Showing 135001 words to 136570 words out of 136570 words
da rai da lafiya ai goben karma yauce zakiga tazo ba wuya agurin Allah daga nan de suka cigaba da tattaunawa akan yanda lamarin ya faru da mahaifin su agidan sarauta ta wani bangaren sunji dadin jin inda yake ta wani bangaren kuma basuji dadi ba yanda yazamo bawa gashi ance baze yaba fitowa ba saide wani ikon Allahn hakade kowa da abun da yake ciwa sun kasa barin hirar kuma basu tashi daga wajen ba dan saleem ma cayayi baze je aikin ba yau yafasa fita basu bar wajen ba har saida akafafara kiraye kirayen sallar azhar suna gun azaune sunma manta da zasu dora abin ci rana saida sukaji kiran sallah sannan mama tacewa Azeema taje ta dora musu ko taliyace ita kuma bari taje tayi sallah shi kuma saleem ya tashi ya nufi masallaci nande kowa gakama gabansa,
_______________*bossay*
gaba dayan su babu wanda labarin be girgiza shi ba amma banda dadda da ita daman ba yau tafara jin irin wannan barazanar tasu ba,
hajiya ce tafara cewa to kinji shiyasa nace mufara sauraron sa yanzu gashi ba shida laifi aciki Ammi tace yana da laifi mana me yasa be sanar damu ba ko nikadai yasanar taya za ayi sugane ya sanar dani inde bada aljanu suke aikiba ai ba yanda za ayi su sani da da yafada ai da tuni mun magance yanda za ayi da ita yarinyar da tun aranar zansa adauko ta da bata shiga halin da tashiga ba yanzu,
Ammi kiyi hakuri wlh ina tsorone shiyasa ban fada miki amma kullum abun yana raina dan Allah ki fahince ni wlh babu komai araina cewar bossay dan Allah kuma ku gafar ceni yafada tare qarasawa kusa da Ameesha da ta durqushe agun tana faman kuka dan Ameesha kiyi hakuri ki gafar ceni ki fahimceni banyi komai dan ganin na cutar da rayuwar ki ko kadan bani da niyar yin hakan a cikin raina girgiza mishi kai tayi cikin kuka tace babu komai ni banga laifin ka ba bakai min komai ba ni daman na yarda dakai nasan bazaka taba cutar dani dan haka inde akain nane kabar damuwa rungumeta yayi sannan yace nagode nagode miki Ameesha Allah ya kareki daga sharrin su sannan ya sake ta ya qarasa kusa da dadda itama yabata hakuri fuskarta ba yabo ba fallasa tace nasan baza ka taba cutar damu ba shiyasa na yarda dakai tun farko kuma daman nasan hakan zata faru duk wanda suka ga nayi kusanci dashi sai sunsan yanda sukai suka rabani dashi shiyasa da suka gaya min bakin ku daya da farko har nafara tunanin ko kaine amma daga baya nagane bakai bane sunyi hakane kawai dan su shiga tsakanin mu muqi zuwa inda kake shiyasa ni kuma na amince daku amma yanzu komai ya wuce ka kwantar da hankalin ka tunda sukayi haka yanzu wasan namu ze fara tumda gaku nasan zaku taimakamin na cika burina tafada tana binsu da kallo daya bayan har ta sauke su akan sameer da yatafi tunani yana yiwa maganar bossay dalla dalla dan yanso yayi nazari sosai yagano wani abun game da maganganun bossay bema san tana kallon sa ba saida tace me jan kunne yasan da shi take dan haka sai kawai yadan kalleta kadan murmushin yake ta sakar masa sannan tace ka basai ka kaini gun hukuma ba ka gyara zan baku labari na saboda na yarda daku amma fa ba komai zan iya warware muku yanzuba kai ya daga mata kawai hankalin ta ta mayar ga sauran ma taga kowa ya ita ya zubawa ido suna jiran suji ta bakin ta,
sameer ne ya kalli bossay yace zamuyi magana dakai sannan kuma dole ka zafafa tunanin akan sanin waye na kusan kusan ka sai kaduba agaba daya wandan da kake tare dasu waye kukafi mu'amala dashi wanda har za ku iya hada alaka dashi kamar yanda yace tahakane kawai zamu iya gano ko waye saboda yayi maka magana me harshen damo nasan inde ka zauna ka nutsu zaka gano waye inma baka gane ba ni zanyi maka wasu tambayoyin in mun zauna kagane ko kai yadaga masa cike da gamsuwar maganar sa shettima ne yace nima abun da nake tunani kenan dole ma yakasan ce koma waye yasanshi din kamar yanda yafada sannan kuma kayi tunani tunda ka fara tunanin dauko sun ba da wanda ka zauna kayi maganar da shi ba wanda yasan zakaje ka dauko tan bakuyi maganar da kowa ba yanzu ba lokacin tunani bane cewar sam kawai zamuyi wannan maganar daga baya yanzu muna sauraron ki yafada yana kallon dadda dan murmushi tasaki da basu gane ma'anar sa ba itakadai tasan ma'anar abunta saboda dan tattaunawar dasukayi ita harta dan gano wani abu amma itama zata qara tunanin akai bayan tagama basu labarin dan gyaran murya tayi tare da gyara zamanta tana fuskan tar kowa,
