Showing 123001 words to 126000 words out of 136570 words

Chapter 42 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5438

yayi ya hango wata mace fara tas kana gani kuma kasan ta hada da bleaching kallon da yayi yace kai ko har yanzu bazakadena kwashe kwashen nan ba ko dan murmushi yayi yace zan dena amma ba yanzu ba sai nagama more rayuwata tukun badan irin sudin ba me ze kawoni qasarku dariya sannan yace su naku nacan me sukayi da said anzo tamu akeyi yace can ai kasan dalili saboda tsaro in bahaka ba old man kasan halinsa ya saka min ido da yawa shiyasa na fiso inzo nafi sakewa kuma yan nan sunfi dandano yafada tare da daga masa gira daya yace hamm Allah ya gyaraka ni wuce ko kunyata ma bakaji ko tafi kar kasa kunnuwana sude na ji zama dakai said wanda yashirya tayar da motarsa yayi sannan yace kaima bakagane bane shiyasa kake tazama ahaka ga ba aure ga baka dan hutawa kana qoqari danni wlh bazan iya jurewa ba ko kwana daya nayi banjini cikin mace ba akwai matsala shiyasa kullum muna manne yace to Allah yashirye ka to waya hanaka auren yace aure ba yanzu ba gwara na waje de shettima yace aikwa in bakai wasaba sai nakai qarar ka gurin old man dinka tunda shikadai kake tsoro ko Allah baka tsoro sai shiko dan tabe baki yayi yace kaga ni zan wuce ka ajiye surutan ka kayi su wani lokacin yana gama fada yatayar da motar tare da daga masa hannu sanan suka tafi shikuma ya koma ciki yana jinjina irin wanna halin na abokin shi da baya jin tsoron Allah kamar ba dan musulmai ba idan katabo masa Allah ma yanzu zai barmaka gurin da tunanin sa ya shiga  ciki dakin yaqara komawa ganin ta akwance cikin kwanciyar hakali yasa shi jin wani farin ciki ya lullubesa shikenan yana fatan daga yanzu qarshen wahalar ta yazo kenan tunda yashigo hajiya take kallon sa ganin gaba daya hankalin sa yana kanta tadan yi masa gyaran murya tace kallon fa dan sosa qeya yayi sannan yace hajiya wlh ina tausayawa rayuwar ta ne hakan nan tun haduwata da ita ta farko naji tana ban tausayi tace Allah sarki Allah yabata lafiya yace amin daga nan suka dan taba hira sannan tace yake ya kwanta tundade ba farkawa zatayi ba sai zuwa gobe ita zata kula da ita da qyar ya hakura ya tafi dakin sa bayan ya shiga ne yagama duk abun da zeyi ya kwanta har baccima yadan fara daukar sa yaji wayarsa na qara da ya duba yagani yayi mamakin ganin me kiran yagani har ta tsinke wani yasake shigowa shima kin dauka yayi da yaga ba dena kiran zeyiba kawai sai yasa wayar a silent yakifata saboda idan ma yadaga besan me zece masa ba kuma besan me zejiba yana ganin watakila ma yakiraahine kawai ya kuma gaya masa wata maganar banzar shiyasa yaqi dagawa ahaka har bacci yadauke shi zuciyar shi cike da farin cikin samun lafiyar Ameesha,

Washe garin tunda ya tashi be komaba yana dakin hajiya yana jiran yaga farkawar ta duk yanda hajiya taso dashi akan yakoma ya kwanta zuwa anjima tana farkawa zata je ta tasheshi amma yaqi fur yace shi bayajin bacci koma hake ya kwanta ba iyawa zeyiba haka ta rabu dashi Ameesha de ba ita ta farka ba sai wajen tara da rabi tafara motsi da hannun ta sanan ta bude idonta duk abun da take akan idon sa da sauri ya tashi ya dawo kusa da ita tare da ruqo hannun ta yana mata sannu da ido kawai ta amsa masa tana qoqarin tashi yayi saurin tashinta ahankali tace zan shiga bandaki da taimakonsa tashiga saboda lokacin hajiya bata dakin tana kitchen ita da me aikinta suna hada breakfast na musamman saboda marar lafiya,
Bayan yakaita bandakin ne kuma sai ta tsaya fitsari zatayi kuma taga ya tsaya yaki fita shiyasa itama ta tsaya shima kuma jiranta yake tayi abun da zatai ya mayar da ita ganin hakan sai yace mata   ko zaki wanka tace eh dan daman tana bukatar yin wankan saboda jikin ta duk wani iri take jinsa ruwa me dumi ya hada mata sannan yace to zaki iya cire kayan ko saina cire miki zaro ido tayi jin abun da yace sannan tace zan iyama na yace a'a baza kiya iyaba wlh wankan ma ai ni zan miki nasan ba iyawa zakiyi ba juya muyi sauri kije kici abinci make kafada tayi tace nide wlh ka fita zanyi komai da kaina yace a'a wlh baza ki iyaba hannu yasa ze cire mata riga tayi saurin riqewa tare da sakin yar qara tace Allah banaso dan Allah ka rabu dani tsayawa yayi yana bin dan qaramin bakinta da kallo tare da binta da kallo tundaga qasa har sama yana so yagano abun da take cewa kar yataba ita bata so ita kaza ita kaza  yana tunani to ita nan me take boyewa yar qarama da ita koma meze gani nawa take gaba dayanta(uhm uhm fa ale shettima akwai fa yan biyun ta kuma sun fara wayo irin sune ma suka fi tada ehhh irin ehh dinnan😎saboda a tsatstsaye suke🙈 bari inyi ta kaina🏃 naga ya watso min harara dan kawai mafadi gaskiya ko qarya nayi jama'a kutayani ji👂)
[27/12, 8:02 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
                  By
          Yaya Azeema 😎

