Showing 117001 words to 120000 words out of 209154 words
to trace Danger’s location, Sir.”
Dikda Zuciyar Chief Ta yanke hakan bai hanasa nuna Farin cikinsa a fili ba.. Yana tafe hannayensa yake fad’in “Then what are we waiting for Detectives.. Move it, faster.. Let’s catch Danger.!” Ya fad’i yana tafe hannayensa alamun Su k’ara sauri.
A haka suka dinga ficewa har dai Mu’azzam yazo ficewa, suka tsaya suna duban juna shida Chief.
Murmushi Chief ya sakar masa kafin yace “Well done Inspector Gamji.. I must congratulate you and your team..”
Murmushi da gefen bakin Mu’azzam ya sakar masa yana Soka bindigarsa jikin belt d’insa kafin yace “Tukunna ma Sir.. Sai kaga Danger da accomplices d’insa behind bars.” Yana ida fad’in haka ya sarawa Chief kafin yasa kai ya shige.
Chief yabi bayansa da mugun kallo yana huci, lokaci guda yake duban allon binciken nasu nan yaga an zana circle an rubuta B.A.T a sama ga kuma question mark cikin circle d’in.. Anyi linking circle d’in da hoton Danger. Zuciyr Chief yai wani irin bugawa.. Gumi ya shiga ketowa Chief tako Ta ina.. Kar dai Maleeka ta sanar da Mu’azzam wani abu akan BAT.. Lallai Maleeka tana wasa da rayuwarta. Ya lura komai zatayi akan Mu’azzam.
Cikin tsananin fushi mai gauraye da tashin hankali Chief ya daki garu kafin yasa kai ya fice daga ofishin.
Kallon da Chief yaiwa Maleeka tasan cewa akwai matsala, tasa kai Ta shige cikin sauri zuciyarta na yankewa.
Mu’azzam ne ya rarraba masu bulletproof vests ko wannensu ya aza saman rigarsa, gaba d’ayansu motar Office suka shiga. Assad ke driving Mu’azzam na gefensa Yusuf da Maleeka suna mazaunin baya.
Saidai suna isa sukaji an soma kaima motarsu attack da harbi alamun su Danger Sun riga sun San da zuwansu an sanar dasu. Take sukai holding positions d’insu Mu’azzam na fad’in”No one shoot.. My wife is in there..”
Suka jinjina kai suna fad’in copy. Su Danger suka ci gaba da harbi kafin daga bisani wutan ya tsagaita.
Mu’azzam ne yai masu alama da hannu da ido kan su soma matsowa kusa suna nufan ginin cikin kwanton b’auna. Haka kuwa akai a hankali suka dinga matsawa kusa cikin bin umarnin Mu’azzam har suka isa ginin..
Wani mutumi sanye da bak’ak’en tufafi fuskarsa rufe da bak’in mask shine yai saitin Mu’azzam zai harbesa ba tareda Mu’azzam d’in ya gansa ba Maleeka ta k’arasa da sauri ta tare wa Mu’azzam harsashin tana kiran sunansa dan ita taga mutumin.. Take harsashin ya sameta a hannunta.. Gaba d’aya suka juyo suna duban Maleeka da ta karb’ewa Mu’azzam harsashi ta duk’a wajen tana cije lab’e rik’e da hannuta yanda harsashi ya huda jini na zuba.. Yusuf da Assad suka k’araso a guje suna ambato sunan Maleeka yayinda Mu’azzam yai Chasing mutumin a guje.. Gini ne upstairs mai tsawo irin abandon gini d’in nan wanda zallan Kango ne.. Haka mutumin ya dinga haurawa sama a guje yana sakowa Mu’azzam harsashai Mu’azzam na kaucewa yana kuma chasing d’insa dan a raye yake son capke Sa. Saida ya bari Mu’azzam ya isa sama saura kad’an ya kamasa kafin ya dirk’o yana kuma kai masa harbi.. Mu’azzam ya kama jikin bargwajajjen staircase din kenan zai dirk’o yabi bayansa yaji kaman kukan mutum cikin wani d’aki dake rufe .. Cikin sauri ya juyo yana duban d’akin ya daina chasing mutumin..
A hankali ya furta “Sadee.!”
Da k’afarsa ya daki k’ofar saida ya b’allata.. Can ya hangota d’aure saman kujera idanunta a rufe haka ma bakinta.. Jikinsa har rawa yake ya isa a guje ya cire blindfold d’in da aka rufe mata ido dashi..
