Showing 57001 words to 60000 words out of 136570 words
nayi maka magana amma kayi min shiru wlh baka da kirki ko kadan nide banji me akace daga can bangaren ba kawai de naji yace wai da gaske ko da wasa kai amma naji dadin hakan Allah yadawo mana dakai lafiya kace muyi babban shiri yauwa daman inaso muyi magana kan batun sabbin ma aikata acikin mutane hamsin da wani abun gasky wadanda muka dauka basufi ashirin da biyar ba saboda yawancin su duk basu cancanci adauke suba shiru yayi yana sauraron abun da dayan yake gaya masa sai can kuma yace ok ba matsala ammafa inaganin basai an ragesuba saboda muna bukatar mutane da yawa saboda dayan bangaren da aka bude kuma babu wasu ma aikata sosai aciki inaga kawai abarsu baza arasa abun da zasuyi ba amma inkana ganin arage din sai yafi sai murage din ko yakace sake yin shiru yayi yana sauraron sa,
Sannan yace ok zan qara bincikawa badamuwa yauwa sai kuma....
Begama fadar abun da yakeso yace ba yaji wayar tayi ƙara ƙit alamun ankashe wayar kenan bin wayar yayi da kallo sannan yasaki murmushi yace hmmm baza ka taɓa canzawa ba Allah yashirye ka ace mutum baze taba jiran kagama magana ba shi inya gama tashi maganar shikenan sai ya katsewa mutum waya yana magana yana kallon saleem da yayi shiru yana sauraronsu sai can kuma yace kayi haƙuri fa ina ta waya nabarka kai kadai,
Saleem yace bakomai wlh naga alamar kamar ma baka ji dadin kashe wayar dayayi ba dr shettima yace wlh banji dadi ba ban gama magana ba yakashe kuma daman halin sane yasaba yiwa mutane haka bashida mutunci wlh ko kadan gashima kuma nan da two weeks zedawo shikenan mun shiga uku sai ya takurawa kowa da masifa kaima wlh kayi hankali dashi dan abu kadan zakai mishi ya koreka daga aiki any mistake game over saikabi a hankali.
Jinjina kai Saleem yayi sannan yace "shine me asibitin kenan, Yace eh shine wlh amma wlh yana da wuyar sha'ani sai ka koyi zama dashi zaku zauna lfy
Saleem ya danyi murmushi tare da jinjina kai sannan yace to Allah yabamu ikon iyawa dashi Allah yasa muhadu dashi lfy mu rabu lfy,
ƴar ƙaramar dariya yayi sannan yace aikwa da ƙyar ace kuhad ku rabu batare da wani abu yahadaku kawai de kayi addi'a Allah yasa matsalar tazo da sauƙi danshi mutum ne wanda ba a iya mishi haka de sukai ta tattaunawa akansa kafin daga bisani dr shettima ya cewa saleem kaga munata batawa mutane lokaci kaje ka jirani a waje kafin infito sai muwace yace to sannan yatashi yana ƙara yi mishi godiya yafita.
yana fita mutane suka ci gaba da zuwa har yagama dasu gaba daya sannan yatashi yafara shirin fita teaiter din da zasuyi ƙarar waya yaji akan table dinshi da mamaki yajuyo tare da ƙarasowa kusa da wayar sai kuma ya tsaya yana kallon wayar to waye yabarta anan begama tunani ba yaji anyi noking yace come in dasallama saleem yayi sannan ya ƙaraso inda yaji wayar tashi na ringing yace afuwan dan Allah wayata namanta yafada yana ƙoƙarin daukar wayar sai kuma ta katse girgiza mishi kai dr shettima yayi tare da dan matsawa dan yabashi damar daukar wayar aikwa saleem na dago da wayar idon dr shettima ya sauka akan hoton wellpaper din da yake kan wayar saleem ƙara zaro idon yayi domin tabbatar da abun da yagani gaskiya ne ko kuma gizo ne amma da maida idonsa kai saleem har yasa wayar a luck yajuya ze fita da har ze tsayar dashi amma ba halin yin hakan saboda saleem har yariga da ya ƙarasa fita tunani ya shiga yi inbe manta ba hoton da yagani kamar fuskar yarinyar da suka hadu jiya tazage shi......
