Showing 69001 words to 72000 words out of 136570 words
inda Baba yake yana kusa da qofa duk yana jin abun da yake faruwa kuma yaji dadin hakan yasan ko ba komai zasu dan samu sauqi,
Bude shi yayi sannan yace Baba fito mukoma nawa dakin sannan kaga yanda nayi da wadan can shedanun murmushi Baba yayi yace ai duk inajinku amma na jinjinawa qarfin halinka yanzu baka tsoron wani abun yabiyo baya yace baba kar kadamu koma me ze faru ya faru a shirye nake yana fadar haka yayi gaba yace baba shiga bari indebo ruwa awaje,
"To" Kawai Baba hace amma baya tunanin ze iya shiga ciki shikadai dan haryanzu a tsorace yake dasu dan haka sai yaja burki abakin qofa yana jiran dawowar sa sai sushiga tare amma shikam bada shiba baze shiga ba suje su huce akansa,
yana gurin Hamza ya dawo gurin da ruwa a hannun sa yace Baba yanaga ka tsaya anan baka shiga baba yayi murmushi yace yaro kai naked jira mushiga dan bazan iya shiga ba nikadai saboda tsaro shiyasa najira ka,
Shima hamzan murmushi yayi kawai yace to mushiga aranshi kuma yace Allah sarki Baba tsoro yake ji kenan...
Suna shiga hamza ya nufi inda shugabansu yake memakon ya yayyafa masa ruwan kawai sai ya juye masa duka akan fuskar sa arazane shugabansu ya tashi yana sauke ajiyar zuciya tare da cewa dan Allah kayi hakuri wlh zanje infada mata gaskiya kaimin rai kar ka kasheni dan Allah na roqe ka..!
Baba saura qiris ya yi dariya amma sai ya hadiye abarsa wai mutumin da yake daka musu tsawa yana musu fada da fadar abun da duk yaga dama amma shine yanzu yake magiya da roqon ayi hakuri to duk ina cika bakin?
Hamza ne yace yaza ayi da inkashe ka saide idan kamin taurin kai to shine zan aika ka barzahu dan haka yanzu zan kafa maka sharadai idan kabi mu zauna lafiya idan kuma kayimin taurin kai kasan sauran gyada kai shugabansu yayi sannan yace na yarda koma me kake so zanyi maka shi kafada kawai.
Girgiza kai hamza yayi sannan yace good man haka nake son ji ashe zamuje da kai abun da nake so dakai shine na farko zakaje ka warware abun da ka kulla sannan zaka bamu hakuri agaban mutane zaka durqusa ka nemi yafiyar mu agaban kowa da kowa sannan daga yau duk inda kaga Baba ka gaidashi kar kasake yimishi kallon banza ko ka hantare shi ko tsawa duk ranar da hakan tafaru sai nayi tsiranka kai bama mukadai ba daga yau banaso na qara jin wani yace kayi mishi sharri akan abun da be aikata ba kace yayi wlh inna kamaka da hakan bawanda zesan lokacin da zan dauke ka incanza maka kamanni, abun na qarshe kuma ko da wasa kar kai gigin gayawa wani abun da naimaka yanzu zamu zauna tare daku anan harsai kowa yaji sauke sannan zaku fita kuma gaba dayanku kuma banyarda wani yanuna alamar anmasa wani abun ba kufita kuciga ba da yanda kuke ina fatan kowa yaji abun da nace yafada yana juyawa yana kallon sauran da sauri suka amsa masa da eh munji kuma zamu kiyaye ya karkada kai tare dacewa good haka akeso dayan dogarinne ya kalli shugabansu yace amma ka cuce mu wlh sai na rama akanka daman kasan duk wannan abun da ka fada qarya kake.!
