Showing 102001 words to 105000 words out of 209154 words

Chapter 35 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3085

na jira. Suka kuma yin sallama kafin Mu’azzam ya dawo cikin ofishin nasu.

Yana shigowa Assad ya K’araso yana fad’in “Barr Ameer Dikko, Safeenah’s lawyer is here.. Yana son ganawa da Safeenah..”

Sunan Ameer da Assad ya fad’i in full shine yai ringing a k’wak’walwar Mu’azzam. Barr Ameer Dikko.

Duban Assad yai kafin ya kuma duba Barr Ameer dake nufosu cikin takunsa na k’asaita.

Ya k’araso yana gaisar da Mu’azzam cikeda izgilanci irin yanda ya saba. Mu’azzam bai ce masa komai ba Sai aiaka masa muguwar kallo da yake yana nanata sunansa cikin zuciyarsa.

Assad ne yai masu jagoranci gaba d’aya zuwa interrogation yanda Safeenah ke zaune tana jira. A d’an Kwana guda da tai cikin Cell har kamanninta ya canza abinka da wacce bata saba da wahala ba. Farin fatar ta dik yayi wani irin jajaja alamun wahala da rashin sabo.

Ameer ne ya soma shiga suka gana kafin daga bisani Mu’azzam ya shigo. Safeenah na ganinsa ta fashe da kuka tana fad’in “My Halal I can’t believe you are doing this to me.. Please ka k’yaleni na tafi gida.. This place is hell..”

Ameer kaw takaici ya cikasa ganin yanda Safeenah ke shagwab’awa Mu’azzam tana wani kiransa her Halal.

Zama yai gefe yana mai aikawa Ameer mugun kallo. Bai amsa Safeenah ba still idanunsa na kan Ameer yake furta “Barrister Ameer Dikko is your enemy.!”

“Barr Ameer Dikko is ruining your home.!”

“Barr Ameer Dikko is very BAD”

“Barr Ameer Dikko you’re BAD”

Cikin rashin gane kalman nasa suke dubansa daga Ameer d’in har Safeenah.

Ameer ya girgiza kai yace “Ban fahimceka ba Inspector..?”

Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Ba Lallai ka fahimta ba amma Iyakacin abinda na sani YOU ARE BAD..”

Ameer ya kuma dubansa kai a k’ulle, lokaci guda Mu’azzam ya ciro wayarsa cikin aljihu yana nunawa Ameer sak’onnin BAD da akaita turo masa kwanakin baya. Ameer ya dubi sak’onnin da tsananin mamaki yana kuma duban Mu’azzam. Safeenah ma mamaki ne saman fuskarta cikin zuciyarta tana furta mai hakan yake nufi.

Mu’azzam yaci gaba da furta “Ko Wanene mai turo mun wad’ann sak’onnin gargad’i yake mun akanka BAD.. And that means yasan Kun jima kuna k’ulla wani abu kenan kaida Safeenah.. Let’s say Ikram Ta fahimci wani abu taakaninku da Safeenah.. And you two silenced her sabida kar ta sanar dani.. Am I right..?” Ya k’arashe yana dubansu su duka biyun.

Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa. Ta shiga girgiza kai tana fad’in “No.. Wllhi wlhi babu komai tsakanina da Ameer.. Wllhi bansan mai wannan sak’on ke nufi ba..”

“Ai dama bazaki sani ba. Amma shi wanda ya turo min wani clue yake so ya bani game da ku biyun..” Mu’azzam ya fad’i yana tsare Safeenar da idanu.

Ameer ya girgiza kai wannan karon yace “Excuse me Mr Office. Mai kake k’ok’arin fad’i.. What are you trying to accuse us of.? BAD everyone can be BAD.. You can also be BAD... Bad is just a word.. So don’t try to complicate things here..”

Murmushi Mu’azzam keyi wann karon yana duban Ameer d’in “We shall see.!”

Safeenah dake girgiza kai tana hawaye lokaci guda Ta soma fad’in “Wait Mu’azzam wllhi zan fad’i gaskiyar abinda ya faru.. Kar ka fara zargina da cin amanarka balle aurenmu ya lalace.. Wllhi zan fad’i komai koda bazaka yarda dani ba.”

Mu’azzam ya jinjina kai yana mai gyara zamansa lokaci guda yai alamawa Maleeka cewa ta shigo ta tattari bayanan Safeenah. Maleeka kaw kaman wacce take jira, nan take ta shigo.. Ameer sai aika mata mugun kallo yake a sace, yana tinanin idan ba Ita ba babu wanda zai tura ma Mu’azzam sak’on BAD dan yasan duk wanda ya tura sak’on so yake ya raba Mu’azzam d’in da Safeenah.. Maleeka ita kad’ai ce takeda wanann Motive d’in.

