Showing 126001 words to 129000 words out of 209154 words
Saida ya bata kusan five spoons kafin ta girgiza masa kai kaman zata saki kuka tana fad’in ita ta k’oshi.
Ya k’ura mata idanu yana mamakin yanda tsiwarta ya ragu, da da ne ba kuka zata sakar masa saidai ta murgud’a masa d’an bakin nan nata da yafi komai d’aukar hankalinsa a kyakkyawan fuskarta.
Wayarsa ce Tai k’ara ya duba yaga Yusuf ne mai kira. Ya d’an mik’e yana amsa wayar kaman zai fice da alama update yake basa kan Assad.
Ganin haka yasa Sadiya saurin mik’ewa zata nufi corridor.. Kafin ta isa k’ofar yai saurin fuzgo hannunta ta fad’o jikinsa, still yana wayar.. Ta soma k’ok’arin cire jikinta dags nasa amma ta kasa dukda cewa da hannu guda kawai ya rik’eta.
Sukai sallama da Yusuf yace masa yana nan tafe yanzun nan. Lokaci guda ya kashe wayar yana duban yanda take ta faman daddage k’arfinta tana k’ok’arin cire hannunsa daga jikinta. Harda ciza labb’a tai alamun Takai mak’ura wajen tattaro duka k’arfinta.
Ya murmusa kad’an kafin yai amfani da d’aya hannun ya tallafo kunkuminta, ya matso da ita kusansa sosai had’ida k’ura mata idanu.. Wani irin fad’uwan gaba ne taji ya sauk’ar mata musamman da ta d’ago ido taci karo da murmushin dake bisa fuskarsa.. Ita zata iya cewa tafi sabawa da d’aure fuska da yake.. Ta alak’anta fad’uwan gaban nata da wannan fake murmushin da Ta gani samar fuskarsa.
“Please let me go..” Ta fad’i kaman zatai kuka.
Hannunsa guda yasa ya d’ago hab’arta suna duban juna, zuciyarta naci gaba da yankewa. Ya soma matso da fuskarsa kusan nata kaman dai zai kai mata sunba.. Tai saurin rintse idanunta tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa.
Saitin kunnenta na dama taji sauk’an labb’ansa, cikin sigan rad’a yake furta “Lets go back home.. The house misses you..”
K’ok’arin tattaro duka k’arfinta tai had’ida turasa baya “That house was never mine.. And it will never be.. Ka mance menene sunan gidan a wajena..? GIDAN ARO..” Ta jinjina kai kafin taci gaba da fad’in “You said it yourself, Mr Inspector..”
Murmusawa yai da gefen bakinsa kafin ya soma matsowa kusanta tana jada baya.. Har saida taji kujera ya tokareta alamun wajen gudu ya k’are kafin Ta tsaya tana mai kwantar da bayanta saman kujerar alamun bataso ya matso kusanta.. Ya kwanto shima had’ida mik’a hannunsa guda ya rik’o bayanta yace “Give your husband a goodbye kiss..”
Bugun zuciyarta ya k’aru ganin abinda yake, what if wani ya bud’e k’ofar ya gansu haka.. Bata ida tinanin ba tai saurin take k’afarsa guda da k’arfin gaske.
Ya d’an saki k’ara yana kame k’afarsa.. Ya janyota ya d’agota tsaye yana fad’in “Hey That was a kick and not a kiss..”
Ta k’unshe dariyarta ganin yanda ya rik’e k’afarsa yana d’an sakin k’ara a hankali kai kace zafi yaji da gaske.
Lokaci guda Ta jinjina kai tace “I know.. Abinda ya kamaceka kenan.. Mr Inspector..” Ta turasa da duka hannayenta biyu kafin ta isa a guje ta bud’e k’ofar ta shige cikin sauri bugun zuciyarta na k’aruwa.
Mu’azzam yabi bayanta da kallo yana murmushi kafin yasa kai ya fice daga parlorn.. Sadiya dake kallonsa ta ramin k’ofa yana ficewa ta Sauk’e ajiyan zuciya had’ida juyowa.
