Showing 18001 words to 21000 words out of 136570 words

Chapter 7 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5442

da kukam haka sukai ta kukan su ba wanda zai iya rarrashin wani sai da sukai me isarsu sannan Azeemar tafara janye jikinta tana ƙara rarrashin maman tata da kwantar mata da hankali duk da dai itama nata hankalin ba akwance yake ba
da rashin dawowar mahaifin nasu gida gashi anje ko ina ba asamo wani labarin saba,

Wasa wasa de sai gashi har wajen magari ba babushi babu dalilinsa ba alamar sa babu alamar me kama dashi, zuwa loƙacin kuwa ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, kowa da irin tunanin da yake, wani yana tunanin ko ansace shi, wani kuma yana tunanin ko wani abunne mummuna yasame shi ko kuma ma mutuwa yayi awani wajen basu sani ba, kowa de da irin nasa hasashen........


(nace Ku tambayi Yaya Azeema.... watakil tasan inda yake wlh😜)

_Announcement!_👇

_*I changed my name from Xeemat to yaya Azeema*_

Don't forget pls comment, likes and share.

My WhatsApp number is 08124226526
Plssss banda kira
             
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#:   💅SARKI SAMEER.....💅
           By
Yaya Azeema😎


             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


   _Allah yagafarta mana Allah kasakawa iyayenmu da Alkhairi Allah yabamu ikon gamawa dasu lafiya Allah yasamu a aljannar fiddausi baki ɗaya Ameen........👏_

Edited 🤗😎

13&14

     *MASARAUTAR SARKI SAMEER*
                    
.......Saboda tsabar mugunta saida suka gama yimishi duk abun da akace musu dan ko tausayin sa basaji bare suduba tsufansan ahaka har sukagama,

Bawan Allah nan yakasa ɗagowa ya kalli koda mutum ɗaya daga cikin su saida yaji sun gama suna shirin janshi zuwa ɗakin ƙasa sannan yace "Dan Allah yaran nan ku taimake ni kamar yanda Allah yataimake Ku kuroƙa min shi kuce yabarni intafi wallahi nabaro iyalaina agida zasushiga damuwa idan bankoma ba, Yagama faɗar haka tare da goge hawayen da yake zubo mishi ba ƙaƙƙautawa, Amma ko kallo be ishesu ba bare yayi tunanin zasuji tauasayin sa suyi abun da yake roƙon su akai,

Yana ji yana gani suka shiga jansa a haka har suka ƙarasa ciki ɗakin dazasu aji yeshi suka jefar dashi a ƙasan gurin yafaɗi ƙasa, Amma duk da hakan da sukayi mishi hakan behana shi, ƙara saurin miƙewa ba yayi saurin tashi yana ƙara roƙonsu dan Allah su taimake shi, amma ba wanda yatsaya bare ma yasa ran zasu saurari magiyar da yake musu har suka ƙulle ƙofar suka juya suka bar wajen duk da haka be karaya ba yataso ya ruƙe ƙofar yana kara roƙonsu har suka bace ma ganinsa sannan yadaka ta, ya koma can ƙarshen ɗakin yazauna yana ƙarewa ɗakin kallo yana tunanin tayanda zeyi kwana har uku agurin  shi kaɗai gurin yana da girma sosai da ɗakunan wajen goma ajere kamar de gidan yari kuma lofofunsu ma duk irin na sale ne, wanda inkana waje kana hango naciki shima kuma yana kallonka gashi babu komai aciki ko tabarma babu ɗakine kawai daman dan mugunta aka ginashi dan ƙasan ɗakin ma ƙasace agurin ba ko suminti bare kuma hasken nepa ko wayar wuta bama ayi wayarin ɗinta ba bare mutum yasa ran in dare yayi zega haske  gashi yayi ƙura sosai ga yana da ta cikashi da alama andade ma ba abuɗe shi ba kuma ba'a gyarashi dan haka ba ƙaramar ƙura gurin yayi ba.