Dr.. Shettima Girgiza kai yashiga yi a fili yace kai ba ita bace kawaide gizo ne mema ze hadata da wannan yaron wata zuciyar ce ta bashi amsa da cewa inkuma budurwarsa ce tunda har yadora pic dinta amatsayin wallpaper sa wata zuciyar tace kode qawar sace nanma de girgiza kai yayi yace ai basa kama da qawarsace tun ajiyan zangane hakan in kuma budurwar sace nanma yaron baze kulata ba tunda shi yana da hankali daga ganinsa baze kula irin wadannan matan ba yarinyar daga ganin tama kasan ba abata tarbiya ba agidan su tunda har take iya cin mutunci nagaba da ita shi sai yanzo ma yake tajin wani bacin ran na taso masa wai shi zatacewa dan iska me bin mata alhalin ko ganinshi bata taɓa yi ba amma take dorarwa waya sani ma ko itace me bin mazan daman ance duk abun da kakeyi gani kake kowama na aikata irinshi arayuwarsa shiyasa ta fadi haka shikadai sai faman saqa da warwara yake yi sai can kuma yasaki wani irin murmushi kamar bashine yake bacin rai yanzu ba ,ba komai yasashi wannan murmushin ba face tunawa da yayi da dayar yarinyar da loqacin da ta ruqe mishi hannu tana ce mishi dan Allah bawan Allah kayi hakuri karabu da ita na roqeka kaji plssss harga Allah hakan da yarinyar tayi ba qaramin tafiya yayi dashiba gashide yarinya ce batafi qanwar qanwar sa ba amma ta burge shi tun ganin farko dayayi mata yaji ta burgeshi shi tunda yake be taba jin yanaso yayiwa wata mace magana ba da nufin wai ta burgeshi sai akan yarinyar nan yar qarama abun har mammaki yake bashi wai shi ya aika yaro yace ayi mishi magana da mace lalle yarinyar nan taciri tuta ta karya mishi record saide bemasamu maganar da ita ba waccen kucakar yarinyar tazo ta bata mishi rai da harma yafasa maganar da yayi niya
gemunshi yadan shafa tare dayin wani murmushin yace Allahn da yahada ni da ita jiya shi zeqara hadani da ita nan gaba in Allah ya yarda zamu qara haduwa dake small girl sunan daya samata kenan tundade besan sunan taba...nocking din office din da akayine yakatse mishi tunani iznin shigowa yabayar....
wata nurse ce tashigo tace sir we are ready, ok I'm coming juyawa tayi tafita shi sai yanzuma ya tuna ashefa zasuyi aiki amma yazauna yana tunanin abun da bashida amfani a halin yanzu agashi har goman ta kusa ma shaf shaf ya gama shiryawa sannan yafito,
yana fitowa ba kowa agun sa Saleem da yake ta faman jiran fitowar tashi yana ganinshi yatashi da sauri ya miqa hannu dan ruqe mishi lap code din da yaruqo be hanashiba ya miqa mishi sannan yayi gaba shikuma yamara masa baya wani dogon corridor suka mika sai da sukayi gaba kadan suka yi kwana suka shiga wani daki wanda dagani daman kasan tiarter room ne nurse biyu ne adakin kowa yayi shigar fara aiki cikin kayan aikin su sky blue sai farar hula da farin face marks suna shiga dr shettima ya karbi rigar hannun Saleem ya shiga wani daki da yake acikin dakin da suke anyi shine sdaman saboda shiga canza kaya ko wani uzurin privacy sai ka shiga kayi har da toilet aciki bayan ya shiga yagama shirya wa yace wa saleem ma yaje ya shiryo,