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                            

      Bismillah........


No Edit

                         81&82

        """"""""""""""""""""""""""""""""

   "Bafa zaki iyaba kibar inyi miki tace uhm uhm nide kabar ni Allah bazan iya tsayawa ka kalle ni ba kawai kaje in kuma bahaka ba to nafasa duk wannan maganr da yakeyi still de ba janye hannun sa ba kwan kwasa kofar bandakin akayi hakan yasashi sakinta hajiya ce tace wai meyake faruwa ne yace hajiya wai bazata tsaya inyimata wanka ba daga waje hajiya ta riqe baki tare da turo qofar tace wanka fa kace taya za ayi ta yarda dallah fita kaban waje sai kace wata yarinya zaka wani ce zaka yimata wanka kallon hajiyar yayi tare da kwantar da kai yace hajiya to meye aciki ni kamar qanwata na dauke ta tace Allah ko ai naga alama to fice min daga nan zanyi mata badan yaso ba yafita dan shi har ga Allah so yake yayi mata din bayan ya fita ta maida hankalin ga Ameesha da tayi wani tsuru tsuru tana kallon su tace yata yi hakuri haka halinsa yake shi be cika jin kunyar abuba bashida ita sam toho inyimiki ahankali tace zan iya da kaina a'a yata bazaki iyaba bakiga jikin ki ba kwariba kibari in dan taimaka miki in gagga sa miki shi kinji badan taso ba saboda matar tunda taganta taga tayi mata kwarjini hakan bazesa tayi jayayya da ita ba tunda de babbar macece ahaka tanaji tana gani ta sutale mata kaya tsaf sanna ta sakata acikin ruwan dumin saida ta gasata sosai sannan ta qara hada wani ruwan ta dirjeta tsafa tabata sabon brush ta wanke bakinta sosai sun dau lokaci aciki kafin ta bata towel ta daura sannan ta dan ruqota suka fita suna fito suka ga baya dakin zaunar da ita tayi sannan ta dauko mata mai ta shafeta dashi kamar de qaramar yarinya haka ta ringa kula da ita bayan tagama yi matane kuma kayan da zata bata tasaka suka fado mata tashi tayi ta nufi wardrobe dinta tanaso tasamo mata doguwar riga wacce zata danyi mata dubawa take tayi amma duk wacce ta dauko sai taga sunyi mata yawa sosai tana cikin haka sukaji sallamar shettima yashigo hannu sa riqe da leda hajiya na ganinsa tagabe meye dan haka kawai sai tasaki murmushi tace yauwa aikwa kayi tunani me kyau kaganni tundazu nake tunani abun da zan bata tasaka na rasa idon sa na kan Ameesha tunda ya shigo ya kafeta da su yana kallon santala santalan cinyiyinta da towel din be gama rufesu lura da hakan yasata dan ringa jan shi duk saitajita atakure saboda kallon da yake mata ba zato ba tsammani yaji antalle masa qeya sannan tace bani kafita beyi musuba yabata ya juya saboda yaji kunyar kamashin da tayi bayan zarowa tayi wata doguwar riga ce ash color sai dan ratsin baki ajikin ta mayafinta ma bakine marar kunya harda bra da fant duk ya siyo mata kala uku uku bata tayi tace tasaka bari taje ta kawo mata abinci kafin ta shirya bayan ta shiryane ta shiga bin kanta da kallo duk da bata gani ba amma tanaji ajikinta tayi kyau ba qarya ahaka hajiya tashigo da faranti a hannun ta tana shigowa sai gashi shima yaqara shigowa duk tare da ita suka ci abincin suna cikin ci kiran sameer ya shigo wayar sa amma sai yaki dauka hajiya tace wayake kiranka ka dauka mana hade rai yayi sannan yace bazan dauka ba ina dauka wani rashin mutuncin ze qaramin kuma inya qara nima ba barinsa zanyiba shiyasa bazan daga tagane akan wanda yake magana sai kawai tayi shiru bata qara tanka masa ba bayan sungama ta tashi tafita da kwanu kan tana fita Ameesha kamar jira take ta fita ta juya ta kalle sa tace nifa tundazu nake so in tambayeka wai ya akai naganni anan duk de naga alamar gidan kune tunda naga kana kama da mahaifiyar ka ina asibitin kuma ina 'yan uwana yace zan gaya miki ba yanzu da marairaicewa tayi tace dan Allah kagaya min yanzu wlh tunda na tashi nake so na tambayeka amma saboda maman ka nakasa yace "ok" sannan ya shiga bata labarin abun da yafaru tun lokacin da yafito tasaka kuka harzuwa lokacin da ya dauko ta har fadansu da sameer ma be boye mata ba atake taji wata muguwar tsanar sa ta kamasa wannan wane irin marar imani ne bashida tausayi ashe so yake yarabata da duniyar ma gabaki daya saide kuma Allah yafishi gashi tasamu lafiya fiya da da lokacin da take ahannun nasa katse mata tunani yayi sa cewa tunannin me kike qanwata karkisa komai aranki kinmanta dashi kawai yanzu bagaki da ranki da lafiyar dan murmushi tayi tace ba komai ni bansa komai araina ba nagode sosai da sosai akan dauwaniya da kake yi dani Allah gabika da gidan aljannar firdausi yace Ameen daga nan kuma suka shiga taba hira yana tasakata nishadi da dariya saboda yadebe mata kewa suna cikin haka hajiya ta shigo tace to kayi bako mutumin ka yabiyo ka har gida duk da yagane watake magana amma saida yaqara cewa hajiya wa kenan tace waye zezo neman ka kaima ai kasani yace to ko uban me yazo yimin dan Allah hajiya kece kawai bana nan tace bazan masa qarya ba kuma daman nama sanar dashi kana ciki dan haka sai kafita zama ma yaqara gyarawa yace ba inda zani wallahi idan yagaji ya tafi hajiya de bata ce masa komai ba ta fice daga dakin dan ta sanar da sameer abun da yace saboda itama bazataso rugujewar alakar su ba komai ya tsananin maganin sa Allah gwara su shirya sudawo yanda suke bata dade da fita ba aka turo qofar aka qara shigowa hankalin su nakan hirar da sukeyi bama suji shigowar sa ba tsaya wa yayi yana qare musu kallo sai yanzu yaji wani irin sanyi da be taba jiba yaji lullubeshi,

