Showing 114001 words to 117000 words out of 209154 words

Chapter 39 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3064

shin kana tunanin alhakin mutuwarsa baya wuyanka..?”

Uncle Salman ya kuma murmusawa kafin yace “Ko mai zakace bazan tab’a amsa laifin da ban aikata ba.. Sannan zaka iya fad’awa D’ansa after all shi jami’in tsaro ne.. Sai yai bincike kan mutuwar mahaifinsa wanda baiyi a baya, kaga yazo masa da sauk’i Sai ya had’a binciken tareda na ‘Yaruwarsa.. Zan d’auke matata mu tafi da alama ba’a maraba damu a gidan nan..!” Yana ida fad’in haka yasa kai fuuu ya fice ya nufi cikin gidan shashen Mamy yana dokawa Shemau kira.

Musaddiq ya fito daga mab’oyarsa yana jin gumi na kuma keto masa.. Meke shirin faruwa da ahalinsu.. Menene wannan daga wannan sai wancan..? Mai hakan yake nufi..? Kaman dai ahalin nasu mummunan baki na binsu.. Bacin haka meke shirin faruwa dasu..? Idan har Uncle Salman yanada saka hannu a mutuwar Uncle namesake (Kaman yanda yake kiran Baban Mu’azzam dan sunansa Musaddiq yaci) Toh kuwa ya kamata Mu’azzam ya sani.. Idan har za’a binciki Safeenah Maiyasa baza’a binciki Uncle Salman ba.. Da wannan tinanin ya shigo ya tadda Daddy ya had’a tagumi da hannayensa duka biyu.

Musaddiq ya k’araso ya zauna kusan k’afan Daddy, ya kifa kansa hawaye na gangaro masa. Lokaci guda yake furta “I heard everything Daddy.. Shin abinda ka fad’i kan Uncle Salman gaskiya ne..?”

Daddy ya shafi fuskarsa da duka tafukan hannayensa yana mai fuzar da fuci “Musaddiq you didn’t hear anything..!” Daddy yace yana duban Musaddiq d’in.

Musaddiq ya girgiza kai cikin rashin yarda kafin yace “Daddy that was a serious accusation, you know.. Tuhumar Uncle Salman fah kake da alhakin mutuwar Uncle namesake.. Daddy idan da gaske ne duk abubuwan da ka fad’i mai yasa bazaka bari a binciki Uncle Salman ba.. Karfa ka mance Daddy kai ka bada go ahead a tafi Safeenah a binciketa, tana a matsayin ‘yar cikinka.. Mai yasa zaka kare D’anuwanka idan har bazaka kare ‘yarka ba.. Daddy idan Uncle Salman shi yai sanadiyar mutuwar Uncle namesake then Mu’azzam needs to know..”

“No Musaddiq..! Koda wasa.. Kar ka kuskura ka sanar da Mu’azzam.. Ko wani cikin ahalinmu idan har kana so ahalin nan yaci gaba da zama a dunk’ule waje guda...!”Daddy yace cikeda gargad’i.

Musaddiq ya girgiza kai yace “But Daddy..”

Daddy ya kuma katsesa “Kana so ka tarwatsa zuciyar Mu’azzam..?”

Musaddiq ya girgiza kai a hankali kansa duk’e hawaye na gangaro masa.

Daddy ya jinjina kai kafin yace “Kana so ka tarwatsa Zuciyar Inne..?”

Nan ma girgiza kai Musaddiq yai alamun a’a.

Daddy yaci gaba da fad’in “Do you think it’s easy for me to live with this..? Musaddiq baka tunanin Mu’azzam ya shiga k’unci da tashin hankali masu yawa.. Ya rasa mahaifinsa tin yanada k’anan shekaru.. Mahaifiyarsa Ta gamu da tsananin jinya wanda tana nan ne tamkar ga babu.. Ya rasa k’anwarsa wacce akai Garkuwa da ita aka kuma kasheta.. Yana tsaka da bincike matarsa da akai niyyan sacewa tun a fari ta zamto prime suspect.. Allah ya rufa asiri ya wanketa da shike batada laifi.. Kwatsam yanzu sai a sanar dashi wannan batu..? Kai ma Kanka adalci kaima D’anuwanka Mu’azzam adalci shin ya cancanci a sanar dashi sa’insan da Uncle d’insa yai da mahaifinsa kafin ya bar duniya..?”

Musaddiq kuka yake sosai yana girgiza kai ba tareda ya iya furta komai ba.

Daddy ya jinjina kai yace “Idan har kana k’aunar Mu’azzam a matsayin D’anuwa bazaka sanar dashi duk abinda kaji yau ba.. Sannan bazaka sanar da kowa ba.. Kamin alk’awari Musaddiq..”

