Showing 39001 words to 42000 words out of 209154 words
da fad’in “And remember, I’m a lawyer. I can defend myself and easily incriminate you.. Kar ki damu ina k’aunarki Safeenah.. And I’ll never give up on you..” Yana ida fad’in haka ya fashe da dariya had’ida katse kiran..
Bibbiyu Safeenah ke gani.. Zuciyarta taci gaba da tsinkewa.. Da dafe dafe ta zauna saman gado, wani irin rawa jikinta keyi.. Ta kuma duban wayarta jikinta naci gaba da rawa.. Tama nemi kukan Ta rasa sai tsananin rawa da illahirin jikinta ke mata.. Har ji take Tamkar zazzab’i ke shirin sauk’o mata.. Ashe kuka ma rahama ne dan ta nemi kukan ta rasa.. Tsoro take kar Ameer ya zamto silan mutuwar aurenta.. Ya zama dole ta kare aurenta at any cost. She needs to be with her husband idan har tana so ta gyara aurenta. Amma mijinta baya nan yana can Fufore dan saida tayi waya da Assad taji Ba’asin abinda ya sami Mu’azzam ya tafi yai abandoning aikinsa tinda Ta sansa kan batun aikinsa.. Sanin cewa Safeenah matar Mu’azzam ce da kuma magiyar data tayiwa Assad d’in ya kuma san halin Mu’azzam d’in ba lallai ya sanar da ita an dakatar dashi na wani d’an lokaci ba yasa shi sanar da Ita suspending nasa da akai..
Tai zaune saman gado tana juya wayar cikin hannunta “What do I do now.. It’s too bad he got suspended.. But he sure had it coming da wannan zafin zuciyar tasa.. Yanzu idan inaso na kasance dashi saidai na bisa cen kenan.. Oh shitt.. I don’t like it there gaskiya bazanje ba.”
Muryar Meema ce ya katseta “You have to.. Ya zama dole kije Adda Feenah and be with your Husband idan har kinaso ki sami kusanci da mijinki.. If not you’ll end up losing him..”
A zabure Safeenah ke duban Meema. Nunata take da tsananin mamaki “How long have you been standing there.. Did you hear everything I said..?” Tai tambayar idanunta na firfitowa waje..
Meema taci gaba da takowa cikin d’akin murmushi saman fuskarta “Why.. Did you say something that I shouldn’t hear..?”
Murmushin yak’e Safeenah tai tace “Sabida na sanki da shegen gulma ne da shiga abinda babu ruwanki shiyasa.”
Meema ta murmusa tace “That’s my personality I guess. And I’m sure you’re used to it.. Addah Feenah you need to follow your husband.. Shawari nake baki..”
Hararata Feenah tai tace “Last time I check komai lalacewa yai da nabi shawarinki..”
D’an tab’e baki Meema tai tace “I’ve done my part tinda na baki shawari, it’s up to you Ki d’auka ko kar ki d’auka..” Ta k’arashe tana duban Safeenar murmushi saman fuskarta. Lokaci guda tasa kai zata fice.
Feenah ta dakatar da ita da fad’in “We are going together Meema.”
Meema ta zaro ido waje tace “Wa ni. Spare me Adda Feenah.. Wann mijin naki lamba d’aya ne a rashin mutunci. Bansan mai zai aikata mana ba wann karon. Chabd’i. Who knows what he might do to us.. Inaga kuraye zai kwance mana wann karon.”
Feenah tace “Kar ki damu we’ll act smart wann karon. Yanzu mai zamuce wa Mommy ga Daddy ma yau na hanya.. Nasan definitely Mommy bazata barmu mu tafi ba..”
Meema ta murmusa tace “Haba Adda Feenah kar ki badani mana, Keda kike da dalilin zuwa k’wakk’wara. Kawai cewa zakiyi mijinki ne yace yana so kije can ki samesa and yana jin kunya bazai iya kiran Daddy ko Mommy ya fad’I ba.. He wants you to have your first honeymoon a garinku..” Ta k’arashe tana kashe mata ido..
