Showing 48001 words to 51000 words out of 136570 words
sai ki ka buya ainasan halinki sarai kawai rabuwa nayi dake jikin ki yaga miki ni naso ma kindawo wani sashen jikin naki aballe da ma sun karkar yaki da sun burge ni wlh tana gama fadar haka tacqara daga bulalar zata zuba mata aikwa ta kwasa aguje tayi qofar gida tana kuka dadda taja tsaki ta koma daki tana cewa gwara da sukai miki hakan dan kinga ina lallabaki shiyasa kike min iskancin da kika ga daman to muzuba nida ke sha shasha kawai wacce bata da zuciya
Ameesha nafita tasamu waje tazauna taci gaba da kukanta sai yanzu take kewar iyayen ta Allah sarki tasan da suna nan da bazasu taba yi mata haka ba amma yanzu gashi ba me rarrashin ta saitaji gaba daya kamar duniyar ta juya mata baya ba me kula da ita haka taci gaba da kukanta gwanin ban tausayi kamar wacce tarasa gata gaba daya yau daya dan dadda ta dake ta shine take ganin kamar ma kowa ya tsane ta tana cikin kukan taji tsayiwar mutum agaban ta tazata dadda ce tazo ta lallasheta ta bata hakuri shiyasa taqi dagowa sai da taji andafa ta sannan sannan ta dago idon ta sai tai tozali da..........
Allah sarki yau ga yar shalelen dadda awaje dadda ta rufe ido ta dumama mata jikin ta da bulala 😂
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
By
Yaya Azeema 😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Ya ubangiji ka karemu mugunji mugun gani tsatsayi da asara fatara talauci annuba cin bashi gulmar mutane manufurci da duk wan abun da babu kyau Allah ya karemu daga aikatasu Allah ganar damu gaskiya duk abun da yaahige mana gaba Allah ya haskaka mana shi Allah ya dora mu ahanya madede ciya Allah yasa mudace duniya da lahira Ameen*
Bismillah.......
28&30
Ɗagowar da zatayi idanun ta suka sauka akan Azeema dake tsaye akanta.
Da sauri tamike tare da dan waro ido sai kuma tadago zara zaran kyawawan yatsunta fari tas kamar ka dauka kadawo dashi jikin ka ta dora akan kyakykyawar fuskarta tashiga goge hawayen da suke zubowa suna wanke mata kan lausassan kumatunta sai yanzuma ta tuna, Ashefa zata je gidan su tama manta gaba ɗaya wlh......
Bata gama tunanin ba Azeema da tun dazu ta zubamata ido takasa magana dan tana tsoron taji abun da zata fada mata dan ita tunaninta ya bata ko Dadda ce ta rasu...
Adan kidime tace subhanallahi kimin bayani wai meke faruwa me akai miki ne kike irin wannan kukan haka? ci-gaba tayi da kukanta taqi bata amsa tambayar duniya Azeema tayi mata amma taqi bata amsa da taga haka kawai sai ta ruqo hannun ta tana janta zuwa cikin gidan.
Suna shiga bataga alamar komai ba daze nuna mata cewa mutuwa akai saboda ba kowa sallama tayi taji shiru ta qarayi nanma shiru sai da tayi ta uku sannan Dadda ta amsa daga cikin dakin sannan tace "ku koma inda kuka fito idan tagama haukan nata kwashigo sai yanzu Azeema tagane abune ya hadasu da dadda ya akai yau aka gansu a rana ita da jikar tata jinjina kai tayi tace besty me yahadaku da Dadda yau naganku arana wane zunubin kika aikata mata harta kaiki ga fita waje kina kuka?
Yanzu ma de banza tayi mata bata ce mata komai ba saide yanzu ta dena kukan sai faman ajiyar zuciya take saukewa na irin wanda yaci kuka ya koshi ganin bata da niyar yin magana yasata qara jan hannu ta suka qarasa shigowa har bakin qofar dakin sannan tace Dadda mushigo. tace "Da ni na hanaku shigowa ne nacede kar ta shigo min daki da kuka dan wlh zan qara ɓata mata rai banaso sakarcin banza.