Mu’azzam ya dubi Safeenah yace “Ehen go ahead ina sauraronki.”

Safeenah ta soma fad’in “Kafin ranan aurenmu nayi receiving phone call daga wani mutumi, he told me he was an investor, yana son sayan Dairy milk da companyn mu ke producing... Ni kuma banso muyi losing client since ni ce ke rik’eda fannin saye da sayawarwa na Company d’in.. I didn’t want to disappoint Daddy.. I wanted to be perfect in his eyes.. Dikda cewa lokacin na kusan aure amma sai nayi accepting business proposal d’in.. Yai fixing date d’in da zamu had’u Mu tattauna kasuwancin, ranan ya fad’o daidai da ranan aurenmu.. Nace mishi bazai yuwu mu had’u mu tattauna kasuwancin wannan ranan ba amma sai yace mun shi baida lokaci daga wannan ranan, saidai a fasa kasuwancin.. Bana so muyi losing client nace masa babu damuwa zamu had’u mu tattauna kasuwancin.. Toh a ranan nayi receiving wannan text message d’in saidai banje location d’in ba dan zuciya na bai kwanta ba maiyasa zaice mu had’u a wani waje ba a Ma’aikatanmu ba.. Ban tab’a business da wani outside the company ba.. Shiyasa zuciyata bata aminta ba.. Kwatsam saiji nayi an tsinci gawan Ikram a wannan location d’in.. Wllhi wllhi Iyakacin abinda na sani kenan Mu’azzam.. Bansan ya akai Ikram ta tafi wannan location d’in da aka turo mun a matsayin meeting place ba..!” Ta k’arashe cikin kuka sosai.

Mu’azzam da yai mata k’uri Maleeka na gefe tana tattara bayanan cikin k’aramar littafi.

Mu’azzam ya kuma duban Safeenah kafin yace “And you expect me to believe your story..? Ta yaya zan San you’re not making it all up..? Idan gaskiya kike fad’i mai ya hanaki fad’i tuntuni..?”

Safeenah ta girgiza kai tace “Wllhi gaskiya nake fad’i wannan shine abinda ya faru.. Naji tsoron kar ka k’i amincewa dani ne shiyasa ban fad’i ba..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “And shi mutumin da zaku k’ulla kasuwancin tare baki da contact dashi ne ko kuwa contact d’in ne ya yanke.?”

Ta girgiza kai tace “I don’t even know him..”

“How is this possible..?”

Tana bada amsa yana kuma rikitata da wasu tambayoyin.

Ta kuma girgiza kai tace “I lost contact with him tin wancan lokacin.. Na karya SIM card d’ina bayan na canza layi dan naji tsoro sosai da aka ce an sami gawan Ikram a wannan location d’in wanda bansan ya akai taje wajen ba.”

“We are in a Global world Safeenah.. Tracking mutumin bazai tab’a yin wahala muddin kin tab’a samun contact dashi.. Unless kuma bakinku d’aya ne Keda shi.. Maybe Kun datse duk wata hanya da zai nuna kun tab’a samun connection dan kawai ku rufe laifin da kuka aikata ke da shi na kisan Ikram.. Admit Safeenah.!” Ya k’arashe cikin tsananin tsawatarwa.

Ameer yai saurin dakatar dashi wannan karon “Inspector ya kamata ka gyara kalamanka...”

Yusuf ne ya katsesu da fad’in “Someone has just confessed to the crime.”

Mu’azzam ya juyo yana duban Yusuf, gaba d’ayansu dake cikin d’akin ma duban Yusuf suke.

Mu’azzam ya girgiza kai yace “Mai kace..?”


Yusuf yace “Wani mutumi ya zo yanzun nan sannan ya amsa laifin kisan Ikram...”


Mik’ewa tsaye Mu’azzam yai yana tambayan Yusuf “Where is he..?”

Yusuf yace “Gashi nan a office d’in Chief ana tattara bayanansa..”

Cikin sauri Mu’azzam yasa kai ya fice yayinda Yusuf ya take masa baya. Maleeka ma bin bayan abokan aikin nata tai.


Safeenah Ta dubi Ameer tace “Mai hakan yake nufi..?”

Ameer ya tab’e baki kad’an yace “Ta yaya zan sani..? Ai ke zan tambaya.. Kwatsam Ana tuhumarki saiga wani ya amsa laifin..? Watak’ila wancan investor d’in ne da kukai deal tare..”

