Showing 123001 words to 126000 words out of 209154 words
yana mai d’ago hannayensa alamun bazai tab’ata ba.
“Did he do something to you..?” Ya tambaya yana dubanta.. Still tana duk’a wajen tana hawaye.
Saurin girgiza kai tai alamun a’a kafin Ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa “He didn’t.. But you did.. I hate you.. And I’ll never forgive you for what you did.. Kaima bakada banbanci dashi.. Kaima D’antadda ne.. Harma ka fi shi.. Sabida shi bai mun abinda ka tasamma min ba..!”
Wannan karon sosai bugun zuciyarsa ke k’aruwa, yana jin kalamanta suna masa zafi a kunnuwarsa da zuciyarsa.
Cikin huci ya k’araso ya kamo arms d’inta, ya shiga jijjigata yana furta “Kar ki sake had’ani da wanann D’aniskan.. I’m your husband in case you forgot.!” Ya kuma jinjina kai yana mai ci gaba da furta “And I’ll touch you, not just once... As many times as I want.. Because you are my wife..” Ya k’arashe rik’e da ita har lokacin hawaye take.
D’an saita kansa yai yana mai fuzar da huci kad’an kafin yace “Get ready now.. We are leaving.. That is idan kinaso ki sake ganin ahalinki..” Daga haka ficewa yai daga bathroom d’in tabi bayansa da kallo jin abinda ya fad’i mata.. Mai yake nufi ko ya samo yanda Su Umma suke ne.. Abinda zuciyarta ya dinga raya mata kenan.
Tai saurin mik’ewa tana addu’an Allah yasa zata dake ganin Su Umma.
Mu’azzam kaw yana fitowa ya fice gaba d’aya daga d’akin abubuwa fal zuciyarsa.
D’akin hutu da aka kwantar da Assad ya nufa. Yanda ya tadda Assad d’in bacci yake bai tashi ba.. Likita ya basa update akan jikin Assad d’in. Ya jima kan Assad yana masa fatan samun sauk’i kafin ya nufo motarsa ya d’auki samples d’in sumar Musaddiq da ya d’auka da kuma hular da suka tsinta a wajen alk’allar Danger.
Maleeka tana reception acting like a Staff ta hangosa rik’eda samples d’in ya nufi Lab.
Shiru tai ta soma tinanin mai zai a Lab.. Lokaci guda ta soma binsa cikin yananyi na b’adda kama.
Da shike asibitin is more of glass nan ta hangesa yana magana da ma’aikacin lab d’in Mu’azzam na mik’o masa samples guda biyu cikin leda.. D’aya hular B.A.T ne d’aya kuma bata iya hango menene a ciki ba.
Tai saurin mak’alewa gefe sanda taga Mu’azzam da Mutumin sun fito yana jaddada masa cewa yana so komai ya tafi perfect.
Mutumin yace baida matsala zai k’ok’ari result d’in ya fito da wuri..
Maleeka ta lab’ab’a ta shige burut cikin Lab d’in ta mak’ale a bayan k’ofa ba tareda sun kula da ita ba.
Daidai sanda Mu’azzam sukai sallama da mutumin ta shige store d’in dake cikin Lab d’in.
Ta ramin k’ofa take hango mutumin yanda ya d’auki Samples d’in da Mu’azzam ya basa da alama aiki yake so ya fara gudanawar kansu..
Maleeka Ta girgiza kai tace “Bazan bari ka samu result mai kyau ba Mu’azzam... Lokaci guda ta janyo wasu takardu nan cikin store d’in suka zubo k’asa wanda hakan yaja hankalin mutumin..
Ya shiga ‘yan dube dube yana neman k’aran mai yaji.. Nan wani ma’aikaci d’an uwansa ya shigo yajasa suka fice yana fad’in yazo ya tayasa duba wani result d’aya Lab d’in.
Suna ficewa Maleeka Ta fito daga store d’in.. Tai saurin zaran handgloves ta rufe yatsunta ciki.. Lokaci guda ta bud’e drawer d’in da taga mutumin ya aje samples d’in ciki..
Tabbas d’aya hular BAT ne d’aya kuma tsillin suma ne ciki..
Ta saki murmushi tana furta “Kashe matarka zai zamto matsala a gareni.. But I thought of something more tangible Inspector Gamji.. Ka jira kaga yanda zanyi tempering Samples d’in nan..” Tai maganar tana murmusawa kafin Ta bud’e ledar da Mu’azzam ya saka sumar Musaddiq ciki.. Ta b’alli nata sumar ta saka ciki sannan ta cire na Musaddiq wanda Mu’azzam ya samu jikin hairbrush d’insa..
