Showing 3001 words to 6000 words out of 136570 words
itafa matar da za ka aura ce ni kuma yar aikin gidansuce taya muka zama ɗaya da ita? kawai sai yayi murmushi shima yace "to kika sani abu aduhu abakar leda ai sai anbuɗa za asan meye aciki ko? kawai itama saitasa dariya, shikuma daman abun da yakeso kenan yana so yaga tana dariya da fararen haƙoran ta jerarru sai yar siririyar wushirya da taƙara mata mugun kyau ga kuma dimples dasuke lotsawa duk lokacin da bakinta yamotsa shide har ga Allah yarinyar tayi mishi dari bisa dari koman ta abun burgewa ne, ko hassadin iza hasada, yana cikin tunaninsa takatse mishi da cewa yaya bossayn Aunty Rasheeda me kake tunanine haka murmushi yaƙara yi yace "kemana tunaninki nake itama yar ƙaramar dariyar tayi, tare da fadin....
"Gaskiya dai Auntyna kake tunani ai naga yanzuma tashiga gida banga wucewar ta tanan ba sai shigarta kawai nagani...
Har yanzu idon sa akan ta sai yace "Dan Allah fa?
Itama tace "Wallahi bari inje inkira maka ita yace a'a rabuda itama kawai wucewa zanyi sauri nake wallahi daman abu nazo karɓa gurinta nayi tunanin ta dawo daga makaranta ne shiyasa ma ko kiranta banyi ba bari in wuce kawai kice mata zanzo anjima da daddare ta ajiyemin abun daɗi ya ƙarasa maganar yana me shigewa motar sa, yana rufewa ya ɗaga mata hannu, ita ma ɗaga mishi tayi tanacewa zan gaya mata Allah ya kiyaye hanya,
yace "Ameen sannan yaja motarsa yatafi ita kuma ta tsaya tana murmushi dan itama harga Allah yamata yana burgeta gashi duk kuɗin da yake dashi baya wulakanta mutane ga ilimi ga dukiya ga kyau ga kyawawan halaye ba ruwanshi da duniya abunsa sam baya tsokane masa ido, saida tagama tunane tunanen sannan tatafi cikin gidan dan tama manta da aiken da akayi mata tana shiga kuma shine taji suna wannan maganar saida ta tsaya tagama ji da ta tabbatar basanan shine tashiga da nufin kan su fito tayi taƙarasa aikin ta tagudu kar suhaɗu shine ko kitchen ɗin bata ƙarasa ba akai mata wannan jibgar ta kwashe duk yanda abaun yafaru ta ƙarasa mata tare da fashewa da wani sabon kukan Dadda da tagama jin abun da akayiwa jikar tata wacce takejinta harcikin ranta ta ɗauketa kamar ƴar cikin ta abun yamata ciwo sosai cike da tausayinta ta fara rarrashinta da kalmomi masu daɗi harsaida taga ta dena kukan sannan ta tashi tace mata taje tayi wanka tazo tayi sallah taci abinci ta kwanta ta huta idan ta tashi daga baccin zata aiketa gidan su AZEEMA...
Da sauri ta gyara zaman ta tana goge hawaye cike da jin daɗi ta amsa da "To" daman tanason zuwa gidan aminiyar tata yau kwanansu uku dayin hutun makaranta amma basu haɗu ba, tashi tayi dasauri ta hau cire kayan jikinta, sannan tafita ta ɗauki bokitin wanka taje wajen yar ƙaramar rijiyar su ta zura gugan da akayishi da ɗan ƙaramin bokitin fenti ta ɗibo ruwa, daga nan tashiga wanka,
Duk abun da take Dadda na tsaye tana kallon ta tana tausaya mata da irin wannan rayuwar da suka tsinci kansu aciki, tagumi ta zabga bisa ga dukkan alamu duniyar tunani ta tafi, bansa me take tunani ba hakan yasa na kwashe komatsain rubutana na bar gidan...
*******************
Wacece RASHEEDA?