Safeenah ta mik’e tana huci “Ai kuwa wllhi sai na shak’e D’anbanza naji uban da yasa ya sakani a wannan ukun..”

Ameer ya tare k’ofa yana dubanta kafin yace “Not too fast Safeenah.. Ki tsaya kiji da mai yazo.”

Harara Ta aikawa Ameer kafin tace “And who do you think you are da zaka dakatar dani.. Wanda yayi crime d’in ya bayyana kansa hakan yana nufin zan zama free sannan zan koma gidan Mijina.. Babu wata alak’a tsakanina dakai dan haka kar ka sake kallon ko yanda nake ne balle kace ka sanni..!”

Shaye da tsananin mamaki Ameer ke dubanta “Safeenah.! Ni kike gayawa magana haka dan wani ya ceceki ya amsa laifin..?”

Dakatar dashi tai da fad’in “Correction Mr Lawyer. Dama ban aikata laifin ba kuma nasan Allah bazai barni na biya abinda ban aikata ba.. Da wannan b’ata lokacin da kake da ka fara processing releasing papers d’ina ne dan ni ba mai laifi bace.”

Ameer ya jinjina kai yace “I see, toh dai kar ki mance ko da wani ya amsa laifin nan akwai wanda ya tura sak’on BAD wa mijinki a gefe.. Mu’azzam bazai kuma yarda dake ba musamman idan ya tina BAD.!” Ya k’arashe yana murmushi.

Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa ta dubesa tace “You are behind this Ameer..!”

Ameer ya murmusa yace “Maiyasa zan tura masa sak’on BAD bayan nasan hakan na nufin d’aure kaina zanyi wajensa.. Ai duk wanda ya tura masa sak’on BAD wani ne da ya fahimci recently ina damunki da waya sannan kuma yana so ya rabaki da Mu’azzam maybe dan shi ya samu kusanci da Mu’azzam d’in..” Yai maganar yana kashe mata idanu guda kafin yace “Aff! I mean ita.. Dan nasan definitely mace ce..!”

Zuciyar Safeenah yaci gaba da yankewa. Ameer ya barta nan tsaye tana tinanin waye yasan tana waya da Ameer yake so ya sanar da Mu’azzam ta wannan hanyar. Waye mafi kusanci da ita wanda yasan komai nata..? Take taji bakinta na furta “MEEMA.!”



*SameenaAleeyou📚*
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*



*34*






*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Mu’azzam yana shigowa ya damk’o mutumin da duka hannayensa biyu yana tambayarsa ma wa yake aiki. Assad da Chief suka janyesa bayan ya kaima mutumin naushi a hanci.

Mutumin yaci gaba da fad’in “Tare mukai niyyan kidnapping Safeenah Gamji domin mu karb’i Ransom wajen Mahaifinta watau Alhaji Marwan Gamji. Ni lebura ne a Dairy Company d’insu dake nan birnin tarayya, a nan na sami contact d’in Safeenah Gamji kasancewarta ma’aikaciya ce a ma’aikatan. Mun tura mata sak’o a matsayin zamuyi kasuwanci da ita..”

Chief ya kuma jefo masa tambaya “Kun tura mata sak’o ta wayarta.. Kaida waye kukayi hakan.?”

“Nida accomplices d’ina.”

“Su waye accomplices d’in naka.?” Wannan karon Mu’azzam ne ya jefo masa tambayar yana murza hannunsa.

“Sagir da Muttak’a wanda akafi sani da Danger.”

“Ya akai kuka sace Ikram..?” Assad ya jefa masa wannan tambayar.

“Kaman yanda na Fad’a maku our target was Safeenah Gamji dan itace mukeda contact d’inta wanda na samo mana daga record na company.”

“Kenan Safeenah kuka so sacewa sai baku sameta ba kuka sami ‘yaruwarta.? Maiyasa Ita baku nemi Ransom d’in ba kuka zab’i ku kasheta bayan kun keta mata haddi..?” Chief ya jefo masa wannan tambayar, Mu’azzam kam huci kurum yake yana aika masa wani irin duba yana jin zuciyarsa na masa zafi musamman da ya tuna saida akai raping Ikram kafin aka kasheta.

Mutumin ya bada amsa da fad’in “Munso amsan Ransom d’in amma Sai muka samu abokin alk’allarmu wato Sagir ya riga ya mata fyad’e.. Bamu shirya haka a cikin plan d’inmu ba shiyasa Sagir ya harbeta. Sai muma muka harbesa muka saka masa bindigar cikin hannunsa muka saita bindigar zuwa k’irjinsa dan yayi kaman cewa suicide yai committing bayan ya kashe Ikram d’in..”