Tasan cewa babu yanda za’ayi nata yayi matching.. Mu’azzam bazai tab’a samun sakamako mai kyau ba..
Sauri sauri ta fice daga lab d’in kafin ta nufi wani store d’in yanda Ta canza kayan jikinta Ta koma Detective Maleekar ta.
Sanda Mu’azzam ya koma d’akin Sadiya ya tadda har ta gama shiri cikin tufafin da ya aje mata.
“Tashi muje..” Ya fad’i yana dubanta.
Babu musu jiki a sanyaye Ta mik’e tabi bayansa.
Ya bud’e mata front seat Ta shige kafin ya shige B’angaren driver.
A k’ofar asibitin ya hango wata kaman Maleeka ta shige ciki cab.. Ya tambayi kansa ko mai take har lokacin a asibitin tinda dai ciwonta bai wani yi tsanani ba.. Wata zuciya Ta basa amsa da fad’in k’ila tana jira taji condition d’in da Assad ke ciki ne.. Da wannan tinanin ya d’auki hanya. Cikin su biyu babu mai cewa komai k’arshe ya kunna karatun Alk’ur’ani mai girma wanda ya sanya ma zukatansu Salaama had’ida natsuwa.
Wani k’aton gini taga sunzo mai manyan Gates har guda biyu.
Yai horn securities da suke tsaron k’ofofin suka bud’e masa cikeda girmamawa suna gaidashi cikin mutunta juna.. Ita har mamaki ma taji da taga yanda yake amsa masu kaman bashi ba.. Ta d’an tab’e baki kad’an ba tareda tace komai ba.
A haka suka shigo cikin ginin wanda kaman gidaje ne da Wani gini daga tsakiya tamkar ma’aikata..
Nan kuma Ta hangi nakasassu na sintiri cikin wajen.. Tana ta duban buwayar Ubangiji.. Allah sarki wasu idan ta gansu sai ta kuma gode wa Ubangijinta da rahama na lafiya da yai mata.. Tabbas idan kana ganin irin wad’ann dole imaninka ya k’aru.. Kaima ba dan ka fisu bane Allah ya Barka haka.. Sannan suma ba wai dan yak’isu bane yaso ya gansu haka.. A’a dukkaninmu d’aya muke wajen Ubangiji wanda yafi wani shine wanda yafi tsoronsa.. Kowa jarabawa yake fuskanta a GIDAN ARO.
Ya isa yai parking a k’ofar wani gida mai kaman apartment. Ya zagayo ya bud’e mata yace ta fito.
Bata fito d’in ba sai dubansa da tai..
“Uncle Cop..” Abinda taji an fad’i kenan.. Muryar da ko a bacci tasan na k’aninta Habeeb ne.. Zuciyarta yaci gaba da bugawa sanda ta hango Habeeb a yazo ya taho a guje ya haye jikin Mu’azzam.
Mu’azzam ya basa hannu sukai handshake harda wani d’an dunk’ule hannayen masu sukai suka tafa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa..
“Ka kawo mana Aunty Sadiya ce as you promised... Ina take..?” Habeeb ya k’arashe yana waige waige..
Sadiya dake k’arasowa kusansu hawaye ne ke gangarowa daga cikin idanunta..
Mu’azzam ya jinjina masa kai yace “Of course little Cop.. Kalli wacece na kawo maka.” Ya k’arashe yana juyar da yaron zuwaga direction d’in da Sadiya ke tsaye tana hawaye.
Ta rungume d’anuwanta tana hawaye. Ta shiga shafa fuskarsa tana jujjuyasa dan dai ta tabbatar “Habeeb kaine.. Ina Su Umma da Ashir..?”
Ya nuna mata apartment d’in da ya fito daga ciki murna fal fuskar yaron “Munyi kewarki Aunty Sady kullum sai Uncle Cop yazo ya duba mu yace zai kawo mana ke..” Cikin sauri ta kuma rungume Habeeb tana hawaye. Lokaci guda ta mik’e tana fad’in “Muje naga Su Umma.”
Ko takan Mu’azzam bata kuma bi ba tama mance tare suke.
Murmushi saman fuskar Mu’azzam ya bisu da kallo har suka shige parlorn.
Sadiya tana shiga parlorn ta hango Umma sanye da hijabi tana fitowa daga corridor tana kiran sunan Habeeb dan taji bud’e k’ofarsa tasan bazai wuce yace zaibi Ashir da Aunty Larai bane.