Me dorina ne ya dora dacewa nima abun da nake so nace kenan wlh ka kuka da kanka idan kowa yasan qarya kake sharri kayi musu ba zakaji dadi ba dan har uwar masarauta ma da take goya maka baya yanzu sai ka karbi hukunci idan ni kwa akasa in hukunta ka to kasani sai na sauke duk dukan da kasa akai min banjiba bangani ba dayan ma yace ai tare zamuyi daman nima haushin shi nake ji tun ba yauba ni banma san me yasa akabashi shugaban muba,
Me dorina yace yana zuwa yana kai qarya da gaskiya yana neman gindin zama ba dole yasamu fada ba awajenta mana abashi shugaba alhalin be cancanta ba.
Shide shugabansu be kula kowannen suba shi babban tashin hanakalin sa shine ta yanda ze tunkari Fulani da zence qara ne maganar da yagaya mata sharri yayi musu besan ta inda ze fara ba inbe fada ba kuma wannan me qarfin dokin yace ze kashe shi to yazeyi inde yana son ransa dole yayi masa abun da yake so in kuma bayaso yaqi fada shikwa yaza ayi yazabi mutuwa akan ya fada da haka ze fada saide yasan kashinsa ya bushe qarshen sa yazo kowa yanzu ze dena yarda dashi sannan uwar masarauta baza ta qara yarda ya rabeta bama bare yafada mata wata magana tayarda,
Hamza ne ya katsesu da cewa kunga ni kuncikani da surutu daya yaje ya debo ruwa kuzo ku wanwanke fuskar ku sannan kowa yamaida abun kansa ya nada sannan kugoge quarar jikin ku da ruwa ku saita fuskar ku yanda de ba wanda ze ganku yace wani abun yafaru da ku kungane ko dukansu sukace eh mungane yace to daya yaje saura kuma yabata min lokaci inyi maganin sa da sauri me dorina ya mike yafita da sauri yadauki boket din da hamza ya ajiye bayan ya watsawa shugabansu,
Be dauki lokaciba yadawo ahakanma kuma saida ya fara tsayawa ya shirya kansa tsab kamar ba abun da yafaru dashi saboda acewar sa ai daman ko bece musu kar sunnuna wani abuba daman baza sununa ba saboda duk wanda yaji ai saiyayi musu dariya ace kamarsu suka tsaya akayi musu wannan dukan dan haka saida ya tabbatar yayi need need sannan yadawo yana zuwa ya ajiye musu kowa yatashi,
Shide shugansu da qyar ya iya mikewa saboda ko wace gaba ta jikinshi ciwo suke mishi ahaka yafara shiryawa shima tare da maida madaurin sa sannan suka goge kayansu da suka baci da qasa saboda ba falasta a qasan dakin bayan sungama hamza yabisu da kallo daya bayan daya ya tabbatar da ba me ganewa wani abun yafa ru dasu sannan yacewa su me dorina sujashi sukaishi hargaban tsohuwar nan danshifa baze iya kiranta da kowane suna ba inba tsohuwa ba ko tsohuwar banza haka yake cemata daman tun ba yau ba saboda daman jininsu be haduba tunfarkon zuwanshi gidan yaji batai mishi ba sam.
Yace kusahsi agaba kuje sannan kuce yafada mata abun da kukaji yana cewa bayan kungama dukanmu munsuma kunje debo ruwa kuka dawo kukaji yana cewa shi ai duk yanda zesa adaki mutum yasani saida ya gargade mu amma mukaqi ji yanzu gashinan ya mana sharrin da ba mu isa nucire kanmu aciki ba watakil ma akshe mu da kukaji haka sai kuka tambaye shi maganar da kukaji yanayi gaskyace ko qaraya yaqar tabbatar muku da qarya yake sai kukaga hakan be dace ba shiyasa kukawo shi domin ayanke mishi hukuncin qaryar dayayi kuma kuce munsuma ko ruwan ma baku watsa mana ba muna can asume Allah yasama bamu mutuba, kungane me naked nufi de kuyi duk yanda zakuyi ku nuna mata ku kuka jishi da kunnen ku ba wani yafada mukuba inkukayi haka shikenan bani ba ku,
Dukan su amsawa sukayi da angama inde wannan ne baka da matsala da hakan yace zaku iya tafiya ruqeshi sukayi daya yaruqe gefen sa dayan ma ya ruqe gefe haka saka sakashi a tsakiya suka fita dashi zasukaishi wajen uwar masarauta.....✍🏿
*Follow me all👇*
Facebook @Azeema dahiru(xeemat)
Arewabooks@azeemadahiru
WhatsApp @Yaya Azeema
Wattpad@xeemat
My WhatsApp number 08124226526
#comment
#share
#likes
#vote
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
By
Yaya Azeema 😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
Bismillah........
