Showing 63001 words to 66000 words out of 136570 words

Chapter 22 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5418

Allah ya yarda ki kwantar da hankalinki sannan ta juya tana kallon bossay tace Aliyu me yake faruwane munga jikinka duk amace me dr. Yace maka huci yadan furzar daga bakin sa sannan yace dadda ba mutuwa tayi ba amma de dr. yace dayan biyu ko tarayu ko ta mutu tasamu accident din brain and blood dole sai anyi mata aiki kuma doctor din dazeyi mata ba yanan sai nan da two weeks zedawo sannan za ayi mata sai yan dakata sannan yadora da cewa yanzu sunce zamu iya tafiya ba wanda ze samu damar ganinta sai angama yimata aiki dadda ce takatse mishi maganar dacewa na shiga uku na lalace yanzu haka za abarta har sainanda sati biyu tana kwance  so ake akashe min yarinya lokacinta beyiba to wlh banyarda ba kaf girman asibitin nan ace ba wanda ze iya duba ta sai wani yadawo daga wani waje gskiya wannan maganar da sake inde ba kasheta zasuyiba faruq ne da yau yafara ganin ta maganar ta taso tabashi dariya amma sai yaruqe yace dadda kamar yanda yaji suna kiranta dashi sannan yace bafa zasu kashe ta ba tunda kikaji sunce haka to sunsan me suke yi wannan asibitin bakamar kowane asibitin yake ba inde kinga mutum ya rasu anan to daman Allah yayi anan ze mutu kwananshi yaqare amma suna aiki da kwakwalwa basa wasa da marar sa lfy kuma zasu kula da ita fiye da yanda kike tunani bossay ne yadora mata dacewa dadda aikin ne ba kowa yake yiba saboda riskinshi sai wanda ya kware a harkar sosai inba hakaba za a iya rasa ranta gaba daya ma dan haka ki kwantar da hankalinki babu abun da ze sameta in sha Allah shiru tayi bawai dan ta yarda dazan censu saidan ba yarda zatayi idan tace zata daga murya akai ina zatakaita dole ta hakura ta bi duk abun da sukace Ammi ce ta ruqota ta zaunar da ita tare da qara tabbatar mata ba abun daze faru da ita saboda tasan asibitin basa wasa da aikin su bare harsuzama barin wani duniya saide idan Allah ne yakarbi abunsa kuma wannan daman ba wanda ya isa yahana idan Allah yaso karba dole ayi hakuri hakade taita kwantar mata da hankali har ta fahimce su Ammi tace to yaje ya karbo number dr. din inyaso sai suringa kira suna jin halin da take ciki da to ya amsa mata sannan ya juya ya ya koma office din be dade ba yadawo yace musu ya karbo su tafi miqewa sukayi gaba dayansu kowa jiki ba kuzari suka fito daga asibitin dadda tace itade amaida ta gida Ammi tace a'a tayi hakuri su wace tare ai bazataji dadin zaman gidan ba ita kadai dadda tace taji su maidata da kwai abun da zatayi sukace to su wuce gidan tare tayi abun da zatayi ta dauki duk abun da zata dauka tunda daman sungama shirya wa sai suje tare sujirata tagama
nanma haka tace musu bata yarda ba kawai suje ita ta zatahau motar haya Ammi tace dadda bafa inda zamu bari kije ke kadai bossay ya dora dacewa daman kuma ga abun da yafaru wai wasune sukaje fa gidan sukayi musu haka kuma take so ta qara komawa haba dadda sai kace ba kyason ranki bekamata ki komaba kar kije suqara dawowa suyi miki wani abun kawai ki muje ni karma kikoma gidan kwata kwata kibar musu komai
Dadda jin batun nasu kowa da abun da yake cewa dole ta hakura amma ita tana da dalilin ta nason komawa to amma kar tadage akan komawar har sufara zargin wani abun dan haka tayanke shawarar kawai ta bisun inyaso daga baya ta saci hanya ta koma gidan (tofa dadda me kika ajiye agidan nifa nafara zargin wannan yar tsohuwar nan 🤔dana kasa fahimtar inda ta dosa har yanzu)jin shirun nata yasa Ammi ta cewa faruq yashiga mota yata fi shikadai  ita kuma zasu hau motar bossay ita da dadda har yajuya ze shiga motar Ammi tace kai naga har wani sauri kake to wlh kayi gudun haukannan sai na saba maka kama jira mu fara tafiya kaikuma kabi  bayan mu saura inga ka wuce mu tana gama fadar haka ta budewa dadda baya tace dadda shiga ba musu dadda tasa kai ta shiga ita kuma ta rufe tasake bude gaba ta shiga  tundazu daman bossay ya shiga dan haka kawai tayar da motar yayi tare da yin rivers yadanna hancin motar yana tafiya kamar bayaso yayin da faruq kuma yake binsu abaya cike da takaicin umarnin da Ammi ta bashi gashi kuma yaga alamar yayan nasu kamar ma yana sane yake irin wannan tafiyar oho
shikam bossay bema san yanai ba dan yama manta da shi abayansa ahaka suka fita daga asibitin kowa zuciyar sa ba dadi ...........
               
