Showing 36001 words to 39000 words out of 136570 words
kwace take amma takasa saboda ba qaramin ruqo Dadda tayi mata ba.
Dadda nata zuba kawai sai ganin mutane tayi tsudum acikin dakitan ta,
'Ai ba shiri Dadda ta mike tsaye da sauri zata zazzaga musu masifa sai kuma ta tsaya cak tana qarewa matar kallo baza ta taba mantawa da wannan fuskar ba arayuwar ta, itama Ammi tsyawa tayi tana kallon ta da mamaki afuskar ta Dadda tace "AMINA!
Itama Ammi amsawa tayi da cewa daman kina nan?
Dadda tace "Eh gashima kin ganni kuwa, Sai Ammi tace "To ai shiknan ma komai yazo da sauqi ta kwana gidan sauqi.
Bossay da Ameesha kasaqe sukayi suna kallon ikon Allah daman sunsan juna, lokaci guda Bossay yaji wani irin farin ciki ya lullue shi ganin yanda Dadda ke magana da Ammin sa shikenan da alama bukatar sa zata biya tunda yaga haka.
Ameesha ce tace Dadda a ina kika santa?
Dadda bata amsa mata ba tace wa Ammi bismillah Aminatu zauna mana, sai ta maida duban ta ga bakin ƙofar ta kalli Bossay da har yanzu yana bakin qofa tace kai kuma kawani tsaya mana abakin daki sai kace dogari sai kashigo ka zauna badan halinka ba ta fada tana hararar sa dukan su saida suka dan dara saboda yanda tayi maganar ita ba farin cikiba ita ba bakin cikiba ita ba fada ba kamar dai na borin kunya tayi ta yanda tayi din abun dole yaba ka dariya Shigowa yayi be zauna ko ina ba sai gurin Ameesha yaje kusa da ita datake tsaye tana mamaki ta kasa magan yaja hannuta suka zauna akan katifar ta yana kallon ta itama shi take kallo zasu fara kallon juna kenan kamar yanda suka saba sai Dadda tace tasar min daga kusa da jika malam yar dariya kawai yayi amma be da niyar tashi hakura tayi tajuya kan Ammi da take binsu da ido sannan tace wai daman kina da babban da bansani ba Ammi tace ba dana bane dadda ta harareta tace shiyasa ai naga kuna kama ko Ammi tayi dariya batace mata komai nan de suka shiga gaisawa da kuma tambayar bayan rabuwa,
Bayan sun gama kuma sai Ammi tace daman Aliyu ne yataso ni wai Sai nazo nataya shi roqonki akan zancen Ameesha da yayi miki yana fada dadda ta canza fuska duk dade daman tasan abun da yakawo su kenan kuma itade tai makon da matar nan tayi mata arayuwa da kunya tace mata a'a, amma kuma bata tunanin zata iya bayar da Ameesha amanar Allah agareta Ammi ce ta katse mata tunanita da cewa Amma fa in badamuwa in kinga da damuwa sai mu hakura kinga bama shiga haqqin kiba ko?
Dadda tayi shiru takasa tanka mata saida ta danyi jimmm tana tunani sannan tace to Amina ni bansan me zance miki ba kinga de ita kadaice dani kinga zama baze min dadi ba kuma tana taimaka min tana deban kewa bazan iya zama nikadai ba Ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan tace to amma meze hana kema kidawo gidan sai kuzauna gaba ɗaya daman ni tun a lokacin nace kizauna amma kika qi yarda to yanzuma akaro na biyu inbazaki damuba ina qara roqanki kidawo gidana da zama.
Zaro ido Dadda tayi tace ni yar gidan ubana kawai goɗai goɗai dani sai in koma gidan mutane da zama ba aiki ba ba komai gsky ni bazan iyaba kiyi hakuri.
