Showing 15001 words to 18000 words out of 136570 words
duk suna cikin wannan tunanin yakatse musu ahi da tambayar me yafaru me ya kawo wannan rikicin ne me ya haddasa fadan haka harta kai ake doke doke cikinsu bawanda ya iya bashi amsa saida yaqara buga musu tsawa yace wai ba magana nake muku ba cikin inda inda hajiya sadiya tace alhaji bafa wani abune ya faruba kawai fa....
Wata uwar harara da yabuga mata ita ta sata saurin hadiye maganar da take yace bafa nason sha shancin nan irin naki ko ya ina ganin abu da idona kice min ba komai dan kin maidani mahaukaci,
shiru tayi tana sauraron magan ganun dayake gaya mata ji take kamar ta shake mishi wuya yaza ai yazo yana mata fada agaban kaskantunan batare da tace mishi komai ba tajuya tabar gurin tana faman sambatu acikin ranta tacika tai fammm da haushi.
ganin tafiyar tata ne yasa shi dawo da hankalin sa kan su dadda yace "dan Allah baiwar Allah kuyi haƙuri nasan halinta akan fadan rashin gaskiyar ta dadda ta jinjina kai tace "ba komai Alhaji amma fa kaja mata kunne akan abun da takeyiwa jikata dan ina hakuri akan komai amma bana hakuri idan aka taba min jika ta tofa sai inda qarfina yakare bana ganin kowa da gemu Ahe.
tana kaiwa nan taja ta suka fita da kallo yabita kamar wani sakarai sannan yajiyo da kansa yana kallon yar tasa da takasa barin wajen kanta akasa yace ke uban me yahadaku fada da wannan tsohuwar daga inama take cikin da shashshhiyar muryar ta daba ta fita tace kakar me aikin muce yace um hum inajinki yimin baya nin abun da ya hadaku kasa magana tayi saboda batasan ma ta inda zata fara yi masa bayani ba ya fahimceta ganin bata da niyar magana yasashi cewa bace min daganan kafin in tattakaki agurin nan marar kunya kawai sai na saita muku zama daga ke har uwar taki me daure miki gindin zama yana kaiwa nan amaganr sa yabi bayan matar tasa yaje yaci yaci gaba da zazzaga mata masifar daman sun saba kwata kwata basa jituwa kamar ba mata da miji ba fahimtar juna atsakanin su shiyasa ma idan yayi tafiya sai ya kusan wata uku hudu be dawoba kuma idan yadawo ko wata bayayi yake kara komawa itama kuma tafi son hakan saboda tafi samu tasaqa ta tawala tai abun da ranta yakeso batare da shakkar uban kowa ba saboda ta tsani atakura mata arayuwar ta tafiso duk abun da ta qudurta yinsa to sai ta cimmashi shiyasa tasu batazo daya ba inde yana nan fa to duk abun datai laifini dan badan son datake mishi ba da tuni ta rabuda shi saidai kuma baza ta taba iyawa ba saboda ba karamin sonshi take shikuma da wannan damar yake mata abun da yaga dama idan tayi mishi hauka kuma yace wlh zata bar masa gida idan bata dena ba haka zataja bakinta tayi shiru dan ta tsani yafada mata haka arayuwar ta haka kullum suke yi ahaka suke rayuwa cikin musgunawa junan su..........
Dadda na fitowa hannun ta ruqe da na Ameesh tana faman zazzaga mata fada tace na hanaki na hanaki aiki a gidan nan amma bakyajin magana gashi nan ai yanda suke cimiki mutun ci ai wlh tunda naga kinfata ko sallama bakimin ba nasan nan din kika taho bayan dukan da suka yi miki jiya sabo da baki da zuciya shine kika kara debo qafafu kika dawo ko tace dadda nifa sabo da makaran tata nake yi ina so inyi karatu wlh tace makaran tar dole ce kibari nan gaba idan kina da rabo kyayi ko kuma idan kinyi aure mijinki ya tsaya miki kiyi tace dadda waye ze aure ni bayan banda asali gashi ma naji aunty Rasheeda tace min ni yar shegiya ce a hanya aka haifini dadda dan Allah dagaske ne ni yar shegiy....