43&44
"""""""""""""""""""""""""""""""
_______*MASARAUTA*
'Shugabansu ne yace dalla malamai kusake ne ko sata nai muku ai sai haka dayan dogarinne ya buge mishi qeya yace baza asaki din ba abun da kayi ai yafi sata ma ai wlh duk abun da akayi mana sai mun ninka shi akanka dan wallahi baza adakeni abanza ba duk kaine silar komai yaqarasa fada yana kallon me dorina
Me dorina ya gyada masa kai yace aini wallahi badan kar wani abunma yabiyo baya kafin mukai shi zamu fara rama dukan da yasa akayi mana
Danyan dogarin yace Hamm ai wlh wannan mutumin beda mutunci da girmanmu yasa mu agaba yana duka duk da bansan shekarunsa ba amma ni inaji ajikina za mu girmesa amma ya rufe ido yaringa lugudan mu kamar 'ya'yansa muda bamuma mukai mishi laifin ba har gwara kaima ka dake shi amma ni da ko tabashi ma banyi ba wlh sai Allah yasaka min dan bazan yafe mishi ba wannan ai cin mutunci ne tunda nake ba wanda ya taba yimin irin wannan dukan hatta iyaye na basu taba yimin ba......
Me dorina yace kar kaga laifin shi ai duk laifin wannan munafikin ne da beyi mishi sharri ba da ba abun da ze hada mu dashi damu, kasan shi ai baya shiga harkar kowa girman kansa ma baze bari yayi mu amala da kowa ba naga alamar yanaji da kanshi kamar wani sarki ko dan sarki yafiya nuna isa, kofa me akeyi idan aka kirashi akan yazo da sauri baya saurin saide kome za ayi mishi ayimishi amma da yangarsa zezo wajen da aka kirashi saikace wata mace";
Ɗayan dogarin yace wlh shiyasa yake ban haushi tun bayau ba abun da yakeyi yayi yawa amma fa bantaba tunani ze iya dukan mu ba wlh yanda yake shiru shiru ashe shima dan iskan kansane aikwa bazan qara shiga gonarsa ba bani bashi abun da yayi min kuma zan rama akan dan isakn nan yafada yana qara talle qeyar shugaban su da yayi shiru yana jinsu amma bashida ikon tofa nasa bakin tunanisa kawai yanda ze kasance idan sun qarasa....
Ahakade suna ta surutun su kowa da abun da yake fada har suka qarasa bakin qofar suna shirin shiga sai shugabansu da yagade da gaske ahiga zasuyi dashi gashi kuma har yanzu be tanadin makaman kare kansa ba kawai sai ya tokare yaqi shiga su kuma suna qoqarin turashi ciki yace dan Allah ku min rai kutai makeni kar muje kufadi komai kuke so inyi muku ko inbaku wlh nayi alkawarin baku komai kuka bukata amma dan Allah kar mushiga shikuma muje nuhada masa qarya yanda ze yarda itama idan ta aikemu sai muje mudawo muce munyi mishi wani abun shikenan batare da kowa yasan me yake faruwa ba kunji dan Allah..!
wata mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita gabadayan su suna nunashi da hannu sai kace sun samu mahaukaci haka suka sashi agaba sunayi mishi dariya kamar sabbin kamu daga dawana,
Aikwa dariyar nan baqaramin haushi ta bawa shugabansu ba.
