Showing 6001 words to 9000 words out of 136570 words

Chapter 3 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5444

Allah yakaimu goben.

Sai ta amsa masa da "ameen" sannan ta maida kallon ta ga yaron da yadaɗe dayin baccin wahala ya lafe ajikin ta sai faman ajiyar zuciya da yake saukewa, shafa fuskar shi tayi cike da tausayin shi tace "Allah sarki Allah yabawa mahaifiyar ka lafiya Allah yaraya mana kai Allah yasa muzauna tare da kai har ƙarshen numfashin mu,

Malam dake gefen ta ya amsa mata da "ameen yana me miƙewa daga wajen yace "ni bari inje in ɗan watsa ruwa in fito kafin yatashi, sai inje in ɗan siyo masa kayan sawa da abubuwan yara yadan rage zafi nasan zaiji daɗin hakan, ki kula dashi dan Allah ya ƙarasa faɗa yana shigewa ɗaki, bayan ta amsa masa da "to" sannan  itama ta miƙe daga gurin takai shi ɗakinta takwantar da shi.

Tun daga wannan rana ba labarin Alhaji shiru shiru tun suna jiran tsammani har suka fara cire rai baki ɗaya suka cigaba da kula dashi tamkar ɗan cikin su, haka suke ta bashi kulawa har yagirma dan shi kanshi zuwa yanzu ba abun da yake iya tunawa a rayuwar sa ta baya suma kuma basu taɓa nuna mishi basu suka haife shi ba  saboda lokacin da abun yafaru bashi da wayo befi irin shekara uku ba inma yakai dan haka ba abun da yake tunawa dan zuwa yanzuma har sun sakashi a makaranta,

Tun yana yaro ƴan mata suke rububi akansa ahaka ma wai begama girma ba yazama saurayi lokacin suna ƙoƙarin fara jarrabawar Junior WAEC yayin kuma da shekarunsa yakai 15 kwatsam sai ga ciki ajikin Hadizatu sunyi farin ciki sosai da samun wannan ciki  murna ba a magana tsakanin waɗannana mata da mijin sunci gaba da ta rairayar cikin a haka har watannin haihuwata yayi ta suntulo ƴarta kyakkyawa tubarukallahu Masha Allah haka ranar suna yarinya taci suna NADEEYA ahaka suka cigaba da rainon ta su da sameer dan shi kamar ma yafisu son ta kullum tana hannun sa abu biyune yake rabashi da ita bacci ko idan yatafi makaranta yana dawowa kuwa zai ƙara ɗaukar ta, itama kuma tasaba da shi dan ko kuka take tana ganinshi zata fara wangale baki tana dariya, haka suke ta rayuwarsu cike da farin ciki hartayi wayo sosai kuma wai duk wannan tsawon lokacin da suka dauka Dadda ko sau ɗaya bata taɓa marmarin zuwa gida ba saide shi wani loƙacin yana zuwa yaga ƴan uwansa yadawo yayi-yayi da ita suje amma tace ita ba inda zata saboda tasan inma taje ba daɗi zataji ba kuma bata da kowa sai mahaifinta shikuma kishiyar mamanta ta mallakeshi ko takanta bayayi bare har yasaurare ta kwata-kwata baruwansa da ita shiyasa itama bata damu da ganin nasaba saboda tana ganin kamar da saninsa yakeyi mata hakan,

Har Nadeeya takai wajen shekara goma bata jeba saida akace mahaifin nata ba lafiya sannan suka shirya gaba ɗayan su, suka tafi, tun a hanya take jin gaban ta na faɗuwa suna zuwa kuwa tun daga ƙofar gidan taga mutane jikin tane ya ƙara yin sanyi ko ba agaya mata ba tasan shikenan ta rasa mahaifin ta,

"Hawaye ne suka shiga rige-rigen sauko mata akan fuskarta sai yanzu take nadama da dana sanin abun da tayiwa mahaifinta tasan bata kyauta ba duk lalacewar uba ubane ba a canza mishi suna da wannan tunane-tunanen taƙarasa shiga cikin gidan ita da Nadeeya shikuma Malam sunka tsaya awaje shida Sameer suna gaisawa da mutane".