Ammi ta numfasa sannan tace to "Dadda na yarda sai kizo amatsayin me aikin tunda haka kike so nanma qin yarda tayi tace nifa kirabu damu muci gaba da rayuwar mu ahaka Ameesha da bossay dasuka zuba kunnuwa suna sauraron su sunajira suji dadda tace ta amin ce amma taki sai suka saka baki suna ta roqonta dan Ameesha harda kukan ta shaɓe shaɓe tana cewa dadda inde kina sona dagaske to kiyarda dan Allah kuma inkika qi yarda to wlh sai kinkaini inda iyaye na suke ko kigaya min suna ina?
Jin wannan batun yasa dadda shan jinin jikinta taji wani iri tasan halin Ameesha inde tace zatai to sai tayi din inde ba ta yarda ba tasan bazata rabu da itaba tunda ta fahimci tanason komawar tasu gidan nasu din dan haka ba tada mafita da yarage ta amince haka suka cigaba da roqonta da qyar ta amince tace ta yarda zata koma din amma da sharadi amatsayin 'yan aiki zasu koma gaba dayansu daga ita har Ameeshan.
Basu da zabin su amince da sharadin ta indan ba hakaba kuma zata iya canza ra ayi dan haka gaba dan yansu sukai na'am dahakan suka ce sun yarada sun amince yarda itama tace to ta amince,
Bossay saboda murna besan lokacin da ya rungume Dadda ba har da dagata sama yana juyawa aikwa ta daddage ta buga mishi duka abaya tanacewa kaga marar kunyar yaro nizaka daga wlh kasaukeni ko ranka yayi mugun baci duk da haka be sauke ta tace wlh zance nafasa tafada tana gartsa mishi cizo a dantsan hannun sa.
Aikwa bashiri yasauketa yana cewa Dadda mungode mungode sosai,
Dadda de ya wujijigata sai faman sauke numfashi take tana haki sukwa su Ammi da Ameesha sai faman dariya suke mata saida ta tsagaita ta kalle sa tace wlh kaide baka da hankali ko kadan inbahaka ba yaza ayi kadaga ni saboda ka rainani ko to wallahi zamusa qafar wando daya dakai zamu raba gari sai na koya maka hankali kai inta kama ma da duka bulala zansa in zaneka da bakafi qarfina ba, shima dariyar yayi yace tab nidin kikafi qarfi wallahi tsaurin ido ne dake tsohuwar nan kiganni babban namiji dani me jini ajika amma kiwani ce banfi qarfinki ba to zamu gwada kwanji nan gaba saikigane idan nafi qarfinki ko banfi ba dan inaji saide a kwashi kasusuwanki akai rami a binne.
Da sauri tayo kansa zata shakoshi yayi saurin gocewa ta kamo iska tana cewa aniyarka ta bika mutuwa kake so inyi ko wallahi saide kai abinne ka bade niba saboda sai naga 'ya'yan, 'ya'yan, 'ya'yan Ameesha sannan zan mutu Ameesha tace kai yaya bakasan dadda ba abun data tsana take tsoro irin mutuwa ba ko yace kuma ko tana so ko bata so sai ta mutu ba dadda tace bakin ka yasari danyan kashi ko zan mutuma ba yanzu ba sai ka mutu ka barni hakade sukai ta fafatawa shi yafada ita ta fada kowa yaƙi yin shiru,
Saida Ammi ta katsasu sannan suka dena Ameesha tace Dadda mu hada kayan mu kinga dare na qara yi,
Dadda tace to aranni muje biki uwar kanzagi ai bayau zamu komaba kuma ba gobe ba tace sai yaushe? tace sai na shirya tukunna Bossay ne yace haba Dadda wani shiri kuma zaki ba kaya bane kawai ni kubarsu ma zan siya muku wasu kar kudau komai wlh kawai kuzo mutafi yanzu dadda tace to sannu qaruna uban yan kudi munqi din sai mundau koman mu ko tsinke baza mu bari ba yace to ai ke sai ki tazama daganan kar ma kizo mu sai mutafi da Ameesha tace itama ba inda zata qafata qafarta.