dadda ce taisaurin rufe mata baki tace kar ki kuskura inkara jin wannan maganar abakin ki kinji nagaya miki suna kawowa dede wajen gate din gidan tafusge hannun ta tace haba dadda kigaya min gaskiya inde bada gaske bane maganar da ta fada me yasa baza kigaya min gaskiya ba kullum inna tambayeki iyayena sai kice mun sun mutu kuma daman ni banyarda dake ba wlh kina boye min wani abun to nagaji wlh inde baki fada min ba yau to nima zan shiga duniya kifada min gaskiya tafada da dan daga murya sama tana fashewa da wani irin kuka dadda da tai shiru tarasa amasar dazata ba ta batasan me zatace mata ba bataso kuma tagaya mata gaskiya yanzu harsai taqara hankali amma taga alamun yarinyar nan baza ta barta ba tunda har tafara irin wannan furucin tana cikin wannan tunanin taje hone din mota akunnen ta daka suka dago suna kallon gurin da motar take basu gama tunanin wanda yake cikin motar ba suka ga Bossay yafito dauke sa murmushi a fuskarsa saida yakaraso kusa sasu sannan yaga kukan da Ameesha take da sauri yace...
"subhanallahi baby meesha me yasa meki haka me yafaru kike kuka haka wa ya dakeki duk yabi ya rikice yana ta fam jero mata tambayoyi wani kukan taqara fashewa da shi bata iya ce mishi komai ba kallon sa yamaida ga dadda yace me yasameta ne cikin inda inda tace tambayar ta gata nan taga ya maka ni bari in wuce gida in tagaya maka tashigo gida tana gama fadar haka tayi gaba harda gudu gudu sauri sauri dan ba qaramin jin dadin zuwan shi tayi ba adede wannan lokacin dan itade har ga Allah bata san me zata cewa yarinyar nan ba da tasa ta agaba shiyasa ma tayi saurin barin wajen da tasan ze rarrasheta kuma idan tashigo gida bazata kulata ba daga haka kuma har tabar zance dan bata da tada magana idan ta tambayi abu bata samuba har lokacin ya wuce shikenan kuma tabarsa saide kuma idan anqara tayar dashi haka halinta yake dadda na wuce ya tako har zuwa gabanta sosai kamar ze shige jikinta cikin wata irin murya me kwantar da hankali yace ya furta babyyy da wani irin salo yaja sunan tare da fidda numfashi ahankali ita kuma ana ta bangaren wata irin faduwara gaba taji kirjinta sa dukan uku uku yake tunda take bata taba tsayawa da namiji ba irin haka sai taji ta duk wani iri kamar an daddaure ta dan haka sai ta danja dabaya kadan gani duk yanda tayi kuma hawayen bedena zubo mata ba kawai sai yadanyi shiru yana sakin wani site smiling ahankali yakara cewa gaya min mana nan ma shiru ba magana da yaga haka kawai sai ya riqo hannun ta yafara janta itama kuma batai mishi musuba tashiga binshi har saida yakai ta girin motar yabude mata back seat ya sakata sannan shima yazagaya ya shiga yazauna akusa da ita tare da kamo hannuwanta duka biyun yariqe qam sakuma yasaki daya yadaga dayan hannun sa ya dora akan kyakkyawar fuskar ta ya fara share mata hawayen amma saide kamar qara zuga ta yake yana share wa wasu na qara kwararo wa dayaga ji yana ta tuna nin shi yanzu me ze mata tasaura reshi dan yagaji daga nin hawayen nata baya so yaga tana damuwa shima sai