Showing 111001 words to 114000 words out of 209154 words
“No, a halin da kake ciki bazan Barka kai kad’ai ba Mu’azzam.. I know you so well, so bazan Barka kai kad’ai ba.”
Murmushi yai da gefen baki still idanunsa naga waje guda “Ka fita Assad.” Ya sake fad’i yana damk’e kan steering d’in sosai.
Assad ya kuma girgiza kai “Bazan Barka kai kad’ai ba Mu’azzam..”
Jinjina kai Mu’azzam yai yace “Fine.. Ka zauna kai kallo..!” Daga haka ya ja motar suka soma falfala gudu saman kwalta. Basu zarce ko ina ba sai daban su Danger da Sagir k’ofar shagon Danger yanda Danger d’in yace Sagir sayen sigari ne kawai ke kawosa basuda wata connection.
Suna isa yai parking Assad Sai dubansa da mamaki ganin babu kowa babu alamun mutum a k’ofar shagon Danger, tamkar dai anyi shara.
Assad ya girgiza kai kurum yana duban Mu’azzam d’in “Kana tunanin zamu sami Danger a nan ne.?”
Mu’azzam bai ce masa komai ba Sai k’urama k’ofar shagon idanu da yai.
Assad bai kuma cewa komai ba sai kwantar da kansa da yai cikin kujera had’ida lumshe idanunsa.
Kusan minti talatin suka kwashe a wajen babu ko tsuntsu da ya gifta. Assad ya d’an fuzar da huci yana duba agogon dake d’aure hannunsa. Ya bud’e baki kenan da niyyan magana suka hango wasu matasa sun nufo shagon.
Mu’azzam zai bud’e Mota Assad yai saurin rik’osa yana fad’in “Mubi komai a sannu Mu’azzam..”
Da tsananin mamaki yake duban Assad kafin yace “That Maniac has my wife yet kana cewa na bari ayi komai a natse..? Assad Wai shin ka mance cewa Sadiya itace target d’in Su Danger.. Ka mance cewa nemanta suke ruwa a jallo.. Ka mance cewa ta dalilin nemanta da suke kowa nata ya shiga had’ari..? If you can’t be at any help kar ka kuskura kai tunanin dakatar da ni..!” Daga haka sauk’a yai ya nufi matasan Assad yai saurin bin bayansa, kamo Mu’azzam d’in yai suka d’an lab’e suna sauraron tattaunawar matasan yanda suke jajen sun d’ebe kwanaki basa ganin Danger bai bud’e shago gashi akwai wata nau’i na k’waya a wajensa kawai suke samu.
D’aya matashin yai tsaki yana fad’in kodai ya daina zuwa nan ne gaba d’aya.. Aiko zai rasa customers.. Muje kawai dallah..”
Ganin zasu shige yasa Assad fitowa daga yanda sukai kwanton b’auna suna sauraron tattaunawarsu. Tuni d’ayan ya arce dan sun zaci ‘Yan kamen Drugs ne..
Assad ya juyo yana duban d’ayan wanda tuni Mu’azzam ya damk’o kafad’arsa ya sharb’e k’afafunsa ya zube k’asa.
Saurayin ya shiga d’ago hannaye yana rok’onsu yana fad’in wllhi basu saye k’wayan ba kuma shi ba D’anta’adda bane.
Assad yace “Munsan kai ba D’antadda bane amma kana Ta’ammudi da miyagun k’wayoyi, zamu iya kulleka akan haka Kasan da wannan.?”
Saurayin wanda duka duka bai fi shekaru 20 ba ya shiga jinjina kai yana kuma rok’on Su k’yalesa..
Assad yace “Zamu sakeka idan ka amsa mana tambayoyinmu..”
“Na rantse da Allah Yallab’ai wllhi Allah shine shaidana ni zan fad’i gaskiya, ina sayen abu wajensa amma ni ba D’antadda bane..”
