde ta shiga yagan pepper soup d’in kaza tana turawa bakinta, hannu bibbiyu takeci kaman wanda za’a k’wace.. K’arshe bud’e jakarta tai tana tura sauran ciki. Kaman wacce ta tina wani abu sai kuma ta d’ago tana duban matar nan majinyaciya. A hankali ta k’arasa kanta ta tsaya gabanta “Na gode kinji. Ba don ke ba da bazan shigo gidan nan har naci dad’i irin haka ba.” Ta k’arashe tana wage baki. Lokaci guda ta mutsuke hannayenta jikinta ta sab’i Jakarta ta nufo k’ofa.
Sauri sauri ta fice tana lek’e tamkar maras gaskiya.

Koda Mu’azzam ya fice baiga alamun kowa ba baiga alamun komai ba gajeren tsaki yai yana girgiza kai yasan bazai wuce shak’iyancin Musaddiq bane suka motsa. Ya yanke shawarin tuntub’ar securities ko sunga wani abu suspicious. Har zai nufa gate Musaddiq ya k’araso yana d’an haki alamun yayi gudu.

Mu’azzam ya dubesa yace “Are you sure kaga wani ya shigo.”

Sosa kansa yake yana duban Mu’azzam d’in “I think it’s just my imagination.”

Kafesa da idanu Mu’azzam d’in yai yana karantarsa “Are you alright.?”

“Of course.. I’m absolutely fine, Inspector.”

Jinjina kai Mu’azzam yai yace “Lets go and ask the security men Ko sunga mutumin da ka gani..”

“No no no.. Nace maka Ina tunanin imagination d’ina ne.. Babu kowa.” Yai maganar yana d’an ciza lab’e bakinsa kad’an irinta masu laifi.

Takowa Mu’azzam yake zuwa gabansa yana mai tsaresa da idanu
“Wait. Are you sure you’re not on drugs.?” Mu’azzam ya tambaya yana duban Musaddiq d’in.

“Kasan na daina tin ba yau ba.. kuma bazan k’ara komawa ruwa ba in sha Allah. Dik da ban maka alk’awari ba amma nace In sha Allah.”

Jinjina kai Mu’azzam yai yana mai kuma karantarsa ba tareda yace komai ba.

Daidai nan Jume ya k’araso suka gaisa da Mu’azzam kafin ya dubi Musaddiq yace ana nemansa a wajen aiki. A tare Musaddiq da Jume suka wuce yayinda Mu’azzam ya nufo cikin gida yana jin dad’in yanda Rayuwar d’an uwan nasa ya Inganta a gidan gonar cikin ikon Allah.

Can Ajidde ta hangosa zai shige, gabanta yai wani irin fad’uwa dan ba komai Ta tina ba sai ganinsa da tai d’aure da towel. Tai saurin rintse idanunta ga k’amshin wardrobe d’insa da ya kama illahirin jikinta. Koda ta rintse idanun ma shi take hangowa. Ta kuma bud’esu tana furta “Wayyo Ajidde shige shigen ki ya kaiki kika gano sa a haka.” Jikinta ta shiga shinshinawa tanajin k’amshin wardrobe d’insa da ya kasa barin jikinta.
Muryar data sinkaya daga bayanta ya sanyata juyowa babu shiri.

Musaddiq ne ke tsaye bayanta ya tsareta da idanu. Ta ganesa shine mutumin da ya taimaketa ya sanyata cikin wardrobe. Kan kace mai ta duk’a saman gwiwoyinta ta d’ago hannu tana rok’onsa ya rufa mata asiri.

“Kin ganeni..?”

Tambayar da ya mata kenan.

Tai K’uri tana dubansa, sai kuma tai saurin girgiza kai alamun a’a

Yashin dake wajen ya d’iba cikin hannunsa ya kakkab’e had’ida shafa sauran saman fuskarsa. Take fuskarsa tai hazon k’ura.

Ajidde na zaro idanu waje tace “Kuran tashe.!” Sai kuma ta soma dariya tana nunasa.




SameenaAleeyou 📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*17*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Harga Allah ta bawa Musaddiq dariya yanda tai maganar amma Sai ya gimtse yace “Zaki min bayani yanzu, what exactly were you doing in there..? Mai kike cikin d’akin mutumin nan..?”