tana shiga wata ƙawarta tun loƙacin da take garin tazo ta rungume ta, tana yi mata sannu da zuwa yimata ya haƙuri haka de akai ta jajantawa juna ana zuwa anayi mata gaisuwa, bata tafi ba kuwa saida tabari akai sadakar bakwai saboda taɗanji daɗin zaman gidan tasamu sauyi daga wajen  HANNE kishiyar mahaifiyar tata yanzu batai mata abun da take mata da ba duk dade bawani sakar mata fuska tayi ba amma ita hakanma yayi mata daɗi, ana cika kwana bakwai suka koma garin su,

Bayan sun dawo ne da ƴan watanni ita ma Nadeeya tafara zuwa makaranta loƙacin tana da shekara biyar shikuma yana da shekara 15 tare suke zuwa da Sameer su dawo kullum shi yake ɗaukanta yakaita har makaranta ahannun shi dake makarantar basu da ma nisa da gidan, kullum kansu ƙara haɗuwa yake suna ƙara shaƙuwa da junansu a haka har yakammala secondary ɗinshi itakuma lokacin tagama primary zatashiga secondary, duk daya gama tashi hakan besa yadena kaita ba kafin yasamu yashiga jami'a, saboda yanzu Malam bashida isasshen kuɗin daze sakashi a university dole sai yajira zuwa wata shekarar sai ya shiga,

Shekar na zagayowa kuwa kamar yanda malam yayi masa alƙawari aka samar masa admission, Allah yasa yafara zuwa university....

Bayan shekara 2
Can nagano ta a tsugunne gaban kurfoti  tana tafaman haɗa garwashin yaƙi kamawa ta tashi tana gunguni ta miƙe tsaye, "Doguwa ce me ɗan jiki irin matan  nanne manya ga tsaho ga jiki kuma fara ce dan har tafi mamanta haske, tana tafiya ta shiga cikin falo tana cewa "Ummi dan Allah kizo kiga wutannan wallahi taƙi kamawa tun ɗazu nake ta fama da ita, taƙarasa faɗar maganar cike da nuna gajiyawa atattare da ita,sannan ta shiga ƙoƙarin zama tana faman yarfe hannu tana cewa wash...wayyo Allah na Allah wutar nan natsani haɗata...

Da sauri Ummin ta ta tace "wallahi Nadeeya kifita daga ido na in rufe bana son wannan banzan sakarcin naki keda komai na mata baki iyaba duk abun da aka saki sai kice ke kaza ke wannan ke wancan ko, "to wallahi daga yanzu komai na gidan nan ke zanbarwa shi zan nadena taɓa ko tsinke tunda abun naki kullum daɗa gaba yake, kin tashi daga nan kinje kin haɗa ta ko sai na tashi kanki,

Tashi tayi dasauri tana turo baki tana ƙoƙarin fita sukayi karo da Sameer ya shigo fuskar ɗauke da murmushi akai,i yace "to raka mata ni da nake namiji ma gashinan ai na haɗa kuma takama saki je ki ɗora abun daza ki ɗora,

Cike da jin daɗi tace "yauwa yayana nakaina shiyasa nake sonka nagode ma..
Ummi ta kalle su tace "Daman mana kyace haka tunda daman ai duk wani abu shiyake ɗaure miki gindi kike yinshi zanyi maganin ku ne gaba ɗayan sai muga in kinyi aure maga uban wanda ze na miki aikin gidan da ba kya ƙauna,

"Da sauri tace "Ummi ni ai ba auran da zanyi gwara inzauna awajen ku nafi jin daɗi gaku ga yayana, me zanyi kuma awani gidan,

Tunda agarin gaɓa gaɓa muke meze hana muzaun muzuba miki ido munajin daɗi, cewa mahaifiyar tata,


"Allah Ummi dagaske nake...

Katseta tayi da cewa kinga fita kiban waje kije kiyi abun da nasaki kafin ranki yaɓaci ya yanzun nan,

Bata kuma cewa komai ba ta juya tafiya tana qara hade fuska ita ta tsani taji ance mata zatayi aure shikenan kuma sai ta tafi tabarsu ita bazata iyaba,

tana fita sameer ya juya ze bita Ummi tai saurin kiranshi tace "dawo kazauna daman ai duk kai kake ƙara lalatata takewa mutane abun dataga dama yarinya sai rashin son aiki ga shegiyar tsiwa kai haka kake son ganin ta ko?