Ido hud’u sukai da Aunty Larai.. Gaba d’aya sai taji kunya ya rufeta..
Aunty Larai ta murmusa tace “Har angon namu ya wuce ne..?”
Sadiya ta sadda kanta k’asa kad’an kafin ta jinjina mata kai a hankali alamun eh.. Aunty Larai ta janyota tana fad’in “Ki saki jiki dani kinji koh.. Mu’azzam d’ah na ne amma babu wani surkunta tsakanina dake dan ked’in ma d’iyata ce.. Mu k’arasa ciki..” Suka shige ciki hannunta rik’e cikin na Aunty Larai suka nufi ciki suka tadda Su Umma.
**
FUFORE
Yau ma kaman kullum tana zaune tana tinanin mutumin da ko sunansa bata sani ba. Iyakacin abinda ta sani shine tayi kewarsa sosai sannan Gidan gonar ya canza tin sanda ya tafi garinsu.
Mama Hindu Ta K’araso Ta sameta tana nan zaune batai wankan ba. Ta d’an girgiza kai ta k’araso ta dafata kad’an tace “Ajidde Wai bazaki tashi Kiyi wankan ki baiwa Aunty Nuratu maganinta ba.. Duba kiga lokaci nata tafiya.. Waima tunanin mai kike ne..?”
Ajidde ta mik’e tana turo baki “Kai Mama Hindu Wai ni idan nazo gidan nan dole ne Sai nayi wanka.. Ni wllhi na gaji haba.. Wai dan Allah Mama Hindu waye ya saka mun wannan dokar a gidan nan..?”
Mama Hindu Ta murmusa tace “Idan ban Fad’a miki ba ma kinyita damuna kenan.. Modibbon Inne shi ya bada wannan dokar.. Yace kullum kafin ki baiwa mahaifiyarsa magani na tabbata babu datti jikinki.. Toh amma ko kefa yanzu Kinga kina wanka kina wanke bakinki.. Gashi asalin kyakkyawar bak’ar fatarki ta kuma fitowa tas gwanin kyau.. Ga hak’waranki yanzu sun dawo farare tas tas.. Tsafta da dad’i ai Ajidde..”
Ajidde ta saki baki da hanci tana duban Mama Hindu.. Sai kuma ta girgiza kai tace “Mama Hindu kina nufin ‘Yaniskan turawa shi ya bada wannan dokar..?”
Mama Hindi Ta girgiza kai tace “Sunansa Mu’azzam.. Ki daina kiransa ‘Yaniskan turawa jami’in tsaro ne idan yaji kina kiransa haka zai kulleki a police station..”
Takaici ya cika Ajidde ta gama kula mutumin Babban D’an rainin hankali ne.. Wato kar Ta tab’a masa mahaifiya da datti jikinta sai tayi wanka.. Ta tab’e baki tace “Shi wannan sam halinsu baizo d’aya da abokinsa ba.. Ni banma San ya akai sukai abota ba..”
Mama Hindu ta girgiza kai tace “Waye abokin nasa..?”
Ajidde tace “Kuran tashe mana..”
Mama Hindu ta girgiza kai tace “Wannan wane irin suna ne kuma Ajidde..?”
Ajidde ta dubeta tace “Toh oho nima bansan sunansa ba.. Amma ai a gidan gonar nan yake aiki... Gashi tinda ya tafi garinsu fah har yau bai dawo ba.. Mama Hindu kinaga zai dawo..?”
Mana Hindu ta murmusa tace “Toh kodai shine ke sakaki tunani kwana biyun nan.. Da alama shine sirkin nawa..”
Baki sake Ajidde ke dubanta sai kuma ta rufe fuska tana dariya “Kai Mama Hindu.. Ni wllhi har kin sa naji kunya.. Kuran tashe Abokina ne kuma Yayana mai tare mun fad’a ehe..”
