Showing 33001 words to 36000 words out of 136570 words
yashiga damuwa kuma a yanda suke zaman mutun ci gaba da familyn ba wanda yazargi wani akan shi yadauke yaron, Amma sarki ya dauki alkawarin duk wanda dasa hannun sa akan faruwar lamarin sai yagane kuransa dan baze hakura ba sai ya dau babban mataki wasa wasa de ahaka har aka dau lokaci me yawa babu labarinsa zuwa yanzu kuwa kowa ya hakura duk sun fidda rai ma gaba daya sun rungumi qaddara,
Allah cikin ikonsa sai ga wani cikin taqara samu nanmade sunyi murna da farin cikin da samun sa shima de haka akai ta renon sa shima kuma Allah beyiba yabare amma da aka kaita asibiti sai akace tasha abun zubda ciki ba qaramin mamaki sukayi ba dajin hakan itade tasan bata sha komai ba to ya akai hakan ta faru daman doctor gimbiya maryama ya gayawa ita kuma tagaya mata sarki be saniba saboda be qaraso ba dan haka sai kawai gimbiya Sabreena duk da tasan bata sha komai ba amma tana tsoran sarki yaji saboda tasan idan yasani ba koda ze yarda da ita tofa dole yadan zargeta ita kuma batason zargi ya shiga tsakanin su dan haka sai ta roqi gimbiya maryama akan dan Allah subar maganar anan bataso sarki yaji saboda batasan yanda ze dauki maganar ba dan wlh itade bata sha komai ba qarewa ma ita wata sani agarin da zatasa yabata maganin zubar da ciki qarewa ma neman sa take Allah yabata kuma sai ta zubar tayaya ma hakan zata faru gimbiya maryama batai mata musuba tace nima tuna nin danake kenan tayanda za agayawa sarki cewa ciki ya zube kuma ta hanyar shan kwaya hakan ba karamar matsala ze haifar ba dan haka nake tunani gara abarshi kawai azin Allah ne yakawo zubewar cikin da wannan shawar warin nasu suka bar maganar akan bawanda zeji,
Bayan sarki ya qaraso kuwa aka gaya masa cewa cikin ya zube yayi jimami sosai amma ba yanda ya iya dole yayi hakuri wanda yabashi shi yakarbe abunsa kuma shi ze qara basa saida tayi kwana biyu sannan suka tattara suka koma masarauta kowa yana zuwa duba ta dayi mata jaje bayan komai ya lafane mahaifiyar sa taqara yi masa magana akan ya qara aure tundade abun da haka yake zuwa beyi mata musuba dan shima zuwa yanzu abun yafara damunsa shima yanaso yaganshi da yara koda magajin sane yasamu dan haka ya amince aka nema masa auren SA'ADATU yar sarkin gombe ce dan haka ba dadewa akayi auren aikwa bata dadeba ta samu ciki da haka har watan haihuwarta yayi ta haifi 'ya'yanta 'yan biyu kuma duk mata ranar suna aka saka musu daya taci sunan babar sa watakon Karima amma ana cemata mama dayar kuma akasaka mata munubiya yara kyawawan farare ne tas saboda sundakko mahaifiyar su data kasance buzuwa gasu da shiga rai kowa sai yabon kyawun su yake suna da shekara ta biyu Allah yaqara bawa Sabreena wani cikin,
Nanma de basuyi qasa agwiwa ba sukayi murna tare da bawa cikin kwakkwaran kulawa saboda kar yasake zubewa Allah kwa yatai maka be zube ba har Allah yasa tahaife danta me kyan gaske dan da kowa mamakin irin kyan da Allah yabashi duk dade mahaifiyar shi ma kyakkyawa ce amma sai yafita kyau sarki yace ta zabi sunan da za asamasa tace akara samata Sameer saboda tana son sunan haka aka qara samishi sunan wanda ya bata,
kawo yana son shi bayama yayyanshi su munubiya kullum suna manne da shi haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da sin junan su,
Sameer yana cikin shekara ta daya dan bekaiba ma kwatsam wani abun mamaki kuma abun al ajabi lamarin Allah ba acewa komai sai ga gimbiya maryama da ciki aikam kowa yayi murna dan sarki kwa yafi kowa farin ciki addu'ar sa ta karbu yau gashi da yaya uku gakuma cikin na hudu ya godewa Allah kawai yake yi atakaicade itama ta haifi dan ta namiji amma abun mamaki yaron sai yasance baya kama da kowa daga cikin iyayen nasa anrasa dawa yake kama amma ba wanda yace komai saboda ba ajayayya da lamarin ubangiji watakil ma kamannin kakansa nawajen sha wani abun yadakko kunsan dan haka bawanda yace komai ranar suna aka saka mishi *SALAHUDDEEN* SALAHUDDEENI MUHAMMAD SAMEER shine sarki na yanzu kuma "ɗa" ga gimbiya MARYAMA wacce ake kira da FULANI...................
