Showing 189001 words to 192000 words out of 209154 words
yazo kai tsaye instead of BA da DA tace dashi wanda yake nufin Danger kai tsaye. Dole wanda ya kashe Maleeka wani ne da ya k’oshi da raining ko dai na ta’addanci ko kuma na aikin tsaro.. Toh wanene wann mutumin.?’ Ya mik’e tsaye ya soma zagaye parlorn. Wayar salularsa ya bud’e yana duba hoton sketch d’in k’asan takalmin da yake da tabbacin na makashin Maleeka ne.. Ta yaya zai samo wann mutumin..? Tambayar da yai karan tsaye a zuciyarsa..
A hankali ya saki murmushi shi kad’ansa yana jinjina kai kama wanda ya tina wani abin. Lokaci guda ya saita garu da pen d’in hannunsa ya jefa. Ai kuwa bai missing target ba. Murmusawa ya kumayi kafin ya furta a fili “Allah ya kaimu gobe zamu buga wasan Naka Chief Jaja..!” Ya k’arashe yana sakin murmushi mai bayyana hak’wara.
**
D’akin taron yayi shiru. Yayinda Deputy Director General (DIG) ke zaune daga center. Manyan ‘yansanda kusan guda biyu suna zaune gefe da gefensa. Chief Jaja yana gefe guda. Sai sauran Team Members d’insu Assad da kuma Yusuf suna zaune gefe guda suma. Duk saman doguwar teburin dake kewaye da kujeru suke.
Mu’azzam yai tsaye yana masu nuni da Farin allon da yai rubutu bisa. Solution d’in da yai saman takarda a daren jiya shi yake rubuta masu saman allon yana kwararo bayanai. Yayinda DIG da sauran ‘Yansandan ke jefo masa tambayoyi sahu sahu yana amsa masu.
Gaba d’aya sun bada hankulansu suna sauraron yanda Inspector Gamji zai zak’ulo makashin Maleeka.
Kallo guda za kaima Chief ka fahimci cikin tsananin tashin hankali yake. Dikda sanyin AC dake busawa cikin d’akin taro Chief Jaja gumi ne ke tsartsafowa cikin jikinsa.
Mu’azzam ya k’arasa jikin allon yana k’are masu kallo gaba d’aya.
Ya murmusa kad’an yana duban position d’in da kowa ke zaune cikinsu yana jinjina kansa yake furta “True failure isn’t missing the target.. True failure is never taking a shot..”
Yaci gaba da takowa still murmushi saman fuskarsa yana d’an kewayesu kad’an yana ci gaba da examining nasu “BA could be either BAD or BAT.. And YOU could be you..!” Ya k’arashe yana jefa pen d’in dake rik’e hannunsa.
A firgice Chief ya d’ago yana duban Mu’azzam dake sakin murmushi yana sarawa DIG, lokaci guda yake furta “puzzle solved, Sir.” Lokaci guda ya d’ago hoton k’asan takalmin dake cikin wayarsa yana nunawa a fuskokinsu..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*59*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin sakanni Zuciyar Yusuf da Mu’azzam ya jifa da alk’ami yake bugu. Ya ware idanu yana duban mutanen dake kewaye wajen suma suna dubansa, babu kaman Deputy Inspector General.
Ko gizau Yusuf ya kasa har saida Mu’azzam ya tako zuwa gabansa yayi folding hannayensa ta baya. Chief Jaja ya kasa d’ago kai ya dubi Yusuf dan baya so su had’a idanu balle a fahimci wani abu. Shiko Assad cikin tsananin shock yake duban Yusuf da Mu’azzam d’in. Mutanen da sukayi dik yanda zasuyi har Allah ya fiddashi daga k’agen da aka masa.. Ta yaya Mu’azzam zai nuni da Yusuf yace shine ya kashe Maleeka.. Wann abu ne da bazai tab’a yuwa ba.. Sud’in abokan juna ne wanda tinda aka soma binciken nan tare suke komai.. No. no it can’t be Yusuf.. Not Yusuf.. Yusuf bazai tab’a zama Traitor ba.. He is a good person.. Shi ya tabbatar da hakan. Muryar DIG ne ya katse Assad sanda yake jefowa Mu’azzam tambaya.
“Mai hakan yake nufi Inspector Gamji.. Ka nuna mana hoton zanen k’asan takalmi sann kayi nuni da Detective Yusuf.. Akwai wani abinda hakan yake nufi ne.?”
