Showing 81001 words to 84000 words out of 209154 words
tace sunyi waya da Mu’azzam kuma yace Ta bari har ta ida recovering zuwa next week.
Aunty Shemau ta aika mata mugun kallo kafin tace “Ke kuma sai Kika biyeshi da shike bakida hankali koh.. Ke ko tinanin wani yanayi mijinki ka iya kasancewa ciki bakiyi..”
Meema tace “Fad’a mata dai Aunty.. And wllh mijin nan nata Allah kad’ai yasan mai yake aikatawa.. Kinsan Daddy bai ganin laifinsa..”
Aunty Shemau ta jinjina kai tace “Ahtoh kinji har ‘yaruwarki Ta fiki tinani.. Maza a wannan zamanin ba abin yarda bane.. Kana kaffa kaffa ma ya ka k’are balle ke da kike uwa duniya yana wata duniyar.. Taimakon ki ake idan kina san mijinki a hannunki idan kuma baso kike tin kafin ki tare aurenki ya k’are a titi ba..”
“Gaya mata dai Aunty..” Meema tace tana mai chatting da wayarta
“Nifa Aunty Shema I trust my husband completely, especially yanzu da muka fara fahimtar juna yake nuna min k’aunarsa.. Amma ni kaina nafi so na koma kusa dashi.. I’ll surprise him kawai saidai ya ganni..”
Aunty Shema tace “Ahtoh Kema dai kya fad’i kina san kasancewa kusan mijinki.. Yanzu bari Muasaddiq ya shigo sai na sanar dashi ya fara shiri dan shi zai maidamu.. Idan Uncle d’in naku ya shigo sai na fad’a masa yanda mukaida Mommy shi zai sanar da Inne komai cewa Visiting Dr zai duba Safeenah dole mu tafi gobe gobe.. Sai ku shirya dan fitar sassafe zamuyi..”
Meema tace “An gama Aunty..”
Tuni Ta mik’e ta soma shiri Safeenah na fad’in ta kirawo mata Hindu ta shirya mata nata kayan.
*
Washe gari kaman yanda suka shirya komai hakance ta kasance. A b’angaren Musaddiq kuwa tinaninsa guda shine tafiya da zai ya bar Ajidde na kwana biyu.
Yau d’in ba Uniform d’in ma’aikatan gidan Gona bane jikinsa, tsaf ya shirya cikin k’anan kaya, dark blue shirt mai d’aukeda k’atoton hoton Paris tower sai jeans, yayi kyau sosai dan zamansa a gidan gonar babu shaye shayen kayan maye har haske ya k’ara asalin color d’insa ya kuma fitowa jajayen idanunsa duk sun koma fafare yanzu.
Safeenah ta dubesa tana fad’in “Ina kuma zaka. I thought we are leaving now..”
iWatch d’in dake d’aure hannunsa na hagu ya kuma dubawa kafin yace “I need to see someone.. I’ll be back soon..” Cikin sauri ya fice..
Safeenah tana kiran sunansa ko amsata bai ba yai saurin shigewa.
“Goshhh.! What kind of driver do we have.. Yau dai wnn tafiya Allah dai kawai ya kaimu lafiya..” Ta fad’i tana rausayar da idanunta.
A daidai yanda suka saba tsayuwa ya tsaya yana jiran k’arasowarta.
Can kuwa ya hangota tafe ta nufo yanda yake.. Tana tafe tana cilla jakan maganinta sama as usual.
Wani irin wawan birki Ajidde taja ganin mutumi D’an gayu tsaye gabanta, gashi dai amma irin murmushin Kuran tashe yake mata.
“Hey Crazy Dove..” Ya fad’i yana kuma sakin murmushi.
Ta shiga mutsuke idanunta tana kuma dubansa “Wai kaine haka..? Toh ina kayan aikin Naka yau..?”
Murmushi ya sakar mata kafin yace “Na d’auki hutu ne.. Zanje garinmu..”
Sai kuma take ta daina murmushin da take idanunta taji suna k’ok’arin kawo ruwa.
Ta girgiza masa kai a hankali kafin tace “Da gaske kake..?”
Shid’inma sanyi yaji jikinsa yayi, a hankali ya jinjina mata kai “Yes.. Da gaske.. But kar ki damu ba jimawa zanyi ba, juts two weeks at most..”
“Ni ban gane mai kake fad’i ba ka fad’a mun da gaske tafiya zakayi ka barni..?” Tai maganar siririn hawaye na gangaro mata daga idanu guda.