Mama Hindu Ta dara kad’an tace “Munsan irin wad’ann yayyen.. Da alama dama shine sirkin nawa.. Ke kaw ya akai bakisan sunansa ba.. Allah dawo dashi lafiya na had’u dashi..”
Ajidde Ta kuma darawa kafin tace “Kai Mama Hindu ni wllhi dariya da kunya kike bani.. Kuran tashe fah d’an gayu ne.. Saima randa zai tafi garinsu da na gansa.. Wllhi yasha gayu cikin kayan da ‘yan gayu ke sakawa kuma ma fah ya fini kyau.. Kinga dukda shi ba fari bane amma ya fini haske.. Kuma ya fini tsawo..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye tana gwada tsawonta da tsayin k’ofa lokaci guda tana bayanin tsawonsa ma Mama Hindu.
Mana Hindu ta murmusa tana mai shigewa shiriritar Ajidde da yawa yake.
Ajidde ta Sauk’e ajiyan zuciya tana duban kanta jikin madubi tana mamakin Mama Hindu tace ta k’ara kyau.. Ta murmusa kafin tace “Yo dama ai ni mai kyau ce Mama Hindu..” Idanunta suka sauk’a Kan Aunty Nuratu sai taga kaman ita take kallo.. A koda yaushe idanun nata saidai kaga Sun kafe waje guda amma yau Sai Ajidde taga kaman dubanta take.. Ta k’araso a hankali tana mai k’ura mata idanu, Ta duk’a tana duban idanun Aunty Nuratu ta d’an soma Yawo da tafin hannunta saman idanun Aunty Nuratu sai taga kaman idanun nata na motsawa ba kaman ko Yaushe da zaka ga idanun tamkar a kafe suke waje guda ba.. Ajidde tai shiru tana tuna bayanan Malama Hafsah cewa ko taga wani canji a tattare da matar da take Jinya ta adana hakan ma kanta, kar tai saurin sanar da mutane dan daga yanda Ajidden ke mata bayanin ciwon ya mata kama da asiri ko tsafi.. Amma da taimakon ayoyin Ubangiji idanma asiri ne ko sihiri zai lalace. A hankali Ajidde Ta furta “Tabbas akwai waraka cikin ayoyin Ubangiji..”
**
ABUJA
Assad ya murmusa kad’an yana dubansa kafin yace “I’m feeling much better now.. Damuwata kawai shine we couldn’t catch Danger.. We were so closed k’iris ya rage mu kamasa ya tsere mana..” Ya k’arashe yana d’an fuzar da huci kad’an.
Mu’azzam ya girgiza kai yace “What’s important a halin yanzu shine lafiyarka.. Let’s all take a break.. Na tabbata a kwana a tashi zamu had’u da Danger watarana..”
Assad ya jinjina kai kad’an kafin yace “Su Hajiya sun taso daga Nasarawa d’azu Shaheed ke sanar dani a waya, anjima kad’an nasan zasu iso.. Yarinyar nan ne mai shegen magana Humaida ita ta sanar da Hajiya. Kuma saida nai warning nata kar ta sanar dasu Hajiya amma ta sanar dasu..”
Mu’azzam ya d’an murmusa kafin yace “Hajiya ai bazata iya bacci ba tareda ta ganka ba..” Mu’azzam bai rufe baki ba ‘yan gidansu Assad sukai sallama, Hajiyarsa wacce itace mahaifiyar Sai K’aninsa mai bi masa Shaheed wanda shi ya tuk’o Su Hajiyan sai ko k’anwarsa Humaida... Suka shigo duk a rikice..
Assad na wurga ma k’anwarsa harara ganin yanda mahaifiyarsa duk Ta rikice. Ta dubi Mu’azzam bayan sun gaisa tace “Ni wannan aiki naku harga Allah tsoro yake bani.. Shin bazaku aje aikin nan ba ku nemi wani. Aiki kullum cikin fargaba da tashin hankali..”