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
                    By
             Yaya Azeema 😎

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                  🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                              

    Bismillah...........

                    39&40

               """""""""""""""""""""""""

________*MASARAUTA*

   Baba na tsugunne gaban dokuna yana musu barruwa wannan bawan me suna Hamza ya shigo gurin da saurin sa kamar ze tashi sama yana zuwa baba ya miqe yace dannan lafiya naganka haka saida hamza ya dan juya baya da gefe gefe ya tabbatar da ba kowa sannan yayi qasa da murya yace yanzu nazo wucewa naji wani bafade yana jin radio kasan me naji aciki yace a'a yace cigiyar ka ake fa kaine SULAIMAN KABEER me shanu  ko?

Baba ya jinjina kai yace eh nine me kaji ance yace naji sunaka sannan ayanda kazo ahaka naji sun lissafo kaminin ka da kuma kayan dakasa baba cike da jin dadi kamar ance mishi yau ze bar gidan sai kuma can daga baya da yayi wani tunani sai yanayinsa ya canza gaba daya hamza yace baba yanzu ya za ayi kenan naji anfadi sunan unuguwar da kake saide kuma bangane kwatancen ba inaso ka qara yimin bayani sosai ta yanda zanfi fahimata budar bakin baba sai yace lafiya qalau yaro nagode basai ka tayani ba kabarshi kawai da mamaki hamza ya kalleshi ya ga tambayar da yayi mishi daban amma kallar amsar da yabayar daban har ze qara magana sai baba yaqara cewa karkace komai wlh nagide kaje yafada tare da dafa kafadunsa yajuya shi irin yatafi nan juyawar dazeyi kuma sai yaga shugabansu gabanshi ne yafadi yana tunani Allah yasa beji me suke cewa ba tunda ga farko sai kuma ya tuna ashe dalilin da yasa baba qin bashi amsa da yayi alokaci daya dake ya iya siyasa shima kawai sai yasaki murmushi tare da cewa baba harda su kora kuma shikenan to natafi yana gama fada kuma yamaida kallon sa ga shugaba dashima shi yake kallo yana binsu da kallon tuhuma saboda beji me suke cewa ba tun daga farko Hamzane ya shafa kansa tare da dan sakin wani murmushin yace oga saidakai Allah barmana kai tuba nake na karya doka daman wallahi nagama komai bani da aikin yi kuma banason zama ni kadai shiyasa nace bari inzo intaya shi tunda naga SHAMSU baya nan ko bashida lafiya ne ko kuma aikenshi akai bande sani ba sai gashi kuma yace ma bayaso intafi amma dan Allah kaina aqasa yafada yana sadda kansa qasa alamar tuba wani kallo ya watsa masa me kama da na tsana sannan yace bance kar naqara ganinku tare ba bakwa jin magana ko to ku jira hukun cin sarki ai daman na gaya muku ku kula tun ranar danaganku na farko nasanya muku ido duk wani motsinku akan ido na kuke yinshi yanzu shigowar ka nagani shiyasa nabiyo ku dan haka kujira kira yana kaiwa nan ya juya yabarsu