Showing 99001 words to 102000 words out of 136570 words

Chapter 34 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5439

yace ya qoshi tace me kaci yace ba komai tace to bana son musu maza dauki kaci ko kadan tea kawai ya iya sha yace mata ya isheshi rabuwa tayi dashi dan tasan halinsa idan ta takura masama ze iya tashi yayi tafiyar sa ita kuma bahaka take soba tana so taji damuwar sa kafin yatafin daukewa tayi da kanta sannaan ta mayar ta dawo sai ta zauna akusa dashi tace gayamin abun da hake damunka ko kaida momma ne ita tabata maka raine ko wanine duk tabi sai faman tambayoyi take jero masa kuma bata samu amsar ko daya ba sai cewa da yayi auntu ba komai kawai garinne banajin dadin sa wata kilma yau ko gobe zan koma, rarrashin shi tayi tare da bugar cikin sa tace dole akwai abun da yake damunka hakannan nasan baza ka tafi ba lokacin tafiyar ka beyiba saide kawai inbaka dauke ni matsayin uwa ba shiyasa bakai matsayin da zan iya sanin halin da kake ciki ba tafada tana miqewa tsaye da qoqarin barin wajen saide tambayar da yajefo matace ta hana ta cigaba da niyar tafiyar  datake yi juyowa tayi dan qara tabbatar da abun da kunnu wanta sukaji sannan bata bashi amsaba ta qara tanbayar sa da cewa magana kake me kace?

sarai yasan taji me yace amma sai yaqara cewa wace ce GIMBIYA SABREENA?

qara maimaita sunan tayi kamar ma batasan sunan ba zama tayi tana fuskan tarshi sannan tace a ina kasanta yace danasani ta ai bazan tambayeki ba tace to a ina kaji sunan nata yace aunty kawai nide kigaya min inzaki gaya min in kuma inje in tambayi papa nasan shi ai ze gaya min tunda ku ba kwaso kufada min dan numfasawa tayi sannan tace shikenan kwantar da hankalinka zan gaya maka nayi mamakin jin sunan abakin ka ne shiyasa kaji ina tambayar ka a ina kaji sunan ta yace ni ba a inda naji tace Allah ko to inbaji kayi ba ko gaya maka akayi  daga sama akayi maka wahahinsa kenan sannu dan baiwa
tafada tana kallonsa,

Qarar ringing din wayarsane ya katse su zarota yayi a aljihu sannan ya duba kan screen din wayar sunan my man yagani be daga ba harsaida kiran ya katse aka qara kira sannan akaro na biyu sannan yadaga tare da yin shiru daga can shettima yafara yin sallama shikuma ya amsa bayan sun gama gaisawa ne shettima ya dora dacewa kataho tundazu fa kai nake jira najika shiru gashi har shadaya ta kusa ahankali yace ganin tahowa anmaida ita tiata room a shirya komai ina zuwa farawa zanyi ba na son bata lokaci,
yace ok sai ka qaraso sannan sukayi sallama dubansa ya mayar ga auntyn tasa sannaan yace inajinki aunty shiru tayi sannan tace ai wannan  long story ne bazan iya baka shi yanzu ba kabari zansaka mana rana kafinde ka koma zan baka labari tunda ga A har Z kaga yanzu kaima jiranka akeyi ko jinjina kai yayi sannan yace eh jirana akeyi amma ai ba sauri nake ba kawai kibani yanzu ba matsala tace a'a ai nagaya maka labarine me tsawo kawai kaje tunda nace zan baka ai zan baka din yace to shikenan naji amma kiban dan aciki dafe kanta yayi tace oh ni karime dole de sai ansaka mutum abun da bayaso to abi biyu zan gaya maka daga nan kuma kar kasake tambayata wani abun ka yarda kai yadaga mata alamar eh ya yarda itakuma ta dora mishi da cewa GIMBIYA SABREENA kamar uwa take agare mu itace matar mahaifinmu tafarko itace uwargida sai mama fulani sannan mahaifiyar mu katsata yayi da cewa to yanzu tana ina ko ta mutu?
tace gaskiya tun muna yara mahaifiyar mu ta bamu labari tace mana anne meta an rasa tare da danta gaba daya su biyun ba a san inda suke har zuwa wannan lokacin suna raye ko sun mutu Allah masani ze qara magana kenan tayi saurin dakatar dashi tace kaje kawai banason wata tambayar zamuyi magana daga baya kamar yanda nagaya maka,

