Showing 66001 words to 69000 words out of 136570 words
ajikin shi ai sai yatafi barzahu da mamakin sa sai yaji dif yadauka yatafi barzahu ma'ana yayi bunga yabar duniya sai kuma yaji wata irin murya da besan taba agun kuma yakasa tantance wa ko tawa ce ji yay ance kai me yasa baka da imani ne wallahi ka sauketa ajikin shi ko taba shi tayi sai nayi maka dari da ita kaji inda dadi mugu kawai marar tausayi kai in wanan mutumin fa a haife ya haife ka fa kai in aka daki babanka zakaji dadi to wlh baza ka dakeshi ba saide duk abun da ze faru ya faru
ahankali baba ya shiga bude idon sa amma yana gama budewa da mamaki bega baquwar fuska agun ba idon sane yasauka akan abun da yafi sashi mamaki da kuma daga hankali ba komai bane yasashi mamakin sai tozali da yayi da bulalar nan a hannun hamza ashe duk wanna zantukan shi yakeyi baba miqewa tsaye yayi yana kallon su ba shikadai ba duk ilahiran mutanen wajen ko saida yayi mamaki da ganin abun da hamza yayi anya yana cikin hayyacin sa yayi bawani abun ya shaba irin wannan katsalan dan din agaban fulani mayake damun sa to kode jinnu ne suka shafeshi kowade da kalar nasa tunanin dan ba wanda yayi tunanin acikin hayyacin shi yake irin wadannan maganganun.....
Wanda suke kira da shugaba ne yayo kansa a harzuqe ze kaimasa duka fulani ce ta da katar dashi da tare da cewa rabu dashi watakil aljanune ajikin shi je kakira malam baba yazo yayi masa ruqiya shugaba ya juya yana kallonta yace ranki ya dade bawani aljanu kawai ranine kibarni in ladaf tar dashi ya shiga hankalin sa bata kula shiba ta taso daga inda take ta zo gaban hamza da har yanzu be saki bulalar ba yayi tsaye kuma ba alamar tsoro a tattare da shi..
fulani da ta tsaya agabansa ta kasa magana tana kallon sa shi kuma ganin tsare shin da tayi da ido sai yasashi sunkuyar da nasa idondan baze iya hada ido da itaba data ga haka sai tace yanzu nagane na tabbatar da kana cikin hankalin ka to kasani ka tafka babban kuskure arayuwar ka kai har ka isa kahana ayi hukuncin da nasa kuma agabana zaka yimin katsalandan acikin abun da nazartar kai waye kasqantan bawa marar galihu marar gata marar asali kamanta lokacin da aka tsinto ka aka kawo ka gidan nan acikin bola kamanta atunamaka tana cikin maganar wata baiwa tashigo jikin ta na rawa tazo ta zube aqasa tace agafarce ni na katse ku daman wata matace tace ai mata iso dake tana nan wajen falon tana jira cike da jin haushi fulani tace taahi kifitar min kar nasake ganin qafar kowa anan kuma koma wace tazo ace mata ta koma bani da lokacin ta yanzu
jiki na rawa baiwarnan ta miqe ta nufi hanyar fita saide kuma bata kai ga fitar ba bakuwar dake tsaye awaje ta shigo ciki kanta tsaye tunda duk taji abun da fulanin tace sakamakon daga muryar da fulani tayi shiyasa tajiyo ta..