"Kai Ummi yanzu meye laifi na danna kula da ƙanwata ita kadaice fa dani dole innu na mata so da kulawa wallahi,

tace "to shikenan ai sai kai tayi kaga nan gaba saika dena zuwa ko ina ka zauna karinga yi mata duk abun datakeso da ayyukan ta dan bazan cigaba da wahalaba bayan ina da budurwa acikin gidana, tana rufe baki yace...

"Ai wannan me sauƙi ne kar ki wani damu Ummi duk zan ringayi wallahi,

Cike da takaicin shi da yake bata shi kwata-kwata komai za ace baze taɓa goyan bayan wani ba sai de yagoyi banyan ta, kallon shi tayi tace "kaga tashi kabar gurin nan kaima, kaida kullum baka canza hali, duk abun da za'a faɗa ma indai akanta ne a iska kake ɗaukar sa, wallahi sai na fara saka ƙafar wando dakai acikin gidan nan idan baka fita daga ido na ba,

Dariya kawai yayi sannan yace "Allah huci zuciyarki Ummin mu, Allah yabar mana ke yabaki tsawon kwana me amfani daga nan har sama da shekara ɗari da wani abun" daman haka yake kullum idan yaga tana ƙoƙarin jin haushi haka ze zauna yai tai mata daɗin baki yana yikuwa zata saki ranta tana jin daɗin hakan har cikin ranta, yanzu ma kamar kullum yace masara tuni tafara sakin murmushi tana amsawa da ameen..., Har ta shantake ma ya fita wajen ƙanwar tasa bata hanasa ba....


Bayan wasu ƴan shekaru ya kammala degree ɗinsa inda yakaranci aikin likitanci fannin kwakwalwa bayan kammalawar sane kuma besamu aikin yiba sai malam ya ɗorashi akan harkar kasuwamci inda yanema mishi tsaron wani shagon amininshi da suke kasuwancin su tare yafara zuwa cikin ikon Allah kuma sai suka samu buɗi adan ƙanƙanan loƙaci,
kuma duk da yawan 'yan matan dasuke kawo mishi ƙoƙon bararsu garashi tunda ga kan ƴan makarantarsu zuwa masu siyayya wajensa amma be taɓa jin ko da wasa wata ta mishiba kwatakwata ba wacce ta kwanta mishi arai har yanzu itama kuma Nadeeya haryau bata kula Samari anmata faɗan amma abanza taƙi ji dan acewar tama bazatayi auren ba,

Malam da yaga abun nasu ba me ƙarewa bane kawai sai yasa mu Ummi loƙacin tana ɗaki yaje da maganar akan yakamata fa suyi wani tunanin abun da yadace akan yaran nan bawai subarsu haka suna kallon su ba,

karkaɗa kai Ummi tayi sannan tace "ni a ganina Malam yaran nan kawai muhaɗa su aure inaganin hakan se yafi ai,

Sai Malam yace "nima nayi tuna nin hakan amma kuma da na hanga sainaga to shi Sameer yaza muyi dashi tundade be san bamu muka haifeshi ba kina ganin hakan zai yiyu kuwa?

Ɗan jim tayi kaɗan sannan tace "Hakane Malam ai daman ko badaɗe ko bajima dole mu sanar dashi gaskiyar al amari kaga kuma yanzu ai yariga da ya mallaki hankalinshi ze fahimce mu ina ganin kawai yanzu ne loƙacin da yakamata musanar dashi sannan muhaɗa aurensu nasan bazeƙi hakan ba duba da yanda suka shaƙu da juna inaganin baza su bijirewa maganar mu ba kokwa yakagani?

yace "maganarki gaskiya ce hakan yakamata muyi kawai ai da zafi zafi akan bugi qarfe kawai je ki kirasu dukan su yanzu ayita taƙare asan inda aka dosa ko,

tace "to" tare da muƙewa ta fita ba jimawa suka dawo ɗakin tare da yaran har taje takira su, gaba ɗayan su suka zauna a ƙasa tare da cewa "Baba barkanka da hutawa"

yace "barkan kude, sannan yayi shiru, saida kowa yanutsu sannan malam yafara salatin annabi sannnan yafara magana a nutse yafara kiran sunan shi yace...