Ɗaya daga  cikin sune da yaɗanji tausayin  mutumin  yajuyo da baya bayan yaga tafiyar sauran da suka yi gaba shikuma sai yayi saɗaf saɗaf yashigo gurin yana sauri sauri kar wani ya lura baya cikin su yaje yajawo wa kansa  masifa,

 Saida ya shigo kuma sai yarasa me zeyi sai yanzu yake tunanin taya ma ze taimake shi yasan de baze taɓa iya fitar dashi daga gidan ba, to wane taimakon zai basa? Ya tambayi kansa,

Daya rasa mafita kawai sai yajuya zai fita, sai ya tsinkayo muryar mutumin yana cewa "Dan Allah yaro kar kafita kazo ka taimake ni ko kuma kaje kaba wa sarki haƙuri yabarni intafi ni nayarda ma inyi kwana kin duk da yake buƙata amma kar ya hanani komawa gida wajen iyalaina, dan Allah yaro ka taimake ni,

Tsayawa yayi cak.. da tafiyar da yake sannan yaɗan juyo yana kallon dattijon da ya bashi tausayi kaɗan sannan ya shiga takawa har yaƙaraso gurin ƙofar sannan ya tsaya....

Murya ƙasa ƙasa yafara magana" yace "Baba ai saide kayi haƙuri dan wallahi inde sarki yafaɗi magana tofa baya canzata saboda baya magana biyu amma zan iya yimaka wani taimako guda ɗaya yanzu kayi duk abun da aka umarce ka harzuwa loƙacin daza ka fara aiki anan, daganan idan muka saba da kai zakaban address ɗin gidan ka batare da kowa yaji ba, nikuma zanyi ƙoƙarin inga nasa anje ansanar dasu halin da kake ciki, Amma wannan maganar tatsaya anan daga ni sai kai kar kabari kowa yaji kuma koda kaji shiru ban maka magana ba, To kar kasake kamin maganar ina sane dakai kuma zan maka magana duk tsawon loƙacin daza kaga naɗauka zan maka magana in Allah ya yarda.

Da sauri bawan Allah nan cike da murna yace "Yaro na nayarda zanyi duk abun da kace bazan bari kowa yaji ba, nagode, nagode, nagode sosai Allah yayi maka albarka kaima Allah yabiya maka buƙatunka na alkhairi yanda ka taimakeni kaima Allah ya taimake ka yaron kirki..

Mutumin da yakira da yaro yace "Ameen Baba, nizan tafi ka kula sosai sai anjima. yace to Allah yakaimu ina ƙara godiya, yace ,"Ba komai Baba yana gama faɗar haka yafice daga gurin shikuma Baba yakoma ya zauna yana dan jin sanyi aranshi, duk dade besan zuwa tsawon loƙacin da zai ɗauka ba kafin ya aika gidan nashi a sanar da iyalan nasa, Amma duk dahaka ya ɗanji daɗi, yasande dole zasuji halin dayake ciki bakamar idan ba a gaya musu ba, har mutuwarsa ta riske shi, tunda ance ya zama bawan gidan yasan bazai taɓa fitaba, saide a fita da gawarshi, amma yanzu Allahamdulillah, ko ba komai yasan bazasu shiga damuwa ba sosai akan basu san inda yake ba, gwara su sani inyaso ko aɓoye sakawo mishi  ziyara wataran yagansu suganshi, hakan ba ƙaramin daɗi yaji ba yana ta tunane tunanen shi ma sai yaji damuwar sa ta ɗan ragu kaɗan.......


....Wata datijuwa  da bazata wuce shekaru sittin da biyar ba nagani zaune kan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin falon red and golding falone me girma sosai an ƙawatashi sosai kamar ba a Nigeria yake ba dan ya haɗu iya haɗuwa,

Tana zaune kan two-seater masu kyan gaske irin na gidan sarauta tayi ɗai-ɗai ana wanke mata ƙafa ɗaya, ɗayar kuma ana daddanna mata gabanta kuma cike da fruits an yanyanka mata tana sha hankalinta kwance kana ganin ta kasan tana jin daɗin yanayin.

