Showing 9001 words to 12000 words out of 136570 words

Chapter 4 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5440

tunda naga bakida niyar baccin naga alamun yau 'yan tsiwarne suka motsa shiyasa kika sani agaba kina sa'insa dani" Ɗan ƙara min bakin ta taƙara tura mata kawai tana haɗe rai alamun fushi take da kakar tata" batace mata komai ba ta juya zata fita cike da jin haushin zantukan Daddar tata ta tsani taga tana wannan tunanin da ita bata san amfanin shi ba(nace injiki ba)

Tana jiyo maganar ta tana cewa "au ko sallamama bazaki min ba to sai kin dawo Allah yakiyaye hanya kinji ko, kigaishe min da maman Azeeman ko tsayawa bataiba bare tasa ran zata amsa mata ahaka tai ficewar ta, amma ta amsa mata da ameen acikin zuciyarta,

Tana fita Dadda tace ja'rar yarinya kawai me tsiwar tsiya da bata da gurin yinta sai akaina dake ni ta raina ai kin iya zuwa anaɗa miki na jaki bazaki taɓuka uban komai saide ni kidawo gida kina min kuka kuma, in rashin mutunci ki yatashi ki sauke shi a kaina ni ban ma san ubanwa kika ɗauko wannan halin ba dan nasan duk iskancin gyatumarki batai irin wannan ba ita kaɗai sai faman zuba take Dadda bade mita ba.......


"Ameesha nafita direct gidan su Azeemar ta nufa tana zuwa ta bubuga gidan.

wani saurayi yazo ze buɗe sai kuma yatsaya yana cewa "waye?

Daga nan tace "ya SALEEM nice..

Tun kan ta gama faɗama ya buɗe da sauri yana sakin ƙyataccen murmushi yace "A'a ashe babbar baƙuwa mukai barkanki da zuwa.

"Itama fuskarta ɗauke da murmushi tace "yauwa ya Saleem barkan kade nasameku lafiya?

Yace "lafiya lau wlh shigo daga ciki mana kintsaya awaje sai kace gidan baƙonki ne yafaɗa yana matsa mata, tashige ciki tana murmushi shikuma yarufe gidan, sannan yabiyo bayan ta suka shiga cikin falon tare....

"Nan ma saida suka ƙara hausawa sannan yace mata "kishiga ciki maman bata nan amma Azeeman tana ciki kije, inkun gaisa kuma kizo muyi zance anan ina jiranki.

Tace "to ya Saleem bari in shiga infito" shima yace mata "to, amma dan Allah kar kuɗaɗe idan kuma kika daɗe har ciki zanshigo in ɗauko ki wallahi,

Dariya tayi tace "kar kadamu hakanma baza ta faruba" yace "tama faru ɗin kiga aiki da cikawa yarinya yafaɗa yana ɗan jefa mata hararar wasa, "bata cemishi komai tasan inta biye mishi ba barinta zeyi ta wuce ba dariya kawai tayi tashige ciki shikuma ya kwantar da kansa yana wani lumshe idanu yana jinta har cikin ransa yake jin sanyi idan yagan ta....

Tana shiga ta tarar da ita tayi ɗai-ɗai tana sharar bacci hankalin ta kwance, ƙarasawa tayi gaban gadon nata tanacewa yarinyar nan bata gajiya da bacci wallahi kullum mutum sai kace me cutar sleeping skilles, hannu ta ɗaga sama da iya ƙarfinta da Allah yabata ta ɗala mata duka a bom-bom ɗinta aikwa a firgice ta tashi tana niyar kwasa aguje tabar ɗakin dan zafin dataji yasa tama manta a ina take,

Dariyar muguntar da Ameesha ta kwashe da ita ne ganin yanda duk tabi ta furgita daga ɗan wannan dukan datai mata" A hassale tatsaya tana kallon ta tare dakai mata duka tana faɗin wlh sai Allah yasa kamin idan banyafe miki ba wannan ai cin zaline da mugunta, kinsan yanda kika tsoratani kuwa ina cikin bacci na me daɗi kizo kitashe ni kuma ma da irin wannan dukan, haka taƙarasa maganar kamar zata fashe da kuka saboda taƙaicin abun da ƙawar ta'ta tai mata,