D’an shafa sumarsa yai yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni, shi kansa bai San yayi sabo har irin haka da Ita ba.. K’ok’arin saita kansa yai Kafin yace “Sati biyu.. Bazan wuce sati biyu ba..” Ya d’an murmusa kad’an yace “Kin tuna nace miki bana alk’awari.. Amma yau zan miki alk’awari.. Bazan wuce sati biyu ba.. Kinji koh.. So you behave while I’m not here..”
Izuwa lokacin kukan da Ajidde take rik’ewa ya fara fin k’arfinta “Kayi alk’awri zaka dawo gareni.. Dan Allah kar ka sab’a alk’awari..”
Duk k’ok’arin Musaddiq yaga baiyi hawaye ba saida yaji hawayen na fita masa daga idanu guda, ya d’an matso kusanta kad’an yana sassauta murya “I promise you.. I’ll come back.. Zan dawo.” Murmushi ya d’an soma dikda hawaye dake zubo masa daga idanu guda yace “Kin manta bamu k’arasa abinda muka fara ba.. Bamu k’arasa bama Aunty Nuratu magani ba.. So definitely zan dawo.. Kimin alk’awari zaki ci gaba da abinda muke.. Zaki ci gaba da karb’owa Aunty Nuratu magani wajen Malama Hafsah sannan zaki ci gaba da zubar da maganin Kyallu..”
Hawaye Ajidde take tana jinjina masa kai “Zan ci gaba, kuma na maka alk’awari bazan fasa ko d’aya ba..”
Ya sakar mata murmushi kafin ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kud’ad’e “Take this.. Dik randa Inna Kyallu tace ki sato mata kud’i Sai ki bata wannan kafin na dawo kinji koh..”
Girgiza masa kai tai tana mai mak’e kafad’u alamun bazata karb’a ba.
Musaddiq ya d’an sha mur yace “Look, idan baki karb’a ba zamu b’ata.. Nasan bazaki so na tafi Ina fushi ba.. So tun wuri ki karb’a..”
Ya k’arashe yana mai janyo jakanta ya saka mata kud’ad’en ciki..
Gani taci gaba da kuka yasa Musaddiq cewa “Hey is not like I’ll be gone forever.. Zan dawo ai ki daina kuka kinji koh..”
Shafa sumarsa yai kad’an dan yasan bazata daina kukan ba a yanda yasan halin Ajidde. Ji yai gaba d’aya ya kasa juran sauraren kukan nata.
Ya saka tafukan hannayensa biyu ya shafa fuskarsa yana fuzar da fuci.
“You take care Crazy Dove.. I’ll surely miss you.. Kina jina kar kiyi abinda zai saka ki a matsala idan bana nan kinji koh.. Zan wuce yanzu.. Till we meet again..” Ya k’arashe yana mata waving yana tafiya..
Cak Ajidde ta tsaya tana kallon yanda yake d’aga mata hannu kukanta na k’aruwa... Bata iya koda motsawa ba Sai duk’awa da tai wajen kukan na zuwa mata gadan gadan.. Haka rabi Misaddiq da kallo har ya b’ace ma ganinta.
Shid’inma goge k’wallan da suka cika idanunsa yai had’ida saurin shigewa yana jin wani abu can k’asar zuciyarsa.
A hanya ya had’u da Jume, Jume ya taresa da tambaya.. Nan Musaddiq ke sanar dashi sallama sukai da Ajidde..
Ya dubi Jume yace “Bansan na saba da yarinyar har haka ba.. Na zaci dariya da nishad’i kawai take sakani.. Amma yau da zamu rabu na d’an kwanaki sai naji kaman duka duniyar babu dad’i..”
Jume ya murmusa yace “Sabo da dad’i amma idan za’ai rabo da zafi.. Kar ka damu abokina.. In sha Allah zakaje ka dawo ka sami Ajidde lafiya.. Allah dai ya nuna mana lokacin biki..”
Musaddiq ya dubesa da mamaki yace “What.. Mai ka ce.. Haba Jume.. Ajidde k’aramar k’anwata na d’auketa so don’t get wrong ideas..”
Jume ya jinjina kai yana murmusawa yace “Munsan irin wad’ann k’annen ai.. Allah dai ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya ya kuma dawo daku lafiya..”
Musaddiq ya amsa da Ameen kafin suka k’arasa yanda sauran jama’an ke jiransu.
Dama Musaddiq d’in kawai suke jira nan aka soma sallama da juna kafin suka shige Mota suka kamo hanya.. Mutan gidan na masu fatan sauk’a lafiya.