agun dan murmushi kawai hamza yayi tare da juyowa ya kalli baba kafin ma yayi magana baba yariga shi dacewa Allah sarki yaro na jamaka ko kayi hakuri dan Allah duk abun da za atambayeka kace nine nake kiranka kai kuma kaga tsufana shiyasa kake kasa zuwa duk lokacin da nakira ka nizan dauki laifin Hamza yace baba kar kadamu dan Allah aide basu isa sunmana abun da Allah beyimana ba Allah yafisu Allah ze karemu daga duk sharrin daze mana dan baze fadi iya abun da yagani ba nasan halinsa said yaqara nasa sharrin yanzu abun da nakeso dakai shine yi sauri kagaya min wannan ce kawai damar da muke da ita tunda ya riga da yaganmu kuma nasan baze dawo ba saide kira yazo garemu fadamin yanzu kawai baba da kallon tausayi yabi yaron sai yaji qaunarsa har cikin ransa ahankali yace yaro baka jin tsoro kawai ina ganin mu hakura Allah ya kawo mana wani taimakon ta bangaren da bamuyi zato ba saboda bana so ta sanadina kashiga wata matsalar hamza yace ba komai kar kadamu ba matsalar da zanshiga yace to Allah yasa sai kuma yayi shiru saida hamza yaqara cewa loqacin fa ya wuce wa baba kayi sauri kafada kar suzo suriske mu anan still baba beyi magana ba sai da ga bisani sannan yadan nufasa numfasawa yace a unguwar kurna nake wajen masallacin na kowa idan kaje zakabi barin hannuka dakke tafiya bayan ka wuce masallacin da kadan sai kayi kwana hagu layi na uku zaka shiga kana shiga zaka ga wasu gida iri daya to basu ba nagabansu zaka ganshi me farin fanti da baqar qofa to nanne gida na hamza yace shikenan angama zan sanar da wani abokina in Allah ya yarda zaije har gidan yasanar dasu ka kwantar da hankalinka zantabbatar da iyalinka sun san halin da kake ciki koda zan rasa raina ne zanfita da kaina  zanmaka wannan aikin da yardar Allah saboda tsabar jin dadi baba har yar qwalla ce ta tarar masa a ido sannan yace yaro Allah yayi maka albarka Allah ya albarkarci rayuwar ka yanda ka taimake ni kaima Allah ya taimake ka aduk halin da ka tsinci kanka Allah baka abun da kakeso duniya da lahira

da ameen hamza ya amsa shima yaji dadin addu'ar da yayi mishi tunda yake betaba samun wanda ze mishi irin wannan addu'ar ba sabo da amaraya yataso shikadai ne aduniyar nan bashi da kowa besan kowaba shiyasa tunda yaga baba yaji ya bashi tausayi kuma yadauke alqawarin taimaka masa domin bayaso 'ya'yan sa sutaso a haka basu da uba rayuwa ba iyaye baqaramar matsala kake fuskanta ba a rayuwa baba ne yakatse masa tunanin sa yace yaro naji kayi shiru tunanin me kake haka girgiza masa kai yayi yace bakomai ni zantafi sai anjima yafada yana juyawa tare da barin wajen baba binsa da ido yayi yana qara jin son yaron aransa yadade yana tunanin abubuwa kafin daga bisani kuma yajuya ya koma dan qarasa aikin da yake yi yana cikin yi yama kusa gamawa

