Showing 90001 words to 93000 words out of 136570 words
saki wani aiki kin san me zakimin tace aa sai ka fada yadan yi shiru sannan yacigaba da cewa ina so kidu ban kiga Sam yana nan ko bedawo ba daga can ta bashi amsa da cewa yaya kamanta baya qasar ma nade ji ance ya kusa dawowa amma banji yaushe ze dawo ba sai yace a'a yadawo ai tundazu da safe naje na dauko shi daga airport muna tare kuma yafito na neme shi na rasa nakira wayar shi kuma yaqi daga dan Allah ki dan bincika har dakin shi kafin inqaraso yanzu zanzo nan sannan ki sanar da kowa da wowar sa ko zakiji wani yace yaganshi sai kifadan kinji tace dan Allah wai da gaske my bro is back amma bansani ba aikwa yanzu zan sanar momma kowa ma zeji kar kadamu tunda kagaya min kuma ai zance yaqare kamar ma sunji ne kasanni ba asani bama inaya bare kuma ance inyi yace yauwa sis shiyasa nake sonki kiyi sauri fa duk yanda ake ciki ki sanar dani saboda zan fara biyawa gida kafin intaho nan din tace to shikenan yanzu kuwa sai kaji ni yace to shikenan nagode sai anjima katse wayar yayi tare da furzar da iska daga bakin shi yace nagama plan A saura kuma nabiyu,
kwana ya yanko da motar shi lokacin da yaqaraso unguwarsu yana zuwa bakin wani makeken gida yayi horn me gadi ya bude mishi ya shiga ciki be tsaya daidai ta parking ba kawai ya kashe motar tare da fitowa ya shiga cikin falon da sallama ya shiga ciki ba kowa a falon dan haka kawai ya nufi part din shi Kai tsaye anan nasamu damar qarewa falon kallo falone iya falo da ya amsa sunan sa zama fadar abun dake ciki ma bata lokaci ne amma kana gani kasan ba na qananun mutane bane domin yanayin yanda aka qawata shi abunde gwanin burgewa fito warshi ce tasa nade na kallon falon kar yakamani yana fitowa ya nufi upstairs yana zuwa yashiga wani daki bayan yayi sallama anbashi izinin shiga yana shiga yasaki murmushi me qayatarwa saboda tozali da yayi da mahafiyar sa kana ganinta kasan ita ta haife shi saboda tsananin kamar da suke yana zuwa yayi hugging dinta yana cewa nayi missing dinki hajiyata tace nima haka amma ya akai naganka tunyanzu lokacin tashi beyiba raba jikinsa yayi da nata sannan yace wlh wancan dan rainin hankalin ne yakeso ya cazamin kai tace wa kenan yace Sam mana tace yaushe yadawo bansani ba yace wlh dazu da safe naje na dauko shi tace to meyayi maka nan yabata labari aikwa tayi dariya sosai tace lalle wannan tasohuwa ta iya qarfin hali shi kuma baya ganin tsohuwace yadan daga mata qafa shide har yanzu baze canza ba yanzu to a ina kake tunani yake yace wlh bansaniba yanzude wayarki zaki dauko mu gwada kiran shi nasan inyaga number kice watakil ze iya dagawa tace to Allah yasa sannan ta miqa hannu ta dauko wayar a gefenta ta miqa mishi karba yayi yabude sanan yayi searching din number yadannan mishi kira saida tai ta ringing ba har yacire raima tana daf da katsewa kawai yaji andaga shiru yayi bece komai ba sai yamiqawa hajiyar sa wayar mirya qasa qasa yace yimishi magana karba tayi tareda kara wayar akunnen ta sannan tace Assalamu alaikum my son dake wayar a hands free take sai dan haka zasuji koma cikin murya qasa qasa kamar da budurwar sa zeyi waya ya amsa mata sallamar sannan yace hajiya Good evening I hope you are fine tace any thing is ok, when you come back basanar wa sai yanzu nake sani daga can yace nace yagaya miki ai daman befada