duk shiru sukayi suna jiran jin tabakinta kowa ya qagu da yaji labarin.......✍
*YANDA LABARIN YAKE*
kamar yadda kukasani de ko ince nake gaya muku nice kakar khadija "khadija shine asalin sunan Ameesha wanda yayi daidai da sunanan sunan mu daya iyayenta suka saka mata Ameesha ba 'yar shigiya bace kuma ba 'yar tsuntuwa bace kamar yanda wasu suke tunani itama kuma take tunanin hakance saboda kinsanar da itan da nayi game da iyayen ta Ameesha jinina ce jikata tace nice na haifi mahaifiyar ta asalina ni 'yar garin damaturece a bagwadas nake dazama daga baya kuma aure ya dawo dani gombe saboda kasuwancin mijina tunda muke dashi Allah be bamu haihuwa ba ahaka muke rayuwar mu cikin kwanciyar hankali kuma muna da rufin asirin mu daidai gwargwado saide ba da mubiyu muke rayuwarmu daga ni sai shi muna cikin haka wataran kwatsam me gidana ya shigo min da wani kyakkyawan yaro cikin gidan dan da farko ma nazata aljanine dan qinyarda nayi da yaron saboda kyan shi saida gabaya malam yayi min bayani akansa sannan nayarda muka shiga cikin falo da yaron anan yake sanar dani cewa ankadai madai mahaifiyar sa ne abakin titi yana kan hanyarsa ta dawowa gida yaci karo da mutane antaru akanta yake tambayar me yafaru ake gaya masa ga mutumin da yakadaita yanzu za azo da motar asibiti atafi da ita yaron tunda yagansa sai ya makale masa yaqi yarda yaje gun kowa sai gurin shi ahaka har motar ra qaraso aka dauki matar inda yake tambayar inda matar da yaron suke wasu daga cikin mutanen suke suma basu san daga inda take ba kawai wayar gari sukayi suka ganta agun ita ba me hankaliba kuma ita ba mahaukaciya ba dan haka babu wanda yasanta alokacin da motar ta iso wajen me gidana ya mika musu yaron amma sai yaqi zuwa ya maqale masa daga nan kawai sai mutumin ya karbi number me gidana yaceze kirashi duk yanda akeciki ze sanar masa idan ta farfado sai yaje ya kaimata danta sannan aji daga inda take ahaka sukayi sallama saide kash ansamu matsalar tashin sanin mutumin a ina yake kuma shi me gidana beye azancin karbar number mutumin ba suka rabu tundaga ranar shiru shiru shiru muna tajira tsammanin kiran bawan Allahn nan amma be kira ba tun muna sa rai har mukazo muka cire rai da kiransa tunda daman bamu da 'da bamu taba haihuwa ba kawai sai muka cigaba da kula dashi tamlar dan da muka haifa da cikin mu haka muke bashi kulawa har yakai lokacin shiga makaran ta muka saka shi makaran tar masu kudi dan yafi samun ilimi sosai muhaka kwatsam sai ga ciki ajikina Allah yaban alokacin da muka gama cire rai da haihuwa amma sai gata ahaka muka cigaba rainon cikin har Allah ya saukeni lafiya muka haifi mace wacce muka saka mata suna NADEEYA, muka ci gaba da kula dasu gaba dayansu kamar yaran mu da suka taso sai suka taso da shakuwa me qarfi kullum suna tare suna manne da juna har suka girma inda alakacin yaron yagama makarantar sa har jami'a ita kuma lokacin ta gama primary tun lokacin muka fahimci dukkanin su basu da abokan rayuwa ita bata kula ko wane saurayi shima kuma baya kula mata duk da irin kyaun da yake dashi ga 'yan mata nata rububunshi amma shi kwata kwata basa gabansa har sukai wani minzali munyi munyi kuma akan kwannen su ya fito da wanda yake so ayi musu aure amma bawanda yayi ko yunqurima saide ma suce su basu samu wanda suke so hasalama ita nadeeya cewa takeyi ita bazatai aure ba ganin haka yasa muka yanke shawara ni dashi akan mu hada su aure kawai tunda sunqi fito da wadan da suke so sameer da bamu taba sanar dashi ko waye shiba sai lokacin muka sanar dashi asalin sa lokacin yasha kukansa muka bashi hakuri daganan kuma muka gaya masu abun da mukeso muyi duk bamusha wahala ba dukansu suka amince ba dau lokaciba muka daura musu aure duk da alokacin yafara samun kudinsa nakansa saboda be samu aiki ba sai me gidana ya dora shi kan harkar kasuwan ci akasuwa duk da yana da kudi kuma hakan be hana me gidan cigaba da yi musu hidima ba dan hatta gida ma shi ya siya masa sannan muka zuba musu komai duk abun da zasu bukata saida muka zuba musu acikin gida hatta abincima me gida nane yake ajiye musu ahaka suka fara rayuwar aure tun basa son junan su har suka fara so soyayya me qarfi ta shiga tsakanin su............✍