fulani dake niyar cigaba daga inda ta tsaya sai kuma ta zabura tare da juyowa dan tabbatar da muryar wadda taji da gaske ne kokuma gizo ne aikwa ta tabbatar ba mafar ki bane sakamakon murmushin da taga matar nayi mata tsayawa tayi tare da juyowa sosai tana fuskan tarta sannan ta qaqaro murmushin dole ta aza afuskarta tana cewa ashe babbar bakuwace ai bansan ke bace lale marhaban shigo tana fadar haka tajuya ga sauran tace ku fita gaba dayan ku zanne ne ku sannan kuma aje a qullesu dakin qasa kafin nagama zan nemeku duk mikewa suka yi gaba dayan su me dorina ya shaqo baba yamiqar dashi shugaba kuma yajawo hamza suka fara jansu za su fita faga falon kawai sukaji bakuwar nan tace WHAT!!!!!! da qarfi tare da sakin jakar hannunta tafadi qasa gaba dayansu dakatawa sukayi tare da kallon ta dan ganin me takeyiwa wannan ihun haka fulani ce tace Hajiya sara meke faruwa ne haka me yabaki mamaki kasa magana tayi sai can kuma tayi saurin daidaita nutsuwarta tare dacewa ba komai fa wannan bulalar ce ta tsorata ni amma de ba mutum ake duka da itaba jin hakan yasa fulani kallon su cike da tsawa tace uban me kuka tsayayi ku bacen dagani da sauri suka fita daga ciki
Bayan fitar su fulani ta naida hankalinta ga hajiya sara tace amma kinban mamaki sai kace yau kika fara zuwa masarautar nan kuma nasan bayau kika fara ganinta ba gaya min nasande da abun da kika gani amma ba wai bulala ba daukar jakarata da tafadi qasa tayi sannan ta koma kan kujera ta zauna itama fulani zama tayi akusa da ita tace ina sauraron ki gaya min hajiya sara tace a ina kuka samo wannan tsohon?
Fulani tace sarki ne ya samoshi yanzu kuma yazama bawanmu karkada kai hajiya sara tayi sannan tace babbar magana ana wata ga wata lokaci zeyi rana zatai halinta daman ance rana bata qarya saide uwar diya taji kunya Fulani da batasan inda maganrta ta dosa ba kuma takasa fahimtar me take nufi tace ke nifa kinsan aduhu kimin baya ni mana yanda zan gane kinzo kina tawasu maganganu daban gane kansuba kin sanshi ne ?
Hajiya sara girgiza kai tayi tace yau nafara ganinsa ma amma shawarar da zan baki shine ki gaggauta korarsa aginda nan yabar gidan nan tun kan lokacin ya qure miki....
Fulani tace kamar ya kince bakisan shiba amma kuma kinace wa inkoreshi daga nan to me like nufi da hakan
Haji ya sara tadan yi shiru tana tunanin kuma wace qaryar zatai mata dabaze sa tagano da wani abun ba aqasa dan numfasawa tayi sannan tace hakan nan nace miki ki koreshi danni kallo daya nayi mishi nagane ba mutumin kirki bane daga ni wani abunne ya kawoshi shiyasa nace ki koreshi amma bawai dan nasan shiba
taqarasa fada tana kallonta danjin me zatace..
Fulani jin abunda tace sai ta sauke ajiyar zuciya a boye sannan tace ai mungano shi yanzu ma hukuncin ake yankewa kika shigo bakiji nace musu akulle suba zan nenesu ai tuni shugabansu yagano min shi shiuasa nake son aiki da wannan bawan yana min aiki yanda ya kamata baya wasa agun aikinshi...
Hajiya sara tace aini nasani kinga nima baki gaya minba amma nagane hakan saboda kina kallon idonshi zaki gane hakan kinsan halina da saurin fahimtar mutum.....
Fulani ce ta saki wani qayataccen murmushi sanna tace ai nasan halinki kwa bari insa akawo miki abun taba sai muyi maganar data kawoki dan nasan halinki baza kizo nan hakannan ba dole saida dalili.
