Showing 120001 words to 123000 words out of 136570 words

Chapter 41 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5405

zauna da ita duk runtsi duk wuya yana tare da ita ze bata kulawa koda ze rasa ransa asanadin hakan saide yahada dashi a hukuncin da zemata yayi musu tare,

Abangare oga sam kwa tunda yafara yimishi magana akan yarinyar tunanin sa ya tsaya cak shi ba magan ganun da yafada masa ne sukayi tasiri a zuciyar sa ba kodaya beji zedena abun da yake ba hasalima haushi suka bashi danji yake kamar ya shaqoshi lokacin da yake saide kuma maganar da ta tsaya masa arai itace tahana sa daukan mataki akan maganganun da yagaya masa dan yana ganin bekai matsaya da ze tsaya agaban sa yana gaya masa magana irin haka ba kuma ya rabu dashi,

jin ance marainiya ce tasa jikin sa yin la'asar ashe duk rashin mutuncin sa yana tausayin marayu hakannan yake tausayin su hasalima yana da gidan marayu da yabude yana yiwa kowa wulakan ci ya taka wanda yaso amma in akace mutum maraya ne to ze daga masa qafa akan duk abun da ze yimasa  musamman da yaji yace bata da kowa bata san kowa nata ba sai yaji ta dan bashi tausayi amma fa kadan tausayin bawani can me yawa ba rasa tunanin dazeyi ya shiga yi shin dame zaiji da abun da yafaru tsakanin sa da abokin sa zaiji ko da wannan yaron da yazo shima yagaya masa magana san ransa yatafi ko da kin kula da yayi da yarinyar nan yanzu kuma besan ina shettima ze kaita ba kar yaje kafin suje yarinyar ta mutu yazama shine silar rasa ran marainiya gashi arashin sani ya kori abokin sa abun da betaba yi ba arayuwar sa yau shine yakama sa fargaba ya shigayi lokaci guda zufa ta tsatstsafo masa shin yanzu ta ina ze fara warware abun da ya kulla dagske fa kansa ya daure yarasa mafita mutanen dake wucewa kowa sai kallon sa yake ganin ya dade agurin a tsaya gashi ya cije baki kowa saide ya wuce saboda basu da kwarin gwiwar tunkarar sa danji abun da ya tsaida shi awajen in sukayi haka tamkar sunyi mishi shishshigine kuma yin haka zai iya sawa ma akori mutum daga aiki gaba daya dan haka kowa yaja bakinshi yayi shiru tare da qarawa motar sa mai ya wuce yabarsa agurin,

Saida yadauki lokaci me tsawo awajen kuma a tsaye batare da ya motsa ko hannun saba drivern sa da tundazu yana daga dan nesa dashi duk da dare ne amma saboda fitilun da suke a zagaye da gurin yasa ba abun da baza ka gani ko allura kajefar saika ga abarka domin gurin kamar rana haka yake...