Suna had’a ido taji wani irin kuka yazo mata.. Lokaci guda yaci gaba da kwanceta yana fad’in “It’s okay.. You’re safe now..!” Ya k’arashe yana mai rungumarta cikin jikinsa.
Wani kukan Ta kuma fashewa dashi jikinta sai rawa yake alamun bak’ar azaba yunwa da galabaita had’ida tsananin tsoro da tashin hankalin da Ta tsinci kanta ciki.
Kaman wacce ta tuna wani abu tai k’ok’arin cire jikinta daga nasa ta shiga girgiza kai tana k’ok’arin matsawa da baya take fad’in “No no no.. Don’t touch me.. Kar ka tab’a ni kar kazo kusana..”
“How do I save you idan ban tab’a ki ba.!” Yai maganar cikin daka tsawa..
Juyawan da zai yaji kaman abu na reading ashe bomb ne a gefe Danger ya aje ma Sadiya da niyyan k’onata.
Mu’azzam bai kuma sauraronta ba ya shiga girgiza kai yana furta “Oh shit..! Come here now..” Ya sunkuceta tamkar Baby ya soma gudu da ita tana cikin hannunsa sai had’e stirs yake yana tsallakewa gudun kar bomb d’in Ta tashi dasu suna cikin ginin.
A can waje kuwa Maleeka dai tana fama da hannunta da aka harba Assad da Yusuf ne sukai chasing mutumi mai bak’in kayan bayan ya samu fitowa daga building d’in.. Suna guje suna bata kashi tsakaninsu.. Nan harsashi ya samu Assad gefen wuyarsa kusan kafad’arsa yanda Bulletproof vest d’in bai rufe ba.. Ya duk’a a wajen yana kame wuyarsa da tuni jini ya soma kwarara..
Yusuf ya dakata da chasing mai bak’in kaya ya duk’a yana duba Assad dake cikin pain yana k’ok’arin taimakawa d’anuwansa.
A can building d’in kaw wata jahilar tsalle Mu’azzam yai still tana rik’e cikin hannunsa daidai sanda Bomb d’in tai exploding..
Haka ya kwanta kan Sadiya ya rufeta ruf sand bomb d’in ta tashi dan ma kar wani abu ya sameta.
Maleeka ma ta juyar da fuskarta tana mai kwanciya flat a k’asa sanda bomb d’in tai exploding.
A hankali komai ke lafawa. Mu’azzam ya mik’e da k’yar yana jijjiga Sadiya dake kwance k’asar sa wacce ta koma tamkar bata numfashi.
Maleeka ta bud’e idanunta da k’yar tana duban Mu’azzam dake ci gaba da jijjiga Sadiya yana fad’in Ta bud’e idanunta.
Lokaci guda yaci gaba da jijjigata yana fad’in “No.. No.. Stubborn head.. Not now.. Please wake up.. Wake up.. wake up now..!” Yana maganar yana jijjigata.
Dukda rad’ad’in ciwon dake jikin Maleeka bai hanata zuba idanu tana dubansu kaman Ta samu TV.. Tinda take bata tab’a ganin Mu’azzam ya birkice kan wata mace ba sai wannan yarinyar.. For the first time da zata iya cewa taga Mu’azzam Gamji dumu dumu cikin kogin soyayya..
Haka ya dinga jijjiga Sadiya yana fad’in Ta tashi.. K’arshe bakinsa ya d’aura saman nata yana hura mata iska..
Maleeka kaw ji tai wani abu ya tokare mata mak’oshi sanda tanga Mu’azzam ya saka bakinsa saman na Sadiya. Tai saurin rintse idanunta had’ida ciza labb’anta.. Shekara da shekaru tana kwad’ayin irin haka ya kasance tsakaninsu sai gashi yau d’in tanaji tana gani a gabanta yake saka bakinsa cikin na wata.. Ji tai zafin ciwon da taji dominsa na k’aruwa.. Ta kuma rintse idanunta da k’arfin gaske hawaye mai zafi na gangaro mata.
Wani dogon numfashi Sadiya taja had’ida bud’e idanunta. Bai wata wata ba ya mak’aleta tsam cikin jikinsa kaman mai tsoron kar wani abu ya kuma raba tsakaninsu.
Daidai lokacin Su Assad da Yusuf suka k’araso. Yusuf na tallafe da Assad wanda jini ke zuba sosai daga jikinsa. Cikin sauri Mu’azzam ya bud’e mota ya zaunar da Sadiya ciki kafin ya k’araso wajen abokansa. Assad ko iya bud’e idanunsa bayayi dan sosai harsashin ta shigesa gashi a waje mai had’ari harsashin ya samesa.
