Showing 21001 words to 24000 words out of 136570 words
har saida yaɗan taɓa ta,
kallon sa tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "Bawai naƙi taimakon ka ba, amma kayi haƙuri bazan iya zuwa gidan kuba da zama hakannan saide idan aiki za aɗauke ni, idan nayi abiya ni danni nafiso innemi abu da gumina saboda gudun wulaƙanci ko gori shiyasa kaga ina jure duk wani cin mutuncin da suke min watarana sai labari, sannan "Nafiso inyi karatu da kuɗin da na nema halak malak ɗina kayi haƙuri idan bakaji daɗin rejecting ɗin da nayi ba, na tayin dakai min kuma koda ina so ma, matsalar Dadda bazata taɓa barina in koma gidan Ku ba tafiso taganni akusa da ita bata son abun da zesa muyi nesa da juna nima kuma banaso inyi nesa da ita, dan Allah ka fahimce ni please kaji.... tagama fadar hakan tare da kallon fuskar sa da taga ya canza gaba ɗaya kuma yaƙi cewa komai kawai ya ƙura mata ido,
Jikin tane yayi sanyi, marairaicewa tayi kamar zatayi kuka, cikin sanyin murya tace "Dan Allah kayi haƙuri kace wani abun, ba wai kayi min shiru ba kana kallona, duk da haka be cemata komai ba, hawaye ya fara ciccika mata ido, haƙuri ta kuma basa ya kuma yi mata banza,
Saida yaga dama dan kansa sannan yace "Ok nagode, zaki iya tafiya, duk laifina ne bansan haka kike ba amma ba komai, wai harni zakicewa zan miki gori zan wulaƙanta ki ko?
Da sauri tace "Dan Allah ka dena fadar haka wlh ni bada wata manufa ba nafaɗa ba, na faɗi kawai abun da yake raina ne bawai kai nake nufi zakayi min hakan ba, yace "Ok Ammi na kike nufi kenan ko kuma 'yan gidan mu ko?
Nan ma girgiza kai tayi tana dan dafe kanta da hannun ta alamar tarasa tayaza tai mishi bayani ya gane tace "wallahi duk bahaka nake nufi ba haba dan Allah me yasa ka kasa fahimta ta ne,
Batare da ya kalle taba yace "In kina so in fahimce ki shine ki amin ce da magana ta, idan kuma ba haka ba, to yanda na faɗa hakan kike nufi,
Shiru tayi bata ce masa komai ba sai daga bisani kawai tace "To shikenan naji inde ta bangarena ne na yarda saide kuma babbar matsalar itace Dadda, wannan kuma saide kaje da kanka ka shawo kanta ta amince dan kasan inde bata yarda ba bani da ikon zuwa dole saida umarnin ta,
Cikin jin daɗi yace "kar kidamu da ita nidaman amincewar ki kawai nake nema yanzu muje tare sai in tambaye ta ɗin ko ?
Tace "To muje Allah yasa adace" yace "Ameen, yana fita daga cikin motar ya koma mazaunin driver ya zauna, juyowa yayi yana kallon ta yace "To ai sai kidawo gaba ko! tace "To sannan ta fito ta koma gaba ta zauna tare da rufo ƙofar, shikuma yayi wa motar key suka nufi gidan kowa da abun da yake saƙawa aranshi, daman shi yana sane yayi mata haka yasan idan bahaka yayi mata ba bazata amince ba, ita kuma anata bangaren tayi mishi hakane dan ta wanke kanta daga gurin shi karya yi fushi da ita, saboda tasan Dadda bazata taɓa yarda ba shiyasa tace mishi ta amince tayanda in Dadda tace mishi bata yarda ba, bazega laifin ta ba saide yaga na Dadda, har suka ƙarasa gaban gidan ba wanda yasake cewa komai.