Shiru yayi bece mata komai amma qasan ransa taf yake da tambayoyi iri iri amma yazeyi dole yabari lokacin dace sannan yaci gaba dajin labarin mikewa yayi yace shikenan to aunty hakan ma nagode bari naje Sai naji kiran naki tace to shikenan sai anjima amma fa banason ta kuara yace ba halina bace ai kinsani yanda banaso a takurawa rayuwata nima banaso na kuma banaso na takurawa mutum yana kaiwa nan yasakai yafice daga sashe na,

yana fitowa ya qara shiga part dinshi yaje yadauko duk abun da yasan ze buqata a aikin sa wanda dole daman saida su tunda tundaga can ya taho dasu bayan yagama hada komai yafito daga sashen nasa yana fitowa kuma be qara zuwa ko ina ba yawuce parking space yana zuwa drivern sa yaqaraso wanjen da saurin sa sannan ya karbi jakar hannun sa tare da cewa yallabai naje na dauko motar tun dazu yace ok muje awaccen yanuna masa wata motar daban ba wacce suka fitaba jiya da sauri ya amsa da to tare da nufar inda take yabude yazarota daga ciji sanna ya daidaita ta hanya yafito ya bude masa yashiga ya. rufe yazagaya shima yashiga sannan yabawa motar wuta suka fice daga masarautar suka dau hanyar hospital din,

S.I.S spatial hospital,

yana gama parking ya fito ya bude masa saida yagama sha kamshinsa sannan ya zuro zara zaran qafafun sa sai kuna yaqarasa fitowa gaba dayansa cikin takunnan nasade da yasaba yanzuma shi yake yi driver na bayansa da jakar suna tafiya ana gaidashi amma hannun kawai yake iya daga musu wasuma basa samun damar daze daga musu hannun ahakade har suka qarasa office dinsa bayan sun shiga ya zauna drivern ya miqa masa jakar tare da juyawa yafice daga cikin office din yana fita kuma saiga dr.shettima yashigo bakinsa dauke da sallama amsa masa yayi ciki ciki wanda ina bakinsa ka kalla bama bazakace yayi magana ba zama yayi tare da miqa masa hannu sukayi musabaha sanna yayi masa barka da zuwa daganan kuma suka shiga tattaunawa akan aikin da za ayi mata bayan sungama a gurguje ya tashi yayi shirin shi tsaf nayin aikin daman already dr.shettima yariga da yagama shirya koma anmaida ita dakin daza ayi mata aikin kawai shi ake jira daman dan haka atare suka fito yana shine agaba shikuma shettima yana binsa abaya da kayan atare suka qarasa ciki yana shiga ya zuba mata ido nadan wasu dakiku kafin yajanye daga kanta yamaida kan shettima yace wanna yar qaramar yarinyar me ya haddasa mata brain trauma ko naji kuma kace ba accident tayiba me yafaru da ita shettima yace wlh nima bansani ba lokacinde dasuka kawota bani nakarbesu ba dr. Jamil ne nima sai daga baya nake jin hakan kuma ban taba tambayar su ba yace ok sannan ya matso masa da wani dan desk sannan yadora masa ka yayakin agefe komai de yana kusa da gadon nata saida ya tabbaatar da ba abun da ze bukata sannan yafita dan bashi wake yayi aikin sa yanda yakamata ba bata lokaci kuwa ya shiga yin aikin sa cikin kwarewa da qwazo yake yin sa kana gani yanda yakeyi kasan baqaramin kai bane tunwajen 12 yafara amma bashi yagama ba sai wajen biyu saura wayar sa yadauka yakira shettima yace yazo su maida ta dakin hutu yana gama gaya masa ya katse kiran,