Cak Umma da Sadiya suka tsaya suna duban juna.. Wani irin kuka Sadiya ta fashe dashi kafin ta k’arasa a guje ta rungume Umma. Umma ma ta rungumeta sosai tana matsan k’walla.. D’iya da Uwa sunga juna dole su baka tausayi idan ka gansu a yanayin.
Umma ta d’ago fuskar Sadiya tana duba “Sadiya ta.. Zan k’ara ganinki ashe.. Alhamdulillah Allah ya kub’utar mana dake..”
Sadiya ta murmusa tana hawaye tana sharewa Umma nata hawayen.. Lokaci guda take jinjina kai tana fad’in “Umma zan k’ara ganinku ashe.. Umma ki k’ara rungumata naji d’umin jikinki..”
Suka kuma rungume juna suna hawaye cikeda shauk’in sake ganin juna.
Daga yanda Mu’azzam ke tsaye ya zuba masu idanu cikeda tausayawa.. Bai shiga ba ya juya ya koma cikin mota yana amsa wayar Yusuf yana tambayarsa ko Assad ya farka.
Yusuf yace “Har yanzu dai allurar bata sakesa ba, amma idan ya tashi zan sanar dakai.”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Alright Detective, sai na jika..” Daga haka sukai sallama kafin yaci gaba da shafa wayar tasa.
A cikin parlorn kuwa Sadiya da Mamanta kaman kar su saki jikin juna.
Sadiya tace “Umma ina Ashir..?”
Umma tace “Ashir Sun fice da Aunty Larai sun shiga cikin foundation..”
Sadiya ta d’an numfasa kafin tace “Aunty Larai kuma..? Wacece ita..?”
“Mu’azzam ya had’amu da ita tin sanda suka kawomu gidan nan shida Abokinsa Assad...”
Sadiya Ta d’an girgiza kai tace “Wai Umma dama ba saceku akai ba..? Toh ya akai kuka Zo nan..?”
Umma ta murmusa kad’an kafin tace “Mu’azzam da Abokinsa Assad su suka kawo mu wannan gida bayan threats da akaita ajiye mana a k’ofar gida Tun bayan d’aukeki da Mu’azzam yai.. Wad’annan bayin Allah babu abinda zamu ce masu face fatan alkhairi”
Sadiya ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Umma mutumin da ya saceni ya rabani daku bisa tilastawa Shi kike yabo har da godiya..?”
Murmusawa Umma tai tana mai girgiza kai “Allah sarki Sadiya.. Da ace Mu’azzam bai d’aukeki wannan lokacin ba watak’ila da yanzu bazamu kuma ganin juna ba..”
“Umma maiyasa kikace haka..?” Ta tambaya cikin rawar murya.
Umma ta numfasa tace “A daren da Mu’azzam ya tafi dake Washe gari da safe aka k’wank’wasa mana k’ofa, Ashir yaje ya duba babu kowa sai wani k’aramin akwati da aka aje mana an rubuta sunana da sunana su Ashir a Farin takarda da jan rubutu anyi crossing.. An rubuta a k’asa cewa za’a shafe ahalinmu gaba d’aya.. Abin ya firgitani sosai sai Allah yasa abokinsa Assad Wanda tin a daren da Mu’azzam ya tafi dake yazo ya dubamu kuma ya bar mun layin wayarsa yace idan wani abu ya taso na kirasa. Toh shine na kirasa na sanar dashi ga abinda muka samu k’ofar gidanmu.. A lokacin suka taho tareda Mu’azzam d’in ban b’oye masu komai ba na sanar dasu sanin cewa su d’in jami’an tsaro ne.. Suka kwantar mana da hankali tareda fad’in zasu kama mutanen dake bibiyan rayuwarmu da izinin Allah.
Akai haka kusan sau biyu sai a k’wank’wasa mana k’ofa muje muga babu kowa Sai sak’o da ake bari mana wanda ba komai bane face threats daga mutanen dake bibiyarki.
A daren ranan da su Mu’azzam zasu kawo mu nan harbi akaita mana a cikin gidanmu cikin dare. Cikin drum na b’oye k’annenki Habeeb da Ashir ni kuma na b’uya a cikin kaya a store..”
Sadiya hawaye Umma hawaye.. Washe gari sassafe mijinki Mu’azzam da abokinsa Assad suka s’aukemu daga wancan gidan wanda ake kai mana hari suka kawo mu nan.. Sun rufe hakan suka bar abun akan cewa sacemu akai domin su b’atar da tunanin ‘Yantadda masu bibiyar ahalinmu... Kinji abinda ya faru damu Sadiya..”