qarasa shigowa yayi jin tafiya yasa shettima dagowa dan ganin me tafiya idonsane ya sauka akan sa da sauri ya miqe yana kallon sa yace malam me kashizo kayimin ko kazo ka qarasa cimin mutuncin dabaka qarasa ba ko kuma kabiyota ne ka qarasa ta to wlh karyarka kafice min daga tun muna mu biyu tun muna sheda juna kafita kafin raina yaqarasa baci bazaka ji dadi ba tunda kai kazo inda nake yanzu ba a asibitin ka nake ba ba kuma agidan ku nake bare kace zaka zaka takani duk maganganun da yake hasalima idon sa ba akansa yake ba yana kanta be tanka masa ba ita kuma tunda ya shigo ta kalle sa ta gefen ido bata dago ta kalle sa ba kuma tanajin idon sa akanta jitayi zaman gurin gaba daya ya gundire ta miqewa tayi zata gita daga dakin dan batajin zata iya zama matukar yana cikin dakin, da sauri shettima ya ruqo hannun ta yace ina zaki zo nan ba abun da ya isa yayi maki inde ina gurin idonta ne duk suka cika da kwalla tace ni kabar ni in fita kawai bazan iya zama guri daya da wanda baya kaunata kuma yana neman rabani da duniya yana so yaga bayana me na aikata mishi da ya tsaneni haka har yake so yaga bayana bayana kuka ne ya kwace mata tafashe mishi dashi jawota yayi jikin sa ya rungume ta yana rarrashinta amma duk dahaka taqi yarda tayi shiru gudun kar kukan nata yayi yawa azo asamu matsala irin jiya dan haka sai kawai yarabata da jikin sa ya share mata hawayen yace ya isa haka kiyi shiru kije gurin hajiya tana falo gyada mishi kai kawai tayi sannan tayi gaba zata fita har ta dan gotashi taji anruqo mata hannu tare da fisgota ta dawo da baya ganin wanda ya ruqota yasa ta qara sakin wani kukan,

