Showing 201001 words to 204000 words out of 209154 words

Chapter 68 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3065

sallama da ita waje.

Ta d’an rage girman idanunta tana dubansa cikeda mamaki “Ni kuma sallama Patrick.. Ni kaw wa na sani a nan..?”

Patrick yace “Matar Oga ce da take gidan nan da..”

Yanzu kam ta fahimci Safeenah ce tazo. Ta d’an lumshe idanunta kad’an tana k’ok’arin saita kanta dan saida taji gabanta ya fad’i da Patrick yace Safeenah ce mai sallama da ita, ta shiga tuna jiya Mu’azzam wajen Safeenar ya tafi bai kuma waiwayanta ba har safiyar yau d’in.

“Ma’am should I go and tell her you are not available..?” Patrick ya tambaya cikeda risinawa.

Sadiya ta girgiza kai tace “Maiyasa bata shigo ba tace ka mata sallama dani..?”

Patrick ya d’an girgiza kai kad’an yace “Nima ban Sani ba Ta dai ce na miki magana bazata shigo ba.”

Ta jinjina kai kad’an tana fad’i cikin zuciyarta ‘K’ila ta tuna arangamarta da Karnuka ne kwanakin baya Shiyasa ta zab’i kar ta shigo d’in.. Da wann tunani Sadiya ta nufi waje da zummar ganin Safeenah..”

Safeenah tana hangota ta bud’e motar ta fito muguwar murmushi saman fuskarta. Sai faman k’are ma Sadiyar Kallo take yanda ta wani k’ara cika da kyau an samu duniya an baje Koli a Gidanta.. Saima rage girman idanunta Sadiyar take tana kare fuskarta da hannayenta sabida hasken rana irin mai zafin nan da ya bayyana. Kana ganinta kasan ba fitan take ba, hutu da jin dad’i sun zauna a wajen. Fatarta kad’ai ka kalla zai tabbatar maka da hakan.

Safeenah taci gaba da tab’e baki tana dubanta.

Yayinda Sadiyar ta sakar mata murmushi tace “Ya kika tsaya daga waje.. Mu k’arasa ciki mana.. Allah yasa da alkhairi kika Zo..”

Safeenah taci gaba da k’are mata kallo tin daga sama zuwa k’asa kafin ta murmusa tace “Ba shiga nazo yi ba. Zuwa nai na baki sak’o..”

Sadiya ta murmusa kad’an tace “Toh banda abinki nan fah gidan Yayanki ne kinga ai bazan hanaki shiga ba matuk’a ba da tashin hankali kika Zo ba..”

Safeenah ta murmusa mai sauti tace “Kar ki nuna mun bariki yarinya.. Tar nake kallonki.. Ki gama duk wani iskancin da kutungwilarki na d’an lokaci ne.. Naji dad’i da kika San cewa ni da shi tushe guda ne.. Kece bare a tsakaninmu.. Har abada mu zamu tab’a rabuwa ba.. Domin kuwa akwai jini mai k’arfi da ya had’amu..” Ta saki murmushi tana mai d’aura hannunta saman flat tummy d’inta da kaman babu komai ciki.. Lokaci guda take ci gaba da fad’in “Shin kin tambayi mijinki jiya da wa yake tare a daren jiya..?” Ta wani rausayar da idanu kafin taci gaba da shafa cikin nata tana fad’in “Koda yake naga kinata kiransa amma yanata katse kiran naki.. Toh Maiyasa ma bazai katse ba alhali yana tsaka da jin dad’insa..”

Izuwa lokacin k’wallan da Sadiya keta k’ok’arin dannewa Sun gama ciko idanunta..