Sadiya na hawaye ta waigo tana duban motar Mu’azzam da alama har lokacin bai tafi ba.. Ta sadda idanunta a hankali tana jin wani kukan na zuwa mata.. Ta matso kusan Umma kafin Ta kamo hannayen Umma tace “Muna nan tare daga yanzu babu abinda zai kuma rabamu Umma.. Ku yafe mun duk ni ce na jefa ahalinmu cikin ukuba.. Watak’ila da banyi tarayya da Sagir ba duk da hakan bai samemu ba..”
Umma ta girgiza kai tana duban Sadiyar lokaci guda take furta “Wannan duk muk’addari ne daga Allah tuni Allah ya hukunta hakan zai faru.. Saidai mu k’ara gode masa da baiwa da yai mana na had’amu da mutanen arziki da yai..”
Sadiya dai bata kuma cewa komai ba Sai kwantar da kanta saman cinyar Umma da tai. Umma ta shiga Shafa kanta a hankali abubuwa fal zuciyarta.. Can k’asar zuciyarta wani tinanin ne ya addabeta.. Batasan dalili ba amma abubuwan dake faruwa suna tuno mata da bayanta.. Kaman d’ai abinda ya faru shekarun baya ne zai kuma faruwa.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*41*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yana nan zaune a mota su Anty Larai suka k’araso.. Gaisawa sukai Anty Larai na zolayarsa ko ya kawo mata surkar tata ce.
Ya murmusa yana shafa sumarsa lokaci guda suka nufi cikin gidan a tare. Aunty Larai ma’aikaciya ce a cibiyar sannan d’iyar k’awar Inne ce a nan Abuja take zaune da mijinta toh tinda mijin nata ya rasu take fama da rayuwa dama Sana’ar d’inki take gashi ta saba da zaman garin sam bata son tafiya Ta bar Sana’arta musamman da shike ba yara gareta ba, Daddy shi ya sama mata aiki a nan cibiyar, takan Zo cibiyar ta koyar da Sana’ar d’ink.. A nan suka kuma had’uwa da Mu’azzam shine har ya nemi alfarmar tazo su zauna dasu Umman Sadiya ko zata d’an d’ebe masu kewa. Yanzu haka a nan cikin cibiyar suke zaune taredasu Ummman Sadiya dashike Aunty Larai akwai sabo da saurin shiga rai tuni suka sake da juna kaman dai Sun jima da sanin juna.
Gaisar da Umma Mu’azzam yai cikeda girmamawa, Umma ta amsa tana tambayarsa jikin Assad.. Yayinda Sadiya ke rungume da k’annenta.. Janyo hannunta ‘yanuwan nata sukai suka shige ciki. Mu’azzam yabi bayanta da kallo har ta b’ace masa.
Umma ta k’ara masa godiyan d’awainiyar da yake da kub’utar da Sadiya hannun ‘yanta’adda da yai.
Kansa a k’asa yaketa sakin murmushi a hankali. Aunty Larai na taya Umma. Daga bisani Umma mik’ewa tai Ta basu waje shida Aunty Larai, nan Aunty Larai d’in ke fad’in bari a kawo masa abinci.
Ya d’an girgiza kai yace zai koma asibiti wajen Assad ne.
Aunty Larai ta mik’e tana fad’in “A’a haba dai Malam D’ansanda da ganinka baka wani ci abinci ba.. Kaga barin turo maka Amaryar taka ta kawo maka..”
Jin zata turo Sadiya ta kawo masa yasa baice komai ba Sai murmusawa kawai da yai.. Aunty Larai ta mik’e ta nufi ciki.
Sadiya na tare da k’annenta Aunty Larai ta shigo.. Sadiya ta kuma gaisar da Aunty Larai cikeda girmamawa kafin Aunty Larai taceda Ita ta taso suje kitchen..
Babu musu Sadiya ta mik’e tabi bayanta.. Suna kitchen d’in Aunty Larai tana nuna mata abubuwan da Zata tayata dasu, Sai janta da hira take Dikda Sadiya ba wani amsawa take ba sai murmusawa da take.. Nan Anty Larai Ta hango alamun cannula hannunta tace “Na mance ashe fah sirkar tamu patient ce... Amma bara na tayaki da d’aukan masu nauyi Kinsan ba’a barin mai Gida da yunwa..”
Sadiya dai batace komai ba sai murmushi da take wanda yafi kama da yak’e. Ta kula Matar akwai magana bakinta baya shiru sam.