Ammi tace dan Allah kutsaya ayi magana tsayayyiya mun wuce dare na qara yi mana fa, tana fada ta maida hankalinta ga Dadda tace "yanzu Dadda ke nanda yaushe kike ganin zaki gama shirya wa sai yazo ya dauke ku Dadda tace "Nan da sati biyu Ammi tace haba Dadda wane irin shiri zakiyi ne har zuwa sati biyu dagaske kamar yanda Aliyu yagaya miki basai kun dau komai ba dan Allah kawai ku taho da kayan jikin ku sai dan abun da ba a rasaba ta bakin Ameeshan ma ni wallahi da yanzu kukazo muka tafi kawai...
Dadda ta katseta da cewa Wallahi kwa bazan mu biku yanzu ba Ammi tace to shikenan ai baza muyi miki dole ba Ameesha tace to ni Dadda zan bisu ke kyataho daga baya nan ma kin yarda tayi da kyar de suka shawo kanta akan gobe da daddare yazo ya dauke su da haka suka yarda,
Itade Ameesha ba haka taso ba taso ace daga yauma tagama kwanan gidan amma yazatayi dole ta hakura zuwa goben daga nan Ammi ta mike tagyar mayafin kanta tare da cewa to dadda mu zamu tafi sai Allah yakaimu goben dadda tace to shikenan Allah yakaimu da rai da lafiya Ammi tace amin tare da bude labulen dakin tana fita tsakar gida sannan Dadda tabiyo bayanta sai bossay da Ameesha suma suka fito hannun su ruqe da na juna kamar kar su rabu haka suke ji har qofar gida suka rakosu suna qarayin sallama sanna Ammi ta zagaya ta bude tashiga shikuma ya tsaya yaki sakin Ameesha yana cewa dan Allah Dadda kibari mutafi da ita wallahi banason rabuwa da ita,
Yace sai kayi kuma in halinka ne danni nagama magana ba yanda ya iya haka yasake ta da qyar badan yaso ba itama kuma bata so yatafi yabarta din saida yashiga mota ya rufe sannan ya zuge glass din motar yana daga mata hannu yace to sai goben itama hannu tadaga masa Dadda taja hannu ta tace dalla malama wuce mutafi nagaji.
Bossay ne ya leko waje yace wai ke bakya gajiya da masifa abun masifa baya miki wahala kulum hayaya hayaya bakya gajiya sai kace kaza.
Dadda da batai niyar kulashi ba amma jin yace mata kaza yasata juyowa afusace zata sauke mishi magana dede da maganar sa kawai yaja motar yayi gaba yana yi mata gwalo yana dariya ya buleta da isaka yayi gaba yana ta tiqar dariya Ammi na tayashi tace wlh naga alama daga haduwar ku yanzu yanzu har ka rainata amma nasan zatayi maganin ka tunda dede take da kai kuma zaku zauna guri daya duk abun da tayi maka wlh ba ruwana kai da ita.
Shima dariyar yayi yace ai Ammi inba haka nake mata ba bazata rage masifa ba kuma nima rainani zatai taringa min masifa ko agaban waye amma idan nai mata haka to bazataiba tasan intayi ma ba barinta zanyi ba kinga daga nan sai ta ringa jan baya dani Ammi tace magani ai ita da halinta ne ai bazata dena saide kai ta hasalata tana maka abun da batai niya ba.
yace "hmm aikwa zamu kwashi yan kallo dan nima ba raga mata zan ba, Ammi taci zamu gani ai shima yace zaki gani kuwa ahakade suke ta tattaunawa suna tafiya.
Dadda kwa kwafa taja sannan tajuya tana kallon Ameesha itama datake tai mata dariya bata kulata ba ta wuce ta tana cewa wlh yaron nan sai yagane kuransa naga alamar besan wacece ni ba amma muzuba mugani dan halak kafasa Ameesha dake bayanta tace lalle yau naga deden dadda Allah ya kara gwara yaringa yimiki haka wlh ke kullum murya asama duk dahaka da Dadda bata kulata ba saboda akufile take wai ita yaron nan ze cewa kaza har tashiga daki tana faman zuba ita kadai.