D’ago idanunsa masu zuban hawaye yai yana duban Daddy kafin ya mik’e k’unshe da bakinsa ya fice wani kukan na zuwa masa.

**

Babu abinda suka tadda a wannan location d’in Sai kangon gini da wasu dangin karyayyun kujeru. Mu’azzam ya shafi sumarsa zuwa fuskarsa yana fuzar da fuci.

Assad ma dafe kunkuminsa yai yana girgiza kai bayan sun gama searching entire location d’in “Mu’azzam stop being stubborn, let’s inform our team members about this..” Assad yace yana duban Mu’azzam d’in.

Da wutsiyar idanu yake duban Assad kafin ya girgiza kai yace “No I think we should inform the entire FCID.” Ya basa amsa da fad’in haka Kafin ya kifa kansa jikin garu. Lokaci guda ya d’ago yana duban Assad d’in. Fuci ya kuma fuzarwa yana shafe fuskarsa da duka hannayensa biyu “She’s so stubborn you know.. Na gargad’eta cewa kar Ta fita ko k’ofa amma saida ta fita.. Yanzu ga irinta nan.. D’aniskan nan ya d’auketa..!”

Assad yace “Ka kwantar da hankalinka Mu’azzam.. Babu abinda zai sameta and you ain’t gonna lose her..”

Da mamaki yake duban Assad jin kalamansa na k’arshe. A hankali ya girgiza kansa kafin yace “I’m only doing my job as a police officer. And I’ll make sure na cire mata stubbornness d’in dake kanta..” Ya fad’i yana murza tafin hannunsa a hankali.

Assad ya jinjina kai a hankali kafin yace “Yanzu Meye abinyi..?”

Duban Assad yai without uttering a word.. Lokaci guda ya d’an girgiza kai yasa kai zai shige saiji yai kaman yai tuntub’e da wani abu. Dakatawa yai ya kuma haska abun da ya taka da hasken wayarsa.

Hular sanyi ce yai tuntub’e da ita.. Ya duk’a a hankali yana kuma haska hular sanyin.. Assad ma ya duk’a yana duban abinda Mu’azzam d’in yake duba.

K’aramar Karan dake gefe Mu’azzam ya d’auka ya d’an tura hular dashi, hular ta bud’u sosai.. Bak’ar hula ce irinta sanyi gaban hular an rubuta B.A.T da manyan harrufa.. Mu’azzam yai shiru yana duban hular yayinda Assad ya zuba masa idanu ganin yanda yake examining hular da idanunsa.

“Assad nasan mai irin hular nan exactly..”

Assad ya dubesa da mamaki kafin yace “Could it be hular Sadiya..?”


Girgiza kai Mu’azzam yai kafin yace “Wait.” Ya shiga whatsapp account d’insa ya bud’e hoton dake display picture d’in Musaddiq, hoton su ne shida Musaddiq d’in da suka d’auka a cikin k’ank’ara a k’asar England ko wannesu yayi shiga irinta sanyi. Hular dake kan Musaddiq babu abinda ya rabata da wannan hular da suka tsinta a warehouse d’in da Danger ke business d’in drugs d’insa.

Zuciyar Mu’azzam yai wani irin yankewa. Assad ya dubi Musaddiq da hular sanyin dake kansa ya kuma duban hular da suka tsinta nan gabansu.

“What is this Assad.. Shin wannan zai iya zama hular Musaddiq ne..? Shin Musaddiq nada connection da Danger ne..? But how..?!” Ya k’arashe cikin tsananin rud’ani.

Assad ya girgiza kai yace “Mu’azzam wannan hula ce kawai, ba lallai ta zama na Musaddiq ba.. Mutane da yawa company guda d’aya.. Ta iya yuwa hular wani ne..”

Har lokacin duban hular yake kafin ya saka karan ya d’an bud’e cikin hular ya kunna hasken wayarsa yana haska cikin hular sosai, nan yaga alamun tsillin gashi cikin hular.

Ya d’ago ya dubi Assad kafin yace “I have an idea.. Ga alamun gashi cikin hular.. We will conduct a DNA test.. If it matches with Musaddiq kenan hular na Musaddiq ne.. And that means Musaddiq nada connection da Danger.”

Assad ya d’anyi shiru kafin yace “Toh amma wane connection Musaddiq zai samu da Danger..?”