Haka sukazo suka shige Ajidde tana duk’e wajen tana kuka, Musaddiq ne kurum ya kula da Ita, ko Ita kanta Ajidden ma batasan shine mai tuk’a motar ba dan har wnn lokacin bai sanar da ita shi jikan gidan bane.. Ta dai zaci ma’aikacin gidan ne kaman yanda ya sanar da ita.
Ta mirror yake dubanta yana driving. Cikin zuciyarsa ya furta “I’ll miss you and your Crazy jokes.. My Crazy Dove..!”
**
ABUJA
Zama yai cikin Mota yana jiran sauk’owarta, waya yake da Assad yana sanar dashi yanzu zasu fita kenan.
Daga d’aya b’angaren Assad yace “Mission continues kenan.”
Gajeren tsaki Mu’azzam yai yace “Don’t you think is too early for this.. Kaga zamuyi magana.. Ka sanar dani idan Kun isa location..” Daga haka katse kiran yai yana mai d’ago kai nan ya hangota tana tahowa cikin doguwar rigar abaya kalan peach Wanda y dace da skin color d’inta.
Ya tsareta da idanu yana dubanta har ta k’araso jikin motar.. Saurin kauda kansa yai ganin Ta d’ago fuskarta. A hankali ya mik’a hannunsa ya bud’e mata frontseat. Bata shiga ba sai mugun kalllon da take aika masa.
“Get in..” Ya fad’i yana tsareta da ido.
“Tell me first, ina zaka kaini.. I’m so tired of your games, you know..” Ta k’arashe cikeda tsiwa
“Do you always talk this much.?” Ya fad’i cikin d’an d’aga Murya.
“Only when I’m forced to..” Ta basa amsa kai tsaye tana mai kauda Kai gefe.
Fuzar da huci yai kad’an kafin ya bud’e motar ya fito “Ko ki shiga ko na shigar dake da k’arfi..” Ya fad’i hannayensa saman belt d’insa.
“Get in now..” Ya kuma fad’i yana mata alama da idonsa cewa ta shige motar.
K’walla ne cikin idanunta amma sai tai k’ok’arin rik’e kukan nata ta shige motar.
Lokaci guda ya zago ya shige suka fice. Suna tafe babu mai cewa k’ala saima duban samb’ala samb’ala hanyoyin cikin garin Abuja da take.. Inama taga ya kaita gidansu wajen Ummanta.. Tana tsaka da tinanin taga ya d’auki hanyar sch d’insu.. Ita kam bama tasan an janye yajin aikin da aka tafi ba. Ta dai yi shiru ta zubawa sarautar Allah idanu.
Bata ida tinanin ba taji yana tambayarta course d’inta.
“And why does it matter..? Ko dik cikin mission d’in Naka ne..?” Ta tambaya tana duban wani b’angaren.
“Wani department kike..?” Ya sake tambaya ba tareda yabi takan wancan tambayar nata ba.
Jin Ta masa shiru ya sanyasa kad’a kai yana fad’in “Seems like you’re enjoying zaman GIDAN ARO..”
Jin abinda ya fad’I ya sanyata saurin cewa “Quantity Survey nake karantawa.. And first year nake.”
Bai kuma bi takanta ba har saida suka isa yanda suke lectures.. Mutane kaw mak’il k’ofan department d’in nasu ciki harda ‘yan ajinsu.
“Wait..” Ya fad’i yana mai ciro waya cikin aljihunsa.
“Take this.” Yai maganar yana mik’a mata sabuwar waya gar k’irar Samsung.
Rausayar da idanunta tai tace “No.. no need for it I guess, Mr Inspector.” Tai maganar tana k’ok’arin bud’e k’ofa.
Saurin janyota yai cikin tsananin b’acin rai “Why are you so stubborn..?!” Yai maganar yana firfito da idanunsa waje cikin b’acin rai.
“Take it now..” Ya fad’i yana mik’a mata.
Baki a ture ta amsa ba tareda ta kuma dubansa ba.
“Incase of emergency.. Don’t go anywhere idan ba tareda ni ba. Idan buk’atar hakan ya kama dole, ki kira lambar dake cikin wayar ki sanar dani... Kije ki zauna da ‘yan ajinku I’ll be waiting for you here.. I repeat don’t think of going anywhere without me.. Understood..?”
A hankali ta jinjina masa kai..
Lokaci guda ya bud’e motar ya fito kafin ya zagayo ya bud’e mata.
Zata shige ya tare gabanta had’ida bata light hug... Daidai saitin kunnenta yake rad’a mata “This is also part of our mission..”
A hankali ta k’ak’aro fake smile ta sakar masa tana mai jinjina kai.
