Showing 96001 words to 99000 words out of 136570 words

Chapter 33 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5431

ai ni ina da hankali ba tababbiya bece walh kin kasheni yanzu da wane ido kike so inkallesa wlh baki hadu ba duk mijin da ya aure ki ya auri mahaukaciya tafada tana fusge wayar ta daga hannun ta,

tace wlh nide ba mahaukaciya bace kar kikara cemin mahaukaciya inba haka ba kuma hmmm tace in bahaka ba me zaki dakenine tace taya zandakeki amma de ni nasan abun da zanmiki kinsan halina innace zanyi tofa sai nayi dan haka kiringa kiyayewa ki iya bakin k.......

kasa qarasa maganar tayi sakamakon idon ta dayayi mata tozali da abun da bata taba zata ba dan batayi tsammanin ganisaba tunda ta sauko kuma bata lura da shiba sai yanzu shikenan tasan kashinta ya bushe ai da sauri tajuya da nufin guduwa tajiyo muryarsa yana cewa wallahi inki bar wajennan sai na canza miki kammani marar mutun ci tsayawa tayi cak amma takasa motsawa dan bata da niyar juyowa, sai nazo na sameki anan kenan?

da qyar ta iya daga qafarta ta juyo kamar wadda kwai yafashewa aciki ahankali take tafiya kamar wata mutuniyar kirki har ta qaraso wajen sa ta tsugunna gabansa kanta aqasa,
Yace sa'ar kice ita da kike mata wannan rashin kunyar ban hanaki yi mata rashin kunya ba kinmata laifi tayi miki magana kuma kin hauta da rashin kunya daman idan ina nan sai kinuna min kinshiryu sai natafi kidora daga inda kika tsaya ko to yau zanyi maganin ki in akace kiyi mata kallon banza ma baza kisake yi mata ba,dan Allah dan Annabi kayi hakuri wlh bazan sake ba daga yau na tuaba bazan qara yimata rashin kunya ba dan Allah kayiwa Allah kar kataba ni kuma kar kabani punishment wlh banda lafiya jiya na farfado daga rashin lafiya saida aka qara min ruwa leda huda sannan nasamu sauki kuma har yanzu banji sauqi ba sosai yace baki da lafiya amma kina da bakin yiwa wani rashin kunya ai idan jikin ki yagaya miki sai kiyi jinyar gaba daya,