Kayan jikin shi yafara ragewa sannan yafita daga dakin zuwa office dinsa yana shiga ya wuce bedroom dinsa na cikin office yana shiga yawuce bathroom yaqara yo wani wankan tare da dauro alwala ya wuce masallaci ahanyar dawowar sa suka hadu da shettima  tare suka shiga office din zama suka fara yi sannan shettima yace yanzu komai nml za su iya zuwa su ganta sameer yace eh amma de son samu subari sai gobe sannan ta dawo hayyacinta yanzu nayi mata allurai dole sai gobe ko zuwa cikin dare ma zata iya farkawa amma banda yanzu dr.shettima yaji dadi sosai yace to Alahamdulillah hakan ma yayi bari nasanar da yayan ta yace ok kawai sannan ya miqe yace zan dan kwanta ina bukatar hutu yana fada yaqarasa shiga dakin yabar sa agun be jira amsarsa ba,

ganin hakan yasa shi shima ya tashi ya fita ya nufi office din sa yana zuwa yatarar da saleem abakin office din nasa dasauri saleem yamiqa masa hannu suka gaisa,   

  shettima yace masa da ka shiga ai ka tsaya daga nan dan sosa kai yayi yace a'a doctor ba ayi haka ba gwara idan kana nan inshiga na kwankwasa naji shiru shiyasa natsaya anan najira dawowar ka harara ya watsa masa sannan yace to yayi kyau yana fada yashige ciki bayan shi yabiyo suka qarasa shiga tare zama sukayi sannan shettima yace albishirin ka da fara'ar sa yace goro doctor ai tunda naganka na fahimci kana cikin farin ciki bani nasha doctor,

wani kallo yayi mishi sanna yace meye hakan kuma wai bani nasha sai kace mace to saide in baka kaci qarewar kashs,

Dariya saleem yayi yace to bani naci din wlh autace ta koya min yace wace auta duk da yagane wa yake nufi amma sai ya basar saleem yace auta de danazo da ita ranar nan shima sai yace ok sannan yace Alahamdulillah tasamu lafiya har an gama yi mata dazu yanzu farkawar ta kawai muke jira cike da jin dadi tare da murna yace masha Allah Alahamdulillah Alahamdulillah Allah kaine abun godiya kai kai wlh baka ji yanda naji dadi ba aikwa bari inyiwa auta albishir daman kullum sai ta dame ni da tambayar ta to yaude zataji dadda dan labariyafada tare da dakko wayar sa daga aljihu ya lalabo number ta yakira tana daga wa yasa wayar a hands free tace hello yayana nakai na ya aiki yace Alahamdulillah albishi rinki tace goro yace fari ko ja tace fari kal kal yace wace kyauta zakiban idan kinji tace koma me kake so kaide kawai bani nasha na matsu inji tana cewa bani nasha yadaga kai suka hada ido da shettima sai kawai yayi dariya sannan yace auta Ameesha taji sauki har angma yimata aikin wata uwar qara tasaki tare da cewa dan Allah da gaske yaya yace zanmiki wasa ne da irin wannan maganar ta ce a'a wayyo Allah na dadi yaya bari intaho yanzu wlh dan na matsu inganta yace a'a kibari sai gobe sai muzo tare tace wlh yaya bazan iya ba duk yanda yaso yaganar da ita qin yarda tayi sai zuba take tana masa magana tana cewa yaya ai har na dakko hijabi ma yanzu zan fito jin hakan yasa dr.shettima kwace wayar daga hannun saleem tare da cire ta daga hands free ya kara akunnen sa lokacin tana cewa mama sai nadawo kimin addu'a hello yaya kanajina yace uhm jin duk dahaka bata gane waye ba saida yace bashi bane diff tayi ta hadiye maganar ta dan sarai tagane muryar waye yace auta kingane me magana dayan yayan kine karba nayi intaya shi baki hakuri kiyi hakuri kibari sai gobe kinji yar qanwata shiru tayi bata ce komai ba kwan kwasa qofa akayi hakan yasa saleem barin wajen dan zuwa yabude qofar,