Azeema ta dan kalli Ameesha da sai faman sauke ajiyar zuciya take sannan tace Dadda bakijita ba ai tayi shiru.
Dadda tace "bismillah zaku iya shigowa riqe da hannuta suka shiga ciki Ameesha na bayan Azeema tana ta faman rarrakubewa tana sunkuyar da kai taqi yarda su hada ido da Dadda.
Azeema nagama shiga ta tsugunna ta gaishe da Dadda da ta amsa mata taci gaba da cin fanken ta da ta soya musu tana ci tana korawa da ruwan bunu amma yaji kayan kamshi fuska adaure dadda ta amsa mata shiru dakin ya dauka na wasu 'yan dakiku sannan Azeema tace Dadda wai me ya hadaki da yar shalelen taki yau?
Dadda tace "Ni ba ruwana tagaya miki inda taje da bakin ta qara tambayar ta tayi saida ta jima sannan tagaya mata amma bata fadi abun daya faru ba tsakaninta da Rasheeda kawai tagaya mata fitar ta da kuma buyan datayi sannan ta shiga cikin gidan sai kuma tayi shiru tana tunanin tagaya musu gsky ko tayi shiru wata zuciyar tace kifadi gsky kar kizo ki qara shiga damuwa da wannan tunanin na zuciyarta ta aminta dan haka kawai sai ta kwashe duk wani abu da ya wakana tagaya musu bata rage komai ba sai ta dorawa Azeema dace wa bayan ta dawo kuma Dadda ta qara yimata shegen duka..!
Da sauri Dadda ta shiga tafa hannu ta a cewa nashiga uku sharri kuma zakimin dan dukan danayi miki gida biyu shima bame yawa ba shine zaki ce namiki dukan tsiya to bari na qara miki sai kifi jin dadin bada labarin ta fada tana qoqarin tashi Azeema ce tayi saurin dakatar da ita tana bata hakuri komawa tayi ta zauna tace wlh sai mun fara sa qafar wando daya dake tunda rashin mutuncin naki kullum gaba yake bakya yin hankali idan bakida zuciya ma yanda sukai miki dukan kwanaki ko wani yace ki koama ai kyace baza kiba amma da qafar ki kika koma gidan wai harda buya dan kinganni ko Allah yaqara ai naso wlh suyi miki dukan da sai kin zauna jinya inyaso sai kidena zuwar musu gida.
Azeema ce ta ari bakinta taci mata albasa tace Dadda kiyi hakuri dan Allah nasan ai daga yanzu baza tasake komawa ba kuma kinji ma ai ba gurinsu taje ba Dadda tace ai koma gurin uban wa taje aide cikin gidansu taje tace kinsan yarinya ce saikin mata uzuri sai a hankali zata ringa gane abin da kike nusanda ita,
Dadda tace ni ina ruwana tama ci gaba ai jikinta ne zegaya mata itade Ameesha yau baki ya mutu ba bakin magana takasa cewa komai sai dana sanin fitar datayi take da taji maganar Dadda da hakan duk bata faruba.
Dadda data gama cin abincin ta ta tashi tafita da kwanan tana fita Azeema tajuyo tace ke wai da gaske ne abun da naji kince tashi zakuyi da wasade kike ko? Tace mata wlh da gaske nake daman nima niyata ina dawowa daga gidan nasu inzo gidanku dan canai ma wuni zanyi saboda sai dare zezo daukar mu sai kuma gashi kinzo cike da mamaki Azeema tace nashigan gadi amma wlh baki da mutun ci yanzu kinsan zaku tashin shine sai yau zaki gayamin daman haka zaman tare yace Ameesha tace wlh bahaka bane nima bansan da tashin ba sai jiya da daddare suka zo nikuma kinga ba wayace dani bare inkiraki.
