Showing 198001 words to 201000 words out of 209154 words
Suna tafe saman kwalta sukazo Shige DownTown Take away.
Safeenah tace Shawarma take son ci. Parking yai yana tambayarta ko akwai abinda take so bayan Shawarma. Ta girgiza masa kai kad’an alamun a’a.
Wallet d’insa kurum ya d’auka ya fice, ya mance wayarsa nan cikin motar.
Safeenah ta dubi wayar tana tab’e baki kad’an, hannunta Takai saman wayar ta d’an Shafa hasken wayar ya bayyana. Ta murmusa cikeda jin dad’in yanda time ya tafi, har kusan k’arfe 12:30pm. Bata janye idanunta daga barin duban wayar ba taji wayar na vibrating. Ta duba mai kira taga an rubuta _Beautiful_ Dogon tsaki Safeenah taja dan tasan shegiyar can ce mai kira. Katse kiran tai. Nan kiran ya kuma shigowa Safeenah ta kuma katsewa tana murmushi take furta “Wann lokaci na ne yarinya.. Sai lokacin da naga dama ya koma miki.. Yanzu ne zakiyi danasanin shiga tsakanina da My Halal har kiyi gangancin baje Koli a Gidana.” Ta murmusa kafin Ta jefa wayar nasa k’asan seat yanda zai kaman wayar ta fad’a wajen bai sani bane.
Ta hangosa yana rik’e da takeaway d’in. Nan ta kuma shigewa cikin kujera tana lumshe idanunta kaman mai bacci.
Duba d’aya Mu’azzam yai mata ya janye idanunsa, sai kuma ya k’ara dubanta yaga kaman bacci take gashi ta tak’ura cikin seat d’in.. D’an rank’wafowa yai yana k’ok’arin kwantar mata da kujeran dan taji dad’in kishingid’an nata.. Safeenah tana jin ya rank’wafo Sai ta fad’o jikinsa da gangan kaman batasan tayi hakan ba. Ya tsaya cak ya daina abinda yake k’ok’arin yi.. Cikin dabara ya janye Safeenah daga jikinsa kafin ya kwantar mata da kujeran. A hankali ya daidaita nasa zaman cikin kujeransa kafin ya soma driving.
Cikin Zuciyar Safeenah fal annashuwa, ta kula yanda yake driving d’in ma cikeda kulawa ne dan kar wani abu ya samu Babynsu.
A haka har suka iso gida. Ya d’an bubbuga kujeran da take zaune bisa “Feenah wake up now.. We are here.”
Ta bud’e idanunta da k’yar kaman mai baccin gaske.
Ta yunk’ura Zata tashi ta d’an saki k’ara kad’an tana fad’in “My back still hurts..”
Sannu ya dinga mata yana fad’in ta k’ok’arta ta fito. Haka Safeenah ta fito daga cikin motar kaman mai koyon tafiya. Mu’azzam ya rik’o sauran tarkacan, danginsu maganinta da takeaway d’in.
Iya dake jiransu dan sanda zasu fice sun had’u da ita Mu’azzam d’in ya sanar da ita zai kai Safeenah asibiti. Nan take masu sannu da dawowa tana tambayar jikin Safeenah.
Har d’aki Mu’azzam ya rakata, ya d’auko ruwa ya bata maganin yace tasha. Babu musu Ta amsa tasha tana kuma narke masa.
Saida ya tabbata tasha maganin kafin ya mik’e yana zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa. D’an shafa aljihun yai yana duba wayarsa yaji bata nan. Nan yai tunanin k’ila a mota ya barta.
Safeenah na hankalce dashi Ta fahimci wayarsa yake nema. Ta marairaice fuska tana fad’in “Yanzu tafiya zakayi..?”
Ya d’an dubeta sai kuma yace “Is there something you need..?”
Tai rau rau da idanu tace “Yanzu idan naji ciwo cikin dare fah..? You heard what the Dr said ai.” Cikin shagwab’a take maganar.
D’an shafa fuskarsa yai yana fuzar da fuci kad’an “Feenah bazai yuwu kiyi amfani da cikin jikinki ki zaunar dani a nan ba.. Kar wann tunanin ya shiga kanki kin fahimta.” Ya k’arashe yana d’an bud’e idanunsa.
Cikin yanayi mai ban tausai ta jinjina kai tace “Na Sani.. I know my place.. You don’t need to remind me.. Nima dan Ina cikin ciwo ne shiyasa na kiraka kuma dan babu wanda zan kira ne..” Ta k’arashe kaman zata saki kuka.