Hajiya sara tace wlh a'a hakannan nazo mugaisa yanzu ma zantafi ana jirana a mota ta qarasa maganar tare da miqewa,
Fulani tace wai da gaske tafiya zakiyi tace "wlh tafiya zanyi jirana akeyi amota fulani tace to shikenan ai nagode ai nazata maganar dakika saba ce ta kawoki amma tunda kince haka to ki gaida gida tace gida zeji sai ankon biyu kuma, fulani tace saide naganki kawai zakice ko kuma sai bukatar ki ta taso.
murmushi kawai hajiya sara tayi sannan tace naji koma me zakice ni kinga tafita tana kaiwa nan tasakai tafice bata jira cewar fulani ba dan ta matsu tabar gidan tunda taga wannan tsohon hankalinta yatashi zaman da tayima jinta take kamar akan qaya tana fita tace tabb nida qara dawowa masarautar nan ai har abada abun da yakawoni ma nafasa aikwa asatin nan ma zan bar qasar nan ma gaba daya bazaki qara ganin qeyata ba tana tafiya sai faman sauri take kamar zata tashi sama.........✍🏿
(haba hajiya sara yazaki barmu cikin duhu baki gaya mana komai bafa gaskiya kar kitafi😭)
_______________®_______________
*ANNOUNCING*
Hello readars Pls wait and read this
Nakusa dena posting akowane group zan ringayi a group biyu kawai 👌
Yan Facebook kuyi sarching din group din sarki SAMEER sannan kuyi join anan zanringa yin posting
Yan group din wasu WhatsApp din kuma ga number ta duk meso yayi min magana insakashi a group din WhatsApp 08124226526
_______________®_______________
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
By
Yaya Azeema 😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
Bismillah.........✍🏿
41&42
'''"""""""""""""""""""""""""""""
___________FULANI
'Bayan fitar baƙuwar tata sai ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman zagaye falon take tana tunanin inde harda gasken wannan mutumin da wata manufa yazo me yasa hajiya sara zatace ta kore shi sai ta koreshi batare da ta dau matakiba ai ba inda zashi ya shigo kenan zata barshine anan ai ta azabtar da shi har sai yafadi wanda ya aiko sa sannan kuma akashe shi wannan shine hukuncin da yadace dashi sai kuma wani tunani ya fado mata to shugabansu yace mata bakin su daya ita kuma hajiya sara batace ahada da hamza ba ko kuma bata kalli idonsa bane dahaka zuciyar ta tayi na'am tabbas hajiya sara bata gashiba shiyasa itakadai de taringa saqa tana warware wa ta kulla wannan ta kulla wancan ta warware kuma jakadiya ta kira bayan tazo tace mata taje ta kira mata shugabansu da kuma me doruna tace suyi sauri suzo su sameta
angama tafada sannan tatashi da hanzarinta tabar falon.....
Bajimawa suka shigo tare suna shigo wa fulani tace suje suyi ta dukan su har sai sunfadi wanda ya turo su kar su raga musu ko kadan kuma kar suyi abun da zasu kashe su batare da sunsan wanda ya aiko suba kawai suyi musu azabtar dasu musamman ma hamza tunda shi na lura yanaji dakanshi to ayi masa abun da sai yayi nadamar abun da yayi a ladaftar dashi abashi horo me tsananin gaske aitayi musu daga nan har waye war gari kuma kar abasu abinci ko abun sha,
me doruna yace angama ranki yadade mu daman umarnin ki kawai muke jira yake uwar masarautar mu matar sarki uwar sarki kakar sarki yanzu zamu aiwatar da abun da kike so hannu ta daga mishi tare da yi musu nuni da hannu alamar ya isa suje suyi abun da ta Sakasu tagama haka kuma bata jira ficewar suba tashige ciki tabarsu agun suma fita sukayi,