"Alhaji Alhassan Ibrahim me nasara shahararran ɗan kasuwa ne akasuwar kwari iyayensa ma duk yan nan garin kano ne, yahaɗu da mahaifiyar ta HALIMATUSADIYA wace yawan cin mutane ke kiranta da sadiya, wasu kuma abayan idonta suce mata halima shirgegiya,
Loƙacin da yake kai kaya gidan su saboda gidansu irin family hause ne wanda yayi ƙaurin suna inkana cikin shi kasha kallo domin gidane wanda kowa abun da yaga dama yake tsulawa gasu maguzawa abunde sai a hankali kawai kuma ita tafara nuna mishi tana son shi, shikam ko dan saboda tarbiyar gidan su batai mishi sai yace gaskya shi ba yanzu zeyi aure ba daga baya da tagane karya yake sai tabazama gun bokaye da malamai hartaci nasara akanshi ta aure shi yanzu haka suna da yaya uku maza biyu mace ɗaya na farkonsu KHALID sai MUSBAHU sai autarsu RASHEEDA wacce aka shagwaɓa tun tana yarinya bata san daidai ba bata san ba daidai ba irin ƴan matan nanne masu mugun rawar kai tun tana yar shekara 15 take tara samari harzuwa yanzu da take university, dan ma Allah ya taimake ta tadan kwaso kyaun mahaifinta da yakasance bafulatani dan mom dinta dauko da anga muni kuma watakil da tarage yawan gili gili dakanta yake saboda tasan intayima ba burge mutane zataiba amma yanzude masha Allah ba laifi tana da ɗan kyaun ta daidai misali,
mutum ɗaya ne yake iya taka mata burki tabar duk abun da take Watakon ALIYU ADAM MAGARYA wanda ake Kira da BOSSAY shikaɗai take shakka shima saboda matsanan cin son sa da Allah yaɗora mata, awani supar market suka fara hafuwa ya bugeta be sani ba kayan hannu ta suka zube a ƙasa tajuyo zatai mishi masifa kawai kuma saitaga yamata kwarjini takasa kawai saita tsugunna zata ɗauka, daidai loƙacinne shima ya tsugunna ze kwashe mata kawai sai hannuwan su suka haɗe waje guda tare da buga goshinsu waje ɗaya sai tai saurin miƙewa tare da dafe gurin tanafaɗin aushhh shima sai yaɗago yana riƙe dariyar shi data kusan fitowa yace....
"Ƴan mata yi hakuri dan Allah ban lurabane" harara tawatsa mishi batace komai gani haka yasa shi cewa ko sai na tsugunna ne za a yafemin umm?
Sai loƙacin ta ɗan saki murmushi tare dace "Eh"
kawai saitaga yana ƙoƙarin tsugunnawar, da sauri tace "laa Wallahi da wasa nake,
Shima sai yayi dariyar tare da cewa "ai da sai in tsugunna yanzu de kin hakura ko?
Kai ta ɗaga mishi" alamar eh,
"Ok thanks" shima ya kuma ce mata,
Batare da ta kalle sa ba tace "U are well come, ƙoƙarin tsugguna wa ta kuma yi dan kwashe kayan ta, Sai yayi saurin dakatar da ita tare da cewa, ai basai kin kwasa ba Madam bari in kwashe miki, bai jira amsar ta ba ya sunkuya ya kwashe mata kayan tukunna yabata,
Tana karɓa ta juya kawai taje wajen biyan kuɗi zata biya Kudin, Sai ta kuma jiyo muryar sa abayan ta yana cewa "kubarta Kawai kar kuƙarɓi kuɗin ta,
Da sauri tajuya tana kallon shi da mamaki, bata ce masa komai ta sake ɗauke kanta ta mayar wajen mutanen tana ƙara miƙa musu ATM ɗin nufin ta suciri kuɗinsu sai ɗaya ya lalle ta yace..