Mu’azzam ya jinjina kansa yace “K’warai kuwa Sir. Hakan yana nufin Detective Yusuf shine makashin Maleeka.. Wann hoton zanen k’asar takalmansa ne.. Idan ka bani dama Sir.. Inaso na umarci Yusuf da ya ciro k’afan takalminsa na hagu kaman dai yanda na zana wann ni kuma zan tabbatar maku cewa shine makashin sann zan fayyace maku yanda ya buga wasan nasa.”
Tinda ya soma magana Yusuf baice komai ba Sai dubansa yake da idanunsa da suka gama kad’awa yana dunk’ule hannunsa cikin alamun rashin gaskiya. Shiko Chief addu’a kurum yake Allah yasa kar wann binciken tonon sililin da Inspector Gamji yakeyi ya k’araso kansa.
Mu’azzam ya k’arasa gaban Yusuf yai tsaye kansa su duka biyun suna aika ma juna wani irin duba. Fuskar Mu’azzam a matuk’ar tsume.
Girgiza kai Yusuf yai yana duban Mu’azzam wanda ko gizau bai ba “How could you..? How could you accuse me of serious crime Inspector.!” Yana maganar ne daga nan yanda yake zaune.
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ka ciro k’afar takalminka na hagu.”
Zuciyar Yusuf bai daina bugawa ba. Bai daina aikawa Mu’azzam kallon tsana ba. Lokaci guda ya zame takalmin ya mik’a masa.
Mu’azzam ya murmusa yana juya k’asan takalmin dan tinda ya hango k’afar Yusuf ya fahimci cewa wann takalmin ne sanye a k’afarsa sanda yai committing crime d’in.
D’ago takalmin yai ya had’e da hoton dake cikin wayarsa yana nuna masu, exactly babu abinda ya raba da zanen dake k’asar takalmin Yusuf, harta lambar takalmin iri d’aya ne Wato size 43.
Yusuf ya soma girgiza kai yana furta “This is rubbish.. Wann zai iya zama takalmin kowa don ba ni kad’ai Company ta k’era takalmi ba.”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “K’warai ba ma kai kad’ai Company ta k’era takalmi ba amma wann hoton k’asar takalminka ne..” Ya d’an gyara tsayuwarsa yana duban cikin idanun Yusuf “Ka zaci ka iya buga wasan ne.. Saidai ka mance a ko wani wasa akwai coach.” Ya murmusa kad’an kafin ya juyo yana dubansu yaci gaba da fad’in “Na kira layin Yusuf a lokacin da na d’auki hanyar headquarters daga can asibitin yanda na gano cewa Maleeka ita ke cin amanarmu.. Amma sai naji wayarsa bata shiga, can kuma Sai naji ana sanar dani line busy.. Kenan Yusuf yana waya a daidai wann lokacin.. After some seconds still wayar bata yanke ba.. Yusuf ya d’aga kirana alamun ya gama wayar da yakeyi kenan..”
Nusawa ya d’anyi kafin yaci gaba da fad’in “Ya sanar dani cewa Officer Maleeka was ready to confess.. Zata bada statement d’inta, zata fad’i duk abinda Ta sani kan wad’anda take ma aiki, mu sameta a apartment d’inta. A cikin team d’inmu ni kad’ai ne bansan location d’in gidan Maleeka yake ba. Abokan aikina sun sani.. So Yusuf yasan gidan Maleeka kenan. Hakan yasa ya turo mun sak’on adireshin gidan immediately bayan mun gama waya.” Ya d’an ci gaba da takawa yana fad’in “Tsakanin lokacin da mukayi waya yaci ace Yusuf yaje gidan Maleeka ya dawo daga yanda yake fiye da yanda nake.. Yusuf yaje location d’in domin ya kashe Maleeka, saidai abinka da k’wararru koda Yusuf ya soma attacking d’inta tayi retaliating. Sukai fad’a irin na well trained police officers.. Har Allah ya bama Maleeka nasaran bud’e fuskar Yusuf wanda probably yake rufe da mask.. Ga dukkan alamu She was shocked sanda taga fuskar Yusuf yazo a matsayin wanda zai kasheta. Sunyi kokawan k’wace bindiga a tsakaninsu kwatsam harsashin ta huda Maleeka a cikinta. Domin kuwa a binciken da akai na gawan Maleeka harsashi na farko a kwance ya huda cikinta ba a tsaye ba, wanda hakan ka iya zama kokawa suke bindigar tana kwance tsakankanin jikkunansu ko wanne cikinsu na son k’wace bindigar kwatsam harbi ya same Maleeka. Sai Yusuf ya k’ara mata harsashi guda dan ya tabbatar ta mutu gaba d’aya, wann yana iya zama dalilin da yasa Yusuf ya harba mata second bullet.. Yayi saurin kawar da duk wata shaida ko alama.. Abinka da k’wararre yayi k’ok’ari yaga bai bar wani trace da zai bayyanasa a matsayin makashin Maleeka ba. Saidai kuma na samu burbud’in glass na frame da ya fad’o ya fashe a lokacin da suke kokawa da Maleeka.. Sann akwai alamun footprint d’insa wanda ya manne jikin tile ba tareda ya kula ba.. Yayi komai ne cikin gaggawa Sai ya nufi mab’oyarsa wanda ga dukkan alamu baida nisa da gidan Maleeka ya canza shigarsa ya k’ona duk wasu abubuwa da yai amfani dasu wajen kashe Maleeka.. Amma fah ya mance bai k’one wann takalmin tasa ba harma yaci gaba da sakata.. Watak’ila takalmin tanada mahimmanci ne a wajensa sosai.. Kaman dai yanda yau ya sakota a k’afafunsa.”