Suna fita basu wuce ko inaba sai dakin qasa inda suka ajiye su hamza kafin su shiga kuma saida suka qara kiran wani dogarin shima me duka ne sannan suka shiga ciki susu uku da qafa suka tura qofar dakin da hamza yake ciki saboda ba adaki daya suka ajiyesu ba suna shiga kuwa basuyi wani aune ba, ba zato ba tsammani kawai suka ga hamza yayi tsalle kan shugabansu ya shaqeshi yana qoqarin rabashi da duniya da sauri sukayi Kansa suna qoqarin rabasu amma ina ko gezau beyiba sai faman huce yake fitar wa sai kace zaki yayi gudu da sarkin dogare yaga haka sai yadaga bulalar hannunsa da nufin yasauke ta akan hamza amma sai hamza yayi wani juyi aka sauke ta akan shugabansu a harzuke dayan ma yadaga tashi amma shima be samu nasarar samun hamza ba sai akan shugabansu ta sauka,
"Shide sjugaba ya yaga takansa dan yakasa ihun ma da yakeso yayi sakamakon shaqar da hamza yayi masa sai maqyar maqyar yakeyi da ido idon shi yayi ja saboda qamshin mutuwar da yake ji,
Me dorun ne yace kai wai kasha kwayane yafaɗa tareda jansa yanaso ya rabasu amma shima sai yasamu tsarabar lafiyayen bugu da sai da yakaishi faduwa qasa dayan ma kansa yayo shikuma ya buga mishi naushi da dayan hannushi saida bakin ya fashe saiga jini na fitowa ,
Hamza ne yafara magana yace "wlh duk wanda yaqara raɓata sai na kashe shi kamar yanda zan kashe wannan munafikin banzan me zuciyar shedan kwata kwata ba Allah aransa yajuya yana kallon shugabansu yace wlh ko kaje kafadi gaskiya ko kuma kabar duniya dan wlh wlh wlh sai na kashe ka idan baka fadi gaskiya ba yanzu ma abun da yasa zan sake ka kenan inaso ka koma yanzu ka gaya waccen banzar tsohowar me zubin saniya marar mutunci,kaje kace duk abun da kafada qarya kake in kuma kanason rasa ranka karkaje kasheka abune me sauki agareni yana gama fadar haka yayi wulli dashi jikake qato yafadi aqasa timm duk girmanshi hakan be hanasa saki qara ba sai haki yake yana goge gumin da ya tarar masa lokaci guda,
Juyawa hamza yayi ga sauran da suke jinyar jikinsu har yanzu basu dawo daidai ba harara ya watsa musu sannan yace kuma idan kunasan ranku da lafiyar ku kar kusake gigin tabani ko kuma ku taɓa Baba to wlh sai na canza muku kamanni kar kuga kungirme ni ba ruwana da girmanku ko wacce tasaku din zan iya lallasata agabanku inyaso a kore ni daga masarautar ko inga uban da ya isa ya kasheni lokacina beyi ba,
Me doruna ne yasamu qarfin tashi yace kai qaramin dan isaka me kwana da wando duk abun da kake taqama dashi nafika ba za ayi yanda kake so dinba kai har ka isa kace mana ga yanda zamuyi bayan qasa da mu kake meye matsayin ka agidan nan to bari kagani hukunci ba fashi yanzu zan ladaftar da kai sai kayi nadamar tabani da kayi kayi babban kuskure...
Wani shegen murmushi hamza yasaki me dauke da gargadi sannan yace ai gani gaka ban hanaka ba dazu ma abun da yasa na tsaya ka dake ni dan agaban waccan banzar ce amma kuma banaso inbata kunya agabanku shiyasa amma bawai tsoran ka nake jiba tunda nazo gidan nan ba tsoron kowa kuma bana shiga harkar kowa yanda nataso nikadai nake rayuwa tun kafin zuwana nan haka nake rayuwa acikin gidan nan ko akwai wanda ze taba cewa gashi nayi mishi abu kodan kunganni shiru shiru to ni ba kanwar lasa bane dan haka ka kiyayi kanka, kar ka shiga harkata inba hakaba kuma hmmmm yafada yana cizon bakinsa irin zaka ci ubanka ne.