"Sameer zan fara dakai domin wannan kiranma gaba ɗaya domin kane cike da ladabi da biyayya yace "to' baba yana ƙara sake zama da nutsuwa domin jin bayanin da akace domin sane,

malam yaci gaba da cewa  "da farko de zanfara maka nasiha akan duk abun da yasame ka kaɗauke shi a matsayin ƙaddar da kuma jarabtar da Allah yayi maka domin ganin zakai haƙuri da tawakkali ko kuma akasin haka ka rungumi ƙaddarar ka da hannu bibbiyu kayi addu'ar Allah ya sassauta maka koma me zakaji aranka, ita kuma Allah ya bata lafiya idan tana raye kuma Allah ya haɗaku, muma ka fahimce muma bada son ranmu hakan ta faru ba kana jina?

Ya amsa da cewe "Ehh, baba in sha Allahu duk da yaɗan shiga ruɗun jin waɗannan maganganun dan har wata faɗuwar gaba yake ji, dan besan inda suka dosa ba,

Malam ya ɗan jinjina kai yace "to masha Allah haka nake sonji ina me ƙara baka hakuri akan abun da zakaji daga garemu, shide har yanzu a ƙagare yake dajin abun daza ace mishi, saida malam yaɗan numfasa sannan yace gaskiyar magana malam sameer bamune iyayanka ba kuma bamune muka haifeka ba hasalima bamusan inda naka iyayen suke ba kawaide a.......

Bai ƙarasa maganar da yake ba sakamakon miƙewar da yaga Sameer ɗin yayi bashi kaɗai bama har Nadeeya saida ta miƙe dan baƙaramin razana sukai ba dajin wannan batun dasauri malam yaka moshi ya zaunar yace "dan Allah ka kwantar da hankalin ka kasaurare mu ko muba kaɗauke mu amatsayin iyaye ba, mu mun dauke ka amatsayin ɗa a garemu yanzuma muna da daliline shiyasa muka gaya maka amma da baza ka taɓa jiba,

Da sauri Sameer yashiga girgizar kai cikin shashsheƙar kukan da yagama wanke mishi fuska yace baba "dan Allah kace min mafarki nake kar kace da gaske ne abun da kake faɗa min, ni wallahi koma ina da wasu iyayem bazan taɓa zuwa wajensu ba ni kune iyayena ku nasani kuma ba inda zani inatare daku har abada bansan wasu ba bayan ku, rungumeshi Malam yayi yace "Sameer ya isa haka dan Allah be kamata karinga irin waɗannan maganganun ba, katsaya ka saurareni da kyau kaji,

kai ya ɗaga mishi kamar wani karamin yaro yazame jikinshi da ga nashi ya zaun a ƙasa kamar mutum mutumi haka yake agun cikin nutsuwa malam ya labarta mishi abun da yafaru abaya da yanda akai yasameshi sosai sameer yashiga tausayin kansa dashi da mahaifiyar tasa a hankali yafurta "Allah yasa tana raye, suka amsa mishi da "ameen, sannan yace baba to a ina mutumin yake?

Malam yace wallahi Sameer muma shine abun da bamu sani ba, da munsani da tuni munje inda yake duk nisan gurin, wallahi babban gangancin da nayi kenan wallahi na rashin karɓar number sa da banyi ba, sannan ya ɗora da cewa yanzu saidai mita addu'a duk inda take Allah ya bayyana mana ita duka suka amsa da ameen...

malam yamaida duban sa ga Nadeeya yace "ke baza ki zauna bane kinyi mana tsaye akai kamar wata yar sanda ahankali takoma ta zauna inda ta tashi   sannan yaci gaba da cewa sai abu na biyu kuma danake so na sanar da ku shine zamu haɗaku aure tunda har yanzu banji wanda yace ga wanda yake so ya aura ba dan haka muka yanke hukunci da mahaifiyar ku kawai ahaɗa ku tare tunda daman kun saba Kunsan junanku kunga kawai sai ayi tuwona maina ko yakuka gani?