Mu’azzam baice k’ala ba Tunda Assad ya soma tambayar mutumin. Kafin Assad ya ankara sai gani yai Mu’azzam ya janyo saurayin ya jefasa cikin Mota. Assad yai tsaye kurum yana dubansa cikin rasa mai zaice. Bayan Mota Mu’azzam ya bud’e ya jefa saurayin ciki kafin ya d’auki hanya.. Assad yai saurin take masu baya saidai bai cimmasu ba mai taxi kurum ya tara yace Su bi bayan Motar Mu’azzam wanda Mu’azzam d’in keta wajajjaga gudu dasu shida wann matashin.
Matashin ya shiga ihu ganin ana wasa da rayuwarsa saman kwalta d’in da babu yawan motoci yana fad’in “Rankaidad’e na shiga uku.. Dan Allah ka tsaya kar ka kasheni..”
Idan motar Ta amsa Mu’azzam ma zai amsa, Sai wajajjagasu yake yana gwara mutumin nan. Lokaci guda yake jefo masa tambayoyi “Ina Danger yake..?”
Saurayin yace “Wanene Danger..? Wllhi ban sanshi ba.. Dan Allah kamin rai..”
Mu’azzam ya jinjina kai kafin ya kuma sharan wata kwana da motar wanda saida mutumin ya kuma buga kansa jikin marfin Mota “A ina zan sami Mutakk’a ..?” Ya kuma jefo masa tambayar daidai sanda suka shige wani bend yanda zai shigar dakai daji.
Saurayin sai haki yake yana furta “Rankaidad’e kamin rai..”
Parking Mu’azzam yai ya bud’e marfin motar kafin yasa hannayensa biyu ya fiddo saurayin wanda tuni ya gama jigata. Sai haki yake yana layi alamun an wajajjagasa.
Daidai lokacin Assad da mai tasi ya sauk’esa a bakin hanya ya k’araso wajen.. Kasasancewar basu shiga can ciki ba yasa manya manyan kwan wutan streetlights ke haskosu tarau.
Mu’azzam na k’ok’arin kicking bindigar. ya saita Saurayin da Ita yana kuma jefo masa tambaya “Tell me now, if you value your life.. Ina Danger yake..?!”
Saurayin dake duk’e saman gwiwoyinsa hannayensa ya d’aga alamun rok’o yana girgiza kai yana Hawaye yake fad’in “Na rantse da Allah ban Sani ba Yallab’ai.. Ni tsautsayi ne ma yakai ni shagon yau.. Dan Allah kamin rai..”
Assad ya girgiza kai dafe da kunkuminsa yana duban yanda matashin ke karkarwa dan tsoro kafin ya dubi Mu’azzam yace “Ka k’yale yaron nan haka, It’s obvious baisan koma ba..” Ya kuma duban saurayin dake duk’e yana rawan d’ari yace “Tashi kaje..”
Saurayin ya mik’e yana godiya, har ya juya zai wuce Mu’azzam ya saitasa da bindiga. Lokaci guda yake furta “If you take one more step, I won’t hesitate to blow your brains out.!” Ya k’arashe yana saita kan saurayin.
Juyowa saurayin yai in a slow motion yana had’o hannayensa yana kuka yana rik’on Mu’azzam yai masa rai.
Mu’azzam ya shiga harbin k’asa gefen k’afafun saurayin, sai tsalle yake yana kaucewa bullets d’in yake fad’in “Na shiga uku.. Kamin rai..!” Yana tsalle yana sakin fitsari a wandonsa dan tsoro.
“Believe me, the next bullet zai sauk’a ne a jikinka Idan baka sanar dani yanda Muttak’a mai saida maku kayan maye yake ba.. Talk now..!” Ya kuma fad’i yana harbin tsakankanin k’afafun saurayin abinka da wanda yasha training ya k’ware wajen saita bindiga da harbata.