Safeenah tai murmushin cin nasara ganin yanayin Sadiyar ya sauya gaba d’aya. Lokaci guda taci gaba da fad’in “My Halal bazai tab’a rabuwa dani ba.. Ni da shi are one.. Haka kikazo kika samemu kuma haka zaki fice daga rayuwarmu ki barmu tare kaman dai yanda kika samemu tare.. Kinsan Maiyasa..?” Ta k’arashe tana kuma matsowa kusan Sadiyar kafin ta janyo hannun Sadiya guda ta d’aura saman cikinta.. Murmushi bai bar saman fuskarta ba take duban Sadiyar wacce ta daskare tana kallon hannunta da Safeenah ta aza kan cikin ita Safeenar “Akwai ajiyar shi a cikin nan.. Zan bashi abinda babu wata mace da ta tab’a bashi a duniyar nan.. Product na soyayyarmu ne a cikin nan.. Tab’a kiji da kyau ki tabbatar da hakan... Kar kiga laifinsa , Kinsan mace mai juna tana buk’atar kulawa na musamman sann jariri na buk’atan d’umin mahaifinsa dole ya katse kiranki..”

Sadiya tai azaman fincike hannunta daga saman cikin Safeenah tana goge hawayen da suka shiga gangaro mata.

Safeenah Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “ Dama na fad’a miki gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Mijina nawa ne.. Ni kad’ai.. Ki fara k’irga kwanakin ki a gidan nan domin kuwa kwanakin ki a gidan nan K’ayaddadu ne.. Zaki fice ki bar mun Gida kaman dai yanda na miki alk’awari.. Bari dai muga mai zai faru yanzu..” Ta k’arashe a daidai sanda ta hangi motar Mu’azzam ya karyo layin.. Safeenah Ta silale nan wajen, tai saurin jifa da takalmanta gefe.. Ta kama k’asan rigarta ta keta.. Ta d’aura hannunta guda akai d’aya kuma ta aza saman kwamkwasonta daga nan ya da take duk’e gaban Sadiya. Ta shiga zunduma ihu tana kame cikinta tana kuka “Wayyo sun kwance mun karnuka.. Wayyo cikina.. Wayyo zan mutu.. My baby.. I don’t want to lose my Baby.. Wayyo Allah na..!”


Sadiya tai tsaye Cak cikeda mamaki tana kallon wani irin makirci da bata tab’a arangama da irinsa ba..




SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*63*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*








Hango Safeenah zaune darshan a k’asa da yai ya sanyasa saurin taka birki. Babu shiri ya bud’e marfin motar ya fito ya nufosu cikin sassarfa, ga Sadiya tsaye gabanta tamkar wacce aka dasa.

“Feenah.. Ke Safeenah lafiya.. What’s going on here..?” Ya tambaya yana k’arasowa.

Safeenah ta kuma kame bayanta tana nishi da k’yar “Wayyo.. Wayyo Allah na.. Karnuka Ta sakar mun.. Wayyo na shiga uku.. Wayyo zan mutu.. Bayana.. Marata..” Cikin kuka taci gaba da nuna Sadiya tana fad’in “Gata nan.. Itace tasa mai gadinka ya kwance mun Karnuka.. Ni banyi niyyan zuwa gidanka ba amma dashike inada appointment da Dr tau shine na taho muje tare tinda kaima Kanada iko akan D’anka kuma ka canci kasan dik abinda ake ciki... Shine wann matar taka tasa security man ya kwance mun Karnuka.. Dama ba yau bane kawai Ta tab’a mun haka.. Ranan ma ta mun haka harda cewa ni mayya ce Ina bibiyanka bayan ka sakeni.. Ai ko da ace Babu aure tsakaninmu nan fah gidan D’anuwana ne zan iya zuwa gidan nan..Amma shine ta kwance mun Karnuka saikace wata b’arauniya, wllhi da k’yar nasha.. Wayyo cikina..!” Ta kuma kurma wani ihun daidai sanda Patrick ya fito da Karnuka.. A nasa tinanin Safeenah ta tare Sadiya ne da fad’a shine ya fito da Karnukan dan ya mata barazana kaman yanda suka mata wancan ranan. Patrick ya turo gate yana rik’eda Karnukan yake fad’in “Ma’am Ta tafi ko na sakar mata su Danny su tayata shawagi..” Yai birki wa kalamansa sakamakon hango Mu’azzam da yai.