“Maiyasa sai yanzu ka zab’i ka fad’i gaskiya bayan tsawon lokacin nan..? Why did you chose to turn yourself in now.?” Jaja ya jefo masa wannan tambayar.

“Sabida naga an kama wacce batada laifi ana tuhumarta kan laifin da Tun asali itace target d’in, shiyasa na zab’i na fad’i gaskiya.. Dan harga Allah nayi nadaman abinda mukayi..”

Chief Jaja ya kuma jefo masa tambaya “Dama kun saba sace mutane ne kuna karb’an kud’in fansa ko Wannan shine karonku na farko..?”

Ya girgiza kai yace “A’a Yallab’ai Wannan shine karonmu na farko kuma shine karonmu na k’arshe dan nikam dai na tuba. Bazan sake ba shiyasa ma na zab’i na fad’i gaskiya.?”

“Now tell us, where can we find Danger.?” Assad ya jefo masa wannan tambayar.

Ya d’ago ya dubi Assad kafin ya murmusa yana mai girgiza kai “Kar ku b’ata ma kanku lokaci Yallab’ai dan bazaku sami Danger cikin sauk’i ba..”

Mu’azzam da tun yana bayani sai faman dunk’ule hannunsa yake yana murzasu naushi ya kuma Kai masa a Hanci ya damk’osa wuyarsa ya shak’esa yana fad’in “We are not playing games with you.. Moron.!”

Chief ya soma harzuk’a yana fad’in Assad ya fitar da Mu’azzam. Lokaci guda ya bada umarnin a d’auke D’an ta’addan a kaisa cikin cell a gark’ame.

Fincika Mu’azzam yai daga rik’on da Assad yai masa, ya d’aura duka hannayensa saman table d’in Chief Jaja ya matso da fuskarsa kusan na Chief sosai kafin ya kad’a kai yace “I swear.! I swear I will get to the core of this case.. And believe me, I’ll give you the shock of your life.. Just you wait and see, Chief Jaja..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga office d’in Assad ya bawa Chief hak’uri yana mai takewa Mu’azzam d’in baya.

Aka bar Chief Sai sakin huci yake yana rage necktie d’insa, Lallai ma wanann yaron baida kunya baida mutunci ya lura dik horon dakatar dashi da akai bai ishesa ba yanzu har yana duban cikin idanunsa yana fad’a masa magana.. Ya kula baida tsoro ne sam babu kuma abinda zai dakatar dashi dukda cewa gashi an samu wani yayi confessing. Yana tsaye yana tinanin Maleeka ta turo k’ofa ta shigo tana sakin huci.

Kallo d’aya yai mata ya d’auke Kai ya k’arasa jikin k’aramar fridge ya ciro bottle water ya b’alle marfin ya shiga kwankwad’a ko zuciyarsa zatai sanyi.

“Tell me now.. What have you done to Mu’azzam.? Naga ya fice kaman Zaki.. Ka sake aikata masa wani abun ne.. Suspension d’in da aka basa na tsawon makonni bai isa ba..”

“Shut up Maleeka..!” Chief Jaja ya daka mata tsawa kafin ya matso kusanta sosai yana huci yake furta “D’aniskan yaron nan is driving me crazy.. Ina d’aga masa k’afa ne sabida ke.. Sabida kince akanshi zaki iya rabuwa dani kuma zaki iya rasa rayuwarki duk akan wanann D’aniskan yaron da ma baisan kinayi ba.. Bayajin bari ba’a hanasa ya dena.. Duk hanyar da za’abi a nuna masa cewa an isa k’arshen case d’in anbi yak’i ya amince yak’i ya dakata ya hak’ura da binciken da yake, anyi duk mai yuwa yak’i ya daina.. Ya rantse sai ya isa k’arshen case d’in nan.. Toh kuwa Ina mai tabbatar miki Maleeka Mu’azzam Gamji yana tono mutuwarsa ne da kansa.. Dan akwai BAT a sama dani duk randa ya isaga BAT Toh kuwa babu shakka mutuwarsa kenan..!”

Maleeka ta shiga girgiza kai tana fad’in “No please.. Dan Allah kar ku kashe shi.. Kar ka bari a kashe shi.. Wllhi idan na rasashi mutuwa zanyi.. Wllhi mutuwa zanyi. Dan Allah kar ka bari a halak’ashi..”

Chief ya murmusa da gefen baki yana shafan b’angaren fuskar Maleeka da hannunsa guda “Baby bani zan kasheshi ba BAT ne zai kashesa..”

Cikin rud’ani Maleeka tace “Bayan BAD akwai BAT.. Toh Waye BAT..?!” Tai tambayar cikin rud’ani..