Mu’azzam sai murmushi yake ba tareda yace komai ba, shi ko Assad girgiza kai kurum yake yana fad’in “Hajiya babu wani abu fah mun saba da wannan cikin aikinmu..”
“Kai tafi can ka rufe mun baki.. Rai guda d’aya ce. Ba wannan ake jiye maku ba.. Aikin tsaro a k’asa irin wannan ai abin tashin hankali ne k’ananan suke shan wahalan ba manyan ba.. Allah dai ya kawo mana d’auki ya bamu shuwagabanni adilai..”
Gaba d’aya suka amsa da Ameen kafin daga bisani Mu’azzam yai masu sallama Shaheed k’anin Assad yai masa rakiya zuwa waje.
**
Bayan sallar isha ya dawo gidan, tin daga k’ofa yake jiyo hayaniyar Mommy tana fad’in sai Safeenah ta tattaro kayanta Sun tafi.. Yanda Ta bar gidan Daddy dole Safeenah ma Ta bar gidan Mu’azzam tinda dik abinda ke faruwa akan Mu’azzam d’in ne..
Yai sallama ya turo k’ofar parlorn.
Safeenah tana ganinsa Ta nufosa a guje tana b’oyewa bayansa fuska shar shar da hawaye “My Halal pls don’t let Mommy do this.. Dan Allah kar ka bari Ta rabamu..”
Mommy na sakin huci take duban Mu’azzam d’in “Kinaji Safeenah idan ni na haifeki kin gama zaman aure da wannan maras mutuncin.. Ki shige mu tafi bana son wani dogon bayani..”
Safeenah Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Mommy no please.. Wllhi I love my husband.. Please don’t make me choose between you..”
Mommy Ta jinjina kai tana huci “Yayi Safeenah.. Duk Kun juya mun baya akan wannan maras mutuncin.. Yayi.. Baga mahaifinku ba bagaku ba.. Yayi kyau.. Kije Safeenah indai namiji ne gaki gashi nan.. Ina nan zaki Zo min kina kuka..”
Ta juyo tana duban Mu’azzam.. Murmusawa tai kafin tace “Bokanka ya iya aiki matuk’a Mu’azzam.. Da alama ka lashe zukatan ahalina.. Bazan tab’a yafe maka ba tarwatsa mun kan ahali dakai..”
“Ke kuma Safeenah na barki da namiji..” Tana ida fad’in haka Ta fice tana sakin huci..
Safeenah Ta fashe da wani irin kuka tana mai duk’awa wajen..
Hannun Mu’azzam taji saman kafad’unta.. Ta d’ago tana dubansa wani kukan na zuwa mata.. Mik’ewa tai Ta fad’a jikinsa tana kukan mai isarta.
A hankali ya d’ago hannayensa ya rungumeta cikin jikinsa.
For the first time da yaji tausayin Safeenah ya d’arsu cikin zuciyarsa tun bayan da binciken mutuwar Ikram ya biyo kanta.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*42*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Meema da Kiki suna zaune parlorn sunyi jigum jigum, harda guntun hawaye a fuskokinsu.. A haka Musaddiq ya shigo ya taddasu. Bai ce masu komai ba suma basu ce masa komai ba, ya haura sama ya nufi d’akin Mommy yana dubata, bai sameta ba sai wata mai aikin gidan guda d’aya tana tattara d’akin Mommyn yanda Mommy tai fashe fashen abubuwa masu fashewa a d’akin dangin su frames dasu flower vase.
Musaddiq yanata bin d’akin da kallo cikeda mamaki. Lokaci guda ya girgiza kai yace “What happened here.. Ina Mommy..?”
Mai aikin Ta girgiza masa kai alamun bata san yanda Mommy take ba.
Bai kuma cewa komai ba ya fito ya sauk’o k’asa ya taddasu Meema dake zaune jigum jigum ko wacce da kalar tagumin da tai..
“Kai ina Mommy..?” Ya tambaya yana dubansu.