tunda yafito yagansa ya zatama tafiya zasuyi kuma sai yaga ya tsaya be qaraso ba  yanaso yazo yaji meye ko tafiya zasuyi  amma yana fargabar masifarsa  kasa jurewa yayi qarfin hali yanufo inda yake gabansa na dukan uku uku yaqarso inda yake kansa aqasa yace 'yallabai tafiya zamuyine jin maganar sa ce ta dawo dashi daga tunanin da yafada be bashi amasa ba kawai sai yayi gaba yabarsa agun da sauri yabi bayansa har ya wuceshi ma yaje ya bude masa qofa yana zuwa ya shiga shima ya zagaya ya bude driver seat yazauna tare da yiwa motar key suka juya gate man yabude musu yadannan hancin motar suka fita tare da hawakan titi suka fara tafiya   tunda suka fara tafiya kawai ya kwantar da kansa akan hannun kujera tare da lumshe idon sa be bude ba har said da yaji motar ta tsaya sannan ya bude su a hankali yasauke su akan driver da ya bude masa kofa yana jiran da fito warsa ahankali ya zuro zara zaran qafafunsa yasauke su qasa da kyar ya iya miqewa jikinsa duk ba dadi be nufi bangaren fulani ba yau sai yanufi bangaren dayar kakar sa tawajen uwa wacce ake cewa maman 'yan biyu ita kuma amfanin ta kenan idan anbata masa rai ko kuma yana neman mafita ya rasa sai yaje ta warware masa dan haka yanzuma ya nufi bangaren ta dan ta magance mishi da kyar yake jan qafarsa har yaqara sa bejira anbashi izinin shiga ba kawai yasaka kai ya shiga ciki lokacin da ya shiga babu kowa a falon sai kawai yanufi dakinta kansa tsaye yana shiga yatarar da ita suna hira da papa tsayawa yayi abakin qofar jin anshigo ne yasasu duban inda suke tana ganin shi ta washe baki tace ja'iri qaraso mana ka tsaya anan tun da kazo sau daya muka gaisa baka sake waiwayen inda nake ba ko sai yanzu yanzu made ince ko batan hanya kayi be papa yace wane irin batan hanya yaro yazo zai gaidake kuma kina wane cemishi yayi batan kai sai kace qaramin yaro qarasa shigowa yayi fuskar sa dam ahade babu walwala zama yayi kawai be tanka musuba tare da kwantar dakan sa akan cinyarta sai kuma yayi shiru papa ne ya kalle sa yace me sunan baba meya faru ne nagan ka haka shiru ba amsa maman 'yan biyu ce ta dora da cewa ainasan daman ba lafiya ba tunda naganshi haka ni daman nasan bahaka nan akazo wajena ba da abun da akenema dan haka papa kabamu waje zamu tattauna bamuso kowa yaji nasan sirrine papa yace aikwa saide in baza ayi ba amma inan zama daram yaqara gyara zama harda dan kishingida kallon sa tayi tace to kwa duk min sa idon mutum baze jiba kagama zaman  kafita baka ji mayi anjima ko jikalle tafada tana kallon tana shafa gashin kansa suna dan hirarsu tun yanajin su sama sama har yadena bacci yayi awan gaba dashi.........✍
[26/12, 10:33 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
                  By
          Yaya Azeema 😎

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                            

      Bismillah........