Ya d’an furzar da huci kad’an yace “Ki kwanta ki huta haka nan.. Ni zan wuce.. Allah ya baki lafiya.. And please ki kula..”
A hankali ta jinjina masa kai tana mai binsa da kallo har ya fice.. Ji tai kaman ta nufesa a guje ta rungume bayansa sabida tsananin kewar kasancewa tare dashi da tai. Ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka gangaro mata.
Shiko Mu’azzam agogon dake manne Parlorn k’asa yake duba har kusan k’arfe 12:am Wato shabiyu na dare.
Duban Iya dake rakub’e gefe yai tana gyangyad’awa alamun fitowarsa take jira. Mu’azzam yai mata sallama cikeda kulawa kafin ya fice.
Mommy tana jin fitarsa ta mik’e ta nufi d’akin Safeenah.
**
A b’angaren Sadiya kaw katse kiranta da yai har sau biyu shine babban abinda yafi d’aga mata hankali gashi har shabiyun dare ta gauta bai dawo ba. Wasu irin k’walla ne taji suna ciko idanunta. Maike shirin faruwa da ita da aurenta..? Tambayar da ya tsaya mata kenan a zuciyarta wanda yasa tuni taji k’walla sun ciko idanunta.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*62*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ta jima sosai zaune a parlorn ko zataji zuwansa amma shiru bai K’araso ba. Jiki a sanyaye ta koma d’aki tai zaune bakin gado had’ida rapka uban tagumi. Wata zuciya tana tuhumarta ‘Kika sani ko ya maida auren Safeenah ne..? Toh amma Maiyasa zaiyi rejecting call d’inta.?’ Tai saurin lumshe idanunta tana San yakice tunanin koma menene cikin zuciyarta. Tashi tai ta d’auro alwala tai sallah raka’a biyu tana addu’an Allah ya sassauta ma zuciyarta. Duk k’alubalen da jarabawa da zata fuskanta a gidan aurenta Allah ya bata juriya da hak’urin cinye wann jarabawar. Tinda aure dama ibada ne. Kuma dik abinda akace ibada ne Toh kuwa dole a fuskanci k’alubale cikinsa. Ta ida addu’o’inta ta mik’e ta haye Gado idanunta kan agogo tana sauraren ko zataji an bud’e gate.
Can taji shigowarsa, maimakon ta mik’e ta nufo parlor sai ta kuma nitsewa cikin gado tana jin wasu hawayen suna zuwa mata. Ita ba jimawan da yai a waje bane damuwarta, abinda bai tab’a yi ba shine katse kiranta.. Kuma har sau biyu ya katse balle tace kuskure ne, gashi bai kuma kiranta back ba.. Wann abin duk yafi sanyar mata da jiki. Tai lamo cikin Gadon tana jiran taji shigowarsa.
Ya turo k’ofan d’ankin nata a hankali, nan ya hangeta kwance saman gado. A nasa tunanin bacci take sai bai shiga d’akin ba Bai tasheta ba ya wuce nasa d’akin.
Sadiya kaw tana jin ya juya bai shigo ba taji kuka na zuwa mata gadan gadan, tana jin sanda ya bud’e d’akinsa ya shige. A yanda tasan shi ko bacci tai a nata d’akin baya tab’a yarda su raba shimfid’a, koda ace bacci ya d’auketa a d’akinta wasu lokutan farkawa take ta tsinci kanta a nasa d’akin ya sureta ya kaita can, wasu lokutan kuma shima kwanciyar yake a nata d’akin ta kula baya tab’a yarda suyi bacci ba cikin jikin juna ba.. Itama d’in zata iya cewa ta riga ta saba da hakan bacci cikin jikin mijinta, ya sabar mata da hakan yabi jikinta..Ta kuma jin wani rauni na taso mata can k’asar zuciyarta. Yanzu idan Safeenah ta dawo dole komai rabawa zasuyi.. Wai dama haka kishi yake.. Haka matan da mazajensu sukeji idan mazan suka kuma kawo wata mace.. Lallai duk macen da mijinta ya k’aro mata aure ta kumayi tawakkali ta amshi k’addararta a yanda yazo mata wann matar ta cika a kirata jarumar mata.. Kuma ta cika a nad’a mata Kambi na sarautar mata.. Tabbas zuciya rauni ne da ita mai juriya da tsoron Allah ne kawai Zata iya jure wann rad’ad’i na kishin.. Allah ka iyar mana abinda bazamu iya ba ka bamu abokan zama na k’warai idan ka k’addara hakan a garemu. Ta kuma lumshe idanunta a hankali siraran hawaye suka gangaro mata.