Allah sarki Azeema akwai saurin kuka kawai sai ga ta tana hawaye tace wlh besty banji dadi ba wlh yanzu tafiya zakiyi ki barni shikenan nadena ganinki.
Itama cikin raurau da murya tana shirin fara nata kukan tashiga gogewa bestyn tata hawayen sannan tace habade zan ringa zuwa akai akai ma saboda duk sanda yaya Bossay zezo zanbiyo shi yasaukeni in yadawo sai ya dauke ni mutafi gida kuma koma banzo ba kullum fa zamu na haduwa a makaranta dan zance mishi yabarni anan basai ya canzan makaranta ba tace yauwa har na danji sanyi wlh amma wai ya akai ma zaku koma gidansu ya akai haka ta faru?
Zaman ta ta gyara sannan ta fara bata labarin duk yanda sukayi, tace gasky na taya ki murna Allah yasa qarshen wahalar ku kenan Allah yasa zaman can alkahairi ne agare ku tace Ameen de besty suna haka Dadda ta kawo musu nasu karin kumallon tace gashi nan idan mutum yaga dama yaci inbega dama ba kuma yazauna da ciki badamuwa ta bace,
Ɗan murmushi Azeema tayi tace haba Dadda abun har ya akai haka ke da zakizo ki bata abaki taci ta qoshi amma zakice mata haka Dadda tace ta mutu bata ciba Azeema tace to ai shikenan Dadda, yauwa Dadda ashe tashi zakuyi to Allah yasanya alkhairi Allah yasa kuje a sa'a wlh na taya ku murna sannan ta dora da cewa muma abun farin cikine yasamemu wlh jiya shine dalilin zuwana gidan nan yanzu...
Ameesha cike da zumudin abun da ya faru tace besty me yafaru dan Allah gaya mana da sauri na matsu inji saida ta ɗanyi dariya sannan tace wlh yaya saleem yasamu aiki awannan babban hospital din S.A.S spatial hospital baki bude cike da murna Ameesha tace dan Allah da gaske kike besty tace mata to zanmiki wasa ne kinsan yana ta nema besamu ba sai jiya aka dauke shi gobe ma ze fara zuwa taqarasa fada tana dan dariya daganin yanda Ameesha duk tabi ta kiɗime kamar ba itace me kukan mutuwa ba.
Cike da zumuɗi Ameesha tace "besty tashi mutafi inyiwa yaya saleem Allah sanya alkhairi tace kin manta me yafaru dake yanzu ko? amma tambayi Dadda inta barki sai muje satar kallon Dadda tayi aikwa karaf idonta ya hadu da nata da sauri tajanye tayi qasa da kanta.
Dadda aranta tayi dariya tace almura ashe kina da kunya basarwa tayi kamar batasan me yafaruba tace kicewa mamanki ina taya ku murna Allah yasa albarka, tace Ameen Dadda daga nan Dadda tayi shiru bata qara tanka musu ba.
Ameesha de duk tasha jinin jikinta tanaso tayiwa Daddar magana amma batasan ta yanda zatayi mata ba Azeema ce ta taba Ameesha ganin ta tafi duniyar tunani tace kinga yanzu kici abincin inkingama sai kiyi wanka kizo kibawa Dadda hakuri ki tambaye ta idan ta barki sai mutafi ko daga mata kai tayi sannan tafara ci tacewa besty kisa hannu muci tace mata wlh ta qoshi kafin tafito takarya bata ta kura mata ba akan sai taci sai tayi shiru taci gaba da cin fankenta daga nan kuma bawanda yaqara cewa komai ba kowa da abun da yake tunanin har tagama ta mike tafita da kwanon sannan tadawo ta daura zanin wanka taqara fita ta dau bokiti ta debi ruwa tashiga wanka.