Saida sukayi me isarsu dan kansu sannan suka tsagaita daga cikin su daya yace lalle sai yau naqara yadda baka da hankali inbanda rashin hankali mu zaka kalla kace zakabamu komai mukeso me kake dashi me ka tara me ka ajiye dazaka iya samu muyi wannan babbar kasadar kamamta abun da yafaru dakai shiyasa kake wannan maganar da ba me yiyuwa bace kana so kake ka qarawa kanka laifi kenan to hakurin da yace zakabasu fa agaban kowa da kowa yazakayi dashi kai bama kayi danasani ba so kake kaqara wata qarya da ta zame maka jiki to wallhai ka canza hali inba so kake akashe ka ba karasa ranka gaba daya...
Yana qarasa fada be jira amsar kowa ba yadanna kansa cikin falon sannan shima yashiga sai dayan ma ya shiga daga bayan su suna shiga jakadiyace a ciki tana 'yan gyare gyare ganinsu yasata cewa lafiya haka ko sallama babu zaku fadowa nutane ciki me dorina ne yace kiyi maba iso gurin uwar masarauta da jin haushi amma bata tanka musuba ta wuce corridor din daze sadata da dakin da fulani take ciki tanzuwa tabuga mata beldoor din dake gefen dakin taciki akace ya akai waye jakafiya tace nice su shugabansu be suke son ganawa dake tana kaiwa nan tajuya dan tasan ba amsa zata samu ba tana zuwa ta tarar dasu sunyi carko carko kamar nonuwan maza kowa ya qame waje guda saikace suna gaban fulani haka tace musu gata nan sannan taci gaba da aikin gabanta
ba jimawa fulani tafito cike da qasaita da izza tana tafiya daidai ta qaraso gurin tare da samun kujerarta ta zauna tana kallon su ganin kowa kamar fuskar su ba annuri yasata cewa ya ake ciki sungaya muku wanda yaturo sudin ko har yanzu taurin kan suke muku
"kasa magana sukayi gaba dayan su kowa yana tunanin ta ina ze fara yimata bayani"......
tace lafine naga kowa yayi shiru me yafarune....?
Ɗayan dogarin ne yasamu qarfin halin cewa ranki yadade yake uwar masarauta sai kuma yadan tsagaita sannan yaci gaba da cewa....daman bayan fitar mu da ganan mukaje gurinsu duk abun da kika fada mana saida muka gama aiwatar da dukan su basu ce mana komai har saida muka sumar dasu mundauka ma ko sun mutu nida me dorina muka fito da saurin mu dan zuwa mu sanar dake sai kuma muna fito sai mukai karo da ruwa a bambu sai nacewa me dorina kafin muje mu sanar dake mufara zuwa mu zuba musu ko Allah zesa su farfado watakil ba mutuwa sukayi ba da wannan shawarar muka debo ruwa muka dawo dakin muna daf dashiga kuma sai muka jiyo dariyar shugabanmu dukan mu da mamaki muka ja burki muka tsaya bamu gama wannan mamakin ba yaqara mana wani sakamako muryar shi da muka tsinkayo yana cewa to qananun kwari yan iska daman ai nagaya muku ku shiga taitayin ku inbahaka ba sai nayi muku sharrin da baza ku taba mantawa dani ba watakil shine sillar mutuwar ku dan ba wanda ze yarda daku nifi shedan iya shedanci saboda ba wanda be yarda dani ba yardar da akayimin cema tasa akaban shugabanci ku kuma nace kuyi biyyaya kunqi to gashinan yanzu zaku gane kurenku sai kusan yadda zakuyi dan baku da mafita ahalin yanzu babun wahalarku ya bude kenan dan daga yau kunyi hannun riga da kwanciyar hankali bare kuma farin ciki......
"Munajin wannan batun nashi muka shiga ciki muna binshi da kallo sukuma lokacin ashe har sun farfado daga suman da sukayi shine muka qara tambayar sa abun da mukaji da gaske yake yayi mana dariya yace da gaskena mu tambayesu muka qara tambayar su suka tabbatar mana da eh hakane abun da yafada duk qarya ce ya shirya miki saboda kiqara aminta dashi"
Shine muka ga hakan be dace ba yayi wasa da hankalin ki yasaki shiga damuwa da tunanin waya aiko su alhalin duk sharri yayi musu
Shiyasa muka yanke shawarar kawo shi gabanki sannan mufadi abun da yayi".............