                         79&80

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

  Ahaka sukaci gaba hirar su basu tasheshiba har saida shadaya ta wuce sannan papa yace mata ta tashe shi inba sotake ya kwana anan ba murmushi tayi sannan tace to inya kwanan ma meye aciki yace qafarki ce zatai tsami ai kato dashi yakwanta miki akan cinya ko zafima bakyaji sai kintashi kinji qafar ta riqe maga tayanda zakiyi tafiya kaide kaiwa kace kana kishi da sabon mijin to kwalelenka de murmushi kawai yayi be kara ce mata komai ba yashiga tashin sameer da hannu dan bude idon sa yayi ahankali yasauke su akan papa qara murza idon sa yayi dan shi yama manta  a inda yake a kwance papa ne yace sai katashi haka ai kar ka karya ta  kawani tsare mutane da ido ko anan kake shirin kwana ne lumshe idon sa yaqarayi sannan ya budesu da qyar ya yunqura ya iya tashi zaune shafa fuskarshi tayi sannan tace ka shiga bandaki ka wanko fuskarka da baki zanje insamoma abun da zakaci nasan kanajin yunwa ga cikin kanan yana kukan yunwa tafada tana dan shafo cikin nasa sannan ta sauka aikwa tana dira qafar tata taji tayi tsamin amma sai ta dake kawai saboda kar papa yagani yayi mata dariya tana fita shima yatashi yashiga yayi abun da tace masa din sannan ya fito zuwa lokacin papa har yafara gyangyadi bayan fitowar sa itama tashigo dakin fuskar ta dauke da murmushi tace yau yaron kirki zo muje idan kaci sai muyi maganar saboda yan sa ido tafada tare da ruqo hannun sa sukafito shikwa papa bema san sunayi ba dan bacci me nauyi ne yadebe shi kamar yanda tace bayan yagama cin abin cin ne yafara yimata bayanin abun da yafaru tundaga A har Z ya kwashe komai yasanr da ita dan jinjina kai tayi sanna tace kaima kayi kuskure ai yarinya qarama ka tsaya kana biyewa shirmen ta a kullum ina gaya maka ka ringa kai zuciyar ma nesa akan wasu abubuwan amma ba kaji yanzu haka ka zaba gashinan ai zaka rasa abokin ka dannasan kaf duniyar nan baka da aboki irinsa kuma baza ka taba samu ba yaro me hankali da gaskiya da riqon amana duk halayen ka yana iya jurewa ku zauna lafiya amma gashi yanzu ka kaishi qarshe kuma kazo kana regretting dan bata fuska yayi yace maamaa nifa ba fada nace kimin ba kawai kifadan yanda zan shawo kansa har insan inda suke banason ta mutu ta sanadin qin dubatan da nayi marainiya ce kawai ni solution zaki ban kallon sa tayi tadan saki murmushi irin nasu na manya kana tace hmmm babana kenan kaide baka bin komai ahankali to yanzu masalaha ta farko shine ka kirashi awaya kabashi hakuri sannan ka nemi yagaya maka inda suke sai kaje kasame su acan din zuwa gobe ko yagani hakan yayi ma tunda ta ambaci kalmar bada hakuri yake binta da wani irin kallo irin kinsan me kike fada kuwa ganin hakan yasa tace ka tsareni da ido hakan beyi maka ba ko to nide inde bata wannan hanyar zaka biba nasan baze dawo din ba kamar yanda yafada din sannan kuma itama yarinyar bazakaji halin da take ciki ba in kuma kana ganin akwai wata hanyar to sai kafada dan numfasawa yayi tare cije lip dinshi na qasa sannan yace gaskiya hakan baze taba yiyuwa ba me nayi mishi da zan bashi hakuri saide kar yadawo wlh zande kirashi inji inkuma yaqi shikenan zan rabudashi yaje duk inda zashi yafada cike da qarajin haushin shi katse shi tayi da cewa yanzu idan yarinyar ta mutu kasande kaine sila kuma me zakacewa mahaliccinka kasande Allah baze barka ba  sai yasaka mata dan haka ina qara baka shawara kaje kayi yanda nace maka din hakan shine daidai kaji baba na kayi hakuri kajekayi din in sha Allah ze sauko kaji "ok" yace mata kawai sannan ya miqe  yace ni zan tafi sai da safe har bakin qofa ta rakosa tana qara jaddada masa lalle lalle yaje ya kirashi din to yace mata amma bawai dan ze bayar din ba shibega girman laifin da ya aiakata ba da har zebada hakuri hakan bata sabuba budunga aruwa zede bi wata hanyar amma banda ta bada hakuri baze iyaba tunani me kake yaji tace da sauri yace bakomai saida safe tace Allah ya tashemu lafiya sannan sukayi sallama ya nufi sashen fulani inda part dinsa yake yana shiga yarage kayan jikin sa ya shiga yayo wanka tare da alwala yazo yayi nafilfili sannan ya kwanta akan makadeden gadon sa yabaje har ya rude idonsa sai kuma duk abun da yafaru tsakanin sa da yarinyar ya shiga dawo masa cikin brain din sa lokacin da zemata allura da magiyar da take mishi duk de wani abu da yafaru tunda suka hadu harzuwa lokacin da yarabu da ita babu abun da be tuna ba sannan yadawo kan fadan sa shettima da maganganun bossay yakasa dena tunani daga ya tuna wannan sai wancan ya fado masa da yagade beda mafita sai yajawo wayarsa lokaci ya duba yaga daya harta wuce amma hakan be hanasa lalubo number shettima ba kiransa ya shigayi amma ba amsa beyi qasa  agwaiwa ba yaqara kiransa dan atunanin sa ko yayi bacci amma yanzuma ba amsa saida yakira sa har saubiyar sannan ya hakura yabarwa gobe tare da yin cilli da wayar gefe ya kifa kansa qasa yana taso yayi bacci amma yakasa ahaka bashi yayi bacciba sai wajen uku bacci ya dauke shi,