Me dorina da yagama kaiwa qarshe duk tsoron sa da mutane sukeyi amma yau wannan mutumin zece wai baya tsoron sa aikwa ya ballowa kansa bala'i yana gama ayyana haka yadaga bulalar sa da iya qarfinsa ze sauke ta akansa aikwa caraf hamza ya ruqeta tare da fusgeta daga hannun sa be kalli kowaba ya nufi hanyar fita har dayan dogarin wanda aka fasawa baki yataso ze ruqosa sun dauka fita zeyi da mamakin su kuma sai suka ga yajawo qofar ya rufe tare da sa sakata sannan ya juyo yana kallonsu daya bayan daya fuskar nan tashi babu digon annuri akanta,
Shugabansu dake jinyar maqogaron sa da yasha shaqa shi yafara mikewa yana neman hanyar buya dan yaga alamar wannan mutumin ba a hankalinsa yake ba kar yaje ya kashesu abanza sai yanzu yake dana sanin abun da ya aikata masa iya tsawan zaman da sukayi dashi besan haka halinsa yake ba yanda yake shiru shiru ya dauka ba abun da ze iya aikatawa ashe sumimu kasim ne be gama tunanin ba yaga ya tunkaro su dukan su bawanda be tsorata da ganin sa ba amma saboda qarfin hali bazaka ga hakan akan fuskar mutum biyun ba saide fuskar shugabansu ne kawai zaka ga zallar tsoro akai,
Yana qarasowa gaban su ya shiga nade hannun rigarshi ya gyara ruqon dorinar sanna yafara sauke ta akan me doruna zuba mishi ita yake ta ko ina har kai saida ya kunce mishi abun da yanade kasa dashi sannan yaci gaba da zuba mishi ita da iya qarfinsa da Allah ya hore masa sude sauran bawanda yayi yunqurin dakatar dashi saboda kar suje yadawo kansu,
Me dorina tun yana daurewa yana rurrufe jikinshi da hannu har yafara hawaye yana cewa dan Allah kayi hakuri wlh bazan sake dukan ka ba hamza yace kama sake mana ai so nake kaji ta ajikinka da kyau kaji yanda mutane suke ji idan ka dakesu kai har dadi kake ji ana tsoronka ana cemaka me doruna to yau ga me doruna yazama me karbar doruna😂,
Hamza be qyale shiba sai da yatabbatar da ya hafa masa jikinsa waje guda saida yaga yafara dena motsi da magiyar da yakeyi sannan ya rabu dashi ya juyo kan sauran tuni suka fara bashi hakuri da magiya amma ina shibesan meye magiya ba a wannan lokacin takan dayan dogarin yafara shima saida ya tabbayar da ya daku sannan yarabudashi yadawo kan shugabansu,
Shugabansu na ganinshi yafara roqonsa shima murmushi hamza yasaki sannan yace kai ko kunya ma baka jiba inyi hakuri fa kace kai kozan hakurama ai bazan hakura akanka saboda kaine ummul aba isin faruwar komai badan kaiba sukansu baza su dake niba kaine kaja musu arayuwata babban abun da nafi tsana kenan ayimun sharri afadi abun da banyiaba sannan aci zarafina akan abun da banda laifi kai kuma duk ka aikata hakan kaga kwa naka ai sai yafi nakowa yana gama fadar haka shima ya rufar masa da duka,
Wani qarfine yake qara zuwan masa sakamakon wani haushi da yake qara tasowa da cikin zuciyar sa dan daga qarshi ma da yaga dorunar bazata gamsar dashiba jefar da ita yayi sannan yasa hannun sa yaringa dukansa kamar zarrare haka yake dukansa ta ko ina har saida shugabansu yadena motsi amma be dakata ba saida yagaji dan kansa sannan ya rabu dashi yazauna yana sauke numfashi yana kallonsu da kowa yake a kwance yakasa tashi ga shatin bulala rudu rudu ajikin su kara kallon shugabansu yayi sai kuma ya fashe da dariya yana nuna sa yace ashe duk kurin banza ne ai nazata kana da qarfi ashe baza ka iya kwatar kanka ba yanzu gaka agabana a kwance a sune kuma ba abun da zaka iya yana gama dariyar yace musu akwai ruwa acikin gurinnan da sauri suka bashi amsa da babu saide an ɗan fita da ga waje ze ga wata bambu akwai ruwa aciki bece musu komai ba ya miqe tare da cire sakatar yabude ya fita yana fita yashiga dakin kusa dashi