Shiga yayi be jima ba ya fito shima cikin shigar kayan aikwa ba qaramin amsar sa kayan sukaiba yayi matuqar kyau acikin su yana fitowa kuma ya tsaya daga baya saboda shi ba abun da ze taba kawai kallonsu zeyi sai wata yar joter da pen da dr shettima yabashi yace yaringa recognize din duk abun da ya fahimta abun da yake da tambaya idan angama sai yayi yace "to"
Sannan yafara aikin dan shine zaiyi aikin sauran dan taimaka masa zasuyi da wani abun cikin kwarewa da kwazo irin nashi yafara gaba tar da aikin Saleem ya tattara duka hankalin sa da nutsuwarsa kan abun da akeyi yana yi yana rubutawa kamar yanda akace kuma yana fahimta Yanda ya kamata....,
*BOSSAY*
"Bossay na kwance akan gadon asibiti da drept a hannun sa ana qara masa ruwa idon sa a lumshe kamar me bacci amma ba bacci yake ba yayin da gefen gadon kuma faruq ne akusa dashi yana yi mishi sannu su Ammi ne suka shigo ita da su Aysha gaba ɗaya de 'yan gidan dukan su suka shigo cikin dakin sai yaran suka shiga gaida faruaƙ da tambayar ya mejiki kuma, Amsa musu yayi dacewa jiki Alahamdulillah shikuma ya gaida Ammi ta amsa itama tareda cewa faruq ya jikin nashi yace da sauƙi de za ace dan har yanzu be bude idon saba kuma beyi magana ba tace to ALLAH ya qaro sauƙin yanzu bacci yakeyi ko kuma idonsa biyu yace mata idonsa biyu duk yana jinku ma karkaɗa kai Ammi tayi sannan taƙara tambayarsa doctor yashigo ne yace a'a be shigo ba nurse ta shigo ta dan dubashi,
Bude idon sa yashiga yi yana ƙarasawa ya saukesu akan Ammi, itam Ammi shitake kallo daga bisani kuma tace sannu Aliyu kai yadaga mata sannan ya yunƙuar ze tashi tayi saurin dakatar da shi tace koma ka kwanta kai ya girgiza mata alamun ta bashshi ya tashi faruƙ ne ya shiga tai maka masa yaƙarasa tashi sai yasaka mishi filo abaya tare da jinginar da bayansa akai yanda zefi jin dadi,
Ɗaya bayan ɗaya ya shiga binsu da kallo sai da yagama kallonsu sannan ya maida dubansa ga Ammi da ƙyar ya iya bude bakinsa yace Ammi ina Ameesha wai meyakawo ni asibiti ni da natafi dauko ta ya akayi naganni annan?
Ammi tace "shiiit ya isa haka zangaya maka amma ka mwantar da hankalin ka kabari sai kaji sauƙi tukunna,
kai ya girgiza mata sannan ya yunqura ze tashi yana cewa "bari inje indauko ta Ammi nasan tana can tana ta jirana da sauri Ammi ta tsayar dashi tanacewa Aliyu wai baka da hankaline ko bakasan baka da lafiya ba kana abun kamar marar hankali kabari kasamu sauqi tukunna sai kayi duk abun da kakeso Ammi nifa lafiyata ƙalau bamma san me yakawoni nan ba dan Allah Ammi kibarni inje in dauko ta tun jiyafa nayi mata alƙawari kar ta daukeni maƙryaci Kinji Ammi dan Allah yaƙarsa fada yana hada hannuwansa alamar roƙo,
Haɗe rai Ammi tayi tace wlh inbaka shiga hankailka ba agurin nan sai na ci mutuncika beƙara magana ba ya koma ya kwanta yayi shiru Ammi ta juya ta kalli furaira tace kiɗebe su ku koma gida muma watakil idan doctor yazo ma ya sallame mu tunda naga jikin nashi da sauqi da to ta amsa mata sannan tasa hannu zata dauki mimi amma sai ta maqe kafada tare da sakin kuka wai ita ba inda zata saide su tafi ita bazata ba, Ammi ce ta wurga mata harar datasa ta shiga hankalinta sannan tace wuce kutafi kafin intattakaki badan taso ba tana ji tanagani gashi sai kuka take amma Ammi bata dakatar dasu har suka fita daga dakin bayan fitarsu ba dadewa doctor shettima ya shigo ciki saida suka gaisa sannan ya dan duddubashi da yimasa gwaje gwaje sannan yacire masa ledar qarin ruwan tunda ya qare bayan ya tabbatar da komai lafiya sannan ya cewa Ammi jikinshi da sauqi sosai dan za aiya sallamar sa ma yanzu dan haka suzo sukabi takardar sallamar da kuma magungunan da zasu siya yaringa sha godiya ammi tayi masa sannan tacewa faruq yaje yakarbo,