Gaba d’aya suka zuba masa idanun jin yanda yake aiki da tunani da iliminsa na bincike yana fayyace masu hanyar da Yusuf yabi ya kashe Maleeka tamkar yana a wajen.
Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Na kira Yusuf naji ko ya isa location amma sai yace mun bai isa ba holdup ya rik’esa.. A yanda akai advancing hanyoyin garin nan babu irin wann holdup d’in da zai hana Yusuf isa wajen Maleeka.. Nayi amfani da lokaci nayi calculating time d’in da ya d’auka kafin ya isa gidan Maleeka.. Kaman yanda nace maku daga yanda yake zuwa gidan Maleeka yaci ace yaje gidan Maleeka ya dawo amma sai yace mun holdup ne ya rik’esa wanda hakan yasa muka isa gidan Maleeka tare tare bayan ya sauya shiga yayi destroying duk abubuwan da yayi amfani dasu wajen kashe Maleeka.. Sanda muka Zo gidan Maleeka mun taddata kwance cikin jini numfashinta yana gab da barin gangar jikinta.” Ya duk’ar da fuskarsa yana duban Yusuf “Yusuf bai k’arasa kan gawar Maleeka ba Sai ya tsaya daga baya dan kar tai pointing d’insa da hannunta. Har saida Maleeka ta cika kafin ya k’araso kanta..”
Ya d’ago yana duban su DIG kafin yaci gaba da fad’in “Sir, bayan binciken da nayi a daren Jiya, a safiyar yau sai nayi tunanin komawa wancan asibitin domin na binciki security da alhakin kula da na’urar ke wuyansa naji wanene ya sayesa ya b’oye wann Footage d’in da muke nema daga farko.. Na nuna masa hoton Maleeka na tambayesa ko itace ta sayesa ta rufe bakinsa da kud’i amma Sai ya girgiza mun kai yace ba ita bace.. Daga nan na soma tunanin hunch d’ina ka iya zama daidai.. Sai na nuna masa hotunan sauran abokan aikina.. A daidai hoton Yusuf ya tsaya yana kuma duba kafin yai pointing nasa yace mun shine mutumin da ya sayesa..”
Ya d’anyi taking excuse kafin ya nufi k’ofa ya tura wani police ya taho da mutumi security d’in asibitin da Mu’azzam ya nemo Footage d’in da yaga Maleeka ciki.
Da tsananin mamaki Yusuf ke dubansa dan baiyi tsammanin Mu’azzam zai iya kamosa haka ba.
Mu’azzam yai nuni da mutumin wanda kansa ke duk’e yace “Wann shine security d’in da Yusuf ya saya da kud’i ya rufe bakinsa dan kar ya fitar da CCTV footage na wann asibitin dana gudanar da binciken DNA test a can. Abun mamaki na tura Yusuf ya gudanar mun da bincike a wann asibitin domin mu kub’utar da abokin aikinmu Assad ba tareda nasan cewa Babban b’eran na tura ya kamo k’aramar B’era ba.. Koda yaje sai ya buga wann wasan.” Ya k’arashe yana sakin murmushi.
Yusuf ya kifa kansa kurum a k’asa dan tuni mutumin ya kuma nuna Yusuf d’in a matsayin wanda ya saye bakinsa da kud’i.