Dr. shettima da yake ta binsu da kallo sai yanzu yasa musu baki yace dan Allah ayi mana afuwa baza musake ba tunda de bamu da lafiya idan munji sauki sai ayimana hukuncin koma ahakura gaba daya yajuya yakalli hamra yace ai kin hakura ko sister baki ta turo gaba tace wlh ban hakuraba qarya take lafiyar ta qalau ba wani ruwa da aka qara mata dukan su da mamaki suka bita da kallo dr.shettima yace da gaske lafiyar ki qalau kai ta girgiza masa tace itace take qarya so take kawai adakeni amma banda lafiya ko momma za atambaya aje atambayeta hamra tace wlh ba qarya nake mata ba lafiyar ta qalau kuma aje atambayi momma din hararar ta amra tayi sannan tace kide ji tsoron Allah me qarya dan wuta kan ajima yamutu idan kika mutu wlh ba ruwan mu ke kika cuci kanki cigaba zamuyi da rayuwar mu cikin jin dadi da walwala wata uwar tsawa yadaka mata da tasata hadiye maganar ta yace idan naqara jin bakinki saina zubar miki hakura anan shiru tayi tana muzure da idanuwa, gashin ta yaja da qarfi kamar ze tsige mata shi qara tasaki tare da sa hannun ta akana nasa tanaso tacire nasa hannun  nata ya ruqe tare da lankwasawa ya murde mata shi sosai har saida yayi qara sannan yasake ta kuka tasaka tana cewa wayyo Allah na hannuna ya karye wlh ka karya min hannu tafada tana dafe hannun tana cewa momma kizo ki taimake ni hannuna ya karye gida biyu qashushuwa na duk awaje suke momma momma hannu yasa ya buge mata baki ya miqe yana niyar fara dukan ta dr.shettima yayi saurin janyeta yana cewa dan Allah ka rabu da ita haka ai hukuncin yaya yawa be saurare saba ya qara yunqurin kamota shima yayi baya da ita yace Allah baza ka qara tabata ba yarinyar nan fa bata da lafiya amma kaki sauraren ta ka hauta hauta da fada ko sokake ka kasheta ne yace eh kashetan zanyi gara ita tafara mutuwar mu saimuyi murnar sha shasha wlh ina baki wasa ba sai na babbala ki agidan nan kafin natafi ke kwata kwata bakyason kwanciyar hankali rayuwar ki sai jawa mutane masifa hamm yana kaiwa nan yafara qoqarin fita sai ga momma nan tafito tundazu tanajin hayaniyar su tun tana cikin bathroom saida tagama shirya tsaf sannan tafito saboda tasan halin yar autar tata da rakin tsiaya abu kadan zata maidashi babba shiyasa bata damu da fitowa ba lokacin da takejin ihun nata saida tagama tana saukowa tace me yake faruwa ne amra na jin haka ta  kwasa aguje ta nufeta tana sakin wani sabon kukan momma shafa bayanta tayi tace ya isa haka gaya min me akai miki wane lafin kikayi da har ake qoqarin ballaki kasa magana tayi saida qyar ta tsagaita kukan nata amma kuma takasa bata labarin abun da yafaru ganin hakan yasa momma zaunar fa ita kan kujera tace shikenan basai kinfada ba zauana zansa azo adubaki anjima sannan ta maida kallon fa ga hamra tace ke kika jamata ko nasan halinki shiru tayi bata ce komai ba saboda tasan ko tafada ba goyon bayanta zatayi ba saboda tafison amra shiyasa kotayi laifi bata ganin ita kuma abun ba qaramin qona mata rai yake ba,

Kai kuma shine daga dawowar ka zaka kamamin ya da duka ko juyowa yayi yace momma wlh yarinyar nan duk ke kikesawa take yin abun da taga dama tace to ba itace auta ba dole tayi abun da takeso kwa yace hmmm aranshi kuwa sai yace  aikwa zan kasheta wataran ko yan karkarya mata qasusuwa yanda bazata taba moruwa ba zama yayi be qara cewa komai ba saboda inyaci gaba ransa ne ze qara baci dr. Shettima ne yafar gaida ita ta amsa masa fuskarta dauke da murmushi datambayar sa ya hajiyarsa take kwana biyu bata shigo ba lafyade ko yace lafiyar ta qalau nande tazauna itama suka qara gaggaisawa gaba daya har sameer bayan nan kuma suka saka aka kawo musu dinner me rai da lafiya da ta saka aka dafa masa na musamman saboda shi haka suka zauna gaba dayan su sukaci amma banda amra da tagama cika ta batse taqi cin komai momma na lura da ita amma bata ce mata komai ba so take idan sun tashi Saka ta agaba taci tasan taurin kanta baza ta taba ci agabansu saide idan basanan,

bayan sun kammala kuma sukatashi sukayiwa momma sallama suka fito dagana kuma suka shiga kowane sashe na gidan suka gaisa sannan suka fito dr. Shettima yace shi ze wuce sai gobe sai yace suje tare kawai yagaida hajiya yayi missing dinta yana son ganinta haka suka nufu parkin space suna zuwa drivern sa yazo ya bude mishi qofa sai yace mishi ya shiga shikadai shikuma zasushiga ta dr. Shettima inyaso sai yadawo dashi gida, atare suka fita daga bayan yana binsu abaya har suka qaraso gidan shiga sukayi lokacin da suka shiga hajiya na falo tana kallon labarai suka shiga da fara'a sosai a fuskarta ta amsa musu da cewa lalle yau manyan baqine agidan namu marhaban ku lale shiga sukayi sannan suka samu guri suka zauna sannan suka gaisa da tambayarsa ya hanya da 'yan gidan nasu a hade yabata amsa dacewa komai lafiya nande suka dan taba hira sannan yace  bari ya wuce dare yayi dan yanzu shadaya ta kusa sallama yayi mata sannan suka fito tare saida yaga tafiyar su sannan ya koma cikin gida...