yaji gaba daya garin ba dadi da yarasa me zeyi mata kawai sai yajanyo ta jikinshi ya rungume ta tsamm a faffadan qirjinshi sannan ahankali yashiga hura mata isaka adede qofara kunnen ta yana hura mata yana cewa shishhh ya isa haka ki kwantar da hankalinki kiyi shiru kinji kai ta daga mishi kawai tayi mamaki jin lokaci daya kuma taji duk wata damuwar ta tafara raguwa sai taji zuciyar ta tayi sanyi lamo tayi ajikinsa tana shakar daddadan kamshin jikinsa sai sukai wajen minti goma kafin yadago ta tare da tallafo fuskart suna fuskan tar juna yama kallon cikin kwayar idonta yace um uhum tell me what happene to you ahankali ta kwace fuskarta daga hannun shi sannan tafara yi mishi bayanin komai da yafaru ba abun da ta boye mishi komai saida tafada mishi ranshi ba kara min baci yayi ba dajin labarin da tabashi akan dukan dasukai mata da ci zarafin da sukai mata akan dan wannan abun da be taka kara yakar ba shi kwata kwata bega abun magana ba anan da har zatakai ga irin wannan danyan hukunci da suka yanke mata yadade yana jima min abun ku ashema duk wannan damuwar tata duk akanshine shene sila kuma saida yagama jima min wajen 5 minutes dakuna irin abun daze yiwa Rasheeda akan wannan danyan laifin da ta tafka sannan yace dan Allah kiyi hakuri ashe duk ni naja miki kiyi hakuri to kuma kar kidamu ni da kaina zan rama miki kai tashiga kada mishi tace kawai ka rabu da ita kar ka qara jamin laifi ta qarasa maganar da kuka dafe goshin shi yayi tara da qara riqe hannun ta yace to shikenan naji kukan ya isa haka ki nutsu muyi magana jin hakan yasata tsayar da kukan tana qara nutsuwa da maida dukkan hankalinta garshi.......
Don't forget pls comment and share it
My WhatsApp number 08124226526
Pls banda kira
****************************
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
By
Yaya Azeema
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Edited 🤗😎
9&10
*MASARAUTAR SARKI SAMEER*
Masarautar Sarki Sameer....... gagarabadau masarauta ce me cike da ɗunbin tarihi, masarauta me adalci, dajin tausayin al'umma, me jin ƙan bayinta awasu shekarun baya da suka wuce, amma banda yanzu da komai ya canza, saka makon sarkin da yake kai a yanzu,
Kwata-kwata ba imani atattare dashi, baya jin tausayin talakawa da duk wani wanda yake karkashin ikonsa, zalinci da mugunta da cin zarafin mutum ba abune me wahala agareshi ba, kuma inde mutum yanaso tasu tazo ɗaya tofa dole shima sai yazama me irin halinsa, watakon mugu irinsa, me irin banzan halayensa,
Yanzu ma kamar yanda ya saba hakanne ke faruwa ahalin yanzu....
"Wani tsohon mutum ne ya haɗe hannayen sa waje ɗaya hawaye na zuba akan fuskar sa kamar tap(famfo) yace "ya me martaba dan Allah naroƙeka kaimin rai badan halina ba, wlh nabaro matata cikin mawuyacin hali bata da lafiya rai ahannun Allah, wlh asibiti zan kaita shiyasa har nazo nawuce ban lura da motar ku ba, wlh kwata-kwata hankalina ba a kwance yake ba ka taimaka kabarni intafi karkasa su rufeni, tuba nake agafarce ni bisa kuskuren da na aikata...