Bayan ya gama bada statement d’insa Mu’azzam yai alama ma D’ansandan da ya shigo dashi cewa ya fita dashi security d’in. D’ansandan ya jinjina kai yana mai furta “Yes sir.” Lokaci guda ya janye security d’in suka fice.
Assad mamaki da tsoron mutanen duniya ya kuma cikasa yayinda Chief keta raba idanu tsoron Mu’azzam fal zuciyarsa ganin ya kama duka yaransa Yusuf da Maleeka. Wanda ita kanta Maleekar batasan Yusuf d’in yaron Chief bane har Sai randa zata bar duniya.. Idan kuwa Mu’azzam zai iya kamo Yusuf haka Tabbas ya kusa cimmasa kenan.. Ji yai kaman ya cire kakin dake jikinsa yai jifa da ita sabida tururin zafi dake kuma fito masa daga can k’asa.
Tafin DIG ne ya dawo da hankalin Chief.. DIG da sauran ‘yansanda suka mik’e suna tafasa Inspector Gamji bisa wann k’ok’ari da yayi na kamo mai cin amanan aikin D’ansanda da kuma k’asa.
DIG yana tafawa yake fad’in “Impressive..! Gamji Mazan fama.. Well done Inspector Gamji.!”
Ai Chief ma tuni ya soma tafawa dan kar a zargesa. Yanayi yana Washe baki yana fad’in wann ba ci gaban Mu’azzam bane kawai ci gaban Team d’insu ne gaba d’aya tinda shine rahamar case d’in ke hannunsa.
Mu’azzam Sai duban Chief yake cikin zuciyarsa yana ayyana cewa saura kai Chief Jaja.. Sannu a hankali zamu iso Kanka Babban B’eran B’eraye.. Bayan mun gama da muk’arabbanka zamu iso kanka ne da izinin Allah.. B’eran banza sai na capko wuyanka In sha Allahu kafin na bar aikin D’ansanda.” Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai mik’awa DIG daketa faman mik’o masa hannu sukai masabaha. Yana kuma masa jinjina had’ida tabbatar masa samun goyon bayansa har a isa k’arshen wann case d’in.
Mu’azzam ya sara masa yana mai masa godiya “Wann nasaran mu ne gaba d’aya NPF Sir, dukda cewa ban kai yanda kake tunanin na kai ba amma na gode da kalaman yabo Sir.” Ya k’arashe yana sara masa dan yasan ba iyawarsa bane ko k’warewarsa ya kaisa wann matakin. A’a taimakon Allah ne da fawalla masa lamuransa da yayi.. Amma ko d’aya bai yarda akwai iyawarsa ko k’warewarsa a ciki ba.
Bayan sun fito daga Zauren taron kai tsaye cell d’in da akai detaining Yusuf nan cikin Headquarters d’in suka nufa shida Assad.
Hannayen Mu’azzam dafe da belt d’insa yake duban Yusuf yana tuna tsawon lokacin da ya kwashe yana cin amanarsu. Bai iya cewa komai ba sabida zafi da zuciyarsa ke masa. Ya tsani a raina masa hankali a ha’incesa.. Sun d’auki Yusuf d’aya daga cikinsu amma daga k’arshe yaci amanarsu..
Assad ne ya iya furta “Why did you do it.. Maiyasa ka aikata..?”
Yusuf ya mik’e ya k’araso gaba garesu yana sakin murmushi “I was only following orders.. Dear Team mate.” Ya k’arashe murmushin saman fuskarsa.
Assad ya girgiza kai yace “Waye yake baka umarni.. Was it Danger..?”
Murmusawa Yusuf ya kumayi “Ka bar shi wanda yake tunanin yanada brain d’in yayi tambayoyin amma ba kai ba wanda mace tai outsmarting naka.”
Izuwa lokacin ran maza ya b’aci, wani irin finciko wuyansa Mu’azzam dake aika masa mugun kallo yai.. Ta cikin kmarafunan cell d’in ya tura hannu ya capko Yusuf ya matsesa sosai kai kace zai fiddosa ta cikin matsin k’arfen ne. Dan wani irin damk’a ya masa ya shak’esa kaman mai shirin aikasa lahira har saida Assad ya k’waci Yusuf d’in da k’yar.
Yusuf ya zube nan wajen yana fidda numfashi da k’yar. Mu’azzam kam sabida b’acin ran abinda Yusuf yai kasa cewa komai yai saima ficewa da yai daga cikin ofishin gaba d’aya.