miki ba kenan tace eh sai yanzu yake sanar dani da sauri dr.shettima yadan daga murya yanda zejishi yace where are you tundazu kakidaga wayata ko ina kafi jin yayi magana yasashi gane cewa wayar a hands free akasakata bayaso kuma yabashi kunya agaban hajiyar dan haka sai yace palace yana fada kuma yakatse kiran bin wayar yayi da kallo sai kuma yayi hanzarin tashi tsaye sannan yace shikenan hajiya ngd bari inje kinga ma min komai sai nadawo yafada a yayin da yaqarasa bakin qofa Da addu'ar fatan nasara ta bishi sannan ya amsa yana qarasa fita daga dakin,
yana fita yafigi motar sa yabar gidan yana fita saiga kiran my sister yashigo da sauri yadaga tare da sa wayar a speaker sannan yace ya ake ciki ne da labari dariya tayi tace me dadi ma kuwa ai bawanda besan dawowar sa yanzu kuma nagayawa momma kana nemanshi shine ta kirashi tace yana ina yace yana hospital wani aiki yakeyi shine face idan yagama tana son ganinsa yanzu de maganar da nakeyi maka yana kan hanyar dawowa yace kai gaskiya na yaba qoqrinki ashe bema dawoba amma yanzu da hajiyata takirashi yace min wai yana nan palace gashi harna fitoma daga gida ina kan hanya tace wlh kawaide gafada maka amma be dawo ba yana kan hanya de watakil ma kuzo atare tunda tundazu akaje dauko shi yace ok saina shikenan sai naqaraso tace ok bey tafada sannan sukayi sallama ta tare dayin rejecteing din kiran sannan yaci gaba da deriving dinshi daman bawani nisa sosai a tsakaninsu dan haka be dade ba yaqarso masaruta yana zuwa kuwa be fito daga motar ba moto ci suka fara shigowa cikin masarautar ajere ajere sunkai wajen goma...........✍
[23/12, 9:23 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
By
Yaya Azeema 😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
Bismillah......
59&60
""""""""""""""""""""""""""""""""""
'bayan motocin sungama shigowa suka daidaita parking sannan suka fara motar gabace drivern yafara fitowa yazagayo yabude mishi qofo saida yaja wajen minti biyar kafin ya zuro qafafunsa ahanakali sannan yaqarasa fitowa gaba dayanshi da sauri dr.shettima shima yabude motarsa yafito qarasowa yayi gurinsa yanacewa sannu da zuwa 'ya labai ko kallon inda yake beyiba yafara tagiya ganin yasashi bin bayan sa duk wanda suka hadu sai yazube yana gaidashi da yimishi barka zuwa amma be amsa wa kowa ba hasalima ko inda suke baya kalla haka yake ta tafiya a tsanake kamar mejin tausayin qasa shide dr.shettima binshi kawai yake azatonsa zega ya nufi part din momma dinsa amma sai yaga yanufi part din Fulani bede tanka masa ba harsuka qaraso bakin part din wadanda suke mata musu baya suka tsaya sukuma suka shiga ciki suna shiga suka tarar da wasu 'yan matan gidan duk sun hallara a falon sai fulani dake zaune kan kujerar ta ta hade rai ta dora qafa daya kan daya yana shigowa ta zuba mishi ido ko kyaftawa batayi yana shigowa 'yan matan da yaran da suka zo don jiransa gaba daya suka nutsu suka fara yimasa sannu da zuwa amma ba wanda ya kula dan ko kallo basu isheshi ba saboda asama yake dan haka yayi wucewar sa part dinshi yana qoqarin yin kwana,