Mu’azzam kaw koda ya shigo ya hangeta tana bacci sai bai tasheta ba dan dama ba kwanciya zaiyi ba, research yake so ya d’an gudanar kan K’ungiya masu safaran mutane da yaci karo dashi cikin bincikensa. Dan haka tuni ya bud’e computer d’insa bayan ya ida shirinsa na bacci ya shiga bincike yana duba ko zai sami wani abu da zai nuna cewa an capke ‘yanta’addan a wancan lokacin maybe suna wani prison serving their sentences. Saidai duk iyakan binciken da zai bai samu labari mai kama da hakan ba.. Bacci b’arawo ne yai gaba da shi nan wajen.
**
A can b’angaren Safeenah kaw koda Mommy ta shigo ta taddata kafeta da idanu tai tana fad’in “Kar ki raina mun hankali Safeenah. Na Sani k’alau kike salon makirci ne kawai ya sanyaki kiran Mu’azzam...”
Safeenah Ta turo baki tace “Toh Mommy ya zanyi Ina son kasancewa da Uban D’a na.. Sai na zuba ido yana can yana cin soyayyarsa ni an barni da dakon yaro cikin jikina.. Mommy meye laifina Dan naso kasancewa da Uban d’a na..”
Mommy tace “Ke tafi can ki rufe mun baki.. Toh a haka ne zaki samu kulawarsa.? Aima saidai ki hau masa kai har kisa yaji baya marmarin cikin naki.. Ke barin Fad’a miki da wann hanyar da kika d’auko sam ba mai b’ullewa bace, bazaki samu kansa ba a haka.”
Safeenah tace “Tab ai wllhi Mommy yanzu na fara babu gudu babu jada baya sai na k’wato abinda yake nawa ne.. Kuma wann D’an cikin nawa shi zai taimaka min mu yak’i wancan shu’umar mu k’wato Babansa daga wajenta.. Idan kuma nai duk abinda zanyi bai working ba sai na sanar da Inne da Daddy nasan matuk’a suka San inada ciki dole a maida aurenmu da Mu’azzam.”
Mommy ta katseta da fad’in “Ashe ke shashasha ce lamba d’aya.. Banda Rashin wayo wayace miki ana sanar da samuwar k’aramin ciki haka gatse..? Idan kika sanar dasu yanzu sam bazasuyi d’okin cikin ba.. Amma idan kika bari suka fahimci haka sai kifi samun goyon bayansu da kulawarsu.. Koda wasa kar kiyi wann kuskuren..”
Feenah ta saki baki tana duban Mommy dan ita bataga mai zai hanasu farin ciki idan ta sanar dasu ba.
Mommy ta katseta da fad’in “Kina jina bazaki sanar dasu yanzu ba.. Ki bari akwai lokacin da na tanadar ma hakan.. Amma idan kika zab’i kiyi abinki ke kad’ai ni bazance komai ba Sai na zuba miki idanu kiyi duk yanda kike so.. Idan kikaje garin shashashancinki da haukarki kika salwantar da cikin kinga ai shikenan kin huta..”
Safeenah tai shiru tana sauraron Mommy.. Sai kuma ta jinjina kai tace “Shikenan Mommy bazan sanar dasu ba zan jira lokacin da Kikace d’in..”
“Yauwa yanzu naji batu.. Tashi muje ki kwanta ki huta..”
Babu musu Safeenah ta mik’e tabi bayan Mommy.
**
Washe gari ma sassafe ya fice Dan ko sallama bai samu sunyi ba Assad na jiransa akwai yanda zasuje sann yana so ya soma biyawa Prison wajen Yusuf kafin suje yanda zasuje da Assad d’in.