Safeenah ta kuma sakin ihu tana rarrafawa Ta isa bayan Mu’azzam Ta rik’e k’afafunsa tana b’uya tana fad’in “Ka gani ko.. Kaga abinda nake fad’a maka koh.”

Wani irin tsawa ya dararawa Patrick wanda saida yasa Patrick sakin chain d’in wuyan Karnukan dan tsoro dan shi sam baisan Mu’azzam d’in ya iso ba..

“Are you stupid.. Ashe kai mahaukaci ne..!” Cikin fad’a fad’a yake maganar wanda zai tabbatar maka ransa a b’ace yake. Patrick fad’i yake “Sorry Sir.. I.. I didn’t know.. You..”

“Shut up.. Just shut up.!” Mu’azzam ya kuma daka masa wani Tabawan.

Sadiya dake Hawaye bud’e baki tai da niyyan magana ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu “Banson jin komai, ki shige gida yanzun nan.!”

Ta saki baki tana kallon ikon Allah. Ta girgiza kai tace “Amma...”

“Bakiji mai nace bane..? Ko kurma ce ke..? Kina iya adana bayanan ki har na dawo..Please.” Ya k’arashe yana mai janye idanu daga barin dubanta.

Take taji hawayen na zuwa mata gadan gadan, Jiki babu laka Ta nufi cikin gidan, yayinda Patrick keta k’ok’arin basa hak’uri yana janyo igiyan wuyan Karnukan.

Ta jikin gate Sadiya Ta mak’ale tana hange Safeenah dake kuka Mu’azzam na tambayarta ko zata iya tashi.. Wani sabon kuka ne taji yazo bakinta.

Safeenah ta girgiza masa kai tana hawaye “I can’t.. I can’t walk.. Wllhi bazan iya ba.. Ni da nasan Karnuka za’a kwance mun a gidanka wllhi da bazanzo ba in the first place..” Kuka ya hanata ci gaba da magana, tana hawaye tana shafa cikin take fad’in “Our Baby Mu’azzam.. I don’t want to lose our child.”

“Ya isa haka Kimin shiru..” Ya fad’i yana d’aukanta Cak cikin hannunsa.

Sadiya Ta kuma fashewa da kuka ta nufin cikin gidan a guje kukan na fin k’arfinta.

Patrick ya bita da kallo cikeda tausayawa dan shi kanshi yasha mamakin tuggun da Safeenah ta k’ulla.

Motar Safeenar Mu’azzam ya shigar da ita gefen mai zaman banza kafin ya zagayo ya zauna a mazaunin driver. Sai matse ido take kaman da gaske tana jin jiki, tana yi tana satan kallonsa yanda ya kai matuk’a wajen tsimewa.

Ya daidaita zamansa saman kujeran ya soma driving. Safeenah na kuma sakin sabon kuka tana fad’in cikinta.

Birki ya taka wanda saida ya sanyata had’iye kukan nata cak, ta d’ago tana dubansa a tsorace.

“Safeenah..!” Ya fad’i a hankali idanunsa naga kwalta.

Ta saci kallonsa kad’an. Lokaci guda yaci gaba da furta “If something bad happens to your pregnancy.. Believe me, you will regret it..!”

Ya d’ago yana dubanta yana jinjina kai alamun tabbatarwa, hannayensa saman steering wheel yake ci gaba da fad’in “Idan kika kashe mun d’a da ganganciniki ki yarda dani, bazan sassauta miki ba har sai kin biya abinda kika aikata... Ki rubuta hakan ki ajiye..” Yana maganar yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa.