Pillow Feenah ta jifa mata tana fad’in “Zaki sani ne.. Well shawarinki yayi, zan fad’awa Mommy Mu’azzam yana so naje Fufore and inaso ke kuma ki rakani.. Ita kuma Mommy tasan mai zata cewa Daddy.. Nasan bazata yarda muje ba amma sai mun fama arranging komai mu sanar da ita.. Ke sai mun isa ma mu sanar mata dan Nasan babu yanda ta iya idan taji Muna cen dole kawai tasan abinda zata nemo ta fad’awa Daddy..”
Meema ta murmusa had’ida mata jinjina da babbar yatsa “You’re genius Adda Feenah.”
Ita kaw Feenah sai murmusawa take tana jin yau d’in ta tsara zance ya tafi daidai.
**
Koda Malam Liman ya samu Baban Sabeer da batun cewa Sadiya da mahaifiyarta basu amince da buk’atarsa ba huci ya dingayi cikin zuciyarsa yana ayyana bai tab’a neman abu ya rasa ba balle ma mace, bazai fara akan Sadiya ba.. Dik yanda zai Sai ya tabbata ya aureta.. Koda ita da mahaifiyarta basa so..
Tabawa ce ta fad’o masa ransa, ya saki wata irin muguwar murmushi kafin yai sallama da Liman yace idan sun canza shawarinsu shi dai yana nan akan bakansa, zai sauk’e masu nauyin bashi a matsayin Sadakin Sadiya..
Baban Sabeera yana ficewa daga Zauren Malam Liman bai zarce ko ina ba sai gidan Tabawa. Tabawa taji mamakin jin Alhaji Isyaku na sallama da ita.
Ta fito mamaki fal saman fuskarta, bayan Ta masa gaisuwan mutunci irin wanda ake ma masu abin duniya.. Ta kuma risinawa tana fad’in “Alhaji inji dai lafiya koh, ko wani abin ne ya faru..?”
Alhaji Isyaku ya gyara babbar rigarsa yana fad’in “Toh lafiya ne ya kawo haka kuma babu komai sai alkhairi..”
Tabawa ta Washe baki dan a tinaninta Alhaji Isyaku zaice yana sonta ne bayan tsawon shekarun data kwashe a unguwar tana zaman kanta. Tabawa ta shiga sanne kai tana mad’e.
Alhaji Isyaku yai gyaran murya yace “Nasan kina so a biyaki kud’ad’en da kike bi bashi.. Musamman wanda kike bin iyalan Malam Ibrahim mai rasuwa..”
Jikin Tabawa ya d’anyi sanyi, ta dubi Alhaji Isyaku tace “Toooh zaka biya masu ne Alhaji..?”
“K’warai kuwa zan biya masu amma fah inada sharad’i..”
Tabawa ta dubesa da mamaki wannan karon “Alhaji sharad’i kuma ni da hakkina.. Hakkin d’imbin jama’a dake kaina ace sai an gindaya min sharad’i a biyani.. Wannan batu ma ai hankali bai kama ba.. Haba haba dai jama’a.. Wllhi Alhaji ina ganin mutuncinka a layin nan dan rufin asirin da Allah yayi maka, kar kasa na daina gani.. Ka gode ma Allah wannan maganar da dare kazo min da ita dan da ace da rana tsage tsage kazo min da ita da na daina ganinka da wannan mayafi na mutunci da nake ganinka da Ita ehe..” Ta k’arashe tana jijjiga had’ida huci..
Alhaji Isyaku ya murmusa cikeda jin dad’in halin rashin mutunci da Tabawa keda shi yasan bazai sami matsala daga wajenta ba.
“Hajiya Tabawa kenan.” Hannu ya zira cikin aljihunsa ya ciro kud’i bandir ‘yand’ari bibbiyu ya mik’a mata “Ungo karb’i wannan..”
Tabawa ta k’yalla idanunta akan kud’i sai kuma tai wani murmushin rainin hankali tace “Haba Alhaji nice za’a min biyan ‘yan tasha a bani kud’ina gutsiri gutsiri.. Ko kasan kullum k’Arya nake wa mutane masu kaya cewa Kaya yana saman ruwa bai iso ba.. Ni fa na gaji da k’anan Murya. Wllhi bazan karb’i kud’i kad’an kad’an ba.. Dubu ashirin fah kake mik’o min..”
Alhaji Isyaku ya murmusa yace “Wataran ma Daloli za’a mik’o miki.. Yanzu ki amshi wannan kiji na Menene..”
Tabawa ta dubesa a yatsine sanda yaci gaba da fad’in “Wnn kud’ad’e da kike gani ba bashin da kike bi bane.. Sune mabud’an hanyar da zaki bi Ki sami kud’ad’enki..”
Tabawa ta dubesa da mamaki, hanu har na rawa Ta amshi kud’ad’en.
Alhaji Isyaku yaci gaba da fad’in “So nake ki saka masu pressure.. Ki matsa masu ki tak’ura masu.. Idan ta kama kice zaki d’ebo masu ‘yansanda kuma zaki maka Su a kotu. Dik yanda kud’ad’enki suka shiga suka fita su nemo su baki. Ni kuma na miki alk’awarin baki wasu kud’ad’en bayan bashinki da za’a biya..”
Mamaki ya cika Tabawa Ta shiga Washe baki tana fad’in “Idan dan wannan ne kar kaji komai Alhaji.. Wllhi rashin mutunci yanzu zan soma masu irin wanda ma ban masu a baya ba.. Kuma babu ubanda ya isa ya dakatar dani..!”
Alhaji Isyaku ya murmusa yace “Da kyau Tabawa.. Sai naga sakamako..” Daga haka sallama sukai shida Tabawa ya wuce yanda ya aje motarsa..
**
Kyallu ta gyara tsayuwarta sosai tace “Kina jina..”
Ajidde dake duk’e gabanta Ta jinjina kai a hankali alamun eh.
“Zakije wannan gidan kuma zaki rufe kanki a d’aki da wannan nakasesshiyar matar, idan ta kama ki shige har cikin drawer kin binciko mana ‘yankunnayen zinari da a warwaro ne zakiyi.. Wannan karon kar ki dawo min gidan nan babu komai Ajidde.. Ke idan ta kama ki saci jiki ki shiga sauran d’akuna nan ne toh fa sai kin shiga kin sato mana abin duniya da ‘yankud’ad’e kinji koh..”
Ta ciro wani laya cikin bujenta Ta mik’a ma Ajidde “Ungo nan amsa.”
Ajidde Ta mik’a hannu Ta amsa da k’yar..
“Layar zana ce da zaran kinga za’a kamaki kafin su shigo cikin d’akin sai ki matsata da k’arfin gaske yanda bazasu ganki ba..”
Nan ma Ajidde jinjina kai tai kafin Kyallu Ta shureta da k’afa tace “Tashi ki daina kallona da wannan zuru zuru idanun naki..”
Ajidde Ta mik’e da k’yar rataye da jakan maganinta Ta fice..
Tana tafe tazo dai dai k’ofan gidan Malama Hafsah, tai tsaye tana duban k’ofar gidan..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*15*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
K’arfe shida na safe sukaji ana bugun k’ofan gidan kaman za’a b’alla.. Bugu ake da k’arfin gaske ana jijjiga k’ofar, bai tsaya a bugun k’ofa ba tuni aka soma jefo duwastu cikin gidan.
Umma dake bisa sallayarta wanda tinda tayi sallan asubahi bata tashi kan sallayar ba tana zaune tana Lazimi da kai kukanta ma Sarki da babu kamansa, majib’icin lamiransu, Mai mulkin sammai da k’assai wanda babu abinda yafi k’arfin ikonsa da buwayarsa.. Babu shiri Umma ta mik’e tana mai linke abin sallarta, Ta aza cazbahan dake hannunta saman abin sallar kafin ta nufo waje.. Kusan cin karo sukai da Sadiya wacce Ta fito daga kitchen tana kalata masu abinda zasuyi karin kumallo dashi.
“Umma bugun k’ofa ake..” Batakai aya ba aka kuma jefo wani Dutsen sai a goshin Ashiru da fitowarsa kenan yana mutsuka ido. Aiko nan ya saki k’ara yana rik’e goshinsa.
A tare Sadiya da Umma suka nufosa dan tuni ya kwanta wajen yana dafe da goshinsa yake fad’in “Kaina kaina Umma.. Wayyo Allah kaina.!”
A fujajan Sadiya taje Ta nemo tsumma ta d’aure masa goshin nasa dan k’ok’arin tsaida jinin.. Umma kaw babu shiri ta nufi k’ofa ganin basu fasa abinda suke aikatawa ba.
Tana bud’e k’ofar ta hangi Tabawa na tsaye wasu k’artan maza guda uku sun sakata a tsakiya ga duwastu a hannunsu. Sai faman sakin huci Tabawa take.
“Yauwa kunaji ku shiga ku fito da dik abinda yake mai amfani ne a cikin gidan.” Tabawa tace tana duban k’artan mazan.
Da tsananin mamaki Umma ke dubanta “Amma Tabawa bakida mutunci.. Shin wace doka ce ta baki daman ki shigo har cikin gidanmu kici mana mutunci dan kina binmu bashi.? Jifan da kika tashemu dashi har kikaji ma d’ah na ciwo bai isheki ba shine zakice ma wad’annan K’artan banzan su shiga gidan mata mai takaba su kwaso miki kayanta.. Anya Tabawa akwai zuciya cikin k’irjinki.. Anya zaki wanye da duniya lafiya..?”
“Toh sai ki hani wanyewa da duniyar lafiya idan kece mai Ita... Ke har zakiyi ma wani wa’azi. Yaushe ma kika tuban.. Yaushe kika daina zuwa wajena kina rok’ona Allah Annabi na samo ma d’iyarki manyan Alhazawa shine yanzu dan duniya ta juye daku zaki bud’e tsartsaman bakinki kice zaki min wa’azi.. Toh wama zai saurari wa’azi daga bakinki.. Koda shike ba laifinki bane ke d’in dama ai tsintacciyar mage ce baki da dangi sai na bariki.. Kai Over Wai mai kuke jira ne.. Ku shige kuyi aikin da na sakaku.”
Suka amsa da Toh Hajiya Tabai.
Umma bata iya furta komai ba Sai hawaye dake ambaliya a fuskarta.
Sadiya ce Tai k’ebebe bakin k’ofar ta hanasu shiga “Babu Wanda ya isa ya keta mana haddi ya shige mana gida ba tareda izinin mahaifiyata ba.. Hajiya Tabawa kar ki bari na maka k’ararki a ofishin ‘yansanda.. Tin muna saida juna ki tattari body guards d’inki ku b’ace mana a k’ofar gida bamu neman tashin hankali..”
Shewa Tabawa tai harda rangad’a guda “Tashin hankali ai cikinta kuke dumu dumu..” Ta k’anne ido tana nuna Sadiya da yatsa “Ke k’aramar maras kunya ni kike ma barazanan zaki kai k’arata wajen ‘yansanda.. Cikin ni da ku wanene yake da abin kaiwa k’ara wajen ‘yansanda.. Ga fili ga doki maza.. Zo ki shige kije kikai k’arata wajen ‘yansanda.. Nasan dikda asarar da na maku bazai kwatan kud’ad’en da nake binku ba... Jeki Sadiya jeki ki kai k’arata ni kuma nayi alk’awarin jaza maku wulak’ancin da ban maku ba a baya.. Over ku shige nace ku tattaro.. Idan bata matsa maku a hanya ba ku had’a da Ita dan nasan zata maku amfani ko rage dare kwayi da Ita dama sauran titi ce..”
Wannan karon Umma ce ta dakatar da Tabawan, cikin tsananin huci take nuna Tabawan da yatsa, lokaci guda take fad’in “Koda wasa kar ki sake aibata d’iyata a gabana.. Idan kuma ba haka ba..”
“Idan kuma ba haka ba Sai k’ak’a..?” Tabawa tace tana ci gaba da jijjiga “K’arya aka mata Ko ba abinda ta saba yi bane..?”
Hawaye ne kawai suke gangarowa daga idanun Sadiya da Ta tare k’ofar gidansu cikin tsananin huci.. Jin kalaman Tabawa take kaman ana dab’a mata wuk’a tsakiyan k’irjinta.. Yayinda su Over ke binta da mayen kallo suna wani shafa hab’a suna fad’in “Kuma fah wllhi dama ta jima a ranmu.. Muna ganin yanda masu manyan motoci suke safara a unguwar nan suna kwasanta... Kawai dan bamuda kud’i ne da muma mun jima da d’anata ai..” Suka k’arashe suna masu sakin shewa irin na cikakkun ‘yan daba..
Daidai lokacin Alhaji Isyaku ya doso lungun yana aza babbar riga yake fad’in “Yaya yaya kai yaya dai meke faruwa ne Wai..?” Kafin Alhaji Isyaku ya k’araso ‘yan daban Tabawa suka aune a guje dan sunsan wanene Alhaji Isyaku yanzu Sai ya kwaso masu ‘yansanda yasa a tafi dasu.
Tabawa sai huci take tana kuma balabala wutan masifa.
Alhaji Isyaku ya k’araso yana tambayan Tabawa ba’asi tamkar baisan komai ba..
Tabawa kaw nan taci gaba da masifa tana fad’in “Toh Wai biya masu zakayi ne Alhaji da zaka wani Zo ka dakatar dani.. Rashin mutunci yanzu na fara ehe idan har baza’a biyani kud’ad’ena ba..” Ta maidoda dubantaga Umma dake tsaye Jiki a matuk’ar sanyaye tana hawaye, lokaci guda Ta kad’a ‘yar yatsarta tace “Kunci sa’a wannan karon.. Had’uwar mu na gaba sai yafi wanann muni idan har baku biyani kud’ad’ena ba..” Ta k’arashe tana mai janye mayafinta fuuu ta wuce..
‘Yan lungun kaw kaman ba safiya ba Sai lek’e ake anyi cincirindo ana bama ido abinci..
Alhaji Isyaku ya risina yana bama Umma hak’uri kan abinda ya faru, idanunsa rabi naga Sadiya wacce maganganun ‘Yan daban Tabawa ya sanyata zama sukuku da ita, gaba d’aya bama ta fahimci su waye a wajen ba, maganganun ne kurum suke Yawo a kwanyarta da dodon kunnuwanta.. Irin kallon da illahirin mutanen unguwarsu ke mata kenan, Fanko, sauran kwalta. Bata tab’a yin danasanin rayuwar da tai a baya na rashin kamun kai irin yau ba.. Ashe mutunci yafi komai.. Mutunci yafi kud’i.. Yau da ace ta rik’e talaucinta ta tsaya a matsayin da Ubangiji ya ajeta da babu wanda zai dubeta ya mata irin wannan mummunan k’azafi maras dad’in sauraro.. A nasu tinanin samaruka da suke d’aukanta a manya motoci mutuncinta take saida masu, yanda take shigan gayu ta rik’e babban waya ita ba d’iyar kowa ba dole suyi tinanin mutuncinta take saidawa ta samu. Abinda bata tab’a kuskuran koda aikatawa ba.. Ta lumshe idanunta hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata.
Kaman Umma tasan tinanin da take tai saurin k’arasowa Ta rik’e hannunta tana girgiza mata kai take furta “Komi kikayi sai an zageki a duniyar nan.. Kar ki bari maganganun su ya dameki kinji koh..”
Alhaji Isyaku na tsaye gefe ya kannare idanu yana dubansu.
Sadiya bata iya furta komai ba har lokacin saima duban Umman da take cikin wane irin yanayi.
Ana haka Ashiru ya fito rik’e da kansa dake jini har lokacin kuka yake.. Kukansa ne ya dawo da hankalin Sadiya, tai saurin ta nufesa tana tambayarsa ko kan nasa ke masa ciwo.
Ga mamakinta Alhaji Isyaku ne ya k’araso yana fad’in “Subhanallahi.. Garin yaya haka Ta faru.. Wannan Ai sai an kaisa asibiti..”
Da tsananin mamaki take duban Baban Aminiyar nata yayinda mak’ota ‘yan lek’e suka ci gaba da bama ido abinci wasu na k’usk’us ganin yanda Alhaji Isyakun duk ya wani susuce kan abinda ya samu su Sadiya saikace ba shi bane kwanaki yazo masu da ‘yansanda.. Tabbas akwai wata a k’asa..
Ba tareda Sadiya tace komai ba ta shiga janyo hannun k’aninta tana fad’in “Umma zan kaisa chemist d’in Ema..”
Alhaji Sabi’u yai karaf yace “A’a ai bazai iya tafiya kan k’afafunsa ba jini ya zuba jikinsa.. Motata na bakin layi barin d’aukesa in kaisa..”
Umma tai saurin girgiza kai tace “A’a Alhaji.. Kawai kaje mun gode Sadiya zata iya kaisa.”
Alhaji Isyaku bai tsaya sauraron Umma ba ya sunkumi Ashiru yana fad’in “Haba dai Umma ai ciwo irin haka da zuban jini ba’a wasa..” Tuni ya shige da Ashiru rungume cikin hannunsa yana masa sannu..
Daga Umma har Sadiya da tananin mamaki suka bi bayan Alhaji Isyaku da kallo babu kaman Sadiya wacce ta kuma komawa tamkar mutum mutumi.. Wai Abban Sabeera da baya k’aunan ganinta da Sabeera shine ke wannan rawar k’afar duk dan sabida Ta yarda da aurensa.. Ikon Allah Wai dama haka mutane suke ne.. Lallai mutumin nan yakai mak’ura a rashin kunya.. Babu kunya har na kiran mahaifiyarta da Umma.. Tabd’i.! Wannan abu da matuk’ar mamaki yake..
Duban juna sukai itada Umma cikinsu babu mai iya cewa komai sai tsananin mamaki da ya lullub’esu.. Umma ta kamo Sadiya Ta maida k’ofar gidan Ta tura dan har lokacin ‘yan lek’e basu daina ba..
Su duka biyun sukuku suka nufo tsakar gidan babu mai iya cewa komai dan har lokacin mamaki bai sakesu ba..
Sadiya ta taimaka ma Umma ta zauna nan tsakar gidan saman tabarma..
Sauk’e nannuyan ajiyan zuciya Umma tai tace “Hmmmm Ikon Allah..! Lallai a gaisheda namiji..” Umma tace tana kuma canza position d’in taguminta a karo na biyu.. Sadiya kam tsaban mamaki tama rasa bakin magana. Kitchen kawai ta nufa yanda take jiwo k’aurin girkin data d’aura alamun ya soma k’onewa..
Bayan kaman shud’ewan awa guda saiga Ashiru ya shigo rik’eda robar Ice cream yana sha ga goshinsa an rufe da bandage. Baban