Assad ya dubi Yusuf ya girgiza kai disappointedly kafin yasa kai yabi bayan abokinsa Mu’azzam.
Saida Chief ya tabbata sun bar Ofishin kafin ya nufi wajen Yusuf.
“Kar ka damu zamu kula da iyalanka.. Sann zan samo maka hanyar da zakai escaping daga prison.. Kawai don’t rat us out.. Ka iya takunka ni kuma na maka alk’awarin zan maka komai..”
Yusuf ya tsaresa da idanu kafin ya murmusa da gefen baki yace “Kana tunanin yanda Inspector Gamji yai rantsuwa Sai ya kai k’arshen case d’in nan bazai kai bane.. Kana tunanin zaka iya dakatar dashi ne.. Idan ni da kai bamu b’ata ji da gani ba.. Inspector Gamji ya riga yasan da zaman Boss At the Top ko ince maka Babbanmu A Tushe..”
Murmusawa Chief yai kafin yace “Yasan abinda ya sani dai amma bazai tab’a sanin wanene Jemage ba. Yusuf ka iya takunka mu kuma zamu kub’utar dakai.”
Yusuf ya tsare Chief da idanu kafin ya soma jinjina kai yana fad’in “You better keep your words domin idan kai failing d’ina Chief believe me I won’t go down alone.. Ni ba kamar Maleeka bane.. You know I also have my own ways of doing things.. Zan baka mamaki idan ka zab’i juya mun baya.”
Chief ya kafesa da idanu kafin ya saki gajeriyar murmushi.. Lokaci guda yasa kai ya bar wajen.
Yusuf yai zaune yana tunanin makomar rayuwarsa data ahalinsa.
A haka har aka kwashe kusan sati biyu suna gudanar da bincike kan Yusuf.
Dik yanda Mu’azzam yaso ya fitar da wani abu daga bakin Yusuf abu yaci tura.. Duk kalan horon da za’aiwa mai laifi dan yayi magana anyi ma Yusuf amma yak’i sanar dasu komai.. Saima raina masu hankali da yai da fad’in Danger ne Boss d’insa.
Shi kaw Mu’azzam Chief yake so ya kama dan yasan Chief shine Babban b’era a Department d’in nasu saidai haka kurum ba tareda hujja ba baida ikon kamasa.
A wajen matarsa Sadiya kurum yake samun sauk’in abubuwan wajen aiki, saiko abokinsa Assad wanda Allah ya nufa ya tsallake tuggun azzalumai.
A b’angaren Sadiyar ma takan ziyarci Su Ummanta, saidai Umma ta hanata zuwa wajensu akai akai. A cewarta ba birgewa bane ace kullum matar aure tana gantali saman kwalta. Kamata yai ta killace kanta a gida ba taita fita barkatai ba hakan ba birgewa bane. Haka Sadiya zatai Ta ture turen bakinta babu dai yanda ta iya ne. K’arshe ma Umma wa Mu’azzam d’in tai magana tace ya daina biye Sadiya Wai idan zai fice aiki Sai ya kawota gida ya aje. Umma tace ya dinga barinta can gidanta idan abokan gira take nema za’a ke kawo mata su Ashir tinda ta kula kaman harda kad’aici ke damun Sadiyar. Dan a ‘yan kwanakin Mu’azzam na yawan jimawa wajen aiki ga fita bincike da suke shida Assad wasu lokutan ma har sukanyi dare sosai. Umma tace da ita ko wace mace haka tai hak’urin zaman gidan miji itama tai hakan tinda tasan ga yanayin aikin mijinta.
A b’angaren Safeenah da Mommy kaw, Mommy sai rainon cikin Safeenah take ba tareda Safeenar ta kula ba. Saidai yawan zazzab’i da k’anan ciwon kai dake damunta yasa Ta soma shakku.. Sai wann lokacin ma take tunanin Ta wuce kwanakin al’adarta tuntuni.. Calendar d’inta Ta duba tana mai kuma mamakin yanda abun ya canza da yawa.. Anya kuwa lafiya take.. Ta soma tinanin kwanaki biyu da suka shige taso zuwa asibiti amma sai Mommy ta hanata tace Malaria ce kawai no need taje a mata test zata bata anti Malaria tasha.. Ita dai cikin Magagin bacci ma ta amshi maganin tasha. Zata iya cewa batasan kalan maganin da Mommy ta bata tasha ba.. Anya bazata tafi asibiti ba.. Ta mik’e tana tunani.. Daidai lokacin Dattijuwar mai aikinsu ta