Mu’azzam ya d’an gyara tsugunonsa kafin yace “Ka mance Musaddiq used to be a drug addict. Danger kuma drugs yake saida wa matasa.. Ka mance musabbabin zuwanmu wajen nan d’aya daga cikin customers d’in Danger shi ya bamu location d’in nan.. What if Musaddiq customer d’in Danger ne..?” Ya k’arashe cikin wane irin yanayi.

Assad ya shafi fuskarsa cikin rashin sanin mai zai furta.

Mu’azzam d’in ma zuba ma hular idanu yai cikin tsananin sanyin jiki. Muryarsa na rawa yake furta “Meke faruwa dani da ahalina Assad.. First Safeenah ce yanzu kuma Musaddiq.. Assad mai hakan ke nufi.. Assad I’m lost.. I .. I don’t know what to do or what to think... Shin wannan duka na cikin wasannin Danger ne..?”

Dafasa Assad yai kafin yace “We are still not sure idan hular nan ta Musaddiq ce Mu’azzam.. Ka kwantar da hankalinka zamuyi DNA test kuma zaka gani hular nan bata Musaddiq bace kawai kamanceceniya sukai kaji koh..”

A hankali Mu’azzam ya jinina masa kai ba tareda yace komai ba. Lokaci guda ya mik’e. Assad ya dubesa yace “Ina kuma zaka..?”

“I’ll be right back.” Ya fad’i yana mai shigewa.

Motarsa ya bud’e ya ciro hand gloves da transparent zip lock bag irin wanda investigators ke storing evidence ciki.. Ya k’araso ya zira hannayensa cikin gloves d’in kafin ya d’auki hular ya saka a cikin transparent nylon d’in.

Ya mik’e suka fice daga wajen jikinsa duk a mace.

Idan yace zuciyarsa bata kusa daina aiki ba yayi k’arya.. Allah ya gani duk k’arfin hali irin nasa wannan bincike na nema ya zautar dashi.. Yanaji za’a iya isa wajen da Zuciyar tass bazata iya d’auka ba.. A b’angare guda ga Sadiya can hannun wannan D’anta’addan.. Gaba d’aya ya rasa Wanne zaiyi.. Ya rasa wane tunani zaiyi.. Assad ne yai driving nasa zuwa gida kafin shi ya nemi abin hawa ya shige nasa gidan.

Safeenah tana jin shigowar motar Mu’azzam ta sauk’o parlor cikin kwalliya na d’aukan hankali tana jiran shigowarsa.

Sanda ya turo k’ofar kallo d’aya yai mata ya d’auke kansa yai shigewarsa.

Safeenah tabi bayansa da kallo shaye da mamaki ganin irin kwalliyar da tai wanda akai dominsa bata ma ishesa kallo ba. A fusace ta mik’e ta haura sama itama.

Yana k’ok’arin shigewa bathroom ta shigo d’akin, tasha gabansa tana ture turen baki tana hawaye “Haba my Halaal.. Ka dubi tsawon lokacin nan da mukai bama tare a matsayinmu na ma’arauta.. And.. And yaufa na tare baka tashi dawowa gidan nan ba sai yanzu.. Sannan daka dawo ko kallo ban isheka ba. Wllhi this if not fair Mu’azzam..!” Ta k’arashe tana hawaye sosai.

Da gajiyayyun idanunsa yake dubanta kafin yace “Safeenah it was a long day.. And I have a lot on my mind right now.. Please don’t add to it with your drama.”

Zai shige Safeenah tai saurin taresa still tana kuka “Sabida mai kake mun haka Mu’azzam.. Idan akan text d’in BAD da aka tura maka ne wllhi nasan wanda ta tura maka..”

Da tsananin mamaki Yanzu kam yake dubanta “Mai kike nufi..?”

Safeenah ta saka hannayenta tana goge hawayenta, lokaci guda take furta “Wllhi nasan wa ta tura maka.. Kuma ta tura maka ne dan ta rabamu ita ta aureka..” Ta fad’i cikeda confidence.

Ya gyara tsayuwarsa yana dubanta, idanunsa akanta ya kuma girgiza kansa a hankali alamun bai fahimceta ba.

Safeenah ta shiga jinjina kai still hawaye bai daina gangaro mata ba “Meema ce Mu’azzam.. Meema ita ta tura maka sak’on BAD dan ka zargeni da cin amanar aurenka ka sakeni Ita kuma ta samu ka aureta.. Meema loves you Mu’azzam.. All this abubuwan da nake Meema ke bani shawari ashe so take naita provoking d’inka har ka gaji dani ka sakeni shine data fahimci Ameer na damuna da waya yana ce min shi bai hak’ura dani ba he still loves me Dikda cewa na zama matarka.. Ni kuma bana kulasa ina goge duk wasu sak’onninsa da kiransa tinda nasan implications d’in hakan zai haifar a matsayina na matar aure.. My sister took my phone and copied his phone number.. Shine take tura maka sak’onnin nan dan ka rabu dani.. Mu’azzam wllhi Allah shine shaida na babu komai tsakanina da Ameer. You need to believe me.. Wllhi I’m telling the truth..”