Itama Ameesha tana shiga kan katifarta kawai ta wuce ta kwanta cikin ranta fari tasss jira kawai take gobe tayi subar gidan sai kuma can ta tuna da bestyn ta Allah sarki yanzu rabuwa zasuyi kenan aikwa gobe da sassafe zataje gidan su acanma zata yini suyi sallama da intana zuwa aqafa tasan yanzu saide ta hau mota saikuma ta tuna da bossay ai yana zuwa zance wajen Rasheeda saita gaya masa duk sanda zezo sai su taho tare yasauke ta agidan su shikuma ta wuce idan yadawo sai yadauke ta sudawo gida haka taita tunane tunanen abubuwa da yawa daga qarshe da taga ta kasa bacci kawai sai ta tashi ta kunna ƙwan dakin ta kalli dadda data gaji da mitar tayi bacci fita tayi daga dakin tayiyo alwala tadawao tayi salloli da qara godewa Allah da nuna farin cikinta akan wannan sauyin dayayi musu lokaci daya tadade tana addu'a sannan ta shafa ta koma ta kwanta bata dade ba kwa bacci yayi awan gaba da ita..........
***********************
Da safe suna tashi Azeema tahada musu breakfast sannan suka ci gaba dayansu Saleem yau bayi niyar zuwa wajen neman aikin da wuri ba saboda kiran dazeyiwa dad din su Rasheeda shiyasa yabari idan suka gama sai yatafi suna gamawa kuwa ya dauko wayarsa yakira shi sannan yasa wayar a hansfree duk sukayi shiru wayar na ringing suna jira suji andaga amma har wayar ta katse ba adaga ba sai yaqara kira shina no respon saida yayi sau uku ana hudun ne aka daga.
Ana dagawa kuma sai sukaji muryar mace tace yana wanka inya fito za afada masa ana gama fadar haka aka kashe ba ajira amasar suba,
Wayar suka bi da kallo gaba dayan su kamar zasuga wacce tayi maganar aciki,
Mamace tasamu damar cewa kabari anjima sai ka qara gwadawa yanzu katashi kashirya katafi ko acan dinma ka kirashi duk yanda kukai inka dawo maji yanda kukai da to ya amsa mata sannan yatashi ya koma part dinshi daman yayi wanka dan haka kawai sai ya shirya shaf shaf yafito,
Har yanzu suna zaune a falon Inda yabarsu, yanzu be zaunaba kawai yayi musu sallama ya fita suka bishi da addu'ar samun nasara..........
************************
Tana kwance kan gado tayi daidai ya fito daga wanka yana tsane jikinshi da towel kalanshi tayi tace tun dazu ake kiranka a waya amma nace kana bandaki,
yace ok saida yagama shirya wa tsaf sannan yadauki wayar ya duba yaga new number ce sai yadanna kira tana shiga ko ringing uku ba ayiba aka daga ana dagawa daga can bagaren aka fara sallama shikuma ya amsa saida suka gama gaisawa sannan saleem yafara yimishi bayanin shine wanda yabawa qanwarsa kati akan yakira shi siyi magana akan batan mahaifinsu saida yagama sannan dad yace mishi ok yagane ai harma yayi magana da dan nasa tun jiya da daddare yanzu yaturo mishi full name din sa da kuma kalar kayan da yake ajikin sa da kamannin sa da shekarun su yafadi de komai yanda in anyi bincike duk wanda yagansa ze gane sa amsa masa yayi da yimasa godiya sannan sukayi sallama ba dadewa kwa yaturo mishi duk abun da ya bukata yana turo mishi shima ya turawa khalid bayan ya tura mishi sai kuma ya kira shi yana dagawa yaqara yi masa bayani sosai sannan yace dan Allah yasa ayi cigiyar nan yau kuma akai sati anayi yace mishi to sannan sukayi sallama yana gamawa ya mike tare da kallon mom datana jinshi bata tanka masa kuma ba bacci take yiba yace ni zan fita amma tayi masa banza saboda tanajin haushin sa tunjiya tunda yayi mata bayanin yanda sukayi da su dadda kuma yace mata Ameesha zata dawo aiki duk wanda kuma yaqara yi mata koda kallon banzane sai ya dau mummunan kwakwaran mataki akai ita kuma tace mishi be isaba hakade sukai ta sa insa har saida yabar mata gidan sai can dare yadawo shine tunjiya take tafaman cika ta na batsewa ahiko be kulata ba dan yasan neman fada take dan haka yanzuma da yace mata ze fita ba kulashi ba be kara bi ta kantaba yasa kai yayi ficewar sa.....