Meema Ta girgiza kai tace “Bamu San ina ta tafi ba.. But she says bazata sake dawowa gidan nan ba..”
Da tsananin mamaki Musaddiq yace “Mommyn.?”
Suka jinjina masa kai.
“Toh mai ya faru..? Maiyasa Mommy zatace haka..?”
“Muma bamu sani ba kawai daga side d’in Daddy mukaga Ta fito tana kuka..”
Kallo ya bisu dashi kafin ya zaro wayarsa ya soma dialing layin Mommy.. Bugu d’aya a na biyu ta d’aga.
Musaddiq hankali tashe yake fad’in “Mommy ina kika tafi..? Nazo gida na tadda baki nan.. Yaran nan sunce min Wai kince bazaki sake dawowa ba..? Mommy what is happening..?”
Maimakon ta basa amsa sai kukan da tai tana fad’in “Musaddiq Daddynku yaci zarafina.. Yamin abinda bai tab’a min ba tinda k’uruciya.. Ko kasan yau har marina yai akan Mu’azzam.. Ka kula da ‘yanuwanka amma nikam na gama zama gidan Mahaifinku.”
Da tsananin mamaki ya saki baki yana sauraron Mommy abinda bai tab’a faruwa gidansu ba, Wai Mommy ta tafi ta bar gidan kuma bazata kuma dawowa ba “Mommy where are you now..?” Ya tambaya yana ficewa.
“Ina Apo gidan Hajiya Faty K’awata..” Ta basa amsa kai tsaye.
“Alright gani nan zuwa Mommy..” Daga haka katse kiran yai ya kuma ficewa daga gidan ya nufi gidan Hajiya Faty kawar mahaifiyarsa.
Musaddiq yai jigum yana duban Mommy yanda take nuna masa farar fuskarta da zanen yatsun mijinta ya fito.
“Daddy ne ya miki haka.?” Musaddiq ya tambaya yana dubanta idanunsa sunyi jazir sabida tsananin b’acin rai.
Ta jinjina masa kai tana kuma matsan k’walla “Dashi da Safeenah duk sun juya mun baya kan Mu’azzam, nasan kaima bayansa zakabi sabida shi d’angata ne bai laifi a idanunku..”
Mik’ewa Musaddiq yai kurum yana sakin huci yana duban fuskar mahaifiyarsa, jinjina kai yai kafin yace “Zaizo har nan ya baki hak’uri ya kuma d’aukeki ya maidake gidanki..!” Daga haka ficewa yai kaman zai kifa k’asa.
Mommy Ta bisa da kallo kafin Ta murmusa tace “Ai jini ba K’arya bane.. Uwa kuwa Ta wuce gaban wasa..” Hajiya Faty ta fito tana dubanta tana murmushi “Ina Musaddiq d’in.. Ko har ya fice ne ba sha ko ruwa ba.?”
Mommy Ta murmusa tace “Ya tafi yayi yak’i ma uwarsa..”
Hajiya Faty Ta dara kad’an tace “Kaji D’an halak haka ake so d’ah ya kasance. Kinga ko baki samu goyon bayan Safeenah ba kin samu na Musaddiq..”
Mommy ta jinjina kai tace “Ita dama wannan ai shashasha ce, kuma Ina nan dake zata Zo min tana kuka lokacin da zai gurza mata ya tabbatar mata cewa ya amsa sunan namiji..”
Hajiya Faty ta murmusa kad’an ta zauna tana fad’in “Bata lokaci soyayya ke d’awainiya da ita.. She will come back to her senses soon.. Ina d’aya matar tasa ne Wai..?”
Mommy Ta tab’e baki tace “Toh wa yasan masa ne Wai Kinsan bazai sanar da Safeenah komai ba dan bai d’auketa da daraja ba..”
Hajiya Faty Ta jinjina kai tace “We need to do a background check on her.. Musan ‘yar wacece kuma daga Ina take sannan ina iyayenta suke dan Kinsan dai Safeenah bayi zatayi ba wannan fad’anta ne amma dole mu dafa mata tinda ita namiji ya lashe zuciyarta.”