Take saurayin ya soma fad’in “Zan fad’i gaskiya wllhi..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ina jinka.”
“Wllhi dama Muttak’a mai shago syrup yake saida mana, da ‘yan chocolates (drugs) Toh wllhi wllhi abinda kawai muke saye wajensa kenan..!” Ya k’arashe yana sakin numfashi da k’yar.
“Ina za’a samu Muttak’a..?” Mu’azzam ya kuma jefo masa tambayar.
“Rankaidad’e wllhi ban Sani ba amma akwai wani abandoned warehouse da wasu lokutan yake cewa mu samesa a can idan zai saida mana k’waya dan kar idon jami’an tsaro yakai kansa.. Wllhi Yallab’ai Iyakacin abinda na sani kenan kansa.. Kuma k’wayar ma na daina sha na tuba wllhi daga yau.. Dama Mamata tayi tayi na dena nak’i amma daga yau wllhi na dena..” Ya k’arashe yana kuma matse k’afafunsa da tuni fitsari ya wanke wandon. Kana ganin yaron Kasan ya gama razana.
“A ina ne Warehouse d’in yake..?” Babu musu saurayin ya sanar dashi yanda warehouse d’in yake. Bai kuma furta komai ba ya nufi Mota Assad ko ya dubi yaron kafin ya k’arasa ya d’aura masa Pcap d’insa da ta fad’i dan azaba yace “Sai kai nasiha ma abokinka Shima ya daina Ta’ammidi da miyagun k’wayoyi domin gobenku tai kyau..”
Saurayin da gumi ya wankesa sai jinjina kai yake yana haki yana Godiya. Daga nan Assad take ma Mu’azzam baya yai cikin sauri, dan tuni Mu’azzam d’in ya kunna Mota. Suka nufi location saida k’wayan Danger da yaron ya sanar dasu.
**
Maleeka ta d’ago tana duban Chief da tsananin mamaki kafin ta girgiza kai tace “I don’t get you.. Chief.”
Ya kuma murmusawa yana mai zama saman gadon Otel room d’in kafin yace “You are on the path of no return Maleeka.. You know too much already..!” Ya mik’e tsaye yana zagayeta yana mata wani irin duba fuskarsa d’aukeda muguwar murmushi.. Lokaci guda ya kamo fuskarta mai cikeda tsoro kafin yace “Turning back will be dangerous for you.. Not only you, you don’t want drag your loved ones into this.. I mean your family..” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.
“Mai kuke so na maku yanzu..?” Ta tambaya tana duban Chief.
Chief ya murmusa kafin yace “Inaso ki haifar da rashin yarda a tsakanin team d’inku..”
“Mai kake nufi da haka..?” Maleeka ta tambaya tana dubansa.
“Detective you know exactly what I mean.. Inaso ki haifar da rashin yarda tsakanin Mu’azzam da abokinsa Assad.. If those two are working together bazamu tab’a cin nasara wajen Kai Mu’azzam k’asa ba. Ina fata kin fahimci abinda nake nufi.”
Girgiza kai Maleeeka tai tana sakin murmushin da yafi kama da yak’e “You know this is not possible.. Those are like brothers.. They always have each other’s back... Bazaku tab’a iya shiga tsakaninsu ba..”
Chief ya murmusa kafin yace “Bazamu iya ba amma ke zaki iya..”
“How..?” Ta tambaya tana dubansa lokaci guda taci gaba da fad’in “We are talking about Mu’azzam Gamji here.. Kasan shi d’in wane irin mutum ne..”
“I don’t know how Maleeka.. Amma dole zaki samo hanyar da zaki saka shakku da kokonto tsakaninsa da amininsa Assad.. Idan kikayi haka, kinada reward mai girma daga wajen BAT..” Ya k’arashe yana mai k’arasawa yanda kayansa ke ajiye ya d’aga ya ciro bunch d’in ‘yan d’ari biyar biyar ya mik’a mata “Somin tab’i ne wannan.. BAT yace a baki kisha minti daidai..”