Fulani data gade da gaske wucewar zeyi be kulataba bare yagaida ita hakan ba qaramin hassalata yayi ba a hassale tace uwarka munubiya marar mutunci kawai kaide wallahi anyi asarar haihuwar ka inbadan rashin mutunci irin naka harkazo ta gaba zaka wuce baza ka iya daga kai ka kalleni na bare insamu darajar da zaka gaida ni kalli yaran nan duk dan sabo dakai suka zauna anan suna jiran shigowar ka amma ko kallon su bakayiba wanna wace irin rayuwa ce tsayawa yayi cak da tafiyar da yakeyi saida tagama surutun ta sanna ya juyo ya zuba mata ido yana kallon ta kamar yau yafara ganin ta a hankali ya juyo yadawo yazo har gabanta batayi wani aune ba kawai tajita asama yadaga ta cak wata uwar ashar ta lalubo ta danna masa tana cewa dan uwarka munubiya kasauke ni wlh sai nayi maganin ka agidan nan baza ka sauke ni saida yagama jujjuyata kamar 'yar tsana ya tabbatar da ta jigata sannan ya sauke ta yana sauke ta tafara jin juwa juwa dan haka da sauri ta zauna akan kujera dabas tana dafe kanta tare da sauke numfashi tsugunnowa yayi saitin sai ya manna mata a hannun da ta dafe kanta dashi sannan yashafa kanta kamar yar baby yana gamawa kuwa yaqara gaba abunsa itade takaici ya hanata magana daman yasaba yi mata irin haka shi kuma ta lura dashi yan maganar ne basa nan shiyasa amma tasan da dole zeyi magana koda baze fada mata me dadi ba amma zeyi mata magana tashi tayi fuuu tabar falon ,dr .shettima yana tagaida ita amma bata tsaya sauraron saba tayi wucewar ta 'yan matan ciki natayi mata dariya qasa qasa saboda karta jisu taci musu uwa gashe da dr.shettima suka shigayi shikuma yana amsawa bayan sungama gaiisawar yabi bayan sam,
Ganin haka yasa suma daya bayan daya suka tashi sukabar part din,
"Shikuma yana qarasawa part din sa ya bude yasgiga yana qoqarin rufewa dr shettima yayi saurin saka hannu yana cewa wai kai wane irin mutum ne Nada fara gajiya da wulakan cinka tunda kazo nake maka magana amma sai faman shareni kake yanzu kuma nabiyoka hargida shine kake qoqarin rufewa kai bazaka taba canza haliba ko to wallahi nima nakusa fita daga harkar ka yafada masa yana hade rai dan shima zuwa yanzu yaji haushin abun da yake masa, dakatawa yayi da tafiyar ya zuba mishi ido sannan ahankali yace meyasa zaka hada ni da momma kansan ba abun da natsana irin asani abun da banyi niyaba kai bazakamin uziri ba nadawo agajiye inaso in huta kazo kuna min hayaniya akai nabarmuku gurin kuma still kaci gaba da bina kana damuna aiki ne nace bazan yi ba that's all nagama maganata yafada yanshige wa ciki saide yanzu be rufe qofar ba jinjina kai dr shettima yayi sannan yabishi ciki tunda shi yake nema dole ya sauke kansa qasa yasan inya ce tahaka zebi dashi to abun da yakeso baze taba yiyuwa qarshema saide kowa ransa ya baci shiga yayi shima sannan yasamu guri a falon sa yazauna yana jiran sa inma barcinne yayi ya tashi ze jirasa dan yau ba inda zashi sari ya amince zeyi mata aikwa anan yayi tazama har wajen sallar magriba amma befito ba saida aka kira salllah sannan yaganshi ya fito cikin jallabiya maroon color da ta amshi jikin shi tayi mishi kyau sai haakensa da kyawunshi yaqara fitowa da mamakinsa da yafito yaga dr shettima donshi duk a tunanin sa yatafi beyi zaton zeganshi ba qarasaw yayi kusa dashi saikuma yayi shiru ya rasa me zece mishi saidaga bisani sannan yace muje massalaci mudawo ok yace mishi sannan ya tashi ya shiga bedroom dinsa ba jimawa yadawo suka wuce masallaci tare..,