"Hajiya bakiji me oga yace ba, yace ki barshi kar ki damu ai nan gurinshi ne gabaki ɗaya,
Tsaye tayi agun takasa motsawa daga gun, har saida ya ƙaraso gurin ya zagayo ta gaban ta, ganin kamar hankalin baya gun sai kawai yahura mata iskar bakinsa a fuskarta" hakan yasa ta ɗaga ido ta ɗan kalleshi kaɗan ta kauda kai sanna ahankali ta furta mishi, "thanks" kamar mutuniyar kirki,
Da kansa ya taya ta ɗaukan kayan suka fita har cikin motarta ya rakata ya ajiye mata a back sit sannan yaɗan leƙa ta windown motar, saboda ita harta riga da tashiga already, tana ƙoƙarin tashin motar..
"Haka za abar ni nikuma Madam?
fuska aɗan sake tace mishi
"Me kakeso?
"Komai ma inaso"
Ɗan hararar shi tayi cike da rashin fahimtar sa tace "Bangane ba!
"To ke nake nufi" yafaɗa tare da tura zura hannusa a aljihu ya ɗauko wani card ɗan ƙarami ya mika mata,
Sannan yace "Please ga number na dan Allah in ba damuwa pls call me inkin koma gida,
Don't forget about me please I swear I'm waiting for your call kinji?
Kai ta ɗan kaɗa mishi tare da cewa "don't worry I will call you later in syaha Allah"
"Ok thank you for accepting me, I'm so happy to meet you"
Itama sai tace "same here" tare da tayar da motar shikuma yama yana tasaniakin smile harsaida yaga taɓcema ganinsa sannan yabar wajen tunda ga wannan ranar suka ƙulla soyayya wace a cikin kaso ɗari nata yafi yawa tafi sonshi akan yanda yake sonta wanda a yanzu jiyake gaba ɗaya ta fitar mishi arai saboda halayenta sun fara isarshi gashi kuma har maganar aure tashiga ciki anyi magana gemu da gemu bare yace yafasa bashi da wannan damar saide hakuri....
Please comment and share..
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
By
❤xeemat....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
3&4
*WACECE DADDA?*
_BAGWADAS_....
"DADDA.. tsohuwa ce me dattako da taka tsantsan akan abun da zaisa mutuncin ta ya zube a wajen mutum tana da haƙuri da kawaice ba ta shiga abun da be shafe ta ba, sannan kuma bata son raini ko kaɗan ƴar asalin garin Bagwadas ce wani yankine agarin DAMATURU..
Asalin sunanta kuma KHADIJA wanda wasu mutanan suka fi kiranta da Hadizatu, ƴar farace ba laifi tana da kyau daidai misali, kallo ɗaya bazaka ce mata muguwar kyakkyawa ba sai ka kalle ta sosai zakagane silent beauty ne da ita kuma tana da ɗan jiki amma ba sosai ba (bata kai Hajiya Halima shirgegiya ba😅😅)
Itakaɗai ce awajen iyayen ta basu da kuɗi amma basa rasa abun dazasuci suna da ɗan rufin asiri, Tunda baza ka kirasu da talakawa tukuf ba, mahaifiyarta ta rasu tunda daɗewa dan haka a hannun kishiyar maman ta taso tasha a zaba kala kala a gurin ta saboda bata taba haihuwa ba dalilin dayasa kenan da batasan darajar 'ya'ya ba....
"Tsaya wa bada labarin rayuwar ta ɓata lokacine muyi gaba kawai ma gane anan gaba.....
"Tana cikin wannan halin yau daɗi gobe wuya duk dadaima wuyar tafi daɗin yawa Allah ya taimake ta yafito mata miji da fitowarsa dayin auren ko wata ɗaya ba a rufa ba babanta yabashi aurenta"
Malam ISYAKU me gwanjo" sunan mutumin da ta aura kenan shima acikin garin yake yanada rufin asirinshi daidai gwargwadon samunshi, Bayan bikin su da sati biyu suka bar garin yadawo da ita garin GOMBE suna zaman lafiyarsu ba wanda yakejin kansu tunbata sonshi harta fara saboda irin kulawar da take samu a wajen sa cike da so da ƙauna suke rayuwarsu saidai haryanzu Allah be basu haihuwa ba abun kullum yana damunta tana tunanin ma anya zata taɓa ganin jinita kafin tabar duniya tana ganin kamar bazata taɓa haihuwa ba"
Ita de tana son yara ko dan su zame mata abun kallo nan gaba tunda bata da kowa yanzu sai mijin ta"
"Tana zaune ta zabga uban tagumi yana tunani, tajiyo sallamar me gidan nata, hakanne ya katse mata tunanin ta, Daga inda take tasa ka buta agaba tana kalla,
Ganin sa yasa ta muƙewa da sauri tana faɗin sannu da zuw.....