Maleeka tai tsaye tana dubansa shida kud’in kafin ta girgiza kai tace “I can’t do this Chief.. Bazan iya cin amanan abokan aikina irin haka ba. I’m not a betrayal... I can’t accept your offer.. I’m sorry, Sir..!” Ta k’arashe cikin tsananin tsimewa tana duban fuskarsa.
Chief ya kuma sakar mata murmushi kafin yace “Kin riga da kin shiga ciki Maleeka. Kuma Bazaki iya fitar da kanki ba.. If I were you zan karb’i kud’ad’en nan kuma nayi biyayya.. Idan har Kinyi valuing rayuwarki..”
Maleeka Ta murmusa kafin tace “You and your accomplices can go ahead and eliminate me but I’ll never ever allow you to destroy Mu’azzam..”
Chief yai wata dariyar rainin hankali kafin yace “I like your courage yarinya.. I wish yanda kike son kare Mu’azzam shi zai iya miki haka.. Shin akan Waye kike d’aga jijiyan wuya.? Mutumin da mata biyu zuk’a zuk’a ke garesa mai zaiyi dake Maleeka.. Dama kin daina b’atawa kanki lokaci ne dan Officer Gamji babu abinda zai dake.. Da wannan kumfan bakin da kike da zuwa kikai kika taimaka masa da neman matarsa da yake wacce aka saceta a safiyar yau..”
Da tsananin mamaki Maleeka ke dubansa kafin ta girgiza kai tace “Kana nufin an sace Safeenah..?”
Ya kuma murmusawa yana mai kishingid’uwa saman gado “Da alama Bakida labarin auren tsohuwar fiancée d’in Sagir da Mu’azzam yai.. And it seems your team members basu sanar dake komai.. Da alama suna zarginki..!” Ya k’arashe yana mai kuma fashewa da dariya.
Zuciyar Maleeka yaci gaba da tsinkewa, Ta shiga girgiza kai tana duban Chief wanda keta kyakyata dariyar mugunta.
Lokaci guda Chief yaci gaba da fad’in “You are Trapped Maleeka.. Idan akwai wanda Mu’azzam Gamji zai suspecting cikin team d’insa Toh ki sani kece.. Tun kafin ki bari ya fara zarginki gwara shi ki dasa masa shakkun Abokinsa Assad cikin zuciyarsa. Dan abinda ya miki saura a halin yanzu shine ki nemawa kanki mafita ba ki tsaya kina b’ata lokacinki kan Mu’azzam Gamji ba wanda sam ba samunsa zakiyi ba..”
Gijif Maleeka ta zauna saman gadon tanajin Hawaye na gangaro mata.. Tanata fafatawa tana k’ok’arin taga ta cire Safeenah daga rayuwar Mu’azzam ashe haukarta take. Yaushe duk hakan ya faru batada labari.. Kenan Yusuf ma ya sani amma bai sanar da ita ba.. Toh mai suke nufi da ita ne wai.. Tana nan tana k’ok’arin karesu gaba d’aya team d’in daga sharrinsu Jaja ashe su suna can suna aiwatar da abubuwansu ba tareda saninta ba.. Tayi imani Mu’azzam Gamji ba son wannan yarinyar yake ya aureta ba saidai sabida ci gaban case d’insu.. Ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na mata d’aci hawaye na gangaro mata.. Dikda haka bataji son Mu’azzam ya ragu koda da percentage guda ne cikin zuciyarta. Tana jin hannayen Jaja a jikinta ta kuma rintse idanunta.
**
Daddy yana zaune parlonsa na k’asa yana duba wasu takardu da suka shafi Kampaninsu yaji sallama kaman Ta d’anuwansa Salman. Ya bar abinda yake ya d’ago da tsananin mamaki yana duban K’anin nasa wanda sam baisan yaushe yazo garin ba.