Wata mahaukaciyar tsawa wani bafade yabuga mishi yace yiwa mutane shiru anan gurin kafin inyi sama dakai,
Da sauri ya haɗe bakin shi guri ɗaya yana kumashe kukan sa da yakeson kwace mishi dan takaici yagama cikashi na wannan tsawar da yaron nan ya buga mishi dukansu dagashi har shi kansa sarkin, bawanda be haifa ba amma suke mishi wannan cin mutun cin saboda kawai Allah yabasu mulki sai suringa cin zalin mutane, yana wannan tunanin"
wannan b'Bafaden da ya buga mishi tsawa yace "Allah ja daranka sarkina me dara taci gida sai ceto wanda bayason akawo masa wurgi cikin lamuransa duk yanshiga hanyarka ya jawowa kansa sarki na daban acikin sarakuna meyanke hukunci cikin adalci (nace hmm ko ina adalcin yake anan wai me adalci ko kunyar faɗama beji ba tir da halinku)
Saida ya gama koɗashi sannan yace, "umarnin ka muke jira ya shugaban mu cire masa kai zai ko canza masa kammani kana faɗa aiwatar wa kawai zamuyi,
Saida sarki yagama shan ƙamshin sa da nuna isa da mulki, sannan yasaki wani ƙasaitaccen murmushi irin nasu na sarakai, sarakan ma mugaye, sannan yace......
"Inaso a fara raba shi da kayan jikin shi, sannan ayi masa doruna hamsin a baya, guda ashirin kuma akan ruwan cikinshi, sai sha biyar a hannunsa na dama,sha biyar kuma a hannun sa na hagu, in aka haɗa duka bulala dari kenan, kafin kuma afara inaso afara zuba mishi ruwan sanyi, idan angama kuma kar abari yasa kayan akaishi ɗakin ƙasa a ƙulle sa har sai yayi kwana uku aciki, sannan kuma banyarda akai mishi abinci kullum ba, yau kar abashi, gobe abashi sau ɗaya jibi kar abashi washe gari kuma idan anfito dashi wajen ƙarfe bakwai na dare sai a bashi, sannan anuna mishi inda sashen bayi suke abashi ɗaki ɗaya a ciki" da safe kuma zai fara aiki a ƙar ƙshin ikona, daga yau ya dawo bawa a cikin masarautar nan yana gama faɗa ya juya zai bar gurin......
Da sauri bawan Allah nan ya rarrafa gabanshi yana cewa "Dan Allah kayi haƙuri ka yafemin,ko kuma duk hukuncin dazaka min kaminshi yanzu, amma dan Allah kar ka hanani komawa gida iyalina da ƴaƴa na zasu shiga wani hali na rashin gani na, dan basu san inda natafi ba ko kuma kabarni inje insanar dasu halin danake ciki na roƙeka kaimin rai dan Allah.
Yana roƙon sa yana faman goge hawaye danshi duk abun dasuka faɗa zasuyi mishi bai faga mishi hankali ba sosai kamar maganar sa ta ƙarshe akan cewa yazama bawa a gidan idan yazauna anan waze kula mishi da iyalansa,
Sarki daya gama fusata da tare shin dayayi ya ɗaga ƙafarsa da ƙarfi ya take mishi hannu ya ƙara gaba yana cewa "ku ƙara mishi hamsin akan ɗarin, sannan kugaya mishi ko dawasa yayi niyar barin gidan nan daga shi har iyalan nasa sai sun ziyarci lahira gaba ɗayan su yana maganar yana tafiya tare da maƙarrabansa suna goya mai baya.
Jin wannan batun yasa bawan Allahn nan ƙamewa agurin be ƙara motsawa ba saida yaji anfara ɗaga shi, za'a fara ƙoƙarin cire mishi riga, haka yanaji yana gani yatsaya kamar mutum mutumi yakasa ko motsi, har aka gama cireta akatafi kan wando shima akacire aka barshi daga shi sai boxes, sannan suka kwantar dashi tare da daddana masa ƙafafu da hannaye, sannan suka fara aiwatar da abun da sarki ya umarce su da suyi mishi.....
**********************
*RASHEEDA*
___Ɗagowar dazatai idanun ta ya sauka akan DADDA da sauri ta zaro ido waje tana ƙare mata kallo a wulakace cikin zafin nama ta ɗaga hannu itama zata mayar mata da marukan da tai mata saide hannun ta baikai ga ƙarasa wa fuskarba taji anruƙe mata hannu.