Suna tafiya dan har sunyi rabi ma atafiyar tasu suna tsakiyar titi mota ta tsaya cak sai kuma ta mutu drivern yace subahannallah me ya samu motar nan kuma fita yayi yana duddubawa ko ze gano matsalar amma bega kowace matsala ba kuma hargidan ya bude yaga akwai mai da yawa said yadawo yace yallabai wlh na duba banga kowace matsala ba amma ina da wani aboki bakanike ne shi bari inkirashi sai yazo ya duba mana yace ok dagana yamaida hankalin sa kan wayar da yake dannawa after 15 minutes sai ga bakanike yazo  shima dubawar ya shiga amma yakasa ganowa wasa wasa de har suka kai wajen minti talatin amma ba bata gyaruba zafine ya ishsahi acikin motar dan haka sai yabude kawai yafito waje saboda yasamu iska sukuma suna ta qoqarin ganin komai ya daidaita amma ba labari agogo ya duba sai yaga har shabiyu ta kusa sai yace dasu wai haryanzu baku gano matsalar bane akira kwararre mana drivern nashine yace ai wannan shine oga awajen su babba ne ya iya aiki shima bakanike dagowa yayi yace wallahi 'yallabai duk gwajin da zan mata nayi amma banga komai wanda yasamu matsala ba komai yana nan yanda yake ni wallahi ma abun mamaki yake ban narashin gano inda matsalar take kowade yayi shiru yana mamakin faruwar hakan drivern ne yayi saurin cewa sir natuna wani abu kwanaki haka ta taba faruwa saidaga baya aka gano sister din kace ta hana motar tafiya ina ganinfa watakil yanzu ma facitace tundade har taqi tashi ka tuna ba laifin da kayi mata a yau bakani kenne ya kalle shi yace yar biyu ce yace masa eh itace wlh haka tayi mana kwanaki qarewa ma Sam agurin mukabar motar ta kwana yace Allah sarki ai yan biyu haka suke nima ina nan ina fama da nawa ba dama kayi musu laifi sai sun huce ta wani bangaren yace hakane haka suke su sai anbisu a hanakali daman suna ta tattaunawa de.....

shikuma yana tsaye yana sauraron sa tab lalle kama biri yayi kama da mutum yafada a zuciyar sa  afili kuma sai yace inazuwa itace ma ai wayarsa yadauko sai kuma yafara tunanin wama ze kira shettima ne yafado masa dan haka sai yakira number sa ringing biyu tayi yadaga daga can yace hello shima yace hello kana jina yace eh me yafaru yace komai ma wai kasan yar banzanr yarinyar nan abun da nayi mata dazu gashi tasa motata taqi tashi tun dazu aka kira bakanike yana duba wa amma taqi tashi sadaga baya na tuna abun da nayi mata dariya shettima yasanya masa sannan yace ai wallahi tayi min daidai maganin ka kenan angaya maka kaci banza mu ai bama yafiya sai mun rama kasan halinmu amma kake cin zalinmu shima saura kadan yasaki dariyar amma beyiba ya danne sannan yace to ni bana manta ba amma duk dahaka wlh tayi laifi koyan zu na koma gida saina hukuntata yace to shikenan muzuba mugani maga waye zefi jin jiki yace ka nidallah ba surutu nakeso ba yanzude ka kirata awaya kabata hakuri sannan kace mata tare muke dakai nasan zata bude yace to Allah yasa bari in gwada kiranta bayan 'yan mitina sai yaqar kiran shin yace to wallahi ta kashe wayarta gaba daya nakira ta hamra ma amma itama bata shiga duk akashe suke kakira momma sai kagaya mata.yace "ok" sannan ya katse wayar da mamakin sa itama sai yajita akashi shide tunda yake da momma betaba kiranta ba yaji wayarta akashe sai yau da yake bukatar ta tuna ni ma yafara yi yanzu shikam yama rasa wanda zefara kira yahadasu da momman sa dady yakira shikuma yace baya gida bedawo ba.........✍