Parking ɗin motar yayi sannan suka fita gaba ɗayan su suka nufi hanyar ƙofar gifan,
Suna ƙarasa shiga da sallama a bakinsu,
Dadda dake ƙoƙarin shiga ɗaki ta tsaya tare da amsa sallamar tasu tana kallon su sannan tace "A'a Bossay kaine da kanka har cikin gidan mu.
Yace "Wallahi Dadda nine, Meesha ta jawoni". tace "Sannun ku da zuwa to bari na ɗauko maka tabarma ko?
Yace "To, yana ta zulumin tayanda ze gaya mata dan sai da yazo sai kuma yaga tayi mishi kwarjini har tafito be dena tunanin ba, Saida tace "To zauna kaji yace to sannu da ƙoƙari saida ya zauna ya cewa Ameesha itama ta zauna,
Dadda kuma ta jawo kujerar zaman tsakar gida ta zauna tace "Ina sauraron ku danna san da magana abakin ku, dan wannan zuwan naka, nasan bana hakannan bane,
Sai kuma suka shiga kallon kallo kowa ya kasa magana harshi me cika bakin yakasa faɗar komai saima cewa da yayi "Ameesha kifaɗa mata mana, Itama tace "kafaɗa mata de bakai kace zaka faɗa mata ba, wallahi nima bazan iya ba,
Dadda de ta zuba musu ido tana jiran jin tabakin su har yanzu ba wanda yace komai da Dadda ta gaji sai tace "wai meye hakanne me kuke son faɗa inbaza kufaɗa ba, intashi in tafi kunyi shiru kuna sa in sa, Ni ina da abunyi inku baku da shi da sauri yace "yi haƙuri Dadda yanzu zamu faɗa daman wai....in wai.... in.... hmm daman ina... ss...son Ameesha tadawo ummm.........
yakasa faɗa sai inda-inda yake, nima kuma nagaji da jira, dan haka nake cewa sai gobe idan Allah yakaimu maji yanda zasu ƙare muji zata amince ko baza ta amince ba.....,
My WhatsApp number 08124226526
Pls banda kira
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
By
Yaya Azeema 😎
*Allah yajiƙan magabatan mu da suka riga mu gidan gaskiya muma intamu tazo Allah yasa mucika da imani Allah ya kyautata ƙarshen mu Allah kasa gaban mu tafi bayan mu kyau Ameen....*
Edited 🤗😎
15&16
***********************
.....…Dadda dataga abun nasu kamar ma raina mata hankali suke ta buga tsaki cike da masifa tace "Kunga wlh bana son iskancin banza fa ya ina tayi muku magana amma kun tsaya kuna raina min hankali kuna gefe-gefe,
Mtswww ta kuma jan wani dogon tsakin tana yunƙurin tashi,
BOSSAY ne yayi saurin cewa "Dan Allah Dadda kiyi haƙuri kitsaya ki saurare mu wallahi yanzu zan gaya miki.
Dakatawa Sannan tace "To inaji faɗi yanzu yanzun na,
Saida yaɗan sosa ƙeya tare da sunkuyar da kansa sannan yafara bayani, a hankali yace "Daman Dadda dan Allah wata alfarma nake nema awajen ki nasan ma zaki min ko Daddar mu? Yayi maganar yana ɗan ɗan satar kallon ta,
Hararar wasa ta watsa masa tace "Ai bazan ma yiba ɗin tafaɗi hakan cikin wasa,
ƴar ƙaramar dariya yayi yace "Haba Dadda ai nasan faɗe kike zama kiyi kodan wannan jikar taki guda ɗaya.
Tace "Kai ni ka isheni da surutu kafaɗi abun da yakawo ka ko intashi.