Gimbiya *MARYAMA* kenan tsohuwa meji da kanta ga mulki, kyau da gayu da ado ba'a magana dan ita bata yarda ta tsufa ba tanaji da kanta sosai fiye da tunanin me tunani, ba fara bace kuma ba baƙa bace amma saboda tsabar hutu yazauna mata ajiki sai takasance tana da ɗan haske fatar ta tana da kyau sosai sai sheƙe take,

Wani Bafade ne yashigo ciki da sallama bayan anbashi izinin shigowa yaƙaraso ciki kansa aƙasa yace "Ranki yadaɗe gimbiyar mu  me ran ƙarfe kici zamanin ki, kici na ƴaƴan ki, kici na jikokin ki, kici na tattaba kunan ki, kici na um hum um ɗin ki, matar sarki uwar sarki kuma kakar sarki jinjina gareki ta ban girma Allah ya ƙara miji lafiya da nisan kwana,

Duk wannan uban kirarin da yake mata ko kallon inda yake batai ba sai da taji yagama sannan batare da ta kalle saba tace "Inajin ka Junaidu meke tafe dakai tayi maganar cikin isa da ƙasaita,

Yana durƙushe agaban ta shima cike da ladabi kai aƙasa yace daman sarki ne yace inzo ingaya miki cewa ansamu sabon bawa amma yanzu haka munkai shi ɗakin ƙasa zeyi kwana uku, daga nan sai afito dashi, a kawo shi gurin ki, ki bashi aikin da ya dace dashi.

Saida tayi jimm tagama taƙamar tata sannan tace "To amma wane irine mutum ne?

yace "Eanki yadaɗe tsoho ne,

"Zaka iya tafiya" abun da tace kenan taja bakin ta ta ƙulle.

Miƙewa yayi ya fita yana sake cewa "Nabarki lafiya uwar masarauta.

Yana fita ta maida kanta ta kwantar asaman kujerar ta lumshe idon ta tana ɗan tunane tunane bata wani daɗe ba,
Ta ɗagawa bayin ta hannu dake gaban ta suna aikin gaban su alamun ya isa haka, amma basu lura ba saboda ƙasa suke kallo data ga haka sai taɗan yi gyaran murya, atare suka ɗago suna kallon ta sai tasake ɗaga musu hannu da su kaga haka sai suka sakar mata ƙafafun sannan taɗan jasu ahankali cike da izza da kasaita ta miƙe daga gurin ta nufi wata kwana,

Su kuma suka tashi suka fita daga falon, Falmata ce tafara cewa "Ramatu hmm wai yau munga takan mu Allah dai ya taimake mu bamu yi wani kuskuren ba da mun sha masifa dan naga yau ƴan muskilancinne akan matar nan kuma akusa take shiyasa ma bata son  yin magana dan idan tayi baza yafaɗi abu me daɗi ba, Itama Ramatu tace "uhm nima de abun da na lura kenan daman Allah Allah nake muyi mugama ta sallame mu tafi kar abun ya rutsa damu, tace "aikam de,
Ramatu tace "Allah sarki wallahi har na tausayawa wannan tsohon da akace ansamo zai zama bawa shiko ko wane irin tsautsayi ne yasa ya faɗa hannun waɗannan azaluman mutanannan gashi ance tsoho,

"Tabb, wallahi nima da naji ance tsoho ne, na tausaya mishi sosai yaseen, haka dai sukai ta surutunsu har suka bar part ɗin gaba ɗaya suka nufi nasu ɓangaren........

......A ɓangaran gimbiya Mama Fulani tana shiga corridor ɗin, ta nufi wata ƙofa me kyau, turawa tayi tashiga batare da ta ƙwanƙwasa ba saida tashiga ciki sannan tayi sallama aciki ciki, amma duk da haka ta ɗan fito laɗan,

Wani dattijo ne dake zaune kan bed da wani littafi ahannun sa yana dubawa bansan meye ba daga gani de kamar ma album ne na hotuna ajiye littafin yayi yana kallon ta batare da ya amsa mata sallamar ba saida tazauna akusa dashi sanan tace "barka da hutawa,

yace "barkan kide me yasame kine? naga kamar ranki a ɓace, tace "ba komai fa kawai jikina ne baya min dadi narasa dalili bata bari ya bata amsa ba taci gaba da cewa  yauwa yanzu ake gaya min wai ansamu sabon bawa ze fara aiki nan da kwana uku,