Cikin ƙunshe dariyar da take cinta tace "ayya besty ta takaina besty ta nikadai I'm so sorry kinji ni ban san zaki tsorata har haka ba kinji ƙawalli ta aminaya ta,

Harara ta watsa mata tace anƙ haƙurin kitashi ki koma inda kika fito ni ba ruwana dake ko a hanya kika gani kar kinuna kinsani yar rainin hankali kawai da wani bakin ki tunna haihuwa da be ƙara girma ba, kinzo har gida kinci zalin na zaki zo kina min daɗin baki to bazan haƙura ɗin ba, ta ƙarasa faɗa tana miƙewa zata barmata ɗakin, tiyi saurin tare gaban ta tanacewa "haba dan Allah nafa baki haƙuri plssssss mana, na tuba bazan ƙaraba ta riƙe kunnata tana matrairai cewa kamar zatai kuka, sai lokacin bestyn tata taɗan saki fuska tace...

"Naji to...,

Sai ta kuma cewa "kin haƙura?

kai ta ɗaga mata alamun eh, aikwa da sauri ta rungumeta tana cewa "yauwa bestyna nagode daman nasan fushin ba inda zashi nasan dole zaki haƙura, ƙoƙarin tureta tayi tana faɗin "au dole ma kikace ko!

Da sauri tace "A'a wlh da wasa nake besty,

"Hmm da bansan halin ki bane sai in yarda, taraba jikin ta danata, sannan suka koma suka zauna,

Ameesha tace "oh ni yar jikar mutum daya nataho da murna ta dannazo na ganki amma nazo sai wani faman wulakanta ni kike.

Azeema tace "kikade wulaƙanta kanki da baki min mugunta ba ai da duk haka bata faruba...

Ameesha gyara zaman ta tayi tana me canza yanayin fuskar ta daga yanda take, sannan tace "to nide abar maganar komai ya wuce, yanzu dai zuwa nai kiban shawara akan gidan aikin can dana keyi wlh nagaji da cin mutuncin dasuke min kullum wahalar yau daban ta gobe daban kullum acikin cin zalina suke dayi min mugunta iri iri kinsan ɗazu Allah ne ya taimake ni amma da tuni yanzu ina barzahu, shegiyar matar nan da jikinta kamar na buhun dankali takusa yimin yankan da ake yiwa rago tsabar rashin imani......

Azeema ce ta katseta da cewa "nashiga uku ni Azeema wane zunubin kika aikata mata haka?

Tace "hmm wlh kawai muguntace da baƙin hali irin tasu ita da yarta amma ni banga abun laifi anan ba wai kawai dan BOSSAY yazo nikuma nazo fita an aikini sai yakira ni naje muna gaisawa.......nan ta kwashe duk abun da yafaru atsakaninsu da kuma abun da sukayi mata ta faɗa mata tana ƙara jin zafin abun aranta tana ɗan goge kwallar da ta zubo mata,

Hannuwan ta Azeema ta ruƙo cike da tausayawa ƙawar ta-ta tace "Allah sarki besty kiyi hakuri dan Allah gaskiya na tausaya miki kuma ai Allah ba azzalumin bawa bane yana sane dake kuma zaibi miki haƙƙin ki nacin zalin dasuke miki Allah yasaka miki kiyi haƙuri besty,

Ɗaga mata kai tayi kawai cike da tausayawa kanta da kanta,

Azeema ce ta ɗora da cewa "nifa wlh besty dama zaki bi ta tawa dakin dena zuwa ma gaba ɗaya,

Kallon ta tayi tace "nima ina tunanin hakan to amma kinsan kuɗin da suke ban dashi nake samu inyi duk wani abu daya kama inyi amakaranta dasu nake biyan kuɗin makaranta na idan nadena zuwa waze nabiya mun waɗannan abubuwan kinga Dadda bawani kuɗi ne da itaba itama kuɗin datake aiki dasu muke ɗan samu muna cin abinci da kuma ɗan ƙananun abubuwa da baza arasaba wlh bansan ya zanyi ba amma harga Allah nagaji da rayuwar nan da muke ciki, ta ƙasa faɗa cikin sanyin murya tana ƙara goge hawayen ta da yake faman zubowa daga idon ta,