Azeema ta kalli Dadda tace Dadda dan Allah kibarta mutafi tare nima zanso hakan tunda kinga daga yau bazamu sake zama irin haka ba kibarmu muwuni yau daya de Dadda tace ba komai kuje mana amma karki gaya mata sonake ta tambaya da kanta dariya tayi tace to Dadda hakan ma mun gode.
Bata dade ba ta shigo dakin har ta gama wankan, shirya wa tayi shaf shaf sannan ta koma kusa da Azeema tace to besty nagama ki tambayeta mutafi kallon ta tayi itama murya qasa qasa sannan tace ki tambayeta da kanki sai tafi yarda zaro ido tayi tace nifa gasky bazan iyaba tace to shikenan sai ki hakura da zuwan hade rai tayi ita adole haushin Dadda take ji dan haka bazatayi mata magana gefe ta koma ta zauna tana ta faman hade rai kuma taqi cewa komai itafa taba tunani saide ta hakura da zuwan dade ace sai ta tambaye ta dan ayau batayi niyar yi mata magana ba kuma idan ta zauna har Azeema ta tafi gidan ba dadin shi zataji ba to yanzu yazatayi meye mafita......
**********************
*MASARAUTA*
Suna qarasawa bakin sashen dogaren suka tsaya daga waje shikuma ya shiga shikadai yana shiga bega kowa a falo ba dan haka Sai yasamu kan wata luntsume miyar hadaddiyar kayatacciyar kujera data gaji da kyau ga ado da akayi mata ita ba irin saraun kugerun falon bane an banbantasu da sauran duk da suma ba baya bane agun kyau din amma ita ta kere musu,
Zama yayi yana zama kuma jakadiya ta taho da hanazarin ta taqaraso gaban sa ta gurfane tana kwasar gaisuwa zata fara yi masa kirari kamar yanda ta saba saboda itace amintacciyar baiwar fulani shekaru da shekaru hannu yadaga mata dan yau baya buqatar jinsu tana gama wa tashi tace bari asanar da gimbiyar tafada tana nufar wajen corridorn da ze sada ta da dakin fulanin,
Tana zuwa ta dakata tare da dan danna belt din dake gefe hakan yasa wadanda suke cikin dakin taji ance meke tafe dakai? tace daman nazo insanar dake cewa me martaba ya qaraso yana falo yana jira tana gama fadar haka tabar wajen saboda tasan ba amsa zata samuba kuma hakance ta faru ba ace komai ba tana fitowa tace sarkin sarakai kuma daya tamkar da dubu kai sarki dan sarki kuma uban sarki kakan sarki in Allah ya yarda Allah yaqara maka lafiya da tsawon kwana Allah ya tsare gabanka da bayanka ya kare gabas da yamma kudu da arewa sama da qasa.
Shide yanzu be hanata ba har tagama sannan ta qara tsugunnawa ta gaidashi sannan ta tashi ta koma inda tafito tana fita kwa saiga sarki Muhammad SAMEER me murabus wanda yanzu suke kiranshi da PAPA, qarasowa yayi tunda yafito yake sakin qayataccen murmushi da ya lullube kan kyayyawar fuskarsa duk da ya tsufa amma kyanshi yana nan ba inda yatafi kuma kana ganin shi tun atafiyar sa zaka gane shidinfa jinin sarauta ne gaba da baya sarauta tabi sassa da gabobi da lungu da sako najikin shi dan jinin yabi ko ina da ina.
Yana qarasowa yazauna yana kallon ɗan nasa yace a'a Allah ja da ran sarkin mu ya qoqari ya fama da jama'a ana wahala ko?
Sarki yace "Papa ai rabin qoqarin ma ai ku kukeyi ni kadan ne nawa ni wallahi ma yan kwanakin nan nagaji da sarautar nan gaba daya bana jin dadin jikina gyara zama yayi sannan yace wai Papa dan Allah wai ba ayin murabus kafin lokaci ya ciki danni wlh nagaji daman nifa tunda ma bason wannan sarautar nake ba bansan ma ya akayi na karba ba ya gama fada da iya gaskiyar sa maganar har cikin ransa yafada.