Baki sake Safeenah ke dubansa, sai kuma ta soma sakin huci tana fad’in “Matarka tayi niyyan kashe min d’a shine zaka tasa ni gaba da fad’a kana gani Ina cikin sever pain amma dikda haka bayan wancan makirar kake bi.”

“Ke kar ki maidani D’aniska.. Nasan abinda nake.. Mai ya kaiki gidan in the first place.. Ni ne zaki raina ma hankali, wani Wai kinada appointment da Dr.. Inace jiya da dare mukaje kikaga likitan.. A yaushe kukayi setting appointment din..”

Ta turo baki ranta a jagule.

Ya kuma gyara zamansa yana fuskantar ta sosai “Kina jina.. Kar ki kuskura Safeenah.. Kar ki kuskura.. I am warning you.!” Ya k’arashe cikeda gargad’i, daidai sanda wayarsa Ta soma ruri. Mommy ce mai kiran nasa.

Ya d’an harari Safeenar dake ci gaba da ture turen baki kafin ya d’aga wayar.

Yana d’agawa Mommy Ta soma fad’in “Mu’azzam idan kana tare da Safeenah bata wayar muyi magana, ga wayarta ta bari a gida sann ta d’auki car keys ta fice ban Sani ba..”

Duban Safeenar ya kumayi kafin ya mik’a mata wayan ba tareda yace komai ba.

Ta amsa tana k’arawa a kunnenta dan ta fahimci Mommy ce. D’add’aya Mommy tai mata sann tace tasa aniya ta dawo gida.

**
Sadiya kaw tana shigewa gida wani sabon kuka Ta fashe dashi, Ta soma tinanin abubuwan da suka faru daki daki, tin daga k’in d’aga kiranta da yai yaita rejecting, sann da ya dawo baibi takanta ba, yanzu ga abinda ya mata, bai saurara daga b’angarenta ba amma ya hau kan abinda Safeenah tace.. Ta kuma tina yanda ya d’auki Safeenar cikin hannunsa ya shigar da ita mota.. Take taji wasu sabbin k’walla suna ciko idanunta. Cikin kuka Ta nufi upstairs ta d’auko handbag da mayafinta.

Tana fitowa Patrick ya tareta yana tambayarta Ina zata ganin har lokacin bata daina matsan idanunta da suka kod’e sabida kuka ba.

“Ma’am please don’t leave.. Laifina ne da na fitar da Karnunkan, Believe me bansan Oga ya iso ba.. Kuma bansan abun zai juya ya zama haka ba.. Dan Allah Ma’am kiyi hak’uri ki dawo.. It’s all my fault.. But I’m sure Oga zai fahimci matar can makirci kawai ta k’ulla.”

K’ok’arin saita kanta tai tace “Kar ka damu Patrick. Ka daina d’ora ma kanka laifi kaji koh.. Bazai ce komai ba dan na tafi..”

“But M’am last time da kika tafi na samu matsala sosai da oga, kar na kuma shiga wani matsalan.”

Ta girgiza kai kad’an tace “Wancan karon da wann akwai banbanci..” Tai maganar tana mai ficewa.

Patrick ya biyo bayanta yana fad’in “Ma’am toh ki bari a kirawo miki Cab..”

Bata sami zarafin sauraron Patrick ba dan tuni ta fice daga gidan. Patrick yai tsaye yana kallonta yana tunanin yanda zasu kuma kwashewa da Mu’azzam.

**

Haka Safeenah ta kumbura ta cika tai fam cikeda jin haushin plan d’inta bai mata aiki yanda taso ba.. Wllhi dole ta sanar dasu Daddy ciki ne da ita tasan zasu sa Mu’azzam ya maidata. Da wann tunanin suka iso gida.

Ya tasata gaba yana biye da ita, har lokacin a kumbure take kaman zata fashe.

Suna haurawa sama suka tadda Mommy tana jiran shigowarsu.