Koda Sadiya ta farka taga har ya fice Sabon tashin hankali ta shiga, ba d’abi’arsa bace fita bai mata sallama ba.. Ko sauri yake zai shigo ya manna mata kiss ya kuma mata sallama ya sanar da ita aiki na gaggawa ya taso masa.. Amma sai gashi yau ya fita kuma sam ita dai bataji alamun shigowarsa ba.. Mai hakan yake nufi..? Tai jigum abin na neman ya d’aga mata hankali cikin k’ank’anin lokaci. Taji kanta na wani irin sara mata ga daren jiya ba wani samun isasshen bacci tai ba, haka tai kusan kwana tana juyi. Kewan gida ne ya isheta.. Taji tana son taje taga Umma da ‘yanuwanta. Tai tunanin kiran layinsa sai kuma ta tuna jiya fah rejecting yai sann bai ko bi takanta ba har wann lokacin.. Jiki a sanyaye ta aje wayar nata ba tareda ta kirasa ba. Tai zaune a parlor kaman marainiya tana tinanin rayuwa da irin k’alubalen data fuskanta a rayuwa.. Shin wann ma wani sabon karatun ne..? Tambayar da zuciyarta tai mata. Kwanciya tai lak’was cikin kujera tana jin ko kitchen kaman bazata iya shiga ba a nan bacci b’arawo ya d’auketa abinka da wacce bata wani sami bacci daren da ya gabata ba.
**
Mu’azzam yai zaune yana jiran fitowar Yusuf a wajen da aka tanada domin ganawa sa prisoners.. Can ya hangosa ya nufo yanda yake wani ganduroba biye dashi.
Mu’azzam ya tsaresa da idanu yana dubansa yanda yake nufosa, a maimakon kayan ‘yansanda kayan prisoners ne jikinsa.. Ya d’an kauda fuskarsa kad’an yana jin wani abu na tokarin zuciyarsa.. Maiyasa abokinsa zaici amanarsa.. Maiyasa Yusuf..?
Daidai lokacin Yusuf ya k’araso gajeriyar murmushi saman fuskarsa, ya zauna a kujera mai kallon na Mu’azzam teburi ya raba tsakaninsu.
“Inspector, what brought you here this early..?” Yusuf ya tambaya yana d’an shafa hab’arsa kad’an idanunsa akan Mu’azzam d’in.
Mu’azzam ya kafesa da idanu yana dubansa, saida ya kwashi tsawon lokaci a haka har Yusuf ya soma gudura, ya saki murmushi yana ‘yan waige waige lokaci guda yana rage girman idanunsa kad’an “You shouldn’t been seen here Inspector.. You know this could be dangerous for me... Kar ka mance they have eyes everywhere.. Suna karantar duk wani movement d’ina..” Ya kuma duban Mu’azzam d’in yana sakin murmushi a hankali “I don’t want to get killed Inspector.. Nida munsan ya criminals suke gudanar da al’amaransu musamman a Prison.. They can easily eliminate me here.”
“Kayi magana idan baka so su kashe ka.. Ka fad’i duk abinda ka sani.. Na tabbata sentences d’inka bazai kai nasu ba.. Yusuf Maiyasa kake karesu.. Maiyasa ka zab’i ka biya laifinsu alhali su suna can suna ci gaba da b’arna.. Yusuf idan ka tab’a valuing aikin ka a matsayinka na jami’in tsaro zaka Fad’i gaskiya.. Yusuf wad’anda kake karewa bazasu tab’a k’yaleka ba koda kayi abinda suke so..” Ya d’anyi fasali yana dubansa Yusuf.. Su duka biyun duban juna suke, kafin Mu’azzam ya kuma daidaita zamansa yana fad’in “If you once valued our friendship zaka sanar dani abinda ka sani..”
Yasa hannu a aljihunsa ya ciro coin d’in Black African Team ya nunawa Yusuf yace “Tell me... What do you know about this..?”
Yusuf ya k’ura masa idanu yana kuma duban coin d’in kafin ya murmusa yace “Mai wann yake nufi..? Wann ai sisin kwabo ne..”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Black Africa Team.. Mai ka sani gameda wann Syndicate d’in..?”
Yusuf ya murmusa kad’an yana shafa hab’arsa sai kuma yace “I don’t know.. Ban Sani ba Mu’azzam.. Bansan wani Syndicate mai wann sunan ba.”
Mu’azzam ya kuma jinjina kai yace “Human Trafficking Syndicate.. But it’s been long destroyed.. Danger is somehow connected to that Syndicate.. Idan har kana aiki ma Danger, I’m quite certain zaka iya sanin wani abu gameda Balck African Team..”
Yusuf ya d’an sosa kunnensa kad’an yana Murmusawa.
Mu’azzam ya kuma tsaresa da idanu yana fad’in “For all time sake Yusuf.. Please do what is right..” Ya k’arashe yana duban Yusuf d’in cikin yanayi na ban tausayi.
Jikin Yusuf ya d’anyi sanyi, Dan shi kansa cin amanan abokansa da yayi sosai abin ke masa ciwo.. Ya d’ago yana duban Mu’azzam ga lokacin komawansa ciki yayi Dan har ganduroba d’in ya k’araso yana jira suyi rounding up.