Kamar daga sama yaji anshaqo shi tabaya tare da miqar dashi tsaye juyo dashi akayi kafin yayi wani yunquri yaji an kifa masa mari begama tantancewa ba yaji qarin wani marin da mamaki yadago yana kallon wanda yake marinsa ganin wannan bafaden da yayi mishi bulala tun ranar da yazo yasa beyi mammaki ba yasan zeyi fiye da wannan ma saboda ba imani ne dashi mutumin da ya mareshi bece mishi komai ba kawai yafara janshi kuma dan mugunta ta baya yake janshi ga shi ya matse masa wuya ana jawoshi ba fada akayi dashi ba part din fulani aka nufa dashi ana zuwa bakin qofar falon ya jefashi ciki kamar kayan wanki aikwa ba qaramar buguwa baba yayi ba dan da kyar ya iya dagowa sannan yadaidai ta kansa yazauna da qyar saboda dauriyace kawai irin tashi amma da ko tashi baze iya yiba yana zama aka shigo da hamza shima jefishi din akai amma dake shi da kwarinshi be kai ga faduwa ba yade yi tangal tangal ze fadi sai kuma ya dake ya tsaya da qafafunsa sannan ya tsugunna tare da sada kansa qasa saboda bama yaso su hada ido da baba shiyasa ya kawar da kansa

fulani ce dake hakimce a kujerarta ta dora qafa dayakan daya tana girgizata ta zuba musu ido tana yi musu wani matsiyacin kallo yayin da gefenta kuma shugabane agurfane fulani tace ina sauraronka fadi abun da kaji suna cewa
saida ya juya yayi musu wani irin kallo me nuni dacewa kunshigo hannu zakuce ubanku saida yasakar musu murmushi batare da sanin fulani ba sannan yace Allah ja daranki ranki yadade uwar masarauta tun zuwan wannan tsohon naga yanayin take taken shi na rashin gaskiya kamar ma da wata manufa yazo gidan  nan ko kuma turoshi akayi domin tarwatsa farin cikin masarauta tunda naga haka sai naked bibiyar shi batare da saninshi ahaka nagano bakinsu daya da hamza kullum suna tare wani lokacin ma adaki daya suke kwana banta ba jin tattaunawar suba sai yau nazo wucewa naga shigarshi  bangare dokuna shiyasa nayi saurin binsa abaya ina shiga kunnena yajiyo min abun da saida na kusan faduwa jinai wannan tsohon yana cewa kai tunda kazo ka kasa tabuka komai shekarar ka nawa amma ba abun da kayi nan da sati daya ni zangama dashi in koma inda nafito inje aban kudade na kai kuma kana nan ana wulakanta ka to ni bazan iya wanna bata lokacin ba dan inagama ko sati dayan bazan ba zan kammala abun da yakawo ni inwuce in barka inkaga dama ka taho inkuma anan zakai tazama saikayi

sai shi kuma hamza yace mishi ai shima yana gab da kammala nasa watakil ma yariga shi gamawa daga nan baqarasa jin maganar tasu ba najuyo saboda bana so sun ankara dani su cutar dani tunda mugayen muta nene su da harzanje ingaywa me martaba sai naga gwara nafara sanar dake ayi gaggawar daukan mataki akansu kafin su cimma mugun nufinsu yaqara sa fada harda dan guntun munafikin hawayen qarya.....