Dariya Papa yayi yace "Kai yanzu Deeni banda abinka a ina kataba ji anyi murabus lokaci beyi ba ai abu uku zuwa hudune suke sa mutum ya sauka daga kan kujera lokacin saukar su beyi ba saide ko in mutuwa ko rashin lafiyar da mutum baze qara iya komai ba ko ka aikata wani gagarumin lafin da zesa asauke ka amma banda haka ba abun dazesa ka ajiye sarauta hakan nan dole sai lokacin murabus yayi,
Papa nagama rufe baki sarki yaqara cewa to kawai insauka sai agayawa mutane bani da lfy nikuma sai in fita qasar waje kaga ba wanda zeyi magana akai ko, papa wata dariyar yayi sannan yace Allah sarki lalle bakaso din nayarda amma ba me goya ma bayan yin hakan nima lokacin da nayi tawa baso nake ba haka akayi min dole nayi har nayi murabus na baka kaima kuma ba yarda zakayi dole kayi hakuri kaci gaba dayi kai da bakai kadai bama kake gudanar da mulkin ba, ga gyatumar ka tana taya ka ita sarauta da mulki sai kayi hakuri kuma saika tsaya tsayin daka domin Allah ne yabaka kuma anaso kayi adalci aciki saboda rana gobe kiyama Allah sai ya.....
Fulani ce ta katsesu da cewa to hirar ta isa haka tayi hakane saboda batason yafara yi mishi nasihar da har zatakai cikin zuciyar sa ta canza mishi tunani akan yarda ta dora shi daman kuma tasaba yi mishi haka duk sanda taji su zefara yimishi wata hirar daban ko yayi mishi gyara akan wani abun da yake ba daidai ba to zatai saurin dakatar dashi.
Guri tasamu tazauna itama, Sarki ne yafara gaishe da ita fuskar ta adan tsuke tace mishi me yakawo ka nan har kuka zauna kuna hirar da ta dace da warda ma bata dace ba,
Sarki yana zaune ya dan kishingida kansa da majinginar kujerar da yake kai yana lumshe ido bece mata komai ba dan shima nashi mulkin yake ji da shi saida yagama shan qamshinsa kamar ma ba agaban ta yake ba sannan ahankali yace daman nazo mugai sane sai kuma dawowar me sunan baba yace min wani satin ze dawo insanar daku, Fulani tace gashi ubanka ko yana dan cikin ka amma shi ze aikoka ko kunya bakaji ba harda debo qafa kazo fada mana shiga dan rainin hankali yafi qarfin yakira mu yagaya mana to kar yadawo ifiritun yaro kawai kwata kwata yaron nan bashida ta ido baya ganin kowa da gashi ni wlh kace mishi kar yadawo yai zanmansa acan har yagama rayuwarsa bama bukatar sa,
Papa ne yayi dariya yace inke bakya bukatar sa ai iyayen sa suna bukatar sa hade rai ta qara yi tace to nide idan ma yadawo kar yasake yazo inda nake kar naga qeyarshi a sashena ya koma can wajen uwarsa dan baze qara zamar min a part dina dan ban manta abun dayayi min ba kafin yatafi, gaba dayan su dariya sukayi mata sarki yace nima daman bacewa yayi ingaya muku ba ni kadai yagaya wa kuma bece ingaya kowa ba shine naga ya dace ingaya muku danna san halinshi baze gaya wa kowa ba shiyasa nafada muku sai a tarbeshi,
Fulani tace wlh ba abun da zan mishi dan intanice ma ko airport ma baza aje dakko shiba saide ya hau motar haya,
Papa yace Allah ya tsare shi da hawa motar haya bawanda yataba haka