Murmushi saman fuskar Uncle Salman ya k’araso yana mai mik’awa Daddy hannu alamun musabaha.
Tsananin mamaki ne saman fuskar Daddy dan ko hannu ya gaza mik’a ma D’anuwan nasa.
Uncle Salman ya murmusa kafin ya zauna gefen Daddy yana mai kishingid’uwa cikin kujera “Aren’t you going to welcome your brother..?” Ya tambaya yana karkad’a k’afarsa wanda ke bisa d’aya.
Daddy ya aje takardun dake hannunsa had’ida zame Farin gilashi wanda yake sanyawa idan zai karatu. Ya karkato yana duban Uncle Salman sosai.
“Salman yaushe kazo garin nan.. Sannan ya akai baka sanar dani kana garin nan ba..?”
Murmusawa Uncle Salman ya kumayi kafin ya gyara zamansa yace “First gaisuwa ya kamata mu farayi dan munga juna a matsayinmu na ‘yanuwa.. Sannan sauran tambayoyi su biyo baya..”
Daddy ya girgiza kai yace “Salman bazaka tab’a canzawa ba.. You like to surprise people..”
Uncle Salman ya kuma murmusawa kafin yace “Exactly.. No one knows me better than my brother.” Ya k’arashe yana sakin murmushi.
Daddy ma murmushi ya sakar masa kafin ya mik’o masa hannu sukai masabaha.
Gaisawa suka shiga yi Daddy na tambayarsa mutan gida.
Nan Uncle Salman d’in ke fad’in ko Shemau batasan yana garin ba, sunyi waya yace mata zaizo sa amma tin lokacin da suke wayar ma yana cikin Abuja.
Daddy ya kuma murmusawa had’ida girgiza kai kad’an kafin yace “Salman kenan. Bazaka daina wannan d’abi’ar taka ba.. Na tuna a baya haka kakeyiwa Inne duk lokacin hutunka sa’ilin kana makaranta.. Zakuyi waya da Inne ta tambayeka ya karatu ka amsa mata komai lafiya. Kuna ida waya saidai Inne ta ganka akanta..”
Suka d’an dara gaba d’aya kafin Uncle Salman yace “Toh haka ai yafi.. ka dinga surprising mutane. Watarana zasuyi kewarka.. Gashi na samu Magaji a zuri’a mai irin halina Wato Mu’azzam.. Yaje yayi aure ba tareda saninku ba ya baku shock da surprise..”
Daddy ya d’ago yana duban Uncle Salman da mamaki kafin yace “Kanada labarin auren Sirrin da Mu’azzam yai ne..?”
Uncle Salman yai k’asaitacciyar murmushi kafin yace “Au dama bai sanar dakai cewa ni ya wakilta na karb’a masa auren ba..?”
Daddy ya girgiza kai disbelievingly yana duban Salman d’in ba tareda ya iya furta komai ba.
Uncle Salman ya murmusa kafin yace “It seems like bai yarda dakai bane shiyasa bai wakiltaka ba ya tsallakeka ya je wajena dukda cewa bama jituwa..”
Daddy ya girgiza kai yace “Salman meye nufinka na karb’awa Mu’azzam wannan auren.. Na tabbata bakayi haka bane dan Farin cikin Mu’azzam.. Kanada dalili.. Because you never loved Mu’azzam..!”
Mik’ewa Uncle Salman yai yana huci kafin ya soma fad’in “Idan akwai wanda baya k’aunar Mu’azzam da ci gabansa that person must be you dear brother.. Let me remind you har yau kak’i ka sanar da kowa ina kake kai dukiyar Mu’azzam.. Kar ka mance Mu’azzam ya kawo k’arfi da zai iya kula da dukiyarsu da mahaifinsu ya mutu ya bari.. Amma har yau kak’i la sanar da kowa harta shi Mu’azzam d’in.. Mai kake nufi da haka.. Ko auren mahaifiyarsa da Kayi ne kake tunanin ka samu cikakken dama da iko akan dukiyarsu..?!”