Zaro idanu waje tai sai kuma tai dariyar yak’e tace “Ban d’aki nake nema kawai sai tsintar kaina nai a wannan d’akin.. Kai kuma fah.. Ba kace min baka shiga wannan gidan ba.. Ya na ganka a cikin gidan.. Kuma da alama ka saba shiga.. Watau dai k’arya ka min kenan..?” Ta k’arashe hannayenta saman kunkumi tana mai tsaresa da idanu tamkar wacce zata kai masa bugu.

“Wait what.. Ke ni nake miki k’arya..?”

Ajidde ta d’an murgud’a masa baki tace “Toh ni bance kayi k’arya ba amma Maiyasa kace min haka..?”

Tsareta da idanu yai dan a yanda ya d’auketa shashasha bai zaci zata iya d’ago zancen da sukai ranan ba.. Ya gyara tsayuwarsa yace “Tsaya ai idan ban mance ba nace miki inada aboki d’an gidan..”

Ajidde Ta zaro ido Tace “Wannan ne abokin naka..? Ai shine mutumin da ya biyoni ranan..”

Musaddiq ya zuba mata idanu da tsananin mamaki “Toh kin dai aikata laifin kenan.. Na tabbata ke mai laifi ce.. Zaki fad’a mun mai kike a d’akin ko kuma yanzu na shiga cikin gidan na sanar dashi komai..”

Cikin tsananin damuwa Ajidde take rok’onsa “Dan Allah ka rufa mun asiri.. Ka rufa mun asiri kar ka tona mun asiri wajensa.. Idan ka tona mun asiri shikenan bazan bawa matar nan magani ba.. Dan Allah ka barni na gwada sa’an magani na akan matar nan.. Nasan zakaso mahaifiyar abokinka ta sami lafiya..” Ta k’arashe cikin tsananin nuna damuwa.

Musaddiq ya jinjina kai yace “K’warai kuwa nafi kowa so Aunty Nuratu Ta sami lafiya.. Zan rufa miki asiri amma sai kin sanar dani gaskiyar Al’amarin..”

Ajidde ta had’iyi miyau da k’yar tana mai kuma zaro idanu “Zan fad’a maka amma saidai idan zaka mun alk’awari.”

Cikin wane irin yanayi yake dubanta wannan karon. Lokaci guda yananyin nasa ya canza, cikin wane irin kakkausar murya yake fad’in “I thought I’ve already told you.. I don’t make Promises.. Bana Alk’awari.. Ban tab’a cika Alk’awari ba.. Kuma bazan tab’a cika alk’awari ba... Kuma na rasata ne ta dalilin rashin cika Alk’awari na.!” Ya k’arashe siririyar hawaye tana gangaro masa.

Cikin tsananin tsoro Ajidde ke dubansa, idanunta Sun firfito waje sabida tsoro. A hankali Ta soma k’ok’arin jada baya..

“Ina zakije.. Bazaki bar wajen nan ba sai kin fad’a mun sirrinki..” Ya fad’i yana dubanta.

Cikin sauri take girgiza kai “Banida Sirri.. Ni d’in kawai magani nake kawowa..” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige.

Musaddiq yasha gabanta yana binta da wani irin kallo wanda ya kuma haifar mata da tsoro “You are a thief..! Ke b’arauniya ce.. Wancan ranan sata kika so yi masa sai ya biyoki kika b’uya.. Wannan karon ma sata kika shiga d’akinsa zaki masa sai Allah ya kawoni kafin ki ida nufinki.. Now you tell me.. Shin wacece ke.. Mai magani ce ke kokuwa b’arauniya ce.?!”

Idanun Ajidde suka kawo ruwa, Ta soma girgiza masa kai tana fad’in “Dan Allah ka rufa mun asiri wllhi nima umarni nake bi..”

“Umarni kike bi.. Umarnin wa..?” Ya kuma tambaya yana dubanta.

Ajidde ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa “Zan fad’a maka komai amma zaka yi shiru.. Bazaka fad’a ma kowa komai ba.. Idan har kana so na bawa matar nan magani.. Sannan zaka taimakeni..”

Musaddiq ya jinjina kai yace “Zanyi duk abinda kikace Idan kika fad’a mun komai..”

K’asar wata bishiya suka zauna Su duka biyun, Musaddiq ya dubeta yace “Ina sauraronki..”

A hankali Ajidde Ta soma karanto masa sana’ar da Kyallu ta d’aurata bisa, ta kuma sanar dashi k’udirin kyallu na cewa muddin tazo gidan bata sato masu wani abu ba ga uk’ubar da zata mata.. Wannan dalili shiyasa take k’ok’arin aikata satan da yace tana yi.