Ina fatande kuna fahimtar yanda labarin yake tafiya kuma kuna riqewa dan yanzu baza ku gane komai ba sai nan gaba, kuma zakuyi mamakin ya akai salahuddeen yazama sarki bayan bashine babban ɗa ba ga Sarki Muhammad sameer muje de zuwa.......
*************************
CIGABAN LABARI.....
'Su Ameesha suna dab da qarasawa gaban gate din gidan sukaji dadda tace gidan qawar taku kenan cak suka tsaya suka kasa juyowa har taqaraso inda suke tace ba magana nake muku ba?
Ameesha ce ta hadiyi wani yawu da ya tsaya mata a makogaro sannan tace uhm uhm dadda bafa wani abu zamuyi ba daman abu zan karbo a gurin aunty lami yanzu zamu fito,
dadda tayi mata wani irin kallo irin to sannu makaryaciya saida taga qare musu kallo sannan tace to kuwuce mu koma gida munafukai wlh baza kushiga ba Ameesha tace dan Allah kibarmu mushiga wlh wani abu me mahimman ci zamuyi tace wane abune da ni baza kufadan ba zaku min qarya kufito tace dadda wlh zamu gaya miki amma kibari mufara shiga mufito tukunna tace wai yarinyar nan wace irin zuciya gareki ke duk wulakancin dasukai miki amma kike qoqarin qara komawa gurin su tace dadda nifa ba wajen su zanjeba tace koma gurin waye bazaki shiga cikin gidan nan ba Azeema dataga abun nasu ba qarewa zeyi ba sai tace dadda dan Allah kibari mushiga yau wajen kwana uku kenan da rasa mahaifin mu ya bata bamuganshi ba shiyasa nazo Ameesha ta rakani muyi yaya musbahu magana akan yatai maka yagayawa yayansu acigita mana a gidan radio ko Allah zesa agano inda yake inma mutuwa yayi zamu sani dadda da taji labarin kamar almara tace yanzu dan baki da hankali wannan babban abun yafaru amma kika kasa sanar dani abun dake faruwa saida na tambaya da bantambaya ba kenan ma baza ku gaya min ba ko Azeema tace dan Allah kiyi hakuri dadda batace mata komai ba tana tunani mafita dan ita wlh bata so sushiga gidan gashi kuma bukatar hakan ta taso yanzu meye mafita to bata gama tunani ba.....
Horn din mota ya katseta mata tunani juyawa sukayi dan ganin wanda ze shiga gidan ganin me gidanne yasasu matsawa su bashi guri dan yasamu damar shiga yana matsowa kusa dasu sai ya tsaya tare da sauke gilas din motar yana kallonau tsaf yagane su dan haka sai yace musu kushiga daga ciki mana kuntsaya anan dadda ce tace mu bashiga zamuyi ba kai tafiyar ka tafada tare da hade rai dan ita duk 'yan gidan ma haushi suke bata...