Saurin cewa yayi "Daman alfarmar da nake nema itace dan Allah ki taimaka kiban Ameesha ta koma gidan mu da zama a wajen Ammi na saboda yanayin halin da take ciki kinga acan ma zata fi samun damar karatu batare da tasha wahala ba ni dakaina zan ɗau nauyinta har ta kammala makarantar ta gaba ɗaya zan tsaya mata, kuma nasan Ammi na zata riƙeta kamar ƴar cikin ta har zuwa lokacin da Allah ze fito mata da miji tayi aure sannan zata bar gidan mu, Dan Allah Dadda kar kice a'a dan Allah ki amince dani wlh zan kula miki da ita fiye da yarda kike kula da ita in Allah ya yarda baza ki taɓa da nasani ba akan ruƙon ta da zaki ban bazan taɓa cutar da ita ba kuma bazata taɓa neman abu ta rasa ba matuƙar ina raye, wannan alakawari na ɗaukar wa kaina ni wlh ko kullumma kike so kiringa ganinta zan ringa kawo miki ita kuna gaisawa kinji Daddar mu, har waya zan siya miki kuringa gaisawa duk sanda kikeso namiki alkawari, yana faɗar haka sai yayi shiru yana jiran me zatace dan yaga kamar fuskarta ta canza.
Har wani tsawon loƙaci, amma beji tace komai ba, hakanne yasashi ɗagowa yana kallon ta amma ga mamakinshi me ze gani kamar hawaye a idon dadda da sauri yace subhanallahi dadda lafiya me yafaru ko na fadi wani abun da ya bata miki rai har kike kuka haka amma still bace da shi komai ba sai ya maida dubansa ga Ameesha da tayi shiru kamar bata san me suke daman tasan hakan zata faru tasan halin abarta shiyasa tace mishi ta amince yanzu yasan yanda zeyi da ita tunda shi ya tsokanota besan halin ta bane da beyi gigin tambayarta wannan babbbar alafarmar dan tasan ko aure ta tashi yi wani ikon Allah ne kawai ze rabasu da ita shi ya katse mata tunaninta da cewa Ameesha kinga fa dadda kuka take bansan me akai mata ba tana dan boye dariyar da takeson kwace mata ganin duk yawani bi yatada hankalinsa amma saita danne ta wani maze tace to nimade abun yaban mammaki ganin hakan yakaqara juyawa gurin dadda yace dadda Dan Allah idan ni nabata miki rai har kike kuka to naroqeki dan Allah kiyi hakuri saida dadda tadan sace kallon sa ta gefen ido taga yanda duk yabi yadamu sai kuma tadan ji tausayin sa amma hakan fa bazesa ta taba amincewa da qudirin sa ba dan abune wanda bazai taba yiyuwa Ameesha ce tace dadda wai meye hakanne kiyi mana magana mana amma kintsaya kinayi mana kuka sai kace wata qaramar yarinya dadda cikin kukan da take ti kuma bata dena ba tace au hakama zakice hakafa yace ze rabani dake kin amince kenan kinyarda kibishi kibarni ni kadai ko to shikenan tafada tana qoqarin tashi tabar wajen wai ita adole tayi fushi dasu shiko Bossay abun yabashi mamaki dan haka kawai yabisu da ido yana kallon ikon Allah Ameesha ce tace dan Allah dadda kitsaya mugama maganar mana sai lokacin Bossay yace yanzu dadda duk wannan bayanin danai miki abanza baki yarda dani ba kenan tace eh ban yarda dakai dinba sai me ko zakai min wani abunne wlh tun muna sheda juna kafita daga idon in rufe in kuma kaqi zan nuna maka asalin kalata bakasanni ba ko to wlh daga yauma kar inkara ganin ka aqofar gidanan ma bare har kashogo min gida karabu da jikata bakai ba ita kar ka sake yi mata magan ko hanya ka ganta baruwan ka da ita kuma katashi kabar min gida dan bana son ganinka wai harda wani cewa saboda halin da take ciki wane irin hali take ciki ko kaga tarasa ci ko sha ko kaganta tana bara ahanya ko kuma talla kaga tanayi ko