Itama jikin tane yayi sanyi fuskar ta ɗauke da damuwa na tausayin ƙawar ta-ta tace "hakane kuma kiyi hakuri kici gaba da kai kukan ki gurin Allah in sha Allah nasan wataran zakiji daɗi arayuwar ki Allah ze share miki kukanki yana sane dake nide shawarar da zanbaki kawai kicigaba da hakuri dasu goben kawai kishirya kije gidan sannan kibata hakuri ko me zasuce miki kar ki ɗaga kai ki kallesu, kuma kar kisa komai aranki, tunda de kin riga kinsan halinsu, dan haka kidena bari maganganin su suna tasiri a zuciyar ki, k ibarsu da Allah kawai shi zai rama miki duk abun da suke miki,

Taji daɗin maganganun ƙawar ta'ta take taji ranta ya ɗanyi mata sanyi,

"Ni wlh tsoro nake ji kar naje ko sun shiryan wani abun ina zuwa su kashe ni ko suban guba inmutu tunda ba ƙaunata suke ba kuma basu da imani ko kaɗan ɗazu fa harda rantsuwar ta wai sai ta kashe ni a dauƙo mata wuƙa,

Azeema tace " ke karkiji komai wlh in Allah ya yardama ba abun dasu miki ai Allah yafisu kawaide ki dage da addu'a Allah ya tsallalar dake daga sharrin su ku rabu lafiya,
Ameesha ta amsa da cewa "To Allah yasa zan gwada zuwa goben, amma nasan da kyar in bazasu ƙara yimun wani abun ba tunda bahaka suka soba ya Musbahu yazo ya tamakeni amma da tuni wani zancen ake yanzu,

"Kedai wai ba nace ki dena damuwa ba kawai ki kwantar da hankalin ki kisa Allah aranki, cewar Azeema,

"To shikenan nagode da shawarar ki zan gwada ɗin, sai ta kuma ɗorawa da cewa "bari inzo in tafi gida kar magrib tamin yayin da ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye....

Azeema tace "to shikenan muje in ɗan taka miki, kinga kuma maman bata dawo ba har zaki tafi" tace "kar kidamu ai wataƙil ma zuwa jibi in ƙara shigowa tunda ke baki da mutun ci bazuwa inda nake kike ba, tace...

"Wallahi kinsan dai halin mama ai ba kullum take barina fita ba ba laifina bane amma dai zan tambaye ta zanzo,

"Hmmm kawai tace mata tana yin gaba, sannan suka fito daga ɗakin suna fitowa idonta ya sauka akan Saleem da yake ta faman zabga mata harara tai saurin cewa "laa ya Saleem dan Allah kayi hakuri wlh namanta shaf na sha'afa muna ta hira, sai yace...

"Daman mana kinshayani tun ɗazu ina ta faman jiran ki ko? To kin kyauta nagode da wulakanci daman ai kin saba"

"Tuba nake yayanmu aimin afuwa bani ƙarawa, tace dashi tana kallon sa tana murmushi,

Harara Saleem yaƙara jefa mata tare da cewa "Sai ki gayawa wanda be sanki ba komai kikai saiki wani ce tuba nake ayimin afuwa bani ƙarawa aimin afuwa kuma gobe nayi sai kin ƙara yi, yafaɗa cike da kwaikwayon muryarta yanda takeyi.

Dukan su sai suka sa dariya saboda yanda yanayin maganar tasa,

Ci gaba yayi da cewa "shikenan saiki tafi daman haka kike so ba kyaso ki zauna muyi hira yana faɗa ya miƙe ya wuce ɗakin sa, saboda bama yaso tayi masa wata maganar.

Tace "Babban yaya ayi haƙuri be tanka mata ba yayi wucewarsa,

Juyawa tayi tace "uhm besty mutafi ina ƙara daɗewa, ta faɗa tanayin gaba,

tare suka fito suna tafiya suna yar hirarsu har takawo ta daidai wata kwana da tanabi zata kai ta hargida sannan sukai sallama kowacce tatafi gidansu......,

****"***************

Musbahu be dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i yana dawo wa kwa be tsaya ko ina dan baya son haɗuwa da mom ɗin shi, sai kawai ya nufi part ɗin shi, saidai kuma kashh bekai ga shiga ciki ba ya tsinkayo muryarta tana cewa....