Tayi shiru bata ƙarasa maganar ba, ta maƙale mata tare dawani zaro ido waje kamar zasu faɗo, "Ganin yanda ta tsorata yasashi ƙarasowa gurin da take, "Da sauri taja baya tana faɗin..
"Malam me kake ƙoƙarin yine sai kace makaho ko kuma idoana nane yake min gizau, kamar fa ɗan aljanu ne a hannun ka, a ina kaje kaɗauko mana shi,
Shiru yayi yana kallon fuskar sa ɗauke da murmushi da yakasa barin fuskar shi,
Bata jira yayi maganar ba ta kuma ɗorawa da cewa "Wallahi Malam kafita dashi kar kaja mana masifa da bala'i muna zaman zamammu, wallahi bada ni ba ka koma da yaron nan duk ma a inda ka ɗauko sa in kuma wani ne yabaka sai ka mayar masa dashi.
Tana kaiwa nan ta juya da ƙoƙarin barin wajen, yayi sauri ya riƙo hannun ta"
Fusge hannun ta tayi, shima yayi saurin ƙara kamo ta, yace "Kefa matsalata dake wataran ƙauyan ci, yana maganar yana janta zuwa falon,
Sake janyewa tayi tare da faɗin "Kaga malam nifa kasakar min hannu na"
"Wai dan Allah Hadizatu meye hakan kikeyi? sai kace ƙaramar yarinya ki nutsu mana ki saurare ni...Sai loƙacin tai shiru tashiga binshi kamar yanda ya bukata ɗin,
Yana shiga falon ya ajiye ta akan kujera, Sannan yace "Ni wallahi kinban mamaki ma yaza ai ki ringa dan gan bawan Allah da aljani mutum nefa kamar ke, ke da ya kamata ma kiyi murna ma da ganinshi amma sai ki hau surutai,
"Yo ni Malam yaza'ai in sani badole ince aljani ba, kamannin sa da wannan kyaun nashi ai bekama da na bil adama ba, tayi maganar tana ƙara leƙen fuskar yaron, sosai ta tsaya tana kallon sa sannan ta kalli ƙafarsa dan taga ni irin ta mutane ce, ba kofato, wai duk dan taƙara tabbatarwa kanta mutum ne ko bashi bane" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Malam tace "To Malam gayamin inda ka samoshi!
Yaron ya kalla sannan yace "Yaron kirki jeka gurin umman ka" kaji,
Yaron binsa ya shiga yi da kallo cike da rashin sani da kuma rashin sanin abun da suke cewa, Saida Malam ɗin ya ƙara yi masa nuni da ita, sannan a hankali yataka zuwa inda take,
Yanzu kam ji tayi bata jin tsoron sa da sauri tariƙe shi tana rumgume shi tsam a jikin ta kamar zata meda shi cikin ta saida ta gaji dan kanta ta sake shi, sannan ta ɗago shi tana cewa "Small boy what is your name?
Kawai sai taji yace mata "Sunana SAMEER da mamaki ta juya tana kallon malam, dashima su yazuba wa odo yana tunanin dama ɗanshine yanda ta ruƙeshi abun sha'awa kamar ɗanta yana cikin tunanin yaji tace..
"Laa Malam kaji ya iya hausa, da wallahi har ina tunanin yanda zan mishi magana tunda ni de ba wani iya turanci naiba sosai bare in mishi ashema duk mune shima dariya yayi yace "Ni ai nazata ma baya magana ko kuma bayajin hausa tunda nataho dashi nake taimi shi magana amma ba uhm bare um um har muka ƙaraso nan...