Yusuf ya mik’e Mu’azzam ma ya mik’e yana girgiza kai “Please Yusuf, do this for our friendship.”
Yusuf na murmushi yake duban Mu’azzam d’in, cikin k’arfin hali yake danne hawayen dake k’ok’arin ciko idanunsa “What Friendship are talking about Mu’azzam.. Abotan da na lalata.. Abotan da bai mana rana ba..? Abotan da ya rikid’a ya koma k’iyayya.. Wann abotan kake magana akai..?”
Mu’azzam ya girgiza kai yace “Bansan dalilinka na cin amananmu ba Yusuf amma na sani you are not like them.. Kai ba kaman su bane.. You still have good in you.. Kar kabi abinda zuciyarka ke fad’a maka.. Kabi abinda mind d’inka yake sanar dakai.. Expose them Yusuf.. Kar ka bari suyi amfani dakai..”
Yusuf ya murmusa kad’an kafin yace “I guess circumstance na rayuwa yakan iya jefa bawa cikin k’addaran da bai tab’a tsammanin zai tsinci kansa ciki ba.. It’s too late Mu’azzam.. Na riga da na makara.. Kaje Mu’azzam, I’ve faith in you.. I know you’ll bring them down.. Nasan zaka kamasu zaka cimmasu watarana.. Sabida ka d’auko hanya..” Ya d’anyi fasali yana rok’on Ganduroban ya k’ara masa mintoci kafin ya dubi Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Zan fad’a maka wani abu guda d’aya.. Kaje ka nemo wanene BAT.. Idan ka cimma BAT ka samu kan K’umurcin da kaketa farauta..” Ya juya zai wuce Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in “Kana nufin Black African Team.. Shine BAT d’in..?”
Yusuf ya murmusa kad’an sai kuma ya girgiza kai yace “Bansan komai gameda wann Syndicate d’in ba.. BAT yana nufin Babbanmu A Tushe.. Ko kuma nace maka Boss At the Top.. Kaje ka nemo shi Mu’azzam.. Ka nemi BAT duk yanda ya shiga ya fita.. Idan ka kamo shi ka gama cin nasara.. May God be with you, Dear Friend..” Daga haka Sa kai yai ya shige Mu’azzam yabi bayansa da kallo.
Furzar da huci yai a hankali yana kuma juya coin d’in cikin hannunsa. A fili ya furta “BAT.!” ‘Is this another mission.?’ Zuciyarsa tai masa wann tambayar. A fili ya kuma furta “Where are you Danger..? Ni da kai ya kamata mu sake had’uwa..!” Ya k’arashe yana kuma juya coin d’in cikin hannunsa. Lokaci guda ya zira coin d’in cikin aljihunsa kafin yasa kai ya fice yana jin wayarsa na ruri. Ya d’aga yana amsa kiran Assad.
**
A sace Safeenah ta d’auki car keys Ta fice daga gidan dan dama Mommy ta mata kashedi Ta hanata fita ko k’ofa sann ta k’wace mabud’an motar ta. Saida ta tabbata Mommy ta Shige wanka kafin ta saci k’afa ta fice.
Bata zarce ko ina ba sai gidan Mu’azzam.
Patrick ya ganeta saidai da mamakinsa wann karon bata masa hauka ba. A mutunce ta masa magana harda cewa ba shiga zatayi ba sak’o tazo badawa ya shiga yai mata iso da uwar D’akinsa.
Patrick ya amsa mata kafin ya nufi cikin gidan.
Sadiya na tsaka da bacci taji ana knocking.. Ta mik’e tana mutsuka idanu lokaci guda tana duban agogon dake manne Parlorn, tana Mamakin yanda bacci ya saceta nan da nan gashi har ta jima tana bacci nan wajen. Gashi baccin ba wani mai dad’i tai ba, bacci ne da babu komai cikinsa face wasu irin mafarkai sarara marassa kan gado.. Gashi ta farka da wani irin azabebben ciwon kai.
Nan ta sinkayo Muryar Patrick yana kuma knocking. Da k’yar ta mik’e tana jin duk jikinta ya mata nauyi.. Ita sai lokacin ma take tuna yau ko azkar na bayan sallan Asuba bata samu tayi ba, duk hankalinta baya jikinta. Ta mik’e tana fad’in gata nan zuwa.
Haurawa sama tai Ta d’auko mayafi ta rufa kafin ta k’araso ta bud’e k’ofar.. Nan Patrick ke sanar da ita ana