Ran Shettima ba qaramin baci yayi ba ahasale yayo kansa yana nuna sa da yatsa yace saketa kasake ta yafada yana qoqrin raba hannu sa da nata amma yakasa saboda baqaramin ruqo yayi nata ya riqe ta gam kamar ze balle mata hannun da karfi shettima yadaka masa tsawa yace nace kasake ta ko kar ranka yazo yana baci bade kace murabu dakai ba kuma munrabu dakai ba to meyasa zaka biyo mu ko sode kake sai ka kasheta hankalin ka ze kwanta har yanzu shide be tanka masa ba duk dashina zuciyar tasa a kusa take cigaba yayi da qorain kwace ta amma yakasa hannu yadaga ze kaimasa duka amma sai ya dakata sakamakon wata qara da Ameesha tasaki ne yadakatar dashi daga abun da yayi niya,

  Da sauri ya yayi kanta ze ruqota amma kafin ya ruqota sameer ya rigasa rungumeta yayi suna cikin haka hajiya ta shigo tace ya isa haka duk naji maganganun ku tafada tana qarasowa kusa dasu hannu tasa ta karbe Ameesha da ga gurin sa sannan tace kusa mu wajen kuzauna kema kuma kukan ya isa haka babu wanda yayi mata musu suka samu guri suka zauna kamar yanda ta umarce su din itama shiru tayi tana shesheqar kuka nan tashiga yimusu nasiha da illar wannan fadan dasuke yi marar amfani kowa ta nuna masa inda laifin sa yake sannan taja kunnen su akan su bawa junansu hakuri kar wanda yaqara cewa wani yarabu da wani suzauna kamar yanda suke da yarinya kuma tunda taji sauke su maidata gurin iyayen ta kawai aci gaba da kula da ita acan suma hakan sai yafi musu kwanciyar hankali yanzu ya dauko yarinya ya kawota wani gidan idan sukaje asibitin kuna basu ganta bafa me zasuce musu wannan ma gangancine kwata kwata be kamata tasss tayiwa kowa fada harda shi uban gayyar da yake tafam cika yana batsewa shettima ne yace hajiya dan Allah kiyi hakuri amma bazan koma aiki a qarqashin saba kawai kowa yakama gaban sa nagaji da zama dashi hajiya ta kalle sa tace daman baka da hankali bansani ba kamanta hallacin da yayi maka ko  badan tasanadin sa ba ka isa ka kawo wannan matsayin dake yanzu komai bata sanadin sane ba kai koma me yayi maka inkana da hankali hankali yakamata kagaya masa haka meyasa baza kai hakuri ba tundade ka riga kasan halinsa ai be kamata ma karingajin haushin wani abun nasa ba tunda kasan duk abun da ze aikata da abun da baze aikata ba kasani bekamata karinga damuwa da halayen sa ba dan haka ina gargadinka kar nasake jin wannan furucin abakin ka sunkuyar da kai yayi kawai bece mata komai ba sannan ta koma kan sameer tace kai fa kana da abun cewa kai kawai ya girgiza be ce komai sannan tace to masha Allah yanzu inaso ku sasanta tsakanin ku ku ko kunyama bakwaji aji kanku idan momma dinku taji me kuke tunanin zata ce duk shiru sukayi suna sauraron ta har tagama sannan tace yanzu yaza ayi da ita yarinya zaku kira gidan sune suzo su dauke ta ko kuma zaku mayar da ita  da kanku sameer ne ya bude baki yace hajiya amma naji kina cewa iyayenta kuma jiya wanda suka kawota daya daga cikin su yace marai niyace bata da kowa batasan kowa nata ba dalilin da yasa ma nazo kenan inji ta bakin yarinyar da gaske ko kuwa qaryane saboda ina son janye duk abun da nafada akanta kallon kallon akashiga yi tsakanin shettima da Ameesha da kuma hajiya, hajiyace ta kalli Shettima tace da gaske ne maganar da naji tunda naga kunfi kusa kai da ita shettima yace wlh hajiya nima bansani ba yanzu nake ji kallon Ameesha yayi yace da gaske ne Ameesha ke marainiya ce hawayene suka shiga zubo mata cikin sheshsheqar kuka tace ni ba marai niya bace amma de bansan suwaye iyaye naba ahannun kakata nataso naganta kuma idan na tambayeta ni wace ina iyayena amma taqi gaya min kuma naji wasu maqotan mu idan suna zagina suna cemin 'yar shegiya kuma dadda tace ni ba yar shegiya bace amma kuma haryanzu bata sanar dani komai game da iyayena ba tun ina tambaya har na dena amma inaji ajikina koma suwaye suna raye saide bansan ina suke ba wannan ne dalilin dayasa kaji nace kar kagaya musu ina cikin hayyacina inso innuna musu ba abun da nasani nasan watakil dadda zata iya bani wata qofar da zan gane wasu abu tunda tasan inma tayi agaba ne bazan fahimta ba,

Sameer ne yakatseta da cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login