Aiko suna shiga Safeenah ta duk’a tana kame cikinta tana sakin k’ara kad’an.

Mommy dake cike fam da niyyan tsefe mata masifa nan tayo kanta tana ambaton sunanta. Mu’azzam ma ya k’araso yana ambato sunan Safeenar.

Mommy ta nufi d’aki babu shiri Ta d’auko mata wasu pills ta mik’a mata had’ida glass of water tace maza tasha.

Babu musu Safeenah Ta amsa Ta had’iyi pills d’in har guda biyu Mu’azzam na mata sannu.

Ikon Allah maimakon ciwo ya lafa amma tana shan wad’ann pills d’in da Mommy ta bata sai ciwo ya k’aru babu k’akk’autawa.

Mommy tai tsaye tana dubanta yayinda Mu’azzam ya d’an kuma duk’awa yana ambato sunan Safeenar wacce da gaske take murk’usoso yanzu kam.

“Feenah can you hear me.. Safeenah do you need a Dr..?” Dik a d’an birkice yake maganar.

Muryar Mommy ne ya katsesa “Babu yanda zataje.. Ba kuma Likitan da za’a kira..”

Da tsananin mamaki ya d’ago yana duban Mommy dake wann maganar ga d’iyarta cikin pain. Ya girgiza kai kad’an yace “Mommy kin kuwa ji mai kike cewa..?”

“K’warai kuwa naji kuma nasan mai nake cewa.. Duba nan kaga..” Tai masa nuni da k’afar Safeenah da tuni siririn Jini ya soma gangarowa.

Mommy Ta kafesa da idanu tana murmushi ga Safeenah kwance k’asa tana murk’usoso tana rik’e mararta.

“Gashi nan.. Ga D’an Naka yana fita... Sai ka duk’a ka tattara d’anka.. Na fad’a maka sai na d’au fansar duk k’uncin da ka jefa mu ciki.. Ba’a cin bashin Hajara a wanye lafiya Mu’azzam.. Wann shine sakamakon duk rashin darajan da ka jaza mana.. A tunaninka zan bari cikin nan ya fice garin sakarcin Safeenah da wautan ta ne.. A’a ai idan na bari D’an ya fice garin haukar Safeenah ai na cutu.. Ban k’untata maka ba kenan.. Naci alwashin ni zan salwantar da wann shegen cikin naka Mu’azzam.. Kaman yanda ka k’untata mun lokuta da dama... Kaman yanda ka k’untatawa d’iyata Safeenah.. Toh D’ah baifi D’ah na kaima kaji dik irin k’uncin da naji.. Gashi nan ga gudan jininka na bin k’asa.. Ka tsuguna ka kwashe gudan jinin naka..” Ta k’arashe tana masa nuni da jinin dake d’iga daga k’afafun Safeenah wacce keta ihu tana neman d’auki tana kame mararta.


A daidai lokacin Musaddiq da ihun Safeenah ya tadashi daga bacci ya shigo parlorn. Cak ya tsaya yana sauraren Mommy dake ci gaba da fad’iwa Mu’azzam ya duk’a ya kwashe gudan jininsa.

Wani irin zufa ne ke tsartsafo masa.. Duban Mommy yake cikin wane irin yanayi.. Ko a labarai bai tab’a ji ko ganin mai hali irin na Mommy ba.. Sabida mugun zuciya Ta zab’i Ta salwantar da jikanta dan kawai ta k’untata masa.. Shin mai yayi wa Mommy da tsanani..? Shin wann wane irin tsana ne.. Shin Sakin Safeenah da yayi a gabanta ne har yakai tai masa irin wann hukuncin kokuwa dai auren da yayi ba da saninsu bane sann ya tare da matar a gidan Safeenah kafin akai Safeenah shine dalilinta na yi masa wann hukuncin..? Shin cikin abubuwan da yai har akwai wanda yakai tai masa irin wann tsartsauran hukunci..?