Mommy Ta jinjina kai tace “Kin kawo shawari.. Zan bar miki wannan a hannunki ki gano mana wacece ita sai musan ta yanda zamu b’ullo wa al’amarin.”
“Bakida matsala idan dan wanann ne k’awata.” Hajiya Faty Ta bata amsa tana mai d’aura k’afarta d’aya bisa d’aya.
**
Chief ya d’aga wayar ya k’ara a kunnensa yana furta “Yes BAT bakada matsala, komai ya tafi as we planed.. Mu’azzam Bazai tab’a samun sakamako mai inganci ba.. Yes munyi tempering samples d’in kaga hakan na nufin result d’in bazai matching ba..” Ya murmusa kafin yace “Bakada matsala BAT. We did a clean job.. I trust Maleeka, she’s good at everything.. Tana d’aya daga cikin best agents d’inmu a FCID. Yes alright shikenan sai na jika BAT..” Daga haka katse kiran yai kafin ya dawo yanda Maleeka ke kwance saman gado.. Alert ya nuna mata na naira dubu d’ari biyar ya shigo wayarsa.
Maleeka Ta zaro idanu waje tana kame baki.
Chief ya fashe da muguwar dariya kafin yace “Idan kika ci gaba da bamu had’in kai kina aiki damu yanda ya kamata haka Zakita receiving alert babu k’akk’autawa.. BAT yace a baki wannan tukurci ne for the job well done..”
Maleeka ta fuzgo wayar hannun Chief tana kuma karance alert d’in lokaci guda Ta saki murmushi tace “Idan ka rasa soyayya sai ka kama Kud’i dan kar kayi biyu babu.. Mecece duniyar dama soyayya ne da kud’i.. A rashin d’aya sai ka samu d’aya domin kaji dad’in baje kolinka..” Suka b’uge da dariya Chief na shafa k’atuwar tunbinsa wanda kaman zashi labor room, lokaci guda ya hauro saman gadon yanda Maleeka ke kwance.
**
Ko parking mai kyau bai ida ba ya fice daga motar, ya shiga tafiya cikin sassarfa ya nufi b’angaren Daddy..
Ko sallama Musaddiq bai ba ya tura k’ofar parlorn ya shiga.. Daddy na zaune tsakiyar parlorn yana shan shayi dan ko dinner bai samu yaci ba Musaddiq ya shigo parlorn cikin tsananin b’acin rai.
“This has to end now Daddy.. Bazai yuwu akan Mu’azzam a tsaya ana wulak’anta kowa a gidan nan ba.. Especially Mahaifiyarmu.. Daddy I’m so disappointed.. Absolutely disappointed.. How could you hit our Mom kawai akan b’acin ran Mu’azzam.. Just yesterday ka hanani sanar dashi wani abu da ya shafi ahalinmu ba Don komai ba Sai dan gudun b’acin ransa.. And bai jima ba kanaji kana ganni Daddy Mu’azzam ya shigo har cikin gidan nan da ‘Yansanda yai arresting Safeenah.. Yanzu kuma Daddy ka d’aga hannu ka mari mahaifiyarmu duk akan gudun b’acin ran Mu’azzam.. Who the hell is he.. Shi waye da baza’a b’ata masa rai ba..! Shi waye da kowa zai sadaukarwa mai girma sabida gudun b’acin ransa.!” Yai fasali gumi na kuma tsartsafo masa yana kuma zaro idanunsa da suka kad’a sukai ja sosai “Daddy na rantse da Allah idan Bakaje ka basa Mommy hak’uri ba, ka d’auko Ta ka dawo da Ita gidan nan.. I’ll expose everything.. And when I say everything.. Ina nufin duk abinda na sani.. Idan yaso zuciyar Mu’azzam ya kumbura kuma ya fashe sabida bak’in ciki