Musaddiq ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana dubanta “Toh ita Inna Kyallu bata tinanin watarana a kamaki.?”

Ajidde ta girgiza kai tace “Inna kyallu bata yarda da fad’uwa ba.. Dik abinda zatayi sai ta masa shiri sosai domin kuwa har layar zana ta bani.. Sannan idan aka kamani babu damuwarta dan cewa zatai dama tin can ni b’arauniya ce.”

Musaddiq yace “Ke kuma kin yarda layar zata taimaka miki..?”

Ajidde tai shiru tana dubansa “Ban sani ba..” Ta basa amsa kai tsaye.

Sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an yace “Zan taimakeki.. Kuma zamuyi aiki tare.. Aunty Nuratu zata sami lafiya in sha Allah.. Sannan Inna Kyallu bazata fahimci komai ba..”

Tai masa K’uri tana dubansa kaman yanda shima ya zuba mata idanun.

**

Zaune take a uwar d’aki ta rapka uban tagumi tana tinanin rayuwa da yanda Al’amara suke kasance masu tun bayan had’uwarta da Sagir. Tana jin Tabawa da Umma yanda Tabawan ke yab’a wa mahaifiyarta maganganun marassa dad’in sauraro saikace ba d’azu tai masu kaca kaca da gida taci mutuncinsu ba, a rana guda karo na uku kenan kafin yammaci Tabawa ke kawo masu samame.. Wannan shine ake kira K’addara ya riga fata, da ace wani zai iya zab’an k’addararsa tabbas da bata zab’i K’addarar sanin Sagir ba balle har ta kasance dashi. Amma saidai tuni K’addararta tazo da hakan a rubuce. Ji take ta dalilinta komai ke faruwa, duk wasu iftila’i da ahalinsu ke fuskanta itace sababi.. Wasu hawayen masu tsananin k’una suka gangaro mata. A daidai lokacin Umma ta shigo.

Ta jima tana duban Sadiyar kafin ta k’arasa gefe da Ita ta zauna, saida suka d’ibi lokaci babu wanda yace ma kowa komai kafin Umma ta nusa tace “Bana San kina saka damuwa ma ranki Sadiya, cuttutuka sunyi yawa yanzu Sai kije kisa ma kanki hawan jini ko ciwon zuciya a ‘yan shekarun nan naki..”
Sadiya ta goge hawan dake kwance saman fuskarta “Umma Wai ni dan Allah ina dangin Abba suke da bazasu waiwayemu ba.. Umma shin basu san d’anuwansu ya mutu bane bazasu dubi bayansa ba Ko dan albarkacin zumunta. Umma kodai baida dangi ne..?”

“Waye kika tab’a ji baida dangi Sadiya. Mahaifinku yanada dangi saidai tin lokacin da yace zai aure ni sukayi farrak’u da danginsa.. Iyayensa sun jima da rasuwa sai ‘yanuwan ne suka rainesa. Sunso su aura masa d’iyarsu shi kuma yak’i amincewa yace sai ni yake so.. Tin daga wannan lokaci suka ciresa daga cikinsu sukai rantsuwa babu shi babu su bazasu tab’a waiwayansa ba har abada.. Sadiya mahaifinki ya sadaukar da abubuwa da dama a sabida ni.. Banida kowa a k’asar nan sai shi.. Na shigo k’asar nan a wahalce a matsayin ‘yar cirani.. Kuma na rasa kowa nawa amma mahaifinki shi kad’ai ne ya tsaya min ya taimaka min ya zamto min sutura..” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’in “Na k’are ina mai masa butulci da raina arzikinsa.. Mutumin da ya sadaukar da komai nasa sabida ni.. Ciki harda danginsa wanda suka guje shi sabida ya zabi ya kasance da matar da bata da kowa a k’asar nan.. ‘Yar cirani data shigo k’asar nan a wahalce.. Shin ki fad’a mun ta yaya bazan ga ba daidai ba.. Ta yaya wacce ta aikata irin wannan butulci zataga da kyau...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Sadiya dake hawaye Ta matso ta rungume mahaifiyarta su duka biyun suna kuka mai ban tausayi.

Cikin zuban hawaye Sadiya ke duban Umma “Umma ki daina fad’in haka.. Bawa baya wuce k’addararsa.. K’addarar ka tamkar inuwarka ce dik yanda ka kaje saita bika sannan idan ka tsaya itama zata tsaya.. In sha Allah zanyi abinda ya dace wannan karon.. Bamuda sauran zab’i da ya wuce na amince da auren Alhaji Isyaku..” Kuka sosai ya kufce mata.