Murmushin Shima ya sakar mata yana mai d’aga mata hannu “Take care wife..!” Ya fad’i yana d’aga mata yatsa guda had’ida kashe mata ido guda.
Fuzar da huci tai tana mai rausayar da idanunta ba tareda tace komai ba.
Lokaci guda Mu’azzam ya zaro shades d’insa ya rufe idanunsa dashi kafin ya zauna saman motar yana jiranta.
‘Yan matan dake zazzaune k’ofar wajen kuwa Sai awwn awwn suke masu dan sunyi bala’in burgesu yayinda wasu suka shagala da kallan mijin nata.. K’ananan maganganu na tashi musamman bayan rumor d’in abinda ya sami saurayin Sadiya Sagir ya isa masu wasu na gulman bata auri Baban Aminiyarta ba ta sami wani had’add’en matashi kuma daga gani He’s loaded . Da yawa cewa suke Lallai Sady Pretty nada sa’a.
Yanda taga anata kallonta yasa dik ta tsargu, haka ta shige sukuku kaman ba Sady Pretty da idan tazo waje sai kowa ya sani ba.. Haka nan da yawa ma shakkun magana suke mata.
Can ta hango Aminiyarta Sabeera zaune cikin lecture hall. Gabanta yai wani irin fad’uwa ganin irin kallon da Sabeerar ke mata.. Lokaci guda Sabeera ta wani d’auke kanta kaman bataga Sady ba.
Cikin sanyin jiki Sady ta nufi cikin hall d’in wajen k’awarta.
Sabeera tana Ganin Sady ta nufota ta mik’e zata fice.. Cikin sauri Sadiya ta k’arasa ta rik’o hannun Sabeerar.
“Dan Allah ki tsaya muyi magana Sabeera..”
A wulak’ance Sabeera ta juyo tana dubanta, lokaci guda tana duban sutiran dake jikinta had’ida wayar dake hannunta.
Murmusawa tai tace “Your true color has finally showed up, dear friend.. Bansan ya akai van fahimci haka ba tuntuni.. Dik ja min kunne da ake akanki ban tab’a sauraronsu ba amma yanzu na yarda.. Kuma Ked’in da alama tsautsayi binki yake Sadiya..”
“Shut up Sabeera..! You know perfectly well abinda kike fad’I ba haka bane...!”
“No you shut up.. Kin mance saura k’iris ki auri mahaifina.. I’ll never forgive you for that Sadiya..”
“But I didn’t marry him.. Did I.?”
“Badon ‘Yantaddan da suke bibiyan ki ba da tuni kin zama matar Babana.. How dare you..? You have no idea wane irin tashin hankali muka shiga nida Mama.. Bakisan yanda Baba ya juya mana baya ba duk akanki.. Sadiya Kinsan irin k’uncin da kika saka ahalina ciki.. My parents almost got separated all because of you Sadiya.. How could you expect me to forgive a betrayal like you..!” Ta k’arashe cikin kuka su dukansu biyun kuka suke.
“Sabeera hear me out first.. Kema kinsan idan ba dole ba bazan tab’a yin abu makamancin haka ba.. Kin sani Sabeera.. Please let’s talk this out first please..”
Girgiza kai Sabeera tai tana hawaye tace “Na yaushe Sadiya.. Bayan duk abubuwan da suka faru Baba yace bazamu ci gaba da zama a garin nan ba.. Dutse zamu koma kuma da zaran mun koma zai sami wani cikin family ya aurar dani..”
Sadiya taci gaba da hawaye tana girgiza kai. Lokaci guda Sabeera Ta jinjina kai tana murmushin da za’a kirasa da yak’e wanda yafi kuka ciwo..
“Kinfi kowa sanin yanda nake son karatuna Sadiya.. Yanzu shikenan bazanci gaba ba.. Dole na sato k’afa na fito domin nayi bankwana da karatuna na k’arshe.. Na tabbata mazajen zuri’ar mu basu bari matayensu suyi karatu.. But at least ke kin samu mai supporting d’inki.. Had’add’en miji mai sonki da k’aunarki wanda zai iya ajiye komai nasa ya biyoki har makaranta ya zauna ya jiraki.. Wacece ake mata haka Sadiya.. Da alama ke d’in kinada sa’a bayan duk abubuwan da kikai, mafarkin ki na auran mai kud’i ya tabbata, not only that he’s every girl’s dream..” Ta k’arashe maganar tana mata nuni da Mu’azzam dake zaune saman mota ya d’aura k’afarsa d’aya kan d’aya yana shafa waya.