Rasheeda ce tafito cikin shirinta na tafiya makaranta jikin sanye da streetgwon da ta kamata kama ta fitar mata da surar shape dinta sosai sai mayafi da ta yafa a kafada sai wayoyinta da key din motar ta dan ko jaka yau bata dauka ba,
Tana fitowa sukayi kicibis da dad dinta da tace dad Good morning yace morning dear how was your night tace fine,
"Okey Good girl har ze wuce tace uhm dad yace yes my daughter what d u want tace dad I need a money be tambaye ta me zatai dasuba kawai yace for how much dear tace 80k yace ok I will send u later inna fita zansa miki 1m tace ok dad thanks yace kidena min godiya inban baki abun da kike so ba meye amfanin tara kudin tace hakane dad girgiza kai yayi kawai sannan yace ok let me go sai nadawo tace adawo lafiya,
Bata jira amsawar saba tashige bedroom din mom dinta tana kwankwasa kofar bata jira ambata izinin shigowa ba kawai tasakai tashiga batare da sallama ba tana shiga taga mom kwance ta dauka ma bacci take sai kuma taga ta tashi zaune sannan ta qarasa kusa da ita tace mom I have to go tana shirin juyawa taji mom din tata tace waike naga fuskarki bawata damuwa tace mom me akai min zan sa kaina adamuwa?
Mom tace "oh hakama zakice kinmanta abun da dadyn ki yafada kenan, baki ta dan tabe tare da daga kafada irin I don't care, it's your fault is not my fault dinnan sannan tace mom wlh you have a problem yanzu meye abun damuwa idan ta dawo sai me abun da ba akan mu take ba kuma nasan baza ta qara gigin yimusu wani abunba tunda tasan intayi me ze faru, kuma bayan wannan ma dad din ai ba mezaman gida bane koma me zamuyi mata ai baze saniba tundade nasa ai bazata gaya masa dan haka wlh ki kwantar da hankali duk zakibi ki takura kanki akan waccen banzar yarinyar da batasan kinayi ba nide kinsan bazan qi yin abun da dad yake so ba saboda nima yana min duk abun danake so kuma yana nuna min irin son da yake min nima kuma inasonshi dan wlh nama fi sonahi akanki mom de tagumi tayi tana jin abun da yartata take fada,
Saida tagama sannan cikin masifa tace tashi kibarmin ɗaki before I lose my temper useless girl kawai ubanwa kika taba ji yace yafison ubansa akan mahaifiyar sa sai ke shasha sha kibarni da abun da yake damuna mana basai kin qaramin wani ciwon kan ba ke kwata kwata arayuwar ki ba ruwanki da duk halin da zanshi ke sabgar gabanki kike to tunda yafini agunki sai ki koma gurinsa kar kisake zuwa inda nake taqarasa fada tana nuna mata qofa da hannu tace get out of my side!
Rasheeda tashi tayi tana cewa ai basai kin koreni ba zan bar miki daki kuma bazan qara zuwa inda kike tunda haka kike so daga cewa nafison dad sai ki kama kishi dashi to kwa zaki mutu dan bazan dena fada ba wlh nafisonshi akanki tana gama fadar haka tabar mata dakin,
Mom