Dayaga haka sai kawai ya bude motar ya fito ya qaraso inda suke yace baba kiyi hakuri dan Allah ni daman inaso muyi magana tun ranar nan naso muyi duk sunban labarin abun da yafaru kuma na dau mataki akan su dukan dan Allah kuyi hakuri hakan baza tasake faruwa ba nasan basu kyauta muku ba abun dasukayi muku kuzo mushiga daga ciki.."Dan Allah baba kar kice bazaku shiga ba,
Dadda da mutumin yayi mata kwarjini kuma daman ga kuma bukatar da ta kawo su dan haka tace ni basai munahiga ba daman wannan yarinyar ce mahaifinta ya bata shine mukazo ataimaka mata abada cigiyar shi ko Allah zesa adace asamu labrin sa awani wajen.
Yace "ayya Allah sarki tun yaushe ne kuma a ina?
Nande Azeema tabashi duk labarin yanda akai ya tausaya musu yace in sha Allah zesa Khalid yacigita musu gobe amma su shiga daga ciki dadda fiu taki yarda haka ya rabu da ita sannan yace to dan Allah yana roqon alfarma ta taimaka tabar yarinyar taci gaba da aikin ta kamar da komai ya wuce yajawa iyalansa kunne bawanda ze kara yi mata komai,
Dadda tace itafa jikarta tabar aiki a gidan sa yayi hakuri kawai yabar wannan maganar shima kuma be bar maganar ba haka yaringa yimata dadin baki da rarrashin ta har ya shawo kanta ta amince akan yabarta zatayi tunani akai yace to hakan ma ya gode sannan yace musu yana zuwa ya koma cikin motar sa ya dakko katin number wayar sa yabawa Azeema yace intaje tabawa yayan ta sai ya kira shi su tattauna akan batun karba tayi tana masa godiya yace ba komai yiwa kaine daga nan kuma ya koma mota ya tayar yakaqara danna horn me gadi ya wangale masa qaton gate din shikuma yadanna kan motar yashiga ciki,
Ajiyar zuciya dadda ta sauke tace to Allahamdulillah komai yazo mana da sauki batare da wata matsala ba suma duk hamdala sukayi sake da godewa Allah sannan suka kama hanyar komawa gida suna tafiya dadda na qara jimamin yanda akai hakan tafaru babban mutum ace ya bata abun da mamaki wlh kowade da abun da yake saqawa aransa har suka qarasa gidan basu wani dadeba Azeema tacewa Ameesha to besty godiya nake bari in wuce gida inje insanar da mama nasan tana can tana jiran dawowata tace to bari muci abin ci saiki tafi ko tace a'a besty na qoshi Ameesha tace wlh sai kinci kinji ma na rantse Azeema tace to ina ruwana da rantsuwar ki nide bazan ciba Ameesha ta hade rai tace to karkici din alaraka taki gona tafada nakara hade rai alamun taji haushi,
Azeema data ga haka sai tace kai besty meye kuma najin haushi to naji zanci amma kadan kuma kiyi sauri dan banaso inkai magariba a hanya tace to sannan ta mike tanacewa yar rainin hankali ai da bakiciba wlh da kinga rashin mutuncin da zan miki dariya Azeema tayi tace to nide naji kiyi sauri malama Ameesha tace anqi ayi din tafada tana ficewa daga dakin bata dade ba ta dawo da kwanon abincin a hannunta ta ajiye agaban ta tace sai muci Azeema tace la wai daman dan wake ne ai da kinga ya min da bazan miki musu ba kinsan ina sonshi sosai gashi mama bataso tana yimana shi saboda ita be dame taba Ameesha tace ai daman dan hakan nace kizauna muci ama kike wani nannoqewa kina so kina kaiwa kasuwa da muna furci wani ni wlh naqoshi ni sauri nake yen yen yen....