Shikuma hakanne yabashi damar cewa ance kar kizo kinqi ji ko to bismillah maza kizo inajiran ki daman nasan danni zaki zo ko.......
[24/12, 9:15 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
                      By
            Yaya Azeema 😎

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                            

      Bismillah........

                            65&66

     """"""""""""""""""""""""""""""""""

"Shikuma hakanne yabashi damar cemata ance kar kizo amma kinqi ji ko to bismillah maza kizo inajiranki daman nasan danni zakizo ko?

Ɗan dakatawa yayi danjin amsar da zata bashi,

'ita kwa daga can bangare tanasa ne da ga mamakin sa saiji yayi tace dan Allah waye ni bangane me magana ba dan murmushin gefen baki yayi kafin yace shikenan sai kinzo inkinzo zakigane ko waye be jira amsar taba yayi rejecting kiran saboda da shigowar su saleem shi da wata nurse saleem yazaun ita kuma tana tsaye tace sir good evening yace fine tace sir daman ankawo wata patient ne za'ayi mata cs ammade yanzu tana labor room saboda ana tunanin zata iya haihuwa da kanta kuma haryanzu de bata haihu ba shine akace asanar dakai kazo kaga halin da take ciki yace gani nan daga nan ta juya ta tafita duban sa yamayar ga saleem sannan ya miqa mishi wayar sa ya miqe yace bari inje in dubata yana kaiwa nan yayi gaba saleem ma tashi yayi yabi bayansa suna fita kowa yayi nasa bangaren daban,

wayar saleem ce taqara yin ring yana dubawa yaga auta ce dagawa yayi tare da cewa autar mama kinde haqura da zancen zuwan ko tace ai har nakusa qarasowa ma shiyasa nakiraka in tambayeka a ina zan sameka kar nazo nai ta bilayi yace kai auta saifa danace kar kizo amma ba kyaji ko tace kayi hakuri yaya wlh bazan iya hakura bane yace to ai shikenan sai kin qaraso din daga nan ya kashe wayar yaqarasa gurin da office dinsa yake zedan qarasa wani aiki kafin ta qaraso din,

Tana shigowa taqara ciro waya tana qoqarin kiranshi karaf idon ta yafada akansa da batai zaton ganinsa ba yanzu batare da tabari yagan taba tayi saurin buya awani dan lungu tana leqensa harsaida ta dena ganin sa sannan ta fita tana sauke ajiyar zuciya tana cewa Allah ya soni be ganni ba da nashiga uku wlh ya takurawa rayuwata faga haduwa yabi yasakamin ido mstwww taja tsaki,

Saide abun da bata saniba tuni yariga da yaganta kawai ya rabu da itane saboda aikin da yakeyi bashi da lokacin ta office dinsa ya koma yadauko wani dan qaramin box ba dadewa yadawo lokacin da yaqara dawowa ita kuma har takira saleem yazo suntafi office dinsa gurin yakalla yaga bata nan kawai ya wuce yaje yaci gaba da aikin sa,

Yaya nifa ba zama nazo yiba kazo muje naganta na wuce gida yace to aide duk gaggawar asara ai tajira samu sai kijira in qarasa abun danake tukunna kuma  doctor  din ma ya Shiga aiki sai yafito zakije tace,  "waye"? tsoron ta kawai kar acemata wannan mutumin da bata qaunar haduwa dashi,