Sai wannan lokacin Chief ya taho wajen da backup harda ambulance dan tinda aka harbi Maleeka dama suka nemi taimakon ambulance.
Kan kace mai an soma basu taimako na gaggawa.
Assad aka fara baiwa taimako dan yafi kowa buk’atan taimakon.
Mu’azzam ya k’araso da sauri lokacin da aka d’aura Assad saman doguwar gadon tura marassa lafiya. Hannun Assad ya kama yana fad’in “Zaka samu lafiya brother.. In sha Allah..!”
Cikin jin jiki Assad ya bud’e idanunsa da k’yar kafin ya murmusa ya jinjina ma Mu’azzam kai yace “Ina Sadiya.. Did you save her..?”
Mu’azzam ya jinjina masa kai yace “She’s dafe now..” Ya d’aga masa babban yatsarsa alamun jinjina yana mai sakar masa murmushi da k’yar.
Lokaci guda aka tura Assad cikin ambulance kafin aka saka masa na’uran oxygen.
Yusuf ya dubi Mu’azzam yace “Zan kula da Assad.. Just go to your wife.” Yai masa nuni da ido zuwa cikin motar yanda Sadiya ke tak’ure waje guda.
Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya d’an dafa kafad’an Yusuf alamun godiya.
Lokaci guda Yusuf ya shige cikin ambulance d’in..
**
Safeenah da taga Mommy bazata d’auki wayarta ba sai ta yanke shawarin kiran Aunty Shemau. Da kuka ta soma ma Aunty Shemau tana fad’in Mommy tana fushi da ita bata d’aga wayarta.
Aunty Shemau ta tab’e baki kad’an tace “Safeenah ni fah na baro gidanku tin daren jiya.. Your Uncle came ya d’aukeni mun taho masauk’insa tare.”
Safeenah tace “Aunty Toh ni yanzu ya zanyi da Mu’azzam ne.. Wllhi Aunty ko kallo fah ban ishesa ba dan Allah kizo ki yanzu..” Ta k’arashe wasu hawayen na gangaro mata.
Aunty Shemau Ta dubi mijinta dake zaune gefe kafin ta d’an sauk’e ajiyan zuciya tace “Shikenan Safeenah zan tambayi Uncle d’in naku idan ya barni zaki ganni..”
Cikin kuka Safeenah tace “Aunty idan Uncle Salman d’in na kusa put him through zan tambayesa da kaina.”
Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Kar Safeenah ina nan zuwa kinji koh.. Kiyi hak’uri. Yauwa sai nazo..” Daga haka katse kiran tai tana duban mijinta da ya kafeta da idanu.
“Mai wannan shashashar kuma take buk’ata..?” Ya tambaya yana duban Shemau.
“Banda akan Mu’azzam.. Kasan ita wannan batada tinani batada hankali sam indai akan Mu’azzam ne.. So take naje gidan nata ta rasa abinyi..”
Uncle Salman ya jinjina kai kafin yace “A tak’aice dai zuwanki garin nan baiyi amfani ba Shemau.. Kin kasa d’auko min wad’annan Documents d’in.. Wad’anda idan na mallakesu tamkar na mallaki kaso na dukiyar Mu’azzam ne da d’anuwana ya handame..”
Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Idan akan abinda ya shafi takardun kud’i ne babu wanda ya isa yama D’anuwanka wayo.. Dik k’ok’arina na rasa ina takardun suke.. Kuma da alama baya sanar da matarsa wasu abubuwan.. Amma mai zai hana ka cire idanunka akan dukiyar Mu’azzam tinda yanzu company dake Adamawa kai kake rik’e dashi harma da gidan gonar..”
Katseta yai da fad’in “Samun mahimman takardun nan su zasu sa Company ta zama nawa gaba d’aya amma muddin ba’a samesu ba baza’a daina cire kason Mu’azzam da ‘yar uwarsa harma da mahaifiyarsa a cikin dukiyar ba. Wann takarda shaida ce zai tabbatar cewa basu da kaso cikin dukiyar.. Inada tabbacin lokacin da Yayanmu ya mutu Marwan shi ya d’auke takardun nan..” Ya k’arashe yana kuma zagaye d’akin lokaci guda yana kurb’an shayi.
Aunty Shemau ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tace “Yanzu kam da ka d’auko ni ai ka b’ata komai saidai mu dake gwada sa’an wani lokaci.”
Fuzar da fuci yai yana mai jinjina kai a hankali.