Dariya Azeema tayi tace au abun jarda cin fuska to wlh saima na tashi na tafi tace bismillah ai ban daure kiba qofa abude take bata qara ce mata komai ba kawai tayi shiru tacigaba da cin abincin ta dan ta lura idan tabiyewa bestyn tata sai sukai dare basu dena ba itama Ameeshan shiru tayi suka ci gaba daci har suka cinye tass sanna tafita da kwanon ta debo musu ruwa suka sha itakuma Azeema ta tashi ta shirya tace muje ki rakani ko tace muje itama hijab dinta tasaka sannan suka fito waje atare suna fitowa tace to ina daddan take tace oho watakil ta fita ko kuma tana bayi muje kawai inna dawo nagaya mata kin tafi tace shikenan muje suka fito suna ta yar hirar su har suka zo inda suka saba raka juna sannan sukayi sallama kowa yayi nasa wajen,
Ameesha na komawa ta duba ko ina taga da gaske de dadda bata nan to ita ko ina taje haka bata gaya mata ba haka ta koma daki tayi zaman jiran dawowar ta amma shiru bata dawo ba har aka idar da sallar magariba sai lokacin kuma tafara jin tsoron gidan da kuma tsoron ina dadda taje haka hartakai dare bata dawo ba dataga de bazata iya zaman cikin gidan ba kawai sai tafito waje dake gurin da hasken fitilar wani gida dake kusa da nasu ta haska har qofar gidan su dan haka tasamu waje tare da zabga tagumi tana hawaye saida tayi wajen minti talatin itakadai dan har tafara kuka wiwi kuma tana tunanin ko taje gidan su Rasheeda kawai tagaya musu bata ga daddar ta tana miqewa saiga wani me keke napep yashigo layin kuma kamar gidan su yake nufowa dan haka ta tsaya taga waye aciki adaidaitar,
Tana tsayawa saiga dadda tafito dasauri dan har ta manta ma bata bawa me adaidaitar kudin ba saida yace hajiya kudin sannan tace yi hakuri yaro namanta wlh yace ba komai tana bashi tawuce gurin Ameesha datayi tsaye takasa motsawa daga gurin,
Dadda na qarasowa tace wayyo Allah na dan Allah kiyi hakuri wlh bansan zankai dare ba matsala akasamu a hanya cikin shashsheqar kukan da taci ta qoshi tace kuma dadda fisabilillahi sai kifita baki gaya minba yanzu da wani abun yazo yasameni fa ko andauke ni tace Allah ma yakiyaye ba abun da ze sameki ma wlh nayi tunanin kan qawarta ki ta tafi nadawo shiyasa ma ban muku magana ba nafita kuma nayi tunanin ma zasu kawo wuta Ashe basu kawo ba yanzu de kiyi hakuri muje ciki ko gaba tayi ita kuma tabita abaya suka shiga cikin gidan............
comment and share
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
By
Yaya Azeema😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Ya Allah duk abun da ba ma gani👀 Allah kagane mana duk abun da bamaji👂 Allah kajiye mana duk abun da yafi qarfinmu💪 Allah kafi qarfinsa ya Allah duk abun da baza mu iyaba👌 Allah ka iya mana Allah kashige mana gaba adukkanin Al'amuranmu Allah kar kabarmun da kanmu tai makonka murke nema duniya da lahira*
Bismillah.......
23&24
********************
'Basu wani qara dadewa ba suka qarasa qofar gidan lokacin da sukaje gidan tara saura befi minti shabiyar ba,
Yana gama dedeta parking din motar yajuya yana kallon Ammi nasa yace "Ammi ga gidan fa yanzu yaza ayi zakifara shiga din dan Allah inyaso inkinshiga sai kituro min Ameesha sai mushigo da ita,
'Wata uwar harara ta maka mishi tace "Haka muaki da kai daman? kaga nifa kar kabata min lokacin ina da abunyi kasani dole na fito adaren nan inbaka shirya shigaba ai sai kajuya mukoma gida takarasa fada tana hararar sa,
Da sauri yabude qofar yafita yana zagayowa itama yabude mata yace ranki yadade, Hajajun mu mushiga ni na isa yanzu ince mukoma gida,
Tace "Ai naga alama baka shirya bane shiyasa nace haka, tana fada tafito daga motar shikuma ya rufe, Sannan ya tsaya wai yanaso tai gaba yabita abaya, Itama ta tsayawar tayi tace "Wai kai me yake damun kane bafa nason shashanci ni kakeso inyi gaba kenan?