A fusace tajuyo tana kallon ɓangaren ta,
Ameesha da ta ruƙe hannun ta tace "Kar ki kuskura hannun ki yataɓa ta dan wlh na lahira sai yafiki jin daɗi sai na miki abun da baki taɓa tunani ba, kuma daman ko bata mareki ba ni da kaina sai na mareki nazubar miki da haƙora nafasa miki baki inga da wanne za kiciga ba da zagin mutane ko angaya miki shiru shiru tsoro ne ta fada tana sakar mata hannun, hannu tasa tashiga goge hawayen dasuke zubowa har yanzu sun kasa tsayawa Dadda da har yanzu bata furta komai ba, sai yanzu tasamu dama, tace "Ai da kin barta dana tantance mata aya da tsakuya da tagane shayi ruwane tana gama faɗar haka taja hannun Ameesha da niyar su fita taji anruƙe Ameeshan,
juyowa tayi taga waye ya riƙeta sai taga ashe matar gidan ce, ƙara tamke fuska Dadda tayi sannan tace "sakar mata hannu mutafi, Daga yau kuma baza ku ƙara ganin ƙafar ta ba, a gidan ku bare har kuji daɗin cigaba da wulaƙan tata ba, ko angaya muku talauci haukane dazesa kuna wulaƙanta ta, "to daga yau tabar gidan marar sa mutunci kawai kuma wlh......
"Bata gama faɗa ba taga ta ɗaga hannu zata mari Ameesha, tayi saurin janye ta ta mari iska, aikwa a haukace tayo kanta zata wawurota taji andaka mata wata irin tsawa, cikin ɗaga murya akace wallahi kika kuskura kika taɓa yarinyar nan sai ranki yayi mummunan ɓaci!!
Da sauri duka suka ɗago suna kallon me yin wannan maganar cike da mamaki.......
***********************
*AZEEMA*
____Tana zaune a gaban maman ta sai shashsheƙar kuka take yiwa mamanta sannan tana cewa "mama ki kwantar da hankalin ki dan Allah, wlh nasan baba ba abun da ze same shi duk inda yake nasan yanzu tunda safiya tayi yana kan hanyar dawowa gida kuma kinga yaya Saleem ma yatafi nemanshi yanzu zasu dawo kinji ki kwantar da hankalinki kar ciwon ki yaƙara tashi kinga da kyar muka samu jiya ya lafa kinji dan Allah, tafaɗa tana kama hannun ta da ɗan girgizata alamun tafahimce ta, Itade sai faman zubar da haway da take,
Suna cikin haka sukaji sallamar Saleem da sauri Azeema ta miƙe tana cewa yaya Saleem kasamo labarin inda yake cike da rashin jindaɗi ya girgiza mata kai yace wlh har yanzu de bawani labari har gurin aikin su naje amma suka ce min sude sunga ya hau mashin hankalin sa atashe yana ce musu sai gobe matarsa ce ba lfy suka ce mishi Allah yabata lafiya sannan ya taho tun daga nan basu ƙara ganin saba, yaciga ba da cewa "kuma duk inda nasan yana zuwa naje amma bansame shi ba kuma banji wanda yace min yagan shi ba, ɗan numfasawa yayi sannan yace "amma bari inyi wanka inƙara komawa ko Allah zesa adace,
Cikin sanyin jiki da rashin jin daɗi tace "ameen Allah yasa adace ɗin, haka ya nufi ɗakin shi jiki babu ƙwari ko kallon maman tasa beyi ba dan bayaso yana ganinta a irin wannan yanayin shima ba ƙaramin tashin hankali yake shiga ba, yana wuce kwa taƙara fashewa da kuka, dasauri Azeema taje gabanta ta rungume ta itama tana ƙara fashewa