gayamin wani mawuya cin halin da kaga tashiga kabar min abata ahaka a yanda ka ganta ba ason tai makon naka inde ta haka zaka tai maketa idan taimakon naka na gaskiya ne kai mata mana tana nan duk abun da take buka ai zaka iya yimata bade kudi bane ko dolle sai tadawo gidan ku kanaso kenan ka lalata min yarinya ko kuma kasiyar da ita to ta Allah bata ka ba jikata tafi qarfinka kurwarta nesa dakai saide kaje kasamo wata amma bada gudan jinin Hadizatu ba tafada tana ta faman hararar sa kamar idonta ze fado qasa Ameesha tace haba dadda wai wane irin maganganu kikeyi ne haka shifa taimako na yace zeyi bawai cutar dani ba ke meyasa baki da yarda ne arayuwar ka ki rage wannan halin naki dan Allah dan wlh ba inda ze kaiki saide ma yakaiki yabaro ki kizo kina da nasani kinsande kuma danasani qeyace kije kici gaba kar kifasa tana gama fadar haka tajuya gurin Bossay da yayi mutuwar tsaye tunda yake arayuwar sa ba ataba cimasa mutunci ba irin nayau daga taimako kuma sai reshe yajuye da mujiya wannan wace iriyar tsohuwa ce da bata da fahimta kwata kwata jifa irin abubuwan datake gaya mishi duk dan yace ze taimaki jikarta tabbb babbar magana yau ya kawo kanshi yajawa kanshi masifa abanza a wofi da yasan haka take wlh da be zoba gwara yabar Ameeahan ta tambaya da kanta inyaso duk yanda sukai tagaya mishi da duk haka bata faru ba wata boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke sannan cikin sanyin murya da kanajin kasan dan dole aka fito da zance yace Nina jawa kaina ni na shigo gonarki da har kike jifana da irin wadannan munanan maganganun kiyi amma kiyi hakuri bansan tahaka zakiyiwa magana ta fassara ba da banzo ba yakarasa fada ranshi ba qaramin baci yayi ba da idonsa har ya canza kala daga fari zuwa jaja jaja yana kaiwa nan yajuya daniyar fita daga gidan sai yaji anruqe mishi hannu gam tsayawa yayi batare da yajuyo ba ahankali ta taka ta koma ta gaban sa suna fuskantar juna ta qura masa ido shima ita ya tsaya yana kallo ko kifatawa basayi har sai da dadda tace nashiga uku ni hadizatu me nake gani haka me kukeyi haka sai lokacin suka dawo hankalin su shiya yafara dauke idonsa daga nata sannan ya mayar da idonsa kan hanayensu da yake a ruqe da na juna sai kuma yajanye yadaga dayan hannu sa ya dora anata da nufin yajanye hannun ta daga nashi yatafi amma sai yaji taqara riqeshi sosai yaqara janyewa amma still yaji taqara ruqewa sai ya dago yana kallon ta sai yaga hawaye a fusakar ta be hana taba sai cewa da yayi sakar min hannu na mana ko intafi ko bakiji abun da daddar ki tace bane kai tashiga girgiza mishi tana cewa nide dan Allah kar katafi kabarni zan bika muatafi tare idan ita bata yarda da kaiba ni nayarda dakai tafada tana jan hannun sa da nufin sutafi amma ko gezau be yiba waro ido yayi yana kallon ta da mamaki yace ke kina da hankali kuwa yafada yana fusge hannun sa daga nata yayi saurin ratsawa ta gefenta yanufi hanyar waje saide bekai ga fitaba yaji tabiyo bayanshi sauri yaqara dan yayi sauri ya shiga motar sa yatafi kan ta kamo itama tana ganin ya qara sauri kawai sai sa gudu aikwa atare suka fito yana zuwa wajen matarsa ya bude ya shiga sai ta ruqe murfin ta hanashi rufewa tace inatyi maka magana kana share ni yace anshareki din ni bakiga abun da akai min ba tace to bana baka hakuri ba kuma naga bani naimaka ba dadda ce ita kuma daman haka halinta yake