Gumi bai daina karyowa daga cikin sumarsa zuwa goshinsa ba, yaci gaba da takowa yana duban Mommy cikin wane irin yanayi.. Jinjina kai ya shiga yi still yana duban Mommy “You.. You’ve gone too far..! Kin tafi da nisa wann karon.. Kin tafi da nisa.!” Ya k’arashe numfashinsa na fita a hankali yana kuma jinjina kai yana duban Mommy da idanunsa da suka gama kad’awa.

Juyawa yai zai fice Musaddiq yai saurin bin bayansa yana kiran sunansa saidai Inaa bai cimma Mu’azzam ba.

Musaddiq ya dawo da sauri ya k’arasa kan Safeenah yana k’ok’arin taimaka mata yana mata sannu, lokaci guda yake aikawa Mommy dake tsaye tana dubansu mugun kallo.

Safeenah kuka take tana fad’iwa Musaddiq “My Baby.. My baby Musaddiq.. My Baby.. I don’t wanna lose my Baby.. Tell me Musaddiq.. Please tell me nothing bad is goin to happen to my child.. Please tell me..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka mai ban tausayi tana kukan tana kame cikinta.

Musaddiq yai saurin rungume Safeenah daga nan yanda take duk’e tana cazgan kuka mai tab’a zuciya.

Hawaye ne yaji suna gangaro masa, tausayi da k’aunar ‘yaruwarsa fal zuciyarsa. Sosai ya rungume kan Safeenah cikin k’irjinsa yana k’ok’arin lallashinta.

Iya ce ta shigo Musaddiq yai mata umarni ta taimakawa Safeenah. Iya ma hankali tashe take k’ok’arin d’ago Safeenar. Tana mata sannu suka nufi d’aki har lokacin Safeenah kuka take cikin tsananin sanyin jiki tana kame da cikinta. Kallo guda zakai mata ka fahimci batama a cikin hayyacinta.

Suna shigewa d’aki Musaddiq ya d’ago yana duban Mommy yana jinjina kai, lokaci guda yake furta “Kin gama mugunta Mommy.. Kin gama cutar da kowa da muguwar zuciyarki..!”

Mommy Ta daka masa tsawa da fad’in “Musaddiq.!” Mommy taci gaba da huci tana fad’in “Ko ban cire wann tsinannen cikin ba Safeenah zata ciresa da haukarta.!”

Hawaye na zubo masa yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Kiyi shiru Mommy.. Kin riga da kin b’ata komai..!”

Mommy Ta soma hawaye tana fad’in “Bazan tab’a yarda na had’a iri da Nuratu ba.. Never Musaddiq..!”

Cikin kuka yake furta “Don’t call my name.. Don’t you dare call my name Mommy.. You are not going to stop Mommy.. Right..? Ke d’in Bazaki tab’a dakatawa ba..!” Yaci gaba da jinjina kai alamun tabbatarwa “Zan sanar da Mu’azzam da Daddy komai.. Duk abinda na sani akanki Mommy.. Zan sanar dasu komai.. Bazan kuma rufa miki asiri ba Mommy..!”

Cikin rashin fahimta Mommy ke girgiza kai tana fad’in “Mai kake nufi Musaddiq..? What are you talking about.. Mai ka sani akaina..?”

Cikin zuban hawaye yake fad’in “Zan sanar dasu yanda kuka had’a baki keda Aunty Shemau kuka d’aukowa Aunty Nuratu mai magani na bogi dan kawai Aunty Nuratu ta fice daga gidanki da kuma rayuwar mijinki.. Naji wayar da kukai keda Aunty Shemau Tun kafin mu tafi Fufore.. Na riga nasan shirinki Mommy..” Muryarsa ya soma rawa sosai yana ci gaba da hawaye yake fad’in “Kin San Maiyasa ban tona miki asiri ba Mommy..? Because you are my mother.. And I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login