Karatu baya muku wuyar karatu saide de rubuta comment ne yake baku wahala ko hmmm,
[24/12, 9:15 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
                     By
              Yaya Azeema 😎

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
   
                        
    Bismillah........

                         63&64

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

"Fulani yaqara kira amma itama sai yaji wayar tana ta ringing amma ba adaga ba, haushine ya ishe shi jiyake kamar ya fasa wayar sai kace itace tayi mishi laifin shettima yaqara kira yana dagawa yace sai kafito kazo ka maidani gida duk wanda nakira bata shiga shettima yace ok ganinan zuwa sannan ya katse wayar cikin motar ya koma yazauna sai faman tsaki yake saki,
saida yadau lokaci kafin ya qaraso yana zuwa sameer yafito ya shiga dagan sannan yacewa idi driver yazo su tafi subar motar agun gobe azo adauka shima bakanike aka sallameshi ya hau mashin dinshi ya qara gaba sukuma suka dau hanya tun ahanya yake ta lissafin hukun cin dazeyiwa yarinyar nan da tasa shi tsayiwa agurin nan har tsawon lokaci haka,

sai faman tsaki yake tayi ranshi duk yabi yabaci shide shettima be tanka masaba sai dariyar sa da yake yi a boye kuma abun da besani ba yana kallonsa ta gefen ido kawai rabuwa yayi dashi  dan bashida lokacin sa ahalin yanzu sai wajen qarfe daya suka qaraso gidan yana ajiye shi kuma ya juya ya koma gida,

direct part din Fulani yashige be tsaya bi takan Amra ba yabarwa gobe yana shiga part din shi ya wuce toilet yayo wanka tare da dauro alawala bayan ya shirya ya shiga jero nafil filu kamar yanda yasaba a kowane dare kafin kwanciyar sa bayan ya idar yabi lafiyar gado tare da lumshe idanun sa yayi addu'ar bacci ya shafa yaja  blanket har zuwa kansa  bawani bata lokaci kwa bacci yayi awan gaba dashi,

Washe gari bayan yayi sallar asuba yakoma bacci be tashiba sai wajen goma yana tashi yayi sauri yayi wanka sannan ya shirya kansa cikin qananun kaya da sukai mugun karbar jikin sa
cikin ta kunsa daidai kamar baya son taka qasa haka yake takawa cike da nutsuwa har ya qaraso sashen fulani ba kowa a falon,

da har ze wuce sai kuma yadaka ta yafara nufar inda dakinta yake dan yagaida ita,

yana qaraswa bakin qofar yadaga hannu sa ze kwankwasa amma sai yaji kamar ana magana qasa qasa dakatawa yayi domin jin abun da ake cewa,

Baqaramar razana yayi ba da jin maganganun da yaji fulanin nafada dan har saida ya dafa bango sakamakon ji yayi gaba daya kamar ze kife ne awajen saida yabari yadan samu nutsuwa amma duk da haka yakasa motsawa atake kuma idanun sa suka sauya kala daga farin zuwa launin ja zufa tafara tsatstsafo masa ,