"To munafiki ina zaka ai daman  zaman jiran ka nake zaka wani zo kawuce sumsum kamar ɓarauniyar mage, sauko kazo nan,

Dafe kansa yayi a hankali yace "kash ya akai ta gansa, bayan ya iya dolen ya juyo yazo har inda take atsaye,

Yana zuwa be jira tace dashi wani abun ba yace "Mom bafa abun dakike tunani bane ni bawai wucewa naiba inasane kawai danna ga bakowane shiyasa na wuce" tace "karya kake yi, gidan uban wa kakai ta?

"Mom gidan su nakai ta mana dan Allah Mom kide na irin waɗannan abubuwan kina ɓatawa kanki loƙaci akan ƴar shilar nan dabata da komai bata da kowa ni wlh mamaki ma nake idan naga kina ɗaga murya akan ta.

shiru tayi tana sauraron sa, sannan yaci gaba da cewa "Ni yanzu abun danake so dake kirabu da ita ni da kaina zanyi miki maganinta da kaina basai kin wahalar da kankiba ai kinfi qarfi kiringa tsayawa da ita wataran ma ai sai ta rainaki kawai kirabu da ita kibar komai ahannu na, zakiga yanda zanyi da ita yanzu ma da na fita da ita ai bakiga yanda naimata ba naci mutuncin ta akan wahalar min ke da tayi ko da wasa gobe bazata sake aikata kwatan kwacin abun da tayi yau ba.

Wata ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara washe baki dan jin batun ɗan nata harda rungume shi dan jin daɗin kalaman sa sai yanzu tagane ashema zubar da ajinta takeyi akan ta, taba kin nashi kuma da gaskiyar shi tasan idan taci gaba watarana yarinyar nan sai ta mayar mata da martani dan ta lura da ita kamar zatai tsiwa wataƙil tana raga musune dan sunfi ƙarfinta kuma tana aiki aƙar ƙashin su ne shiyasa amma idan suka ƙureta wataran reshene zai juye da mujiya....

Sunanta da ya kirane yadawo da ita daga tunanin data tafi, amsa masa tayi da yauwa Son wlh harkasa naji sanyi araina wlh ai na ɗauka bayanta kakebi shiyasa kaji ina tai maka haka amma yanzu tunda ka ganar dani kuma ka ɗorani ahanya daga yanzu ba abun daze ƙara haɗani da ita bare hartakai da raina ni zan ringa haɗe mata rai ba ruwana da ita idan kuma tai min kuskure duk min ƙankantar sa zan gaya maka ka hukunta min ita kaji!

"Yauwa Mom haka nake son ji dazarar ta miki ba dai-dai ba ki gaggauta sanar dani kawai zaki ga me zai biyo baya, tace...

"To shikenan ba matsala wlh baka ji yanda naji daɗin maganar nan taka ba" yace "Mom ni bari inshiga ciki dan wlh a gajiye nake, tace "to baka ci komai ba haka zaka kwanta?

yace"Eh Mom kar kidamu naci abinci agidan su wani a bokina, tace "Shikenan to sai da safe yace Allah ya kaimu, sannan ya wuce yana me jin dariyar mahaifiyar tashi da tayarda da shirgatan dayayi, ta yarda kuma loƙaci guda bahamagiya kawai(inji ni fa ba injishiba😂)

yana tafiya itama ranta fes fess tahaura sama kai tsaye bedroom ɗin Rasheeda ta nufa tana shiga tasameta tafito daga wanka tana shafa mai taje ta zauna abakin gadon nata tana kallon yarta ta tace "my daughter you know what?

Tace "No Mom, saikin faɗa naga tunda kika shigo kike sakin smiling what happened? Tace "Ke! Ashe duk shirme muke akan yarinyar nan sai yanzu da yaron nan yake ganar dani sannan nagane duk yanda sukai da shi ta kwashe ta gaya mata tana ƙara sakin smiling taga yar tata ko juyowa ma batai ba bare ta tanka mata.

Tana kallon bayan tace "daughter yade, naji kinyi shiru bakice komai ba ko bakiji daɗin hakan ba ne?