Amsa mata yayi da cewa dr.shettima mana wanda kika zauna agurin sa ranan "ok" kawai tace
sunan ta qara maimai tawa aranta itabata ma san sunan saba sai yau tabe baki tayi alamar sunan be mata ba, kallonta saleem yayi yace me kike tunanine haka kai ta girgiza tace ba komai kawai ina tuna yanda mukai rayuwa da Ameesha Allah ya tashi kafadun ta Allah yasa mu dawo yanda muke ni yaya wlh dama su dawo gidan mu ko ya kagani banaso tayi min nisa nafiso kullum mukasan ce tare nayi missing dinta sosai taqara sa maganar muryarta ciki da rauni kamar zatayi kuka kallon ta yayi yace Allah sarki ai in Allah ya yarda gobe iyanzu kuna tare zakiganta har sai kingaji tace wlh yaya bazan gaji da ganin besty naba nafiso ma kullum muna tare da juna,
To yaza ayi kinga yanzu sun riga sun dauke su ba yanda za ayi muzo muce subamu ita ina ganin basu iyaba bamuba tace hakane yaya amma ni ina ganin mugwada tambaya amma sai komai ya daidai ta tasamu lafiya sosai ni sai in fara yimata maganar ma kafin  maganar taje sama nasan idan ta amince komai zezo da sauki yace to Allah yasa nima zanso hakan kinga ma qara cika gidan tace eh wlh tafada sai faman murmushi takeyi kamar zancen ya tabbata haka suka ci gaba da tattaunawa har wajen la'asar sannan yace mata bari yaje yayi sallah daga nan ze duba idan yagama sai yazo suje tace shikenan sai yadawo yana fita ta qara gyara zama saboda ba sallah zatayi ba wayar ta dauko qirar hauwie y 6 da saleem yasiya mata tun satin baya da yasamu wasu kudi daman yayi mata alkawari dan haka yana samu ya siya mata gallery ta shiga ta bude wata folder ta shiga ta qurawa wasu hotuna ido tana kalla ahankali ta shiga shafa hoton da hannun ta tare da manna masa kiss ahankali tace ina sonka ina sonka ina sonka a kowacce rana sonka qaruwa yake a cikin zuciya ta narasa yazanyi da son wanda besan da zamana ba aduniyar nan sonka kaddara ce agare ni ina azabtuwa da sonka  a ina zangan ka awace duniyar kake  mutun ne kai ko aljani bansani ba Allah yabayyana min kai a gaske ko sau dayane arayuwata nasan zan samu sassaucin radadin da nake ji araina duk da nasan hakan baza ta taba faruwa ba wanda yake awata duniyar daban dabansan ta ba ta ina zamu taba haduwa lumshe idonta tayi sai hawaye kuma hannu tasa ta share tana qarajin radadi a zuciyar ta  kamar yanda tasaba aduk lokacin da ta zauna irin wannan tunanin akan wannan bawan Allahn da bansamu damar ganin fuskar shiba  kwanatar da kanta tayi akan hannun kujerar  tare da manna wayar akan kirjinta tana rungumeta kamar me rungumar mutum ita kadai tasan abun da take ji aranta,

A wannan yanayin saleem ya shigo ya tarar da ita mamaki ne yakama sa ganin qanwar tasa ahaka sunan ta yakira amma shiru bata amsa ba hannu yasa ze karbi wayar hannunta firgigit tayi ta dawo hayyacin ta tare da qara damqe wayar a hannun ta kollonta yashiga yi cike da mamakin ta sai yace auta lafiyar ki lau kuwa me yake damun ki saurin kawar da damuwar ta tayi dan kar yagane halin da take ciki amma ina duk yanda taso hakan ya gagareta budar baki tayi da niyar cemishi ba komai amma kawai sai hawayen da take ruqewa suka shiga sauko mata da sauri yanzauna kusa da ita yace subhanallahi auta wai meke faruwa me kika gani awayar ban muga hannu yasa ze karbe yagani,
ganin hakan yasata saurin sakin wayar aqasa  saboda hakane kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login