**
‘Yansanda ne tin daga k’ofar asibitin har cikin asibitin. Tuni an shiga da Assad d’akin operation.. Sadiya ma Ta k’ara fainting a asibitin dole aka bata Gado dan gaba d’aya babu k’arfi da kuzari jikinta gashi har lokaci bata daina razana ba sabida abinda ya faru da Ita. Da alama tin safiyar ranan da aka d’auketa bata saka komai a cikinta ba.. Kwana guda kenan tai babu abinci ya tsoro da razana dole aka d’aura mata ruwa a nan asibitin.
Mu’azzam yana zaune gefenta yana dubanta idanunta a lumshe, da gani baccin azaba take da kuma tsoro. A hankali yakai hannunsa saman goshinta yana shafawa a hankali “Bazasu k’ara samun damar cutar dake ba.. Na miki alk’awari..” Ya fad’i idanunsa akanta
Lokaci guda kuma yai shiru yana nazari.. Maiyasa suke bibiyanki da ahalinki.? Maiyasa suke so su shafeki Keda ahalinki..?
Zuciyarsa Ta basa amsa da fad’in ‘Sabida suna tsoro kar Sagir ya sanar da ita wani abu tinda har saura kad’an ya aureta.. Zasuyi tunanin yarinyar tasan duk wani shirinsu daga wajen Sagir.. Watak’ila harta ahalinta ma sun sani..”
Shafe fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kafin ya mik’e yana duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu.
Fitowa yai daga d’akin ya dubi ‘yansanda guda biyu dake tsaye k’ofar d’akin yace su kula sosai babu mai shiga Sai likitan nan da suka gansu tare..
Suka jinjina kai suna sara masa. Lokaci guda ya shige nan ya hangi Maleeka ana rufe nata wound d’inta a dressing room.
Kaman zaisa kai ya shige sai kuma ya dawo da baya. Da wutsiyar idanu Maleeka take dubansa.. Ganin ya tsaya yana dubanta ya sa Maleeka marairaicewa kaman yau ne bullet ya soma kuskuranta.
Mu’azzam ya nufo d’akin still idanunsa akanta, daidai lokacin da aka fama rufe mata ciwon.
Ta d’ago tana dubansa, k’warjininsa ya hanata duban k’wayar idanunsa, hakan yasa Ta sadda kanta a hankali.
Hannayensa dafe da kunkumi yake dubanta “You shouldn’t have done that, you know..”
Ta d’an d’ago a zabure tana dubansa jin abinda yace
Mu’azzam ya kuma jinjina kai kafin yace “Maisa zaki karb’a mun harsashi.? Next time kar ki sake abu makamancin haka Maleeka.. Get well soon..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige.
Maleeka Ta saki baki da hanci tana dubansa, Ta tare masa harbi harsashi ya sameta maimakon ya samesa amma ya rasa abinda zai fad’a mata sai wad’ann kalaman.. Maimakon yai mata godiya ko ya nuna kulawarsa akanta amma abinda zai iya fad’i kenan sabida tsaban girman kansa da isansa.. Tai k’wafa tana jin zuciyarta na mata wani irin k’una.. Nurse d’in ta k’araso tana fad’in bari a k’arasa rufe mata ciwon.
Tsaki Maleeka tai tace “Barshi bana buk’ata..”
Nurse d’in tace “But infection zai iya shiga ki tsaya a k’arasa rufewa.”
A kufule Maleey tace “Ank’i a tsaya d’in.. Baza’a tsaya ba.. Infection d’in ya gama shiga a daidai lokacinda wanda akaji ciwon dominsa ya nuna rashin kulawarsa.” Tana ida fad’in haka ta mik’e tana huci.
Chief ne ya shigo yace ma nurse d’in ta d’an basa Moment da Maleeka. Babu musu nurse d’in ta basu waje.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*39*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chief ya k’ura mata idanu yana girgiza kai “Ban yarda baki sanar dashi komai akan BAT ba.. If you can take a bullet for him na tabbata zaki iya masa komai.. So you better tell me the truth right now.. Mai kika sanar da Inspector Gamji gameda BAT.?” Ya k’arashe kaman zai shak’ota.
“Wane irin rantsuwa kake so na maka..? Na rantse maka da Allah ban sanar dashi komai ba.. Yanda kaga ya rubuta B.A.T jikin board haka nima na gani.. I’ve no clue mai hakan yake nufi..”
Jaja ya jinjina kai ya d’an kuma matso da fuskarsa kusan na Maleeka. Cikin yanayi na gargad’i yake furta “You better be telling the truth.. Because once I find out k’arya kike mun Maleeka..?” Ya murmusa kafin yace “Ki fara k’irga kwanakinki..”