A fusace Daddy ya mik’e kaman zai mari Uncle Salman sai kuma ya dakata yana nunasa da yatsa “Kar ka bari na tono abinda ya wuce shekaru masu yawa Salman.. Nayi shiru ne Salman sabida bana so ahalinmu Ta tarwatse.. Nayi shiru ne sabida bana so k’unci ya halak’a mahaifiyarmu.. Nayi shiru ne to protect Mu’azzam from you..!” Ya k’arashe yana nuna Uncle Salman hannunsa har rawa yake.
Cak Musaddiq dake k’ok’arin shigowa parlorn ya dakata yana sauraron abinda Mahaifin nasa ke fad’i zuciyarsa na wane irin yankewa..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*37*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Shaye da tsananin mamaki Uncle Salman ke duban Daddy kafin ya girgiza kai kad’an “Mai kake nufi..?”
Daddy ma jinjina kan nasa yake fuskarsa gauraye da tashin hankali yake furta “I lived with this Salman tsawon rayuwata.. I know exactly what happened that day.. Ranan da Yayanmu Abubakar ya rasu..!”
Uncle Salman ya kuma girgiza kai kafin yace “I still don’t get you.. Shin mai kake nufi..?”
Daddy ya jinjina kai yace “Naji sa’insan da kukai dashi.. Ka masa rashin kunya cewa ko ba dad’e ko jima sai ka karb’e position d’insa.. I was in his office that day, we were to inspect the factory together dan har mun saka rigunan leda irin wanda ake sakawa idan za’a shiga inspection.. Da naji tattaunawarku sai na fasa shiga inspection d’in nai niyyan komawa gida domin na samu Inne mu tattauna batun had’in kan ahalinmu dan tinda Baffah ya rasu kake rashin kunya wa Hamma.. Baka ganinsa da gashin ido ka kafa idanunka akan matsayin da yake rik’e dashi.. Na fito na barku a cikin Factory.. Koda na dawo gida labarin mutuwar Hamma ya riskemu cewa he was stuck in a cold room... I didn’t want to suspect you Salman because you are our brother.. Na aje wannan a cikin zuciyata ban sanar da kowa ba sabida banaso na raba kan ahalinmu ko na lalata zumuntar mu, sannan banaso bak’in ciki ya kashe mahaifiyarmu mu kuma rasa ahali... Nayi zaton idan ka samu abinda kake so Wato Company zaka rabu da Ahalin Hamma ka cire ido akan Kaso na dukiyar Mu’azzam.. But still ka d’auki tsana ka d’aura akan Mu’azzam kaman dai ba ciki guda kuka fito da Mahaifinsa ba.. Na zab’i na adana masu dukiyarsu sabida D’anuwa irinka Salman.. Shin ka zaci na rayu da wannan abun cikin zuciyata abu ne mai sauk’i..?!” Daddy ya k’arashe yana girgiza kai hawaye na gangaro masa.
Uncle Salman murmusawa yai kafin yace “Is this how you welcome a guest, Dear Brother..?” Ya kuma murmusawa kafin yace “Matsalar shine baka da wata shaida da zata nuna cewa ni na kashe Yaya.. Quite alright na fad’i duk abubuwan da kace nace amma abinda bazan tab’a yarda na aikata ba shine kisan Yaya.. Ban kashsa ba lokacin sa ne yayi kuma shiyasa ya mak’ale a d’akin K’ank’ara..”
Daddy ya jinjina kai kafin yace “What if baka aikata ba amma maganganun da ka fad’a masa sun janyo ya yanki jiki ya fad’i a cikin d’akin K’ank’ara hardai ya mutu ba’asan yana ciki ba.. What if wann maganganun Naka sune silar mutuwarsa