jin kamar mutum ze fito ne yasa shi yunqurawa da kyar sannan yayi saurin barin wajen yana qara mamakin wannan matar shifa daman tuncan yagane wasu take taken nata bata da gaskiya acikin gidan nan shiyasa yafara saka mata ido inde yana gari tofa komai take idonshi akanta kuma dan rashin zamansa ne ma agarin amma da tuni yagama gano ta saide kawai besan abun da take kullawa bane to tabbas ya yafara hasa sho abun da yake zargi akanta yana wannan tunane tunanen har yaqaraso part din momma dinsa fadawa yayi cikin falon ko sallama babu ya shiga mommo dake fitowa daga kitchen taga yanayin da yake ciki da sauri ta ajiye abun hannunta ta qaraso kusa dashi tana duban shi cike da kulawa sannan tace son me yafa ne naga kashigo ko sallama babu ga  yanayin ya canza wa yabata maka rai da farar safiyar nan tafada lokacin da takamo hannun sa suka zauna kan kujera sannan taqara saka hannun ta duka biyu acikin nasa ta ruqo nasa sannan tace fada min me yafaru shiru yayi na wasu lokuta yakasa furta komai saidaga bisani sannan yakira sunan ta a hankali ya furta momma amsa masa tayi cike da maida hankalinta gareshi saboda jin yanayin muryar sa yaqara tabbatar nata da cewa ba lafiya akwai damuwa a tattare dashi numfasa wa tayi sannan tace inajin ka fadamun abun dake faruwa saida yaqara yin dan jimm sannan yace momma inason jin labarin masarautar nan tundaga kan me sunana danajin kunce sunansa naci har zuwa kan wannan banzan sarkin baki tariqe tare da cewa waye banzan sarki shiru yayi be bata amsa ba ta dora dacewa wai kai haryanzu baza ka canza wannan dabi'ar taka ba marar kyau uncle din naka kake cewa banza mahaifi yake agurin kafa inde zaka iya zaginshi batare da kaji komai aranka ba nima nasan watarana sai kazageni tunda ba shakkar uban kowa agaba na bakajin komai idan ka zagar min qannen alhalin suma iyaye suke agare ka wai har sai yaushene zakai hankali yaushe zaka dena samin damuwar daukin magana dakake yi kullum kai idan kazo garinnan sai kabata min rai kakejin dadi ni wallahi zaman kama acan yafiya min kwanciyar hankali akan zaman ka agidan nan tafada ranta abace saboda ta tsani taji ya zagar mata dan uwa shikuma halinsa kenan besan meyayi masa da ya tsane shi haka,

""ahankali iya budar bakinsa sannan yace sorry daga nan kuma be qara cewa komai ba ya mike tsaye tana qoqarin daka tar dashi amma ina har ya bar falon,

ahanya suka kicibusa da Amma (karima) yar biyun momma (munubiya) cike da kulawa take binsa da kallo kawar da kansa yayi yana niyar ratsata ya wuce ta dakatar dashi akallon farko ta fahimci halin da yake ciki dan haka kawai sai tace muje part din inason ganinka kai ya girgiza mata alamar a'a rai ta dan hade tare da yimasa hararar wasa sannan tace yaushe muka fara yat jayayya dakai abun da kakeyiwa mutane yau zakamin kenan nan ma kan ya girgiza mata tace to wuce mutagi inde ba hakabane abun da nafada be qara tanka mataba yabi hanyar part dinsa ita kuma tabin sa abaya,

Ajiyar zuciya momma ta sauke tare da   sakin labulen window da tadaga tana kallon su dan tunda yafota ta bude taga inda zashi dan bataji dadin abun da tayimasa ba tasan tabbass yana da damuwa tunda taga hakan a idon sa gashi kuma yazo yana tambayarta tabashi labari to dole a kwa abun da yagani ko yaji amma bata gaya masa komai ba ta haushi da fada duk da shiyaja amma itama ganin laifinta take da bata tsaya ta saurare saba amma yanzu hankalin ta yadan kwanta tunda de 'yar uwarta tazo kuma har ya yarda yabita to tasan zata iyayin maganin matsalar tashi,

bayan shigar su sashen nata suka zauna sai kuma ta tashi ta nufi kitchen dakanta ta hado masa breakfast ta kawo masa tace maza ci sai muyi maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login