Murmusawa ya kumayi kafin yace “Jemage kikeji, baya farauta sai cikin dare.. BAT is worse than BAD.. Abinda zan iya fad’a miki kenan.. Idan ya ci gaba da Digging zai isa wajen BAT, idan ya isa nan kuma believe me ya hak’o kabarinsa da kansa.. Zaifi masa kyau idan ya yarda ya tsaya a nan domin BAT baida d’and’anin imani...!”

Suna cikin maganar wayar Chief ta soma ruri, sunan BAT ya bayyana saman screen d’in.

Zuciyar Maleeka yai wane irin tsinkewa ganin BAT ya bayyana.

“Get out now..!” Chief ya fad’i yana dubanta.

Yanda ya bud’e murya gaba d’aya yai maganar saida ya d’an firgita ta.. Tai saurin sa kai ta fice daga ofishin dukda taso taji abinda BAT da Chief zasu tattauna akai.

Tana fitowa taga wayan Ameer na shigo mata. Tai k’ok’arin saita kanta kafin Ta keb’e domin amsa kiran Ameer.

Tana d’agawa Ameer ya soma fad’in “Well done Officer.. Kinyi k’ok’ari da kika tura wa Mu’azzam sak’on BAD.. Tabbas sak’o ya isa ga Mu’azzam har ya nuna mun.. Well done..”

Fuzar da huci tai kad’an kafin tace “Look Ameer, I don’t know what you are talking about..”

“No no no.. Don’t you play dump with me Maleeka.. Ke kad’aice kikeda motive na turawa Mu’azzam wanann sak’on.. But koma yaya ne I must thank you domin kuwa sak’on zai taka babban rawa a auratayyan Mu’azzam da kuma Safeenah musamman yanzu da aka wanke Safeenah Banida chance d’in kareta a Kotu kinga sak’on BAD zai amfani domin kuwa na tabbata a halin yanzu Mu’azzam bazai tab’a yarda babu wata alak’a tsakanina da ita ba..” Ya k’arashe yana mai fashewa da dariya. Lokaci guda yaci gaba da furta “Good job Officer.. Keep it up.. Dole na baki kyautar kiss ta cikin waya..” Ya k’arashe yana mai kissing wayar yana kuma tintsirewa da shewa.

Zama Maleeka tai gijif saman kujera abubuwa cunk’ushe cikin zuciyarta, ita yanzu bata Ameer da ahirirtarsa take ba. Damuwarta shine wanene BAT wanda Jaja yake tarayya dashi wajen ruguza Mu’azzam.. A baya tayi tarayya da Jaja ne dan tasan Tabbas Jaja nada masaniya kan case d’in mutuwar Ikram, dan ta tab’a tsintar text message wata rana cikin wayarsa bayan Sun gama aikata mai zasu aikata a hotel room, sak’on ya shigo wayar Chief.. A lokacin wayar na aje gefenta kan gado yayinda Jaja ke bathroom.. Nan taga an turo sak’on kuma zallan sunan Safeenah Gamji kawai taga an rubuta a sak’on shiyasa tai zargin Safeenah nada alak’a da case d’in mutuwar k’anwar Mu’azzam.. Hakan ne yasa ta nemi Barr Ameer suka had’a team ta sanar dashi abinda take zargi gameda Safeenar shi kuma Barr Ameer yai amfani da abinda Maleeka ta fad’a masa yana Barazana ma Safeenah da cewa yasan wani abu gameda ita. Amma a halin yanzu batajin zata iya, Dikda cewa tin farko bataci dunduniyar Mu’azzam ba, ita kawai abinda take so shine ta fidda Safeenah daga rayuwarsa ita ta samu gurbi, bayan wannan batada wani motive na ruguza Mu’azzam.. Yanzu da rayuwarsa ke cikin had’ari ta damu matuk’a.. Batasan mai zata aiwatar ba.. Idan ta sanar dashi ga abinda Jaja yakeyi tasan Tabbas ba Mu’azzam kawai ba harta itama zata rasa rayuwarta ne.. Zata rasa Mu’azzam domin kuwa Tabbas su Chief sai Sun karsa matuk’a bai dakata da binciken da yake ba.. A b’angare guda tasan Mu’azzam da kafiya akan duk abinda yasa gabansa.. Batajin zai dakata da binciken nan.. Gaba d’aya Maleeka ta rasa wanne zatai, zuciyarta ya gama karaya da hidiman Jaja.. Tana matuk’ar tsoron ta rasa Mu’azzam.. Lumshe idanunta tai hawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login