bata da yarda kuma sai danaga maka daman amma kaki jina yace to yanzu ai naji na kuma gani dan haka sai kikoma tunda de tace bani ba ke tace wlh nikuma bazan yarda ba saide katafi dani dafe kan shi yayi yace nikam yaude naga takaina ita tasamin ciwon kai da fadan ta ke kuma kinzo zaki kara min wani akai dan Allah kirabu dani yafada ranshi adan bace dan shi wlh yarasa yanda zeye besan me ze cemata ba gashi tazo ta nace mishi sai ya tafi da ita kakar ta kuma tace bata yarda ba to taya ze dauke ta yatafi da ita batare da amincewar ta ba kukan da tasakane yadawo dashi daga tunanin da yakeyi sai yafito waje shima kawai ya zuba mata idanu na wasu lokuta sannan yace naji amma kiyi shiru kiji abun da zance miki dasauri kwa tayi shiru hannu yasa yashiga goge mata hawayen sannan yace yanzu ki koma gida zanyi magana da Ammi na sai tazo da kanta nasan de bazatai mata abun da tai mata abun da taimin ba kuma zata qara yarda idan taganta zatagane cewa da gaske nake kema kuma sai kikara lallaba daddar taki ta yarda kafin inkawo Ammain nawa murmushi tasake tace dan Allah dagaske kake yace nataba yimiki wasane tace a a yace kitafi gida tace to shikenan sai kunzo din dan Allah karfa kaqi zuwa kabarni inta faman jiranka yace zakiji ni in sha Allahu tace to Allah ya yarda kuma Allah yasa dagaskene yace wlh zan ma fasa kinmaida ni maqar yaci kenan tace a a nibance ba yace to naji yafada yana qara komawa cikin motar ya rufe ya tayar tare da dago mata hannu alamar bye itama hannun ta daga masa yaja motar sa yayi gaba yabar ta agurin yana tunanin qaryar da yayi mata daman da ta rabu dashine yayi mata wayo yatafi amma shikam baze qara dawowa gidan su ze rabu da itane kamar yanda kakar ta ta bukata nacewa bashi ba ita to kwa hakan ce zata faru dan baze kaqar bari su hadun ba saide wani ikon Allahn kuma.saida taga bacewar motarsa sannan ta nufi hanyar qofar gidan nasu dadda dake labe tana hango su tun fitowarsu ta biyo bayansu jira take kawai taga yasata amota ze tafi da ita ita kuma tafito waje tayi mishi ihun marawon mutane ta tara masa jama'a sai kuma taga akasin haka tana ganin Ameesha ta taho zata shigo tai saurin komawa ciki tashige daki Ameesha tana shiga itama ko sallama bataiba ta nufi dakin nasu nan ma batai sallamar ba tashige ciki ko kallon inda take batai ba ta wuce kan yaloluwa katifarta takwanta saboda haushin daddar tata takeji matuka na cin mutun cin da tayiwa bawan Allah nan duk irin mutuncin da yake da shi ga hankali amma ta rufe ido taringa zazzaga masa masifa son ranta itako dadda daman haka take so dan bataso ma suyi maganar taci gaba da ninke musu kayan da ta yanzu ta tsiri ninkesu bawai dan tana so ba har tagama ba wanda yacewa wani ta tafasa saima ajiyar zuciya da taji Ameesha nasauke wa alamar tayi bacci kenan tana gamawa ta tashi tafita daga dakin tanufi kitchen domin tasa ma musu abun da zasuci..
**************************
Tashin hankali Allah sarki wasa wasa yau har anyi kwana uku kenan amma ba labarin batan mahaifin su Azeema sunyi iya qoqarin su har sungaji da neman sa dan zuwa yanzu ma ba inda suke zuwa yawon nemanshi sun fidda rai ma akashi sun fawwalawa Allah lamuransu suna addu'o'i akan in yana raye Allah ya bayyanar musu dashi inkuma ya mutu Allah ya jikanshi yayi masa rahma Allah yahadasu a aljanna baki dayansu haka suke ta addu'a safe rana dare basa gajiya