Da tsananin mamaki yake dubanta kafin ya saki gajeriyar murmushi yace “Safeenah Anya lafiyarki..? Kin kuwa San mai kike fad’i.. Meema fah.. Meema ce take sona ni Mu’azzam Gamji.?”

Safeenah tai saurin jinjina kai tana hawaye “Wllhi itace mai son rabamu..”

Girgiza kai ya kuma dan Yanzu kam ya soma tunanin k’wak’walwar Safeenah ya samu matsala. Wai Meema ce mai sonsa, toh yaushe ma yake wasa da Meema da har wannan rainin zai shiga tsakaninsu.?

“You are not well Safeenah..” Ya fad’i yana girgiza kai kafin ya rab’a ta gefenta ya shige bathroom.

Kuka ta kuma fashewa dashi ta zauna dirshan a wajen tanayin mai isarta.. Ta mik’e ta nufi nata d’akin ta d’au waya ta shiga kiran Mommy dan gaba d’aya kanta ya cunkushe ta rasa mai zatai dan dama Meema ce mai bata shawarin ya abinda zatayi Toh gashi sun b’ata da Meemar akan Mijinta ya zama dole ta samar ma kanta mafita tinda babu Meema.

Taita kiran wayan Mommy bata d’aga ba, Safeenah ta silale nan saman carpet tana kuka dan tasan Tabbas Mommy fushi tai da Ita tinda bataso ta tare gidan Mu’azzam ba.

Shiko gogan yana fitowa da yaga Safeenah bata d’akin Sai ya danna lock ma d’akin ya soma shirinsa. Daga nan sallah yai shafa’i da wuturi ya jima yana kai kukansa ma Ubangijinsa a matsayinsa na bawa gajiyayye wanda ya gaza sai abinda Ubangijinsa ya masa.. Sosai ya k’ask’antar da kansa gaban mahaliccinsa yana rok’onsa ya kawo masa d’auki a al’amransa. Daga bisani janyo laptop d’insa yai da zummar bincika wasu files da kwanakin baya yai saving.. Amma gaba d’aya ji yai baida kuzari tamkar dai wanda aka zare ma laka. Ya tura laptop d’in yana mai lumshe idanunsa. Ita kurum yake hangowa cikin k’wayar idanunsa da zuciyarsa.. Memories d’in da sukai sharing a gidan da kuma fita waje da suke da sunan mission shi yaita Yawo a kwanyarsa idanunsa da kuma zuciyarsa. Kaman wanda ya tina wani abu ya mik’e ya nufi drawer d’in da ya aje picture d’in da aka masu a park. Ya k’ura ma hoton ido, su duka biyun murmushi ne saman fuskokinsu amma kana ganin murmushin dake bisa kyakkyawar fuskarta zaka fahimci akan dole takeyi.. A hankali yakai yatsarsa guda yana shafa saman hoton daidai fuskar Sadiya. Labb’ansa ne suka fara motsi, harshensa ya soma furta “Don’t you worry.. I’ll find you.. In sha Allah I’ll.. I promise you..” Ya k’arashe yana mai lumshe idanunsa da sukai matuk’ar masa nauyi.

Safeenah kaw koda ta dawo taji d’akinsa a rufe nata d’akin ta koma ta fad’a kan gado tana mai kuma fashewa da wani kukan.

Washe gari ma batasan fitarsa ba dan yanda Mu’azzam yai kusan kwana zaune yana sak’e sak’en mafita kan abubuwan da suka taru sukai masa yawa haka Safeenah tai kusan kwana tana aikin kuka itama. Bata wani samu bacci ba sai kusan asuba. Dama sallahn ba wai ya wani d’ad’areta sosai bane musamman sallar asuba wanda zai katse mata baccinta. Sai rana ta fito tangararau take sallarta. Allah ka shiryar damu ka datar damu ta farki mik’akk’iya. Ameen!

**

Kana ganin k’wayar idanun Mu’azzam zaka fahimci dare ne mai tsawo ya kasance a garesa kafin wayewar gari. Abinka da Farin mutum nan da nan wahala damuwa ko jin dad’i yake nunawa tattare dasu koda kuwa sunyi k’ok’arin b’oye hakan.