Tace "Tab ɗijam ikon Allah sai kallo, yauwa tsayama fara gaya min inda ka ɗauko shi tukunna,
Saida ya gyara zama sannan yace "Yanzu kuwa zan baki labari, Saida yaƙara fuskantar ta da kyau sannan yace "Wallahi ina kan hanyar dawowa a wajen unguwar Sarire naga mutane da yawa sun zagaye gurin, To kinsan nide bana son inga ana rigima kawai sai naje na kutsa kai nashi ina shiga kuma naga yaron nan akan wata baiwar Allah da take kwance ga jini sai zuba yake daga kanta yana ta faman kuka yana cewa ummi ummi amma ko motsi batayi kamar ma marar rai,shine na ƙarasa gurin da sauri na kamo hannun shi sai yayi saurin riƙe ni yana faman rirriƙeni yana nuna min inda take, sai na rungume shi, sannan na juyo ina cewa mutanan "yanzu dan Allah saikace ba musulmai ba kuna ganin halin da take ciki ita da yaron ta amma ba wanda zai taimake su kun tsaya kun zuba musu ido haba dan Allah, saida na gama faɗa na, sannan wani Alhaji ya ƙaraso inda nake ya miƙo min hannu muka gaisa, sannan yafara min bayanin cewa ya kira motar asibiti yanzu zasu ƙaraso, yaron kuma da yagani bawan da beje wajensa ya rarrashe shi ba amma yaƙi yarda da kowa shiyasa kawai suka zuba musu ido amma ba dagan gan hakan tafaruba,
"Sai loƙacin na ɗanji hankali na ya kwanta kuma alamu sun nuna cewa shi yabuge matar kenan, muna cikin haka motar asibitin ta ƙaraso dasauri suka fito suka ƙaraso inda take suka ɗauke ta suka sakata a motar sannan Alhajin yace suyi gaba gashinan zuwa sannan suka tafi sai yajuyo ya kalle ni yace "To alaramma yaron fa zamu tafi dashi"
Sai nace "To" ina miƙa mishi yaron amma sai yaƙi yarda fur yaje gurinshi shi dole sai ni, da naga haka sai nace wa Alhajin meze hana kabarmun shi a wajena inyaso sai in baka number ta duk yanda ake ciki sai kagaya min idan tasamu lafiya, koma rasuwa tayi duk da daima bama fatan hakan Allah yaba ta lafiya de shine fatan mu, "Ameen yace sannan yazaro waryasa a aljihu yace in faɗo mishi number tawa, karanto mishi nayi ya rubuta sannan yace...
"To shikenan ni zanwuce duk yanda ake ciki zakajini sai musan abun yi kuma daga ita har ɗan nata sabo da na tambayi ina danginta? Sai suke ce min wallahi ba wanda yasan daga ina take kawai suma wayar gari sukai suka ganta a gurin ita ba me hankali ba kuma bazakace mata mahaukaciya ba tunda kayan jikin tsaf tsaf complete amma kuma tambayar duniya anmata amma ko sau ɗaya bata taɓa buɗe baki ba bare ma su sa ran zata amsa saidai duk wanda yaji tausayin ta yabata abinci takarɓa tabawa yaronta yaci yaƙoshi sannan taci sauran kuma kullum tana rungume da ɗanta bata sakin shi ko kaɗan bare ataima ke shi ahak take zaune agun, wajen kwana biyu har zuwa yau da ban kula da itaba na bigeta, wallahi kwata-kwata ban lura da tahowar taba ya ƙarasa gaya min cikin sanyin jiki, daga nace "Allah sarki haka Allah yatsara yaje kawai Allah ya kiyaye gaba, yace "Ameen, sannan yashige motarshi ya tafi, ni kuma naɗora yaron amashin muka taho gida, "to kinji dai yanda akai nasamo shi mutane ba aljani ba,
Bai jira tayi magana ba, ya kuma cewa "Ni sai yanzu ma nake jin taƙaici, nima da na amshi numbarsa da yanzu sai inkira sa inji yanda ake ciki,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke cike da jimamin labarin da yabata tace gaskiya dai da kasan ka karɓa, amma dai shikenan ai tunda yace zai kiraka kuma nasan zai kira ɗin tunda ya faɗa mujira zuwa gobe mugani kawai, yace "To