Sabeera taci gaba da furta “I don’t know ko zamu sake had’uwa ko bazamu sake ba.. But for now, ni Sabeera ina ce miki Goodbye..!” Ta k’arashe tana mai juyawa..
Cikin tsananin sanyin gwiwa Sadiya Ta silale ta zauna saman kujera.. Hawaye suka ci gaba da gangaro mata, cikin zuciyarta take furta “Allah sarki Sabeera bakisan abinda ke faruwa da rayuwata bane.. Baki San wane irin walak’antaccen aure nayi ba duk da bazaki fad’I haka ba.. A fili kuwa Fad’i take “Ki yafe min Sabeera.. I never wanted any of this to happen.. Ki yafe mun k’awata..” Ta k’arashe tana mai kifa kanta saman desk hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta.
Mu’azzam dake zaune waje waya ya samu daga Assad, lokaci guda yace “Alright I’ll be on my way..”
Yana katse kiran ya shiga kiran wayan Sadiya.
Sadiya da kanta ke kife tana mance da wani waya saida taji ringing har cikin kanta da shike wayar na saman desk d’in ne.
Tasan shi kad’ai ne zai kira tinda shi ya bata kuma bata saka lambar kowa ba sannan bata bama kowa ba.
Batace komai ba koda ta d’aga, daga d’aya b’angaren yace “Zanje yanzu ana nemana.. Don’t step a foot out of that hall.. Ki zauna a nan ki jirani kinji koh..”
Ya d’anyi fasali kafin ya k’ara jaddada mata “Kar ki fita ko k’ofa ne Sadiya.. You wait for me right there kinji koh..!” Daga haka katse kiran yai kafin ya shige Mota ya d’au hanya.
Yana katse kiran Ta kuma fashewa da sabon kuka.. Ai kuwa koda ta tabbata ya fice a makarantar Mik’ewa tai tana goge hawayenta “Ka rabani da kowa nawa Mr Inspector.. This is the perfect opportunity for me to escape..!” Tana ida fad’in haka tai fitowarta itama lokaci guda ta nufi gate tana neman abin hawa..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*28*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A cikin Mota suka had’u da Sabeera, saidai cikin dukansu biyun babu wanda ya fahimci suna cikin motar har saida Sady Ta fad’i destination d’inta. Sabeera ta waigo suna duban juna, sai kuma ta kauda kanta ba tareda tace komai ba. A haka har suka iso unguwar tasu babu mai cewa k’ala..
Da shike waje guda suka sauk’a Sadiya Ta dubi mai motar tace “Malam dan Allah kai hak’uri lungun can kawai zan shiga na amso maka kud’inka.. Akasi aka samu ban fito da Jaka ba.”
Mutumin ya dubeta ya girgiza kai yace “Hajiya Kinsan ba’a haka.. Ki biya kud’in ki kawai ki tafi..”
Zata kuma magana Sabeera ta ciro kud’i ta bawa mai taxi d’in tace “Malam namu ne mu biyu, ‘Yaruwata ce tare muka saba tafiya dama..” Daga haka Sa kai tai zata shige. Sadiya ta dubeta murmushi saman fuskarta “Na gode..”
Sabeeran batace mata komai ba sanda suka soma takowa daga nan bakin babban kwalta yanda aka ajesu.
Sadiya ce ta soma fad’in “Ina fata wata rana ki sami gurbi a zuciyarki ki yafe mun Sabeera.. Nasan Kinsan maganan bashin Hajiya Tabawa dake kanmu wanda Baba yace zai biya mana amma saidai idan zan amince da aurensa.”
Katseta Sabeera tai da fad’in “Basai kin maimaita ba na sani tinda har ya kiraki da Baby a gabana.”
Sauk’e ajiyan zuciya Sadiya tai kafin taci gaba da fad’in “Ba auren jin dad’i nai ba Sabeera. Dan ni ko a labarai ban tab’a karo da labarin irin aurena ba.. Auren Mission nai.. Sannan a GIDAN ARO nake zaune gidanda sam ba nawa bane kuma ko wane lokaci za’a iya sallamata.. Mr Inspector ya aureni ne ba wai dan yana k’aunata ba Sabeera.. Da zaran ya ida mission d’insa zai sallameni daga rayuwarsa Wanda zanfi kowa Farin ciki da hakan..”
Sai sannan Sabeera ta d’an dubeta da mamaki..
Sadiya ta murmusa Wanda yafi kuka ciwo taci gaba da fad’in “Sabeera amfani dani kawai yake domin ya cimma burinsa ya samu wani clue da zai