Jim yayi kamar bazai yi magana ba sannan yace "Shiyazo neman aikin da kanshi ko siyansa kukayi ko kuma halin naku kuka yi niban san a masarautar da ake yin haka ba yanzu fa bada bane ace dole sai kasa mutum yazama bawanka ta ƙarfi da yaji yakama ta kucanza tsari a masarautar nan wallahi, kuma meyasa zak....

wani uban kallon da ta zuba mishine yasashi hadiye maganar da yake sai kuma yayi ƙasa da murya yace kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyar ki nayi shiru wallahi kuma ni daman bada wata manufa na faɗi hakan ba.

Cike da masifa sai kace ɗan cikin ta kamar ba mijinta ba kuma sarki me murabus ba haka take mai masifa tace "Wai ban hanaka samana baki akan tsarin masarautar nan ba ina ruwanka damu ne ko dan kaga nace mishi duk abun da yayi a masarautar nan yasanar dani nikuma inzo ingaya maka shine zaka fara yimana shishshigi to daga yau ba abun da zaka ƙara ji daga cikin abun da yake wakana game da masarautar mu,

"Nacefa kiyi haƙuri ko, nadena daga yau duk abun da za kuyi kuje kuyi tayi yafaɗa yana gyara kwanciyar shi tare da juya mata baya itama bata ƙara ce mishi komai ba ta tashi fuuuu tashige bathroom shikuma yabita da kallo yafara tunanin wai me yasa yazama haka ace matar shi ce zata na mishi faɗa haka kamar ma shine ƙasa da ita ba itace ƙasa dashiba shi abun yana bashi mammaki ganin yakasa ɗaukan mataki akai saide duk abun da tace shi za'ayi to kode tayi mishi.... yana cikin tunanin yaji kansahi yana mishi wani irin juyi kamar ze bar jikinshi haka yasa hannu biyu yana dafe kan yana ambaton duk addu'ar datazo bakinshi  daman yasaba duk lokacin da irin haka tafaru yafara tunanin faruwar irin waɗannan matsalolin domin yasamo solution to atake a lokacin yake jin irin wannan matsanan cin ciwon kan daga nan kuma bacci ya ɗauke shi idan yatashi kuma ya manta duk abun da yafaru to yanzu ma hakance tafaru yana cikin addu'o in kwa bacci ya dauke shi.

Bayan kwanciyar shi da befi minti uku ba ita kuma tafito jikin ta sanye da rigar wanka tana fitowa ta tsaya tana binshi da wani shegen kallo sannan tasaki wani irin murmushi me cike da abubu wa masu wuyar fassarawa aranta kuma tace "hmmm dani kake zancen kaci gaba kar kafasa, nima kuma bazan fasaba muzuba mugani shege kafasa ni da kai aga waye winner, a fili kuma sai tace "A sha bacci lafiya ta wuce gaban dressing mirror tana shafe jikinta da mayuka da turaruka saida taga ma tsaf sannan ta nufi wajen wardrobe ta ɗauko wasu baƙaƙen kaya tasaka tare da dakko wata balar hula kallart ja tasaka sannan ta nufi wani waje ta bude labule sai ga wata yar ƙaramar ƙofa dan in ba agaya maka akai ba, zaka rantsa babu komai awajen saida ta tsaya tayi wasu surutai sannan tasa hannu ta buɗe ƙofar tasa kai ta shiga ciki,

Nide tsoro ya hanani shiga bare inɗauko muku rahoto dan haka na tsaya awaje ina jiran fitowarta saida ta ɗauki wajen 30 minutes sannan ta fito, nagan ta sai faman zufa take tana goge zufar da hannun ta directe bathroom ɗin ta ƙara komawa amma bata daɗeba tafi ta ƙara cire kayan jikin nata tasa wata atamfa yellow collar riga da zani ne sai ta ɗauko ɗan kwalinta ahannu bata ɗaura ba, ta dawo kan gadon tazaun agefen gadon kusa dashi  tana kallon mijin nata,

Kamar yana jin ta ