Showing 99001 words to 102000 words out of 209154 words

Chapter 34 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3057

yasa zan tsaya na kula da kai.”

Duban fuskarta yake musamman d’an bakinta da taketa faman turo shi gaba kafin ya soma k’ok’arin mik’ewa zaune, yace Ta mik’o masa pillow.

Baki a ture ta isa ta d’auko pillow d’in, ya d’an matsar da bayansa alamun ta saka masa pillow d’in jikin gadon. Nan ma fuska babu walwala ta k’arasa ta saka masa pillow d’in ya d’an jingina bayansa.

“Sai mai kuma.?” Ta tambaya Cikeda k’osawa.

Juyawa yai gefen bedside yanda magani da ruwan gorar ke ajiye yace ta mik’o masa. Babu musu Ta isa tai yanda yace d’in.

“Saura cup.” Ya fad’i yana dubanta.

Babu musu ta sauk’o downstairs ta haura masa da glass cup. Ya dubeta yace ta zuba masa ruwan ciki. Nan ma babu musu tai yanda yace Ta mik’a masa.

Maganin ya d’auka ya b’alla yasha, lokaci guda ya maida kansa ya jingina jikin pillow d’in had’ida lumshe idanunsa.

“Zan iya tafiya..?” Sadiya ta tambaya tana dubansa.

Still idanunsa a lumshe yake fad’in “I might need something.. You stay here until I fall asleep.. Amma idan baki so na kaiki kuma fine.. Kina iya tafiya..”

Idanunta sukai raurau, ta koma gefe ta zauna ta tak’ure cikin hijab d’inta Dan ji take sanyin AC d’in dake d’akin ya mata yawa ga sanyin damina.. Gaba d’aya sai kan nata yaci gaba da sarawa.

Suka d’ibi lokaci a haka, yana nan kishingid’e idanunsa a lumshe. Sadiya kaw Sai rawan d’ari take tana daga can gefe tak’ure cikin hijabi. Maganin dake gefensa Ta hanga takeda tabbacin na rage rad’ad’in ciwon kai ne. A hankali ta sad’a’d’a ta d’auko maganin da ruwa ta b’alli guda biyu tasha ko zataji sauk’in ciwon kan dake damunta.

Mu’azzam yana jinta saidai bai bud’e idonsa ba baice komai ba har ta dawo da maganin Ta ajiye.

Ta koma taci gaba da tak’urewa tana rawar d’ari. A haka take jin ciwon kan nata na raguwa saidai kafin tai wani aune bacci yayi gaba da ita nan yanda take zaune.

Ya bud’e idanunsa yana dubanta, nan yaga tayi bacci.. Ya dubi maganin yaga har guda biyu tasha, yasan dole zai mata k’arfi sannan zai sakata bacci.

Yai mata K’uri yana dubanta yanda ta tak’ure tana bacci. A hankali ya mik’e ya isa ya d’aukota ya kawota kan gado ya kwantar. Lokaci guda ya rage sanyin AC d’in. Hijab d’in jikinta ya soma k’ok’arin zame mata Dan ta samu tai baccin a sake. Nan yaji bugun zuciyarsa na k’aruwa a lokacin da yake cire mata hijab d’in.

Kasancewar duk English wears ya saya ya aje mata a wardrobe d’in yasa bata da wani tufafin sakawa face su. Saiko dogayen riguna dangin abaya. Nan yaga wata jan riga ce doguwa Wanda ta d’an kama daga k’irji zuwa ciki saiko k’asan dake baje shine a jikinta.. Yai saurin kauda kansa gefe yana jin zuciyarsa na kuma tsinkewa..
A hankali ya lumshe idanunsa yana furtawa a hankali “What’s wrong with you Mu’azzam.. Kar kyaun jikinta ya rud’eka Ta riga Ta rabar dashi ma wasu banzaye.. Ita d’in bata cancanceka ba.!” Tina hakan da yai Sai ya kuma jin zuciyarsa na masa zafi.. Cikin sauri ya janyo bargo ya rufa mata, ya sauk’o daga saman gadon ya dawo nan k’asa yanda ya tashi ya kuma kwanciya yana lumshe idanunsa, saidai duk rufe idon da zaiyi kyakkyawan surar jikinta yake gani.. Ya mik’e ya zauna yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa.. Meke faruwa dashi..? Badai sha’awan yarinyar nan yake ba.. Kai never..! God forbid..! Ya kuma lumshe idanunsa, ji yai zaman d’akin na neman gagaransa. Ya mik’e ya bud’e k’ofar balcony yana shan fresh air na damina.. nan yaji k’aran hadarin dake sararin samaniya na k’aruwa. Kan kace mai an soma ruwa kaman da Bakin k’warya. Ya mik’a fuskarsa waje ruwa na zubo masa saman fuskar nasa, idanunsa a lumshe ko zai daina ganinta amma babu abinda ya canza Ita d’in dai yake gani.. Ya yarda sha’awanta yake sannan bai tunanin zai iya rik’e kansa har gari ya waye.. Toh amma ta yaya zai had’a jiki da fasik’a irinta..? Wata zuciyar tace masa ai kai ba fasik’anci zakayi da ita ba ka biya sadaki, ka fanshe sadakinka tinda dama Ta saba a biyata kud’i ta bada jikinta.. Kai Naka ta halattacen hanya zakayi akwai igiyan aurenka har guda UKU akanta wanda sun halatta maka Ita. Ya bud’e idanunsa yana fuzar da fuci a hankali.. Toh amma ta yaya zai soma tunk’aranta da batu irin wannan aima sai ta rainasa ta maidashi D’anhannu irinta.. Ya saka hannayensa biyu ya shafi sumarsa da suke wet ya maidasu baya.. Zuciyarsa tana fad’i masa this is the perfect opportunity for you Idan baka so ta fahimci wani abu ya shiga tsakaninku kaje mata a cikin barci bazata fahimci komai ba.. Besides tinda an samu suspect shikenan zaka rabu da ita bazata kuma dawowa cikin rayuwarka ba.. Da wannan tunanin Mu’azzam ya dawo cikin d’akin. Yana tina suffarta da kuma ni’imtaccen k’amshin da yaji cikin jikinta.. A cikin baccin ya dinga sarrafa sassan jikinta yana mamakin mace da ta gama yawon ta zubar jikin nata bai sake ba, komai zamzam kaman dai na sabuwar budurwa wacce bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.. Tin daga nan jikin Mu’azzam ya soma yin sanyi yanajin zuciyarsa na masa wani irin rauni.. Bai ida shan mamaki ba saida yazo shiganta yaji kirif babu alamun ta tab’a tarayya da wani d’a namiji.. Cikin tsananin sanyin jiki ya tsaya cak ba tareda ya ida nufinsa ba.. Ya d’ago yana duban fuskarta wanda har lokacin idanunta a lumshe suke alamun bacci take.. Take yaji bugun zuciyarsa ya k’aru.. Toh kodai idan mace tayi tarayya da wasu mazan bayan wani lokaci idan ta jima batayi ba tana komawa budurwa ne..? Da kansa ya bama kansa amsa da fad’in no never.. Sabo Sabo ne.. Koda ace baisan halitta ‘ya mace practically ba ya sani a karance.. A hankali yaji bakinsa na furta “She’s verging..!” Cikin tsananin sanyin jiki ya mik’e kaman wanda aka zare ma laka. Ya shiga janyo mata tufafinta yana maida maida mata. Ya janyo bargo ya kuma rufa mata bayan ya gyara mata kwanciyarta. Yai zaune had’ida mata K’uri yana duban fuskarta lokaci guda yana jin wani abu mai kaman tausayinta can k’asan zuciyarsa.. Kalaman b’atanci da ya dinga fad’a akanta yake tunawa da irin wulak’ancin da ya dinga yi mata.. Toh kenan batabi mazan bane kokuwa dai sharri ake mata..? Toh Wai shin meke faruwa ne..? Ya kuma tambayar kansa yana dubanta. Tabbas ya shiga rud’u da rashin sanin abinda zai yarda dashi.. A hankali ya mik’e daga kan gadon ya nufi bathroom ya d’auro wankan tsarki. Ya dawo cikin d’akin har lokacin baccinta take. Drawer ya isa ya d’auki takarda da pen yai rubutu saman takardan ya linke ya ajiye mata nan gefenta.

Sadiya kaw maganin bai saketa ba Sai wajajen k’arfe bakwai na safe, Ta mik’e taji idanunta sun mata nauyi.. Nan ta ganta a d’akin Mr Inspector saman gadonsa.. Take ta soma tuna abinda ya faru a daren jiya, ya sanyata zaman d’akinsa da sunan baida lafiya.. Tai saurin mik’ewa tana k’ok’arin sauk’owa daga saman gadon, nan taga takarda ya fad’o.. Ta mik’a hannu ta d’auko tana addu’an Allah yasa takardan saki ne ya ajiye mata. Allah yasa Ta gama mission d’inta kenan.. Da wannan tunanin ta warware takardan. Zuciyarta ne yai wani irin tsinkewa sakamakon abinda ta gani rubuce cikin takardan

_Thank you for taking care of me last night. Dare ne mai cikeda rud’ani.. Dukda cewa babu abinda ya faru, but still kiyi wanka ki tsarkake jikinki_ Sai aka rubuta Mr Inspector daga k’asan note d’in.

Jikinta ne ya d’auki rawa, ta k’unshe bakinta da duka tafukan hannayenta tana girgiza kai.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Mai ya faru da ita.. Mai Mr Inspector ya aikata mata.. Tasha magani ya sakata bacci.. Kenan Mr Inspector yayi attempting raping d’inta alhalin tana bacci.. K’ank’ame jikinta ta soma hawaye na zubo mata, cikin tsananin rawar murya take furta “Monster..! Monster.. How could you..? You are a monster..!!!” Ta fashe da wani irin kuka tana k’ank’ame jikinta. Ya mata abinda bazata tab’a yafe masa ba. Ta mik’e tana kuka ta nufi nata d’akin ta fad’a bathroom.. Haka tai wankan tana kuka tana darje illahirin jikinta.. Sosai take kuka tana jin tsanar Mu’azzam wanda bata tab’a yin irinsa ma wani bil Adam ba.

Bayan tayi wanka tayi alwala tai sallah har lokacin kuka take tana jin zuciyarta na mata wane irin zafi.. Ya bud’e mata jikinta, sannan ya kalle mata jikinta harma yayi abinda yaga dama da jikinta alhakin tana bacci.. Cikin k’unan zuciya hawaye na zubo mata take furta “He’s a Rapist.. He tried to rape me while I was asleep.. How could he..?!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin wani kukan. Ta mik’e tana goge hawayenta. Lokaci guda ta koma d’akin nasa Ta d’auki pen d’in da paper d’in da ya rubuta mata note d’in. Can k’asan rubutun tana hawaye Ta soma rubutu itama.

_I’ll never forgive you for what you did last night.! Aside from being a Kidnapper you are also a rapist, Mr Inspector. You are a Criminal, baka cancanci zama D’ansanda ba. Kai d’in D’antadda ne.. Zan iya yafe maka komai, all the insults wulak’anci and all.. But abinda kayi daren jiya abu ne da bazan tab’a yafe maka ba.. Har abada. The game is over, and the mission is accomplished. Mr Inspector_

Ta ajiye masa nan kafin Ta mik’e ta nufi gate tana hawaye.



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*33*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Zaune ta tadda D’ansandan saman benchinsa, yana ganinta ya mik’e yana sara mata “Good morning Ma’am.” Ya fad’i cikeda risinawa.

Sadiya tai k’ok’arin saita kanta kafin tace “Morning..”

Shiru ya d’an biyo yana sauraron mai zatace.

Kanta ta d’an dafe kana tace “Magani nake son zuwa saye zaka bud’e mun k’ofa yanzu.”

Ya d’an dubeta yana girgiza kai “Ma’am I’m really sorry.. I was instructed not to let you out.”

Ta tsaresa da idanu tana dubansa tana kuma kame kanta “I told you magani nake so, ko so kake na mutu maka a wajen nan.. Kai D’ansanda ne kafi Kowa sanin mai hakan ke nufi idan na fad’i maka a wajen nan.. So you better let me out now..”

“Ma’am I’m sorry.. Idan na barki kika fice, Boss won’t sapere me. Kiyi hak’uri ki koma cikin Gida..”

“Am I a prisoner da bazaka barni na fice ba.?” Ganin ya kifa Kai k’asa bai amsata ba ya sanyata dafe kanta tana ‘yank’ararraki kad’an tana k’ok’arin duk’awa k’asa alamun tana jin jiki.

Police d’in ya matso a daburce yana tambayarta “Ma’am are you alright... Do you want me to call Boss..? Ma’am..”

Bata amsa Sa ba Sai kame kanta da cikinta take tana fad’in idan bazai barta Ta fice ba shi yaje ya nemo mata maganin.. Yanda takeyi dole kayi tunanin da gaske batada lafiya.

Cikin daburcewa ya mik’e yana k’ok’arin zaro wayarsa da niyyan kiran layin Mu’azzam.

Sadiya ta kannare ido tana dubansa daga nan yanda take kwance nan ta soma fad’in “Hey what are you doing.? Can’t you see I’m in pain. Just go to any nearby pharmaceutical and get me medicine.. Wayyo cikina.. Kaina.. I can’t breath..!” Abubuwan da ta dinga fad’i kenan daga nan yanda take kwance wanda ya kuma birkita mutumin. Gashi ya gaza samun layin Mu’azzam.. Dole ya fice yana fad’in bari ya nemo mata magani. Yanda ya fice haka ya bar k’ofan a bud’e ko tinawa ya kulle baiba.

Aiko sanda ta tabbatar ya fice ya bar ma layin sannan ta mik’e tana hamdalah. Ba tareda Wani b’ata lokaci ba tasa kai Ta fice daga GIDAN ARO. Ta juyo tana duban gidan bayan ta fice, hawayen da ya gangaro mata ta goge kafin tace “Wannan shine k’arshe bazan kuma dawowa cikinka ba in sha Allah.!” Tana ida fad’in haka tasa kai Ta soma sauri sauri tana mai ficewa daga layin gaba d’aya.

**

Assad ya shigo Coffee shop d’in yana mamakin kiran da Mu’azzam d’in yai masa yace Su had’u nan da sassafe irin haka.

Assad ya k’araso sukai musabaha still mamaki saman fuskarsa. Mu’azzam ya tambayesa abinda za’a kawo masa. Nan yace a kawo masa coffee d’in shima. Yai zaune yana duban Mu’azzam d’in yana jira yaji da mai zai fara. Bayan an kawo wa Assad nasa order d’in ya sinkayo muryar Mu’azzam na fad’in “Nasan ka tab’a aure zama baiyi dad’i ba Kun rabu da matar..”

Assad ya dubesa da mamaki jin yau kuma da wannan batun yazo, shi ya zaci ma wani ci gaba suka kuma samu daga binkicen da suke.

Assad ya jinjina kai yace “Haka ne.”

Mu’azzam ya kuma sipping hot coffee d’insa kafin yace “Kanada experience, kasan halittan mata kenan.”

Yanzu kam aje cup d’in dake hannunsa Assad yai yana duban abokin nasa da tsananin mamaki wanda a baya sam bai irin wad’ann zantukan.

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Inaso na maka tambaya a matsayinka na wanda yakeda experience.”

Assad ya jinjina kai yace “Umhum ina saurarenka.

“Idan mace ta gama yawonta da biye biyen maza, after some time ta jima batabi mazan ba tana koma sabuwa ce kaman dai budurwar da bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.?”

Bagatatan Assad yaji zancen wanda har saida ya kusan fuzar da coffe d’in da ya shiga bakinsa sabida dariyan da yazo masa.. Da alama abokinsa ya shiga missed call.. Ya k’unshe bakinsa yana darawa a hankali dan Yanzu kam ya gama gane Ina tambayoyin Abokin nasa suka nufa.

Mu’azzam ya aika masa mugun kallo cikeda takaici “You are not serious, you know. Ya ina tambayarka abu kana wani dariya..”

“Toh kuka kake so nayi.. Abun ne abun dariya.. Budurci guda d’aya ne ai.. Halitta ne da Ubangiji ya Karrama ko wace d’iya mace dashi, wacce ta watsar da wannan karamci nata tin a titi bazata kuma samunsa ba, bazai dawo ba duk gyaran da za’ayi kuwa.. Bazata tab’a zama kaman wacce ta Martaba wannan karamci nata ta rik’esa da kyau ba.”

Mu’azzam ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana mai sipping coffee. Lokaci guda Assad yaci gaba da fad’in “Shiyasa shaidar zina dai takeda matakai daki daki..Ku guje ma mummunan zato ma bayin Allah.. So tari wanda ka munana masa zato shine na k’warai d’in. Sannan so tari wanda ka kyautata masa zato shine na banzan. Amma ko yaushe ana so mutum ya kasance mai kyautata zato.. Ku guje ma d’aukan maganganun mutane domin shi d’anadam a Kullum aibunka yake nema ya yad’a, Sai ya yad’a aibunka sau d’ari kafin ya fad’i alkhairinka guda d’aya.. Ga aibun a tattare da shi amma shi bazaiga nashi ba sai yaje yana hangen na wani.. Allah yasa mu gane ya kuma datar damu.”

Mu’azzam ya amsa da Ameen. Yana mai ci gaba da shan coffee d’insa. Time ya duba yaga Wai har tara na safe Ta d’an gauta ya kamata Su k’arasa Office.. A tare Suka mik’e Mu’azzam yai settling bill d’insu kafin suka nufo waje.
Babu b’ata lokaci suka nufo ofishinsu.

Suna isowa suka tadda Daddy a k’ofan Ofishin nasu. Assad ya dubi Mu’azzam “Wa nake gani kaman Daddy..? Allah sarki ni wllhi duk yafi bani tausayi a al’amarin nan.. Mutumin nan yana k’aunarka Mu’azzam, kaga yanda ya juya ma d’iyarsa baya yak’i ya bama k’arya goyon baya dukda cewa yanada halinda zai iya sakawa a kashe case d’in nan a rufe case d’in gaba d’aya sabida d’iyarsa amma baiyi haka ba.. Gaskiya na jima banga mutum mai dattako da kiman Daddy ba.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “K’warai Daddy mutumin kirki ne.. Bai cancanci d’iya irin Safeenah ba.. Unfortunately bamu zab’en ahali, farkawa muke kawai mu ganmu tareda mutanen da Allah ya hukunta zasu zama ahalinmu.. Sannan ko wanne ahali sunada nasu k’alubalen da suke fuskanta.. Mu kuma irin namu k’alubalen kenan.. Mu k’arasa..”

Assad ya jinjina kai kafin suka nufo yanda Daddy ke zaune. Gaisawa sukai gaba d’aya kafin Assad ya Shige ya basu waje.

Daddy ya dubi Mu’azzam wanda jinkinsa ya d’anyi sanyi da ganin Daddyn.. Ko Babu komai Safeenah d’iyar Daddy ce jininsa ce dole zaiji wani abu can k’asan zuciyarsa dukda kuwa k’arfin halin da yai.

Mu’azzam yace “Are you here to see Safeenah.? Mu k’arasa sai a kira maka ita..”

Daddy ya girgiza kai yace “Ba Safeenah nazo gani ba Mu’azzam.. Kai nazo gani..”

Mu’azzam ya d’an gyara zamansa yana duban Daddyn.

Daddy yaci gaba da fad’in “Mu’azzam bazan hanaka hukunta Safeenah akan laifinta ba idan har an kamata da laifin.. Amma inada wata alfarma guda d’aya da nake son rok’a daga gareka.”

Mu’azzam ya d’an d’ago ya dubesa “Alfarma kuma Daddy.. Ai ka wuce alfarma a wajena Daddy.. Umarni kawai zaka bani..”

Daddy ya murmusa cikeda jin dad’i kafin ya jinjina kai yace “Allah ya maka albarka Mu’azzam.. Alfarmar da nake nema wajenka shine, dan Allah kar ka saki Safeenah har sai an gama bincike an sameta da laifi.. Kamin wannan alk’awarin cewa bazaka rabu da ita ba har sai an tabbata Tanada laifi.. This is the least I can do for my daughter bayan juya mata baya da nayi..” Ya k’arashe yana duban Mu’azzam d’in cikeda kulawa.

Cak Mu’azzam ya tsaya ba tareda ya iya amsa Daddy ba, saima sadda idanunsa k’asa da yai.

Daddy yai gyaran murya yaci gaba da fad’in “I know it’s not easy, ace kana shari’a da matarka.. But please do this for me.. For our family Mu’azzam.. Kar ka saki Safeenah until she’s proven guilty.. Ina rok’onka ne a matsayin mahaifin Safeenah.. Please Mu’azzam..!”

Ganin Daddy na k’ok’arin had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o yasa Mu’azzam saurin kamo hannayen Daddy ya hanasa aikata hakan. Yana girgiza kai yake fad’in “Dani da Safeenah Kai Babanmu ne gaba d’aya Daddy.. Yanda zaka umarce Safeenah tai abu ko Musaddiq haka nima zaka mun.. Daddy bazan saketa ba kaman yanda kace.. Safeenah zataci gaba da zama matsayin matata..”

Daddy ya sakar masa murmushi yana k’ok’arin maida k’wallan dake k’ok’arin ciko idanunsa “Na gode Mu’azzam.. Thank you for this.. Allah Ubangiji ya maka albarka ya kuma maka jagora.”

Mu’azzam ya amsa da “Ameen Daddy..”

Daddy ya mik’e yace “Alk’ali ya sanar da Court Hearing d’in ne..?”

Mu’azzam ya girgiza kai yace “Muna sauraro tukuna Daddy.”

Daddy ya jinjina kai kafin yace “Ni zan wuce Company.. Sai na ganka a gida..”

Mu’azzam ya jinjina kai yana mai rakiyawa Daddyn har zuwa yanda motarsa ke ajiye driver

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login