washe gari da gudu ya shiga wani daki akidime yace tana ina yarinyar tana ina tanbayar ka fa nake kamin shiru kagaya min inda take be gama rufe baki ba yaga anturo ta akan gadon asibiti za asaka ta a mota bisa ga dukkan alamu kuma bata nufashi da da gudu yayi kanta azafafe shettima yayi saurin da katar dashi idonsa duk ya canza kala kamar ma kuka yayi da kyar ya iya bude bakin shi yace yanzu burinka ya cika ka kasheta ko to kasani baka ta mutu abanza ba dan sai na bimata hakkin ta nima da hannuna zankasheka yanda kazama sanadin mutuwar ta to nima nine sanadin rabaka da duniya yana gama fadar haka yayi kukan kura ya cakumo shi  yashiga naushinshin ta ko ina tare da shaqe mishi wuya hannu yasa yana qoqarin kwace kansa amma yakasa saboda irin ruqon da shettima yayi masa bana wasaba ne  tun yana gani har ganinsa yafara daukew kuma yana taso yaay magana amma maganar ta makale taki fitowa hannu yasa suka fara kiciniya shi yanaso ya kwace shikuma ya riqeshi gam ya hana sa damar yin hakan tafiya yayi luuu zefadi da sauri ya bude idon sa tare da miqewa zaune yana tattaba wuyan sa ko zeji hannun mutum saide ba komai ajiyar zuciya yasauke tare da katanto addu'a idan mutum yayi mummunan mafarki ashe tunda yatashi yayi sallar asuba ya koma kuma sai yafara wannan mafarkin dan shi duk atunanin sa gaskiya ne agogo ya duba yaga har goma ta kusa wayar sa yadauko akan bed side drower kiran shettima yashiga yi amma ba adaga daga qarshe ma sai yaji wayar sweach up akansheta gaba daya ta kaicine ya cika shi yanzu yanaji yana kiransa amma ya kashe wayar yana sane lalle akwai matsala kenan betaba tunanin haka daga garesa ba ya dauka duk cika baki hake ashede ze iyadin text ya dan tafa ya tura masa sannan ya ajiye wayar yaje yayo wanka yafito ya shirya sannan ya baro part din be je ko inaba agidan kawai ya nufi inda motar shi take yanazuwa driver ya bude masa ya shiga sanan yace masa nasarawa zasu tunda yaji haka yasan inda zasu dan haka yadauki hanyar gidan su shettima ,

Shettima kwa jiya yana barin asibiti da ita a tunanin sa yatafi  da ita abuja sai kuma ya tuna wani abu da sauri ya zaro wayar sa wata number naga yasaka ana dagawa bayan sun gaisa yake cewa yake cewa ya kashigo nan ne naji kace zaka shigo tun wancan satin daga can najiyo wata murya ance na shigo mana gobe na zan koma ai yace ok yanzu kana gida yace yace to dan Allah zankawo ma patien ka duba min ita ko zakazo gidan mu ka dubata kawai yace ok ba matsala bari inzo din kawai amma meyake damun ta adan takaice de yayi masa bayani yanda ze gane sannan sukayi sallama yaji dadi sosai wanda yakira wani abokin shine da suka hadu acan iyayensa duk yan nan ne amma sun koma can da zama gaba daya karewa ma shi acan aka haifeshi shiyasa komai nasa irin nacanne ba abun da yake irin na 'yan Nigeria shima kuma duk fannin yake karanta shi haryanzu be gama ba  tasanadin shi yasaba da Nigeria har yake shigowa hakannan yadan huta sai yakoma wataran ma idan yazo ba lalle bane su hadu saboda shi abun da yake kawoshi daban yana zuwa ne yayi holewar sa da 'yan mata yakoma saboda yana jin dadin rayuwa da 'yan matan nan qasar,