Suna zaune a ofishinsu gaba d’aya.. Maleey (In Halee’s voice. Lol) Maleeka idanunta akansa tun shigowarsa Office d’in. Tinanin maganganun Chief ne fal zuciyarta, a b’angare guda kuma ga wani irin kishin Mu’azzam d’in da take.. Ita da taji an sace Sadiya ma addu’a take Allah yasa Danger ya maida shegiya matarsa koma ya kasheta gaba d’aya.

Mu’azzam d’in na tsaye gaban Farin allo wanda hotunan mutanen dake da alak’a da case d’in a jajjere anyi linking d’insu gaba d’aya da arrows ko Wanne da matsugunin da aka ajesa duk wanda ya tab’a samun alak’a da case d’in.

Mu’azzam ya kuma Jan wata Doguwar arrow daga kan hoton Danger yai cycle, ya zana k’atuwar question mark a cikin cycle d’in kafin ya rubuta B.A.T a saman cycle d’in.

Assad ne kawai ya fahimci mai B.A.T ke nufi, hular da suka tsinta ne jiya da dare a wajen saida drugs na Danger. Ita kaw Maleeka zuciyarta ne ya dinga bugawa tana tambayar kanta kodai Mu’azzam yasan da batun BAT ne.? Batakai ga samo amsar tambayar da zuciyarta ke mata ba wayar Mu’azzam d’in ta soma ringing..

Koda gani Danger ne mai kira, nan take yai masu umarni gaba d’aya su shirya tracing Danger da zaran ya d’aga wayar. Kowa ya zama in position. Duban Maleeka da ta zama wata sukuku da Ita yai yana karantar Ta kafin yace “Tap trace location.” Yai mata alama da ido kan computer d’in dake gabanta a d’an tsime kafin ya d’aga wayar.

Cikin sauri Maleeka tai k’ok’arin saita kanta tana mai jinjina kai kafin tai abinda ya umarceta.

Daga d’aya b’angaren Danger ya soma fad’in....





SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*38*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





“Kar ka b’ata lokacinka trying to trace my location. Dan bazaka tab’a samuna ba.!” Danger yace daga d’aya b’angaren.

“What do you want.. Tell me..!” Mu’azzam yace cikin k’ok’arin tsawaita conversation d’insu da Danger.

Danger ya dara yayinda Mu’azzam ya dubi su Assad yana son sanin ko sun samu location d’in Danger.. Assad yai masa alama da hannu saura ten seconds yaci gaba da jan Danger da surutu..

“Yarona da kuka kama nake so, ka bani shi na baka matarka in exchange..”

Murmusawa Mu’azzam yai kafin yace “You know that’s not possible..”

Danger ya jinjina kai yace “Your wife’s life is on the line here Inspector.. Da alama har yanzu baka yarda tana wajena bane.. Amma idan bakayi abinda nake umartanka ba zan zamar da ita tawa yanzu nan.. Nayi duk abinda naga dama da ita..”

Ji yake zuciyarsa na wani irin tafarfasa, ga gumi dake tsartsafo masa “Don’t you dare.!” Ya fad’i cikin tsnanin karaji yana mai buga teburin gabansa.

Danger ya shek’e da dariya kafin yace “Da alama har yanzu baka yarda matarka tana hannu na ba.. But let me put her through maybe zaka yarda..”

Kukan Sadiya Mu’azzam ya jiyo tana fad’in “Please don’t.. Don’t hurt me please.. Have mercy dan Allah..”

Danger yaci gaba da fad’in “Kaji koh.. Zan baka awa ashirin da hud’u ka saki d’anuwana da kuka kama, idan ba haka ba ka saka ma ranka wannan Beauty d’in ta zama tawa..!”

“I’ll kill you...!” Mu’azzam ya fad’i zuciyarsa na tsananin bugawa yana sakin haki a hankali.


D’if Danger ya katse kiran a daidai lokacin da sukaci nasaran samun location d’insa.

Take Maleeka tace “Location found.” Tana maganar tana sanar dasu ga location d’in. Gaba d’aya suka soma zame headphones d’in suka mak’ala a kunnuwansu suka mimmik’e suna shirin ficewa operation.

Daidai lokacin Chief ya shigo sanda suketa shiri cikin sauri babu kaman Mu’azzam wanda gani yake kaman bazai isa wajen ba, alla alla kawai yake ya ceceta ya kuma damk’o Danger da hannayensa.

Chief yai tsaye yana dubansu yanda kowa ke sauri cikinsu sai shirya alburusai suke cikin bindigoginsu. Yusuf na sanar dasu wani tsohon building ne Danger yake can wajen gari.

Assad ya sarawa Chief yana fad’in “We were able

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login