Cikin zuban hawaye Umma ke dubanta lokaci guda take girgiza kai alamun a’a “A’a Sadiya, bazan bari ki sadaukar da rayuwarki da farin cikin ki sabida zunubaina ba.. Nasan bansan yanda zanyi ba.. Amma inada tabbacin Allah bazai bar mu haka ba da sannu zai kawo mana wani mafitan..”

Sadiya tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata “Watak’ila mafitan kenan Allah ya kawo mana Umma. Watak’ila Alhaji shine mafitan angaremu.. Umma idan muka zauna haka bamusan mai Tabawa zatayi gaba ba.. Bamusan ko Malam Aminu zai bar muci gaba da zama a nan ba.. Umma ‘yan uwana nake tunani.. K’anne na nake tunani, bana so suna ganin irin wannan tashin hankali.. Umma abin yayi yawa.. This has to end Umma.. Ni kad’ai ce ya kamata nayi abinda ya dace.. Umma ki sanar da Malam Liman ni Sadiya na amince ya aurar dani ga Alhaji Isyaku... Zan rabu da Sabeera rabuwa Ta har abada.. Bazan k’ara kallon cikin idonta ba.. Watak’ila Wannan shine hukuncina a rayuwa.. Hukuncin abubuwan da nayi ma Abba a lokacin da yake raye.” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Umma ta rungumeta su duka biyun suna masu fashewa da wani irin kuka mai tab’a zuciya.
**

Koda labari ya iski Alhaji Isyaku cewa Sadiya da mahaifiyarta sun amince da batun auren Zo kaga Farin ciki wajensa, jinsa yake sabon ango.. Lallai tarkonsa ta d’anu ko banza zai mallaki wannan kyakkyawan yarinyar da ya jima yana kwad’ayin kasancewa da Ita.. Bayan isha ya shirya tsaf yasha wankansa ya fesa kwalliya da babbar riga ya nufo gidansu Sadiya.

Da k’yar Umma ta shawo kanta tace taje su gaba taji da mai yazo.
Haka badon taso ba ta zira hijab d’inta ta fito.

Yana ganinta fari’arsa ya k’aru “Assalamu alaki kyakkyawa ma’abociya annuri..” Ya fad’i yana mai k’arasowa.
Sanin darajan sallama yasata ta amsa ciki ciki kanta na duk’e k’asa.. Ta soma k’ok’arin duk’awa da niyyan gaishesa.

“A’a tashi tashi kayanki.. Haba ai saidai ni na duk’a miki Gimbiyata.”

Takaici ya turnuk’eta, ta rintse idanunta a hankali tanajin zuciyarta na mata zafi.

“Ki saki jikinki. Kuma ki saka a ranki cewa ni masoyinki ne..”

“Masoyi kuma Baba..? Kodai b’atan kai kayi ne.? Ni ce fah Sadiya k’awar Sabeera wacce ka datse alak’armu da Sabeera sabida banida kamun kai.. Ko ka mance ne..?”

Murmushin da yafi kama da yak’e yai kana yace “Yaro dai yaro ne. Toh banda abinki Sadiya ai ba komai yasa bani k’aunar alak’arku da Sabeera ba Sai dan bana so ku shak’u ku samu kusanci da juna gudun kar randa duk nazo miki da wannan batu nawa da ya jima a birnin zuciyata kice bazaki iya ba sabida k’awance da d’iyata da kuke.. Idan kika cire wanann ni babu wani abinda zaisa na rabaki da Sabeera.. Ki yarda dani Sadiya, ni wllhi ba sabida komai na rabaku da Sabeera ba sai dan kar ta zamto mana cikas a tsakaninmu.. Banaso ta zamto shamak’i ma soyayya ta dake..” Ya d’an nusa yana mai gyara zaman babbar rigarsa “Wato Sadiya na jima Ina k’aunarki saidai bansan Ta yanda zan tunk’areki da wannan batu ba har sai zuwa wannan lokaci..”

Sadiya dake dubansa cikeda tsananin mamaki, dan itakam kunya ma take ji masa, murmusawa tai tace “Sai wannan lokacin ka sami dama. Lokacin da banida wani zab’i da ya wuce na amince da buk’atarka koda ace bana so. Shin ko ba haka bane Baba.?”

Saurin katseta yai da fad’in “Ko d’aya.. Ba haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login