fita sukayi tare ita kuma ta tashi ta fara dan har hada abun da sukayi amfani da shi jiya daddare iya kayan da aka cire mishi ne sai wanda suka zo dashi yanzu ta ajiye masa agefe tace ya tashi ya shirya kafin faruq ya dawo sanna ta hade kwanukan da faruq yayi breakfast dan ta ajiye su gefe saboda ba nasu bane na asibitinne qa idar asibitinne ba azuwa da abinci ko abunsha komai kuke buqa ta kuna fada za akawo muku,
Kollon sa ta qarayi tace "ko baka shirya tafiya bane mu qara kwana nace ka tashi ka shirya amma kana kwance still inbaka son tafiyar ai sai muqara neman aqara mana kwanakin ko da sauri yatashi yace "Ammi wane irin muqara kwana me za ayi da zaman asibiti inba dole ba yanzu zanshirya fa tace ai nazata kana buqatar zamanne yace "a'a yana qarasa fada yatashi ya shiga toilet ya canza kayan ya fito fitowar sa tayi daidai da shigowar faruq dan haka ko zama ma beyi ba yace mu wuce to faruq yadauki ledar da aka zuba kayansa aciki,
Shikuma bossay ya ruqe hannun Ammi yace su tafi kallon sa tayi tace to ruqe hannun nawa na meye sakar min hannu malam yace Ammi meye aciki kibar ni kawai bata qara cemasa komai ba suka fita daga dakin suka fito harabar asibitin parking space suka nufa inda motar faruq take, faruƙ ne ya budewa Ammi back seat tashiga yayi saurin budewa bossay front shima ya shiga sannan ya zagaya shima ya bude ya shiga mazaunin driver tayar da motar yayi tare da saita hancinta ya bata wuta saida ya kusan zuwa bakin gate din sannan ya dan tsagaita gudun me gadi wa wangale masa tafkeken gadin shikuma yafice yana hawa kan titi ya qara kwasa aguje...
Ammi da takasa haukri tace "nikam wai faruq soyake ya kashemu lokacinmu beyi bane ko kuwa sai faman gudu kakeyi ko ance inbakai gudun ba baza muje ba sannu sannu ai bata hana zuwa saide adade ba ajeba ko,
Ɗan sassauta gudun yayi tare sa cewa Ammi hakan shine gudu ni wallahi dan dake nema aciki nake haka dani kadaine ai da tuni nakusa zuwa gida bare yanzu safiyace ba wani go slaw bossay ne yace Ammi ai daman shi bashi da lissafi be iya tuqi ba shiyasa ma banso Abba yabasa mota yanzu ba yafiya rawar kan tsiya,
Ammi tace ai bansan haka yakeyi ba to wlh idan baka gyara ba nida kaina zan kwace ta inyaso sai ka ringa gudun da qafarka gudu sai kace zaka tashi sama dan shiru yayi sannan yace "To Ammi nadena aranshi kuwa haka yake cewa yaza ayi inringa tafiya kamar me jin bacci ai tafiya da gudu tafi dadi lokacin da zanyi ma basani zakuyiba ai yana zancen zucin kuwa yaji bossay yace qarya kake ai baza ka dena ba ni nasan halinka.
Yace "haba yaya me yasa zakace haka kai da yakamata kayi min addu'ar denawan kuma sai kawani ce ba zan dena ba, Bossay yace to qarya nayi yace A'a amma in Allah ya yarda nadena bagashiba yanzu ma ina tafiya ahankali....