Yanzu ma shiru tayi mata ba amsa tana tunanin yama za'ai hakan tafaru Yaya Musbahun da ko laifi kaimishi befiya ɗaukan mataki ba har saika ƙureshi sannan zakaga bacin ransa da irin matakin daze ɗauka shine kuma har ze gaya mata wannan maganar ta yarda da wannan ta tsuniyar tashi dan wlh wannan tatsuniyace kawai ba wani mataki da ze iya ɗauka amma tunda ita mahaifiyar tata bata gane ba gwara kawai ta rabu da ita idan taga beyi komai ba da kanta zata gane cewa shirgata kawai yayi, dan haka kawai sai ta juya tace "Mom hakan ma yayi kawai kibarshi da itan tunda haka ya buƙata,
tafaɗa mata tare da ƙaƙalo murmushin da bekai zuci ba iyakarsa kan lebe.

Itama murmushin taƙara yimata tare da cewa "niko ina saƙon da nace miki kije gurin Saratu ki karɓo min?

Tashi tayi daga inda take tana fam yatsina fuska tace ni wlh naman ta, saidai gobe idan ban manta ba naje in karɓo miki.

"Shikenan ai sai goben kawai. Cewar mom,

Rasheeda tace "uhm hum" tana ƙarasawa wajen makekiyar wardrobe ɗinta  tazuge part of dressing sleep ta ɗauko wata fingileliyar riga iyakar ta gwaiwa amma tana da ɗan kauri kaɗan tasaka tadawo wajen bed ɗin ta da har yanzu mom ɗin nata tana zaune agun tana kallon ta,

Saidai tahau kai sannan tace "Mom why are you looking at me like dat!?

Ɗan girgiza mata kai tayi tare da cewa "nothing", tace "ok, zan kwanta so u can leave?

Miƙewa tayi tace "Good night tafaɗa tana ƙarasa fita daga ɗakin,

Saida taga fitar sannan ta gyara kwanciyar ta tare da jan blanket takwanta ta bayan ta kashe light ɗin ɗakin ta ɗauko wayar ta tashiga contact ta ɗauko wata number tare da danna mata call da naga anyi saving ɗin ta da my everything,

Tana kira amma har tagama ringing ba a ɗaga ba, daɗa kira tayi nan ma aba'a daga ba har sai da ta kira wajen sau goma, amma no answer haka ta haƙura tayi cilli da wayar gefe tanjin haushin ƙin ɗagawar da yayi,

Haka ta kwanta sai faman juye juye take takasa baccin tana cikin hakan taji wayar tafara vibration da sauri ta ɗauko wayar a inda tayi cilli da ita, da sauri tayi answering gudun kar kiran ya katse (nace ko ɗan jan aji irin namu na mata babu kar kibada muman malama Rasheeda)

Tana ɗagawa, daga can ɓangaren akace "Assalamu alaikum babyna..!

Ahankali ta lumshe idonta tanajin yanda sonshi ke ƙara shigarta ko sallamar da yayi mata bata amsa ba,Cike da shagwaɓa tace "babyyyyy harda wani jansa tana karyar da kai, "u didn't pick my call why?

"Am sorry baby wlh bana kusane kuma bagashi nakira ba kin sande inagani bazan ƙi ɗaga warki ba ko? Ɗan turo baki tayi kamar tana gaban sa tace "to naji ykk?

yace "lafiya lau and you? shima ya dawo mata da tambayar, sai tace masa "ba lfy ba,
yace what wrong with you? Baby na faɗa mun me ya faru" tace "duk bakai banee! yace "Ni kuma me nayi? tace ɗazu bana gan ka da wannan banzar yarinyar ba kuna ta fam dariya kuma sai kallon ta kake wata kon ko baka san ma me kayi min ba, ta ƙarasa faɗar maganar kamar zatai mishi kuka.

Buɗar bakinshi sai cewa yayi which girl kike magana akai?

cike da taƙaicin tambayar tashi tace kana nufin baka santa ba? ta dawo masa da tambayar"

shikuma yana sane yace mata haka saboda banzar data kira da yarinyar shiyasa yace mata be gane wacce take nufi ba,

Ci gaba yayi da cewa "Sorry nifa kin min bayani yanda zan gane kwata-kwata ban fahimci wace banzar yarinyar kike nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login