Fulani bata son lokacin da ta miqe tsaye ba tana takawa ahankali cike da qasaita ta qaraso gabansu  tsabar yanda takejin zuciyarta nayi mata quna dan tazo wuya qiris take jira dan  zata iya kashesu da hannun ta kafin su sukashe su gwara ita tafara kashesu amma bahalin yin hakan ayanzu  saboda tanaso sufara fada mata wanda ya turo su zaga yasu  ta shiga yi  batare da ta tanka musuba saboda da tana tunanin wane irin hukunci zatayi musu
Allah sarki bayin Allah sunyi tsuru tsuru da su suna mamakin irin wannan sharrin da yayi musu musamman baba be taba tunani irin wannan sharrin ze musuba shikam hamza beyi mamaki ba sosai saboda daman yasan halinsa tun ba yauba yasaba yiwa mutane sharri amma kuma betaba gani yayi irin wannanba daga kai yayi sai suka hada ido da shugaba wani murmushi yasakar masa tare da kashe mishi ido daya kawar dakai hamza yayi tare da ayyana abubuwan dazeyi wa wannan mutumin idan angama yankewa musu hukunci sai yaji ya qara tsanar mutumin nan ko ganinshi ma baya sonyi kallon sa yamayar ga baba dake ta faman rawar jiki ga zufa da take zubo masa duk yabi ya fita hayya cinsa yana tunanin irin hukun cin da za ayi masa san ba qaramin tsure wa yayi ba dan yasan babu wanda ze yarda dasu kowa in yaji hakan baze yi tunanin suna da gaskiya ba saboda ba wanda ze tsaya yaji ta bakinsu akan zancen  haka yake ko ba haka bane

Fulani ce ta data gama binsu da kallon tsana sannan ta koma kan kujerarta ta hakimce sanan tacewa wani bafade da suke kira da me doruna shine wanda yaje yataho da baba har ya mareshi kumafa ba asashiba kawai zallar mugunta ce irin tashi.......
kiranshi fulani tayi ya qaraso kusa da ita da hanzarinsa yace gani yake uwar masarautar nan umarnin ki kawai nake jira za arabasu da ransune yanzu ko sai anjima....daga mishi hannu tayi sannan tace mishi afara hora min su yanzu kafin suyi bayanin wanda ya aiko su tana gama fada yace yanzu kuwa kamar anyi angama yana gama fadar haka ya miqe tare da zaro wata narkekiyar zabgegiyar makadediyar zugegiyar shambareriyar 😂bulala ga wani tsayi da kauri  da duk kallon kurillar ka baka isa ka gano da me akayita ba dan ko doki kaga andakeshi da ita sai yabaka tausayi  bare kuma bil adama wanda ganinta ma kadai ya isa sa mutum shiga taitayinsa komai yake sai ya nutsu dan qaniyarsa......

yana zuwa ya daddage iya qarfinsa yadaga ta shimfidawa hamza a gadon baya aikwa ta shigeshi runtse idonsa yayi qam begama tantance zafin ba aka qara dora mishi wata jiyayi kamar yasaki kuka amma bazeyi ba saboda taurin rai irin nasa yanaji kuma ko motsi beyiba kuma be bude idon saba saida yaji antsaya da dukansa sannan ya bude idonsa da duk sun canza kala daga fari zuwa jajawur kamar gauta sai fuskarshi da ya hade kamar anyi mishi albishir da gidan wuta daga su yayi ya sauke su akan me dukan nashi da yaga ya tsaya akansa qeqam yaqi matsawa harara ya watsa mishi sannan ya kawar da kansa shima harar yayi mishi tare da matsawa daga gurin shi sannan ya nufi wajen baba da niyar shima ya bashi tashi alawar me zaki
Allah sarki bawan Allah baba ai tunda yaga bulalar ya tsure dan lokacin da akayi mishi ta farko bada irin wannan bace wannan ba qaramin tayar mishi da hankali tayi ba ga jikinshi sai faman kyarma yake ido yayi zuru zuru sai faman hadiyar yawu kake da qyar dan shima neman barin ma kogaronsa yake da yaga andaga ta kwa ansauke ta ajikin hamza ai tuni yasaki futsari awajen  dan ji yayi kamar ajikin shi ta sauka😂 (Allah sarki baba daga dukan wani sai sakin futsari to ina ga kai aka daka watakil kuma sai kasakar musu tutu ka lalata musu falon da hamami)

Yana gani andaga ta za asauke mishi ita abaya yayi saurin runtse ido yana addu'ar Allah yasa yacika da imani dan yasan wannan bulalar idan ta sauak

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login