A haka suka nufo parlorn rik’e da trays na abincin. Bakin Aunty Larai bai shiru ba. Sadiya tana direwa Ta mik’e da zummar tafiya saiji tai Aunty Larai ta rik’ota ta dawo da ita.. “A’a Haba Amaryarmu.. A ina kika tab’a jin an k’yale maigida yaci abinci shi kad’ai.. Zauna gefensa kunaci tare yana kallon kyakkyawar fuskar nan taki haka akeyi.. Kakanninmu sunce hakan na k’ara dank’on k’auna tsakanin ma’aurata.”
Mu’azzam ya saci kallonta jin abinda Aunty Larai Ta fad’i.. Kana ganinta kasan dan dole take aiwatar da komai.. Dan dai Babu yanda ta iya ne.
Aunty Larai Ta mik’e Ta kunna masu tv tana mai fad’in “Yauwa na barku lafiya.. Ku cinye komai mu gidan nan ba’a bari mana sauran abinci..” Tana ida fad’in haka ta shige ta janyo k’ofar corridor d’in ta rufe aka barsu su biyu parlorn.
Kaman babu mai cewa komai Mu’azzam ya d’an dubeta kafin yai gyaran murya yace “Aren’t you hungry..?”
Ta girgiza masa kai alamun a’a..
“You must be.. Bayan drip babu abinda kikaci..” Ya fad’i yana dubanta kafin yace “Serve us now..”
Ita mamaki ma yake bata yanda yakeyi kaman dai babu wani abinda ya faru.
Ta d’an d’ago baki a ture tace “I’m Ok.. Ni bazanci ba..”
Ya jinjina kai yace “Toh ni zan ci.. Serve your husband..”
Gyara zamanta Ta d’anyi kafin tace “Mr Inspector.. As far as I know the mission is over now.. kuma na baro GIDAN ARO.. Why don’t you end this fake marriage once and for all.. Ka sanar dasu cewa auren mission mukai kuma ya k’are..”
Murmusawa yai kad’an kafin yace “As far as I know, I didn’t sign any agreement.. Bamuyi haka a rubuce ba.. Iyakacin abinda na sani shine inada shaidu da zasu tabbatar da cewa ni mijinki ne, and that means zakiyi duk abinda na umarceki... And don’t get this wrong dan na kawoki nan.. I brought you here because of what the Dr said.. Ba dan yace a kawoki nan d’in ba da Gida muka wuce.”
Ya nad’e hannaye kafin yai mata alama da ido zuwa plate d’in “Serve your husband..”
Ta d’an juyar da kanta tana fuzar da fuci kafin ta juyo tana dubansa “Kana tinanin na mance abinda kai mun ne.. Bazan tab’a yafe maka ba kuma zanyi k’ararka a ofishinku na ‘yansanda..”
Wannan karon dariya ne yazo masa, ya d’an ciza labb’ansa na k’asa kad’an had’ida kauda kansa yana mai danne dariyarsa. Lokaci guda ya juyo yana dubanta “Oh really..? Toh idan kikaje filing case d’in mai zakice..?”
Tana huci tace “First I’ll file a case of kidnapping.. And second..” Sai kuma tai shiru kaman wacce aka rufe mata baki, Ta kasa duban cikin k’wayar idanunsa, sai ma kauda kai da tai tana sakin huci a hankali.
Mu’azzam ya murmusa kafin ya janyo plate d’in ya soma zuba abincin yana ci gaba da fad’in “A ina aka tab’a k’aran miji dan ya d’auke matarsa..? As far as I know babu dokar data hana haka koda ta yahudu ce.. Na biyunsa zakiyi k’arar miji dan zai amshi hakkinsa wajen matarsa.. Wanann ma banaji akwai yanda za’a saurareki.. Am I right..?” Ya k’adashe yana dubanta.
Idanunta sukai rau rau.. Tasa d’aya hannun nata tana gogewa.. Baice mata komai ba har ta gama goge hawayen kafin ya d’ibo abinci cikin spoon yace “You’re still weak, Oya open your mouth..”
Ta dubesa a dak’ile, sai kuma ta mak’e kafad’ar ta alamun ta k’oshi.
Ya tsime sosai wannan karon “Idan bakici ba Kinsan Allah zan d’aukeki mu tafi gida yanzun nan.. Kinsan zan kuma zan aikata hakan..”
Jin abinda yace ya sanyata bud’e baki a hankali. Ya saka mata spoon d’in cikin bakinta. Ta lumshe idanunta a hankali wani hawayen na gangaro mata.. Yayinda Mu’azzam yai mata K’uri yana duban fuskarta.
Ya sake d’ibo abincin ya kuma kaiwa saitin bakinta, ta kauda kanta gefe.. Tsareta da idanu wann karon yai ba tareda yace komai ba. Hakan yasa babu yanda ta iya ta kuma bud’e bakinta.