Ɗan sosa kyayarsa yayi sannan yace "Sorry Ammi muje yafada yana yin gaba ita kuma tana biye dashi abaya har suka shiga gidan da sallama abakin su saida sukai wajen sau uku sannan Dadda ta amsa musu su tana cewa...
"Wai suwaye ne a tsohon daren nan suke damun mutane ya akai? me yakawo ku? me kuke nema? gurin wa kuka zo? sai faman jera musu tambayoyi take batare da tajira amsar dayaba kuma tana cikin dakin bata fito ba,
Bosssay ai tuni hantar cikin shi tabashi wata irin qara jikake qurrrrr ahankali yadago yana kallon Ammi itama shi take kallo aranta tana jinjina masifar wannan matar daga sallama ko lekowa batai ba amma sai faman zuba take sai yanzu taga ashe Bosssay bashi da lefi da yake cewa baze kara zuwa ba tamaga kokarin sa yanzu da ya iya zuwa duk da yana jin tsoro amma ya yarda ya shigo.
Dadda ce ta katse mata tunani ta dacewa wai bamaga na nake bane anyi shiru ko barayine? inma kune to saide kusace ni dan banda abun da zaku sata acikin gidan nan😂kuji tafa taya za ayi barayi suyi sallama inbanda abun Dadda,
Ammi ce tayi qasa da murya tana yar dariya tace "wlh kazo mukoma tundade kanajin abun da take cewa alahalin ko lekowa batai ba kar muje muna shiga ta buge mu da wani abun,
Shima qasa qasa yayi da murya yana cewa "Ammi plss wlh ba abun da zatai mana ke kifara shiga inta ga macece baza tace miki komai ba, tace "Naqi din.
Saida ya qara roqonta sannan ta dan daga murya sama tace "baba bakine, kifito ki ganmu, mu ba barayi bane,
Jin muryar mace kuma tace bakine yasa Dadda dan sassauta murya tace baki daga ina kuma, ko baku da suna ne?
Saida Ammi taqara kallon Bossay tace "To kajide me tace saikagaya mata ni nagama nawa kuma wlh nagaji da tsayiwa zan koma, idan baza kayi mata bayani ba,
yace "Ammi Allah innace mata nine baza ta kulamu ba watakil ta hadamu ta zage, suna ta faman tunanin mafita kawai sukaji Ameesha daga cikin dakin tace "Yaya Bossay kushigu kawai ba shi kadai harta Ammi abun ya matukar bata mamaki ta ya akai yarinyar tasan sune tundade basuyi magana da qarfi ba bare tace taji muryar Bossay ita kuma datayi maganar tasan basu taba ganin juna ba ko a hanya bare kuma tasan muryarta.
Jin shirun nasu yasa Ameesha qara cewa "Wai bazaku shigo ba tanadaga cikin dakin take magana saboda Dadda ta ruqeta ta hanata fita amma da tun sallamar farko zata fita saboda tasan basu da wani da zezo musu gida yanzu bawanda suka sani kuma daman tun randa yagaya mata zezo da Ammin sa take jiransu dan haka yanzu tanajin haka jikinta yabata sune,
Ammi ce ta ɗan ɗaga murya tace "gamunan, tana fada tajiyo Dadda na cewa
"In kunsan kune kar kusake kushigo min daki bana ce kar kasake inqara ganin qafarka agidan nan ba baka jin magana kenan harda dakko min mace kazo min da ita to bazan bayarba,
Kin hakan kawai sai bossay yaja hannun Ammi suka nufi dakin, Ammi na tajan hannun ta da nufin ya saketa Amma yaqi har saida yakaita cikin dakin sannan yasaketa shikuma ya tsaya abakin qofar,
Dadda dake bayani hannuta ruqe da Ameesha da taruqe ta gama sai faman kwace