hankali yake tuqin dan yanzu hankalinsa ba qaramin kwancuya yayu ba yasan beda matsala tinda ya hadu da makel sunansa Abbas amma yan can kowa da haka yake kiran shi babansane kawai yake cemasa abbas saboda shi yarada masa kuma yana son sunan,

yasan be da wata damuwa zeyi masa duk abun da yakeso ahaka har yaqarasa gidan yana gama parkin ya fito ya dauko ta ya nufi cikin gidan da ita dakin hajiyar sa ya nufa da ita yana zuwa taganshi da yarinya akidime take tambayar sa a ina yasamo ta ko bigeta yayi ne ce mata komai ba saida ya kwantar da ita akan gadonta sanan ya shiga yi mata bayani sosai taji tausayin yarinyar ya shigeta sannan tace gaskiya banji dadin abun da sam yayi ba ko ba komai ai ya tasaya mata saboda rashin lafiyar ta amma yanzu ka tabbata wanda zezodin ze iya yace eh hajiya shimafa kwararren likita ne yagama kwarewa kuma har yanzu bedana neman ilimin ba yana aikin sa kuma yana qara neman wani ilimin kinsa su sunfison kimai sai sunyi zurfi sosai aciki suke hakura tace to masha Allah daman Allah inya hanaka ta wani wajen saikaga ya buda maka tawani wajen suna ta tattaunawa de akan matsalar har wayar sa tayi qara dubawa yayi yaga makel ne ke kira da sauri yadaga tare da cewa ya ka iso me yace masa yaece ok gani nan fitowa yana katse wayar yace hajiya bari inje in shigo dashi tace to maza bayan fitarsa ba dadewa suka dawo ciki tare ya ruqo masa yar jakar da yataho da ita bayan ya gaida hajiya yafara dubata yace ai doguwar suma kawai tayi sakamakon kukan da tayi ne har yataba mata kanta sanadin hakan kuma komanta ya tsaya saboda ba adade da yi mata aiki ba kuma daman irin hakan na faruwa shiyasa akafiso mutum idan anyi masa anaso yasamu nutsuwa sosai karya ringa shiga damuwa ko ana yawan yi mishi hayaniya duk hakan ze iya jawo watamatsalar sun gamsu da bayanin sa sannan sukace in Allah ya yarda za akiyaye cigaba yayi da aikin sa yasaka mata wani abu abaki bata dade ba kwa ta sauke wani wahalallan numfashi hamdalah suka shigayi suna yimata sannu saida ya dubata sosai sannan yabasu magungunan da za sudorata akai da kuma hanyoyin da zasubi wajen ganin hakan bata sake faruwa yace inde anyi haka to da wuya ma takai sati bata dawo normal ba adan kwanaki zata dawo yanda take kamar da sunji dadin bayaninsa sosai musamman shettima da har dan murmushi yake saki sannan ya shiga yimasa godiya  hajiya ma tayi masa tata sannan yaqara yi mata allurar bacci dan tasamu isashen bacci yace musu kuma ko zuwa gobe zata tashi rass kawai de bazata dawo kamar yanda take ba sai ahankali sannan adan ringa gwada mata tafiya saboda dadewar da tayi a kwance shima sai ahankali qafafunta zasu ware sosai yayi musu bayani dalla dalla bayanin dashi ogan ma beyi musuba shikwa komai yasanar dasu daga haka kuma sukayi sallama shettima ya rakasa har motar sa ya shiga leqawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login