Ammi ta katseshi da cewa karma kadena din kaci gaba wataran zaka halaka kanka katafi barzahu kai kajoyo ba wani ba yar dariya yayi yace Allah Ammi kuma sai kunji saima kunfini ji tunda ni natafi ku zanbari da kuka ke zakizo kina kuka kinacewa yanzu yaron nan yatafi yabarmun saida na hanasa gudun nan amma yakiji yanzu gashi yayi mana asarar kansa murasashi har abada yanzu bazan qara ganin sa ba Allah sarki Allah yaji qanka Allah ya gafar ta maka Allah yasa ka huta kina gama fada kuma sai ki qara fashewa da wani kukan yana fada yana gwada yanda zatayi da hannu wlh sai kinfi kowa shiga damuwa ko nayi qary.....
Be qarasaba yaji saukar dukanta a damtsan hannusa tace Allah ya kiyaye inyi kuka akanka dafe gurin yayi yace wallahi Ammi fade kike ko bahaka ba big bro yafada yana kallon bossay harar sa bossay yayi yace bansaniba din,
Ammi kuma tace wai yaushe nafara wasa dakai ne har karainani haka yace Ammi ni na isa inrainaki wlh bahaka bane nide kawai gaskya nafada kuma kema kinsan.....
Bossay ne yadaka masa tsawa yace dalla malam rufewa mutane baki kaje ka mutum mana wayadamu da kai dariya faruq yaqarayi sannan yace kumana akwai wadanda suka damu dani ne kamar ku wata hararar bossay yaqara yi mishi tare da jan tsaki be qara tanka masa ba Ammi ma shiru tayi mishi dan tasan gaskyar yake fada amma batason a ringa zancen ma sai taga kamar hakanne ze faru da su ahanya shima shirun yayi yaci gaba da tuqinsa ahankali ba wanda ya qara cewa komai...
Sai daga bisani bossay yace "Ammi dan Allah muwuce mudauko su Ameesha kafin mu koma gida tace a'a kabari sai gobe yace Ammi dan Allah kiyi hakuri muje wlh banason yauma ta wuce banjeba tace wai bakasan baka da lafiya bane yace Ammi wai bagani lafiyata qalau ba nifa ba inda yake min ciwo.... yauwa Ammi dan Allah gayamin ma me yasameni yafada yana juyowa dan yaji me zatace mishi saida ta dan numfasa sannan tace muje gida tukunna sai ingaya maka yace Ammi pls kigaya min yanzu nide nasan lafiya lau nafito daga gida sai kuma yayi shiru yana tunani daga nan kuma me yafaru dashi sai lokacin yatuna tabbas lokacin da yaito daga gida sai yaga wata mota a gabansa sa ya tsaya yana tunanin ko suwaye ji yayi an bubbuga masa glass sai yabude yafito yaga wani mutum amma fuskarsa arufe take tunda ganan kuma be qara sanin inda kansa yake ba sai a asibiti ajiyar zuciya yasauke yana tunanin to me yafaru dashi me mutumin yayi mishi kuma waye shi meye hadinsa dashi bashida wanda zebashi dan haka dole ya haqura da tunanin ahaka bawanda yaqara magana acikin su har suka qaraso gida.
Yana gama daidai ta parking din suka shiga gida afalo suka zube dukan inda sauran yaran kuma daman suma duka suna falon sannu suka qarayiwa yayan nasu yana amsa musu bayan nan kuma sai yamiqe yace Ammi bari naje na shirya inje indauko Ameesha tace to tunda ka nace yazanyi dakai dan murmushi yasaki sannan yawuce batare da yace mata komai ba
yana shige ya sutale kayan jikinshi daga shi sai boxers ya Shiga toilet bedade ba yafito jikinshi sanye da towel ya daurasa a qugunsa sai wani kuma dayake goge sumar kansa gaban dressing mirror yaje yagama shafe jikinsa tsaf tare da fesa body spray masu dadin qamshi sannan ya wuce wajen wardrobe yabude ya dauko wani black jeans da red shirt sai p cap itama black sanyawa yayi ajikin shi tare ba qaramin kyau yayiba kayan sun matuqar amsar shi sai kyaunshi yaqara fitowa lakami yadauko shima