Tunda suka fara magana fulani ta kafe su da ido ko kifatawa batayi har saida suka kai qarshen maganar tasu sannan tasamu damar cewa naji duk abun da kukace.....
juyawa tayi tana kallon shugabansu da ta gama yarda dashi sannan tace kafadi abun dakayi da baikin ka ina so inji yafito daga bakin ka sai infi yarda yanzu ina ganin kamar bahaka bane qarya suka fada baka aikata hakan ba gaya min tafada tana qara kafe shi da idanun ta.
Sunkuyar da kai yayi yakasa magana saida ta qara maimaita mishi sanna ahankali yace dan Allah kiyi hakuri wlh sharri shedan nan laifi sukayi min shiyasa na rama ta wannan hanyar amma ina neman afuwa bazan qara aikata makaman cin hakan ba nayi nadama yaqarasa fada tare da qaqalo hawayen mufurci yana gogewa amma still kansa na qasa yakasa dagowa yakalle ta..............."
Jinjina kai fulani tayi tace ka aikata babban laifi kuma dole kaima a hukun taka daidai da abun da kayi nafarko kayimin qarya kasani cikin damuwa da tunani iri iri sannan kasa anyi musu hukunci batare da sun aikata komai ba kayi musu sharri kuma kana qara fadan min wai sharrin shedan ne ai kaine shedan din bawani ba saikace sharrinkane tuna kaima shedan dinne....
"dan haka daga yanzu nasauke ka daga shugabansu sannan kuma daga yau saikayi sati kana aikin kowa na gidan sannan kaje zasuyi maka bulala hamsin agaban kowa da kowa sannan
kafadi abun da ka aikata da bakinka kowa ya sheda halinka sannan kar nasake ganin ka a sashena gaba ko da wasa kar ka kuskura ka qara rabar inda nake kaji nagaya maka
tana gama fadar haka tace zaku iya tafiya dashi kufara bashi horon dukan agaban kowa da kowa sannan yafara aiki daga yau.....Sai sukuma wadancan kufito da su daga gurin ayi komai agaban su bayan nan kuma inason ganin su akawo minsu.....
Tana gama fadar haka ta miqe tare da barin wajen bata jira jin ta bakinsu ba ta shige ciki....
"Sukam cike dajin dadin hukuncin da aka yanke mishi suka tisa qeyarsa gaba suka fito daga falon shide binsu kawai yake dan baahida tacewa koma me sukayi mishi yanmsan shiyajawa kansa kuma yadau ka ma hukuncin da za a yanke mishi sai yafi haka shiyasa beji komai ba har suka kawo shi tsakiyar masarautar sannan me dorina yacewa dayan yaje ya taho da su hamza da hanzarinsa kwa yajuya be jimaba ya dawo tare da su sannan yace yaje yagaya wa me shela yayi shela kowa yafito yazo nan nan ma da hanzarin sa yaqara juyawa dan zuwa gurin me shela..........
Hamza ne yakalli su yace me aka yanke mishi nan me dorina yabashi labari tunda ga A har Z""
Babane yace Alahamdulillah Allah ne abun godiya da ya cecemu faga hannu wannan azalaumin Allah ya fika gashi kai zaka karbi hukuncin da kake so ayi mana gashi yajuya kanka daman ance idan zaka gina ramin mugunta ka gina daidai da kai "yanzu wa gari ya waya waye aciki qaiqaeyi yakoma kan masheqiya....
Hamza ne yadora da cewa ni wlh hukuncin nan ma bemin kajira nawa hukuncin bayan ka gama karbar wannan,
Allah sarki shugaba yayi tsuru tsuru da ido bashida bakin magaba yayi danasani yafi cikin kwantena....
Suna ahaka me shela yafara shela ko ina da ina aikwa nan da nan gurin ya fara hada mutane mata da maza kowa sai fitowa yake domin bawa idonsa abinci kafin kace gurin