"bayan sundawo ma direct suka wuce part dinshi saboda yanzuma basu tarar da fulani ba a falo suka zauna sannan dr. Shettima yadanyi gyaran murya sannan yafara magana yanzu dan Allah ya kakeso inyi da bayin Allahn nan andade da kawota amma yau kazo suna jin dadin dawowarka kai kuma ka watsa musu qasa a ido hakan kayi adalci kenan akan dan qaramin abun da betaka kara yakarya ba yakamata ka canza hali wallahi, "tunda yafara magana yake kallonsa saida yaji yayi shiru sannan yace kagama to bazanyi mata ba duk abun da zaka fada kafada danni na riga da nayanke shawara kuma bazan canza ba yana kaiwa nan yayi yunqurin tashi dan barin wajen da sauri ya dakatar dashi dan Allah sam karkamim haka kataimaka kayi badan niba dan son da kakewa iyayenka kuma wlh zan gayawa papa ko kuma inba haka ba wlh Allah inbakai mata ba baqaramar matsala zamu samuba dakai zan cire hannuna akanka daga yau bani bakai kuma zan barmaka hospital dinka,
katsashi yayi da cewa oh dan Allah fa zaka iya barina almost twenty years muna tare amma yau rana daya saboda wata banzar yarinya zakace zaka rabu dani to bismillah ga hanya nan zaka iya tafiya,
cike da taqaicin amsar da yabashi ya tashi ranshi duk abace yace shikenan nabarka lafiya indai na cika dan halak baza ka qara ganina ba kuma kar kazo inda nake daga yau bani bakai yana kai qarshen maganar sa yasa kai yafara tafiya har yakai bakin qofa yana daf da fita ya tsimkayo muryarsa yana cewa zanyi shikenan just because of you cak ya tsaya tare da juyowa a hankali yace da gaske kai yadaga masa alamar tabbatar wa Allah sarki dake yana matuqar son ayi mata aikin yama manta da wulakancin da yaga ma yi masa yanzu da sauri yadawo wajen sa tare da yin hugging dinsa yana masa godiya yaji dadi sosai da har yakasa boyewa inka kalli fuskar sa zaka tabbatar da hakan,
yace amma bro kasan da hakan shine saida ka gama wahalar dani haka harkasa na fara fadar abubuwan da nake ganin bame yiyuwa bane dan jinjina kai yayi sannan yace lalle sai yanzu na tabbatar da yanda kadamu da ita da harzaka iya barina akanta inasane ai nayi maka haka dana gane yanda ka naga kamar kadamu da itane sosai saikace yar uwarka wai meye hadinka da ita dan murmushi dr.shettima yayi sannan yace komai ma kallonshi yayi sannan yace kamar ya komai ma kasanta ne wacece ita?
Shiru yayi kamar me nazari saikuma yace bansan ta ba bansan komai akantaba nide kawai yarinyar ta burgeni tunganin farko danayi mata tunkafin akawota asibitinmu kuma hakannan nakejin yarinyar tana matuqar ban tausayi bansan meyasa ba wlh yaqarasa maganar awani irin yanayi, "sam da yagama jin shirmen shi danshi awajen sa shirme yake jin abun dan haka yace to lalle kam kana ruwa saikaje kaitayi nibanda lokacin irin wadannan abibiwan naka yanzu kataso muje wajen momma yafada yana qarasa miqewa tsaye shima be qara tanka masaba saboda yasan koma me zece mishi ba fahimta zeyiba gwara kawai yayi shiru hakan sai yafi, miqewa yayi shima suka fito tare lokacin da suka qaraso faolon fulani dr.shettima yace baza kaje wajen mutuniyar takaba ku sasanta kasande dazu kayi mata laifi yanzu cike take dakai,
yace kai rabu da tayi tagama bazanje ba inbatayi wasaba ma nadena shigowa part dinta idan nazo garinnan tafiya takura wlh, kallon shi yayi yace hmmm bade kasan gaskiya amma meye abun takura anan yace bazaka gane ba kawai mubar maganar shiru yayi har suka gama fitowa daga falo suka nufi inda bangaren su momma din yake suna tafiya suna dan hirar jefi jefi dan qarfin maganar ma dr.shettima ne saide idan yaga dama yake cemishi uhm ko uhm uhm......,
*WAYE SAM..?*
*PLS KU TSAYA KU KARANTA WANNAN DAN TSOƘACIN DAZANYI*
"Dan tsokaci ga wasu makatantan nasan mutane da yawa in akazo za a bada labari ko fadar asalin mutum suna tsallakewa basa karantawa to wlh inde har baka tsayawa ka karanta wani labarin da zan bayar ba to ze zamana kamar kana gaba kana baya saboda baza ka fahimta ba ko ka karanta ba komai zaka gane ba yanzu bare kuma ace baka karantawa to koda kayi gabama baza kagane komai ba dole saida na baya zaka tashi na gaba duk wani abu da na rubuta yana da amfani nan gaba saboda bakomai nake fada ba yanda zaka gane sai da kadan kadan zan fara warware muku har muhau hanya afara littafi dan yanzu kawai muna sharar fage ne daga nan kuma zamu fara somin taɓi sannan mufara gundarin labarin dan har yanzu akaso dari na littafin ko kaso biyar bamuyi ba yanayin labarin me tsawone dan haka nakebin sa ahankali nake komai daki daki"""
______________*SAM*
cikakken sunanshi shine SAMEER ABDALLAH SAMEER,"shidane ga munubiya,munbiya yar gidan sa'adatu wacce akece mata maman yan biyu abaya inbaku manta ba nace sa'adatu kishiyar fulani Amaryar sarki Muhammad sameer me murabus wanda akecewa papa,loƙacin dasu munbiya suka taso suna ƴan mata sai sarki da da qanensa suka yanke shawarar hada yiwa ƴaƴan su auren zumumta ayi tuwona maina ita munubiya aka aura mata babban dan waziri ALƘASIM kenan ita kuma karima aka aura mata babban dan galadima ibrahim kenan autan su sarki muhammad ALƘASIM waziri yana da mata daya matar ba yarnan qasar bace shima da yaje karatu England ya hadu da ita said soyayya ta shiga tsakanin su me qarfi hartakai su da aure amma fa da qyar iyayenta suka yarda suka bashi ita kuma suka gindaya masa sharadai kala kala aciki harda baze qara aure ba saide yazaun da ita kadai saboda son da yake mata yasa duk abun da suke so yace yaji ya yarda ya amince inda ahalin yanzu suke da yara biyar maza uku sai mata biyu, ABDALLAH, sai muhammad, sannan HASHIM,mata kuma suna da sumayya da ANISA,wanda a halin yanzu matan duk sunyi aure kowace ma da ƴaƴanta suma mazan duk sunyi aure amma banda auwal dake shine auta kuma dan gayune ƴan mata basa gabansa rayuwarsa yakeyi shikadai....
shikuma ibrahim galadima matansa biyu,yana da yara biyu kacal saboda dayar matar bata taba haihuwa ba sai uwargindan shice ta haifa mishi yaran AMINU da AMINA, aminar batai aure ba itama har yanzu sai babba dan shine wanda ya auri karima ƴar biyun munubiya wanda ayanzu suke da yara uku dake suma ƴan biyune sai Allah duk yabasu ƴan biyu itama tana da ƴan biyu amma mazane nata AMMAR da AMAR sai autarsu RAHMA,
"sai Abdallah miji ga munubiya,sune iyayen sameer wanda akecewa sam sukuma wasu daga gidan kakanninsa kenan irin su muhammad da qannensa sai kuma matayensu da wasu manya de wadanda suka isa dashi su suke cemasa mesunan baba saboda sunan sarkin da yarasu mahaifinsu wasu kuma sukan ce masa uncle sam, wasu kuma abokanen sa na school suke cemasa sas atakaice de yana da sunayen wajen hudu kowa da abun da yake cemishi,
SAMEER ABDALLAH SAMEER shima shine babba awajen su sai qannen sa mata da suma ƴanbiyu ne Hamra da Amra su ukune awajen iyayensu,
Sameer bashine kakansa ba a ƙa'ida sunan Alƙasim yakamata yasa ka to amma dayake sarki muhammad yadora duk wani da akan