Duk shiru sukayi tare da sadda kansu ƙasa,

Malam ya kuma cewa inda me magana yayi dan ba wanda zamuyiwa dole a cikin ku kunji,

Sameer ne yace "Baba ai duk yanda kukayi daidaine ni bani da zaɓin da yawuce naku saidema godiya dazan muka akan abubuwan da kuka min da ɗawainiya dani da bani kulawa ai ba abun da zan iyasaka muku dashi sai addu'a Allah yabiku da gidan aljannar fiddausi yabaku abun da kuke nema duniya da lahira Allah kuma ya.....da sauri malam yakatseshi da cewa "ya isa haka munyi maka ne domin Allah kuma tamkar ɗan da muka haifa, kai da Nadeeya duk ɗaya kuke agurin mu, yanda idan munyi mata wani abun bazata tayi mana godiya ba haka kaima bama so kayi imdai irin wannan godiyar ce, dan haka kadena ma na godiya kuma kacigaba da kallon mu matsayin iyayen ka ko da wasa bamaso muga ka canji daga abun da kakeyi kajini...

Yace "In sha Allahu bazaku taɓa ganin wani canji da gareni ba aure kuma Allah yabamu zaman lafiya,

malam ya amsa da ameen sannan yakalli Nadeeya da ta sunkuyar da kai tunda taji anyi maganar haɗasu aure,

Malam yace "to kefa muji ta bakinki ko kina da magana? da sauri ta giragiza kai alamun bata da magana yace to naji daɗi da biyayyar ku agaremu kuma Allah yabaku masu yi muku kamar yanda kukayi mana suka amsa da ameen sannan yaƙara dayi musu nasiha sosai kuma me ratsa jiki itama Ummi ta ɗora da tata suna gama yimusu  yace musu zasu iya tafiya, ya sallamesu, su kayi musu godiya da sallama sannan suka miƙe suka fita kowannen su jikin sa babu kwari.......
               
     
  Sai mun haɗu ana gaba,

Wannan shafin bazan mata da shiba dan har kusan kuka yasani sai da nagama typing  ɗinshi tsaf posting kawai yarage min, Arashin sani banyi saving ɗinshi ba yagoge gaba ɗaya 😭 naji ciwon abun sosai wlh gashi kuma ni nayiwa kaina da kaina bare inhuce akan wani. 😭😭



Plss comment and share this book
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#:   💅SAEKI SAMEER....💅
By
           ❤xeemat...love❤

       🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Edited🤗😎

5&6

         _Cigaban labari......_

"Furgigit Dadda tayi tadawo daga duniyar tunanin da ta tafi sakama kon taɓatan da Ameesha tayi,

Ajiyar zuciya tasauke tana kallon ta tare da cemata wai harkin gama shiryawar?

"Eh" tace mata, Sannan ta ɗora da cewa na daɗema da shiryawa, harma fa naci abincin kuma tunɗazu nake miki magana amma kintafi tunanin da kika saba, wai dan Allah Dadda kigagaya min abun da kike tunani kusan kullum baki da aikin yi sai tunane-tunane,

Ahankali tace "hmmm bazaki gane bane Ameesha amma kiƙara haƙuri akwai lokacin dazan gaya miki komai sai kin kaƙara girma tukunna,

"Baki Ameesha ta turo mata tace "Daman ai kullum haka kike cewa Dadda ni wai duk wannan girman danayi wane irin girma kikeso inyi kuma?

tace "Sai kin ƙara hankali tukun"

"kina nufin daman kallon mahaukaciya kike min kenan" Da sauri tace mata a'a nibance ba daga cewa sai kin ƙara hankali sai kuma kimin sharri ni yaushe kikaji nace miki mahaukaciya?

"To Dadda mekike nufi da hakan duk wanda akace mishi sai yayi hankali ai ana nufin mahaukacine shi bashi da hankali kenan,

Kallon ta tayi tana ɗan sakin murmushi, sannan tace "to yi haƙuri ni bahaka nake nufi ba, kizo kitafi kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login