Har ya juya zai fice ya kuma dawowa “Ki tabbata kin samo mai Mu’azzam ya sani gameda BAT.. Wannan shine next Assignment d’inki..”
Murmusawa Maleeka tai kafin Ta girgiza kai tace “Da alama har yanzu bakusan da wa kuke dealing ba Sir.. Do you think this is an easy task..? We are talking about Mu’azzam Gamji here..” Ta gyara tsayuwarta kafin taci gaba da fad’in “Guy d’in nan is a complete savage. I risked my own life for him.. I took a bullet for him.. But a simple thank you ya gaza fad’a.. Irin wannan mutumin nan ne kuke tsammanin shiga jikinsa abu ne mai sauk’i..? Mu’azzam Gamji is not like every other guy.. Kuyi hak’uri amma zai matuk’ar wuya ku kaisa k’asa..”
Chief ya murmusa kafin yace “Ko bai fad’a miki ba yasan he owes you a huge of gratitude.. And deep down ya gode miki.. Kuma bazai tab’a mance sacrifice d’in da kika masa ba.. Kawai kaman yanda kika ce ji da kansa bazai barsa ya nuna miki hakan ba ko ya furta.. But believe me kin samu yardarsa daga yanzu.. Mu’azzam Gamji will never doubt you bayan sadaukarwa mai girma da kika masa.. Ki ringa da kin samu yardar Mu’azzam, yanzu abinda ya rage miki shine kisan mai yake ciki, kiyi uncovering duk wasu abubuwan da ya sani especially akan BAT.” Ya murmusa kafin ya kuma furta “Get well soon sweetheart..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.
Huci Ta kuma saki kafin Ta fito waje, nan ta hangi motar Mu’azzam a wajen. Ta d’an d’aga gira guda sama tana duban motar.. Toh kenan bai tafi bane ko k’ak’a.? Wata Zuciyar ta bata amsa da fad’in Ina zai tafi tinda Queen of his heart tana kwance anyi admitting nata.. Ta fuzar da fuci mai zafi tana furta “Goddamn your pride Inspector Gamji..!” Tana ida fad’in haka Ta nufi motar tasa dan a zatonta ko zata hangosa ciki.
Tai tsaye tana k’are wa motar kallo.. A backseat ta hango wani abu cikin transparent nylon.. Tai saurin matsowa tana duban abun.. Hula ce d’auke da rubutun B.A.T a fuskar hular.. Take ta soma tina abinda taga Mu’azzam ya rubuta saman allon bincikensu.. Kenan wannan ne clue d’in da ya samu gameda BAT ko menene.. “I need to find out what he knows.” Ta furta a hankali tana mai ficewa daga asibitin lokaci guda ta tari Cab ta shige tana dialing layin Chief..”
**
Kai tsaye bayan ya fito daga asibitin gida ya wuce dan ya samu yai wanka ya sake fitowa. Bud’e k’ofar parlorn da zai ya hangi used tissue papers baja baja a k’asa wanda Safeenah tasha kukanta ta goge fuskarta dasu, ya hangi dining table nan ma yaga a wargaje, ko ina very scattered.. Ga plates a saman dining table d’in ga abinci har saman table d’in tin daga cikin takeaway pack har k’asa.. Ga ledojin da aka sayo abincin ciki suma suna nan a wajen ba’ai disposing nasu ba.. Fuzar da fuci yai a hankali kafin ya nufi upstairs cikeda k’yank’yanin gidan gaba d’aya kaman ba kwana guda Safeenah tai cikin gidan ba ko Ina kaca kaca..
D’akinsa ya nufa ya soma rage kayan jikinsa. Daidai lokacin Safeenah ta shigo taci uwar gayu kai kace ba itace tai kaca kaca da gidan ba tsaban yanda Ta tsara gayu ma jikinta. Fuskar nan Sai k’yallin kwalliya take an zubo da gashi sai zuba k’amshi ake.
Saurin K’arasowa tai tana k’ok’arin b’alle masa botiran rigar nasa. Ganin bai gwasaleta ba ya sanyata kuma rausaya idanu tana ci gaba da b’alle masa botiran cikin salo na jan hankali “My Halal banji zuwanka ba..” Ta fad’i cikeda shagwab’a.
Kauda fuskarsa yai kad’an kafin yace “Ina zakiji kina can kinata tsara kwalliya ma jikinki kin bar gidanki kaman bola..”
Ta d’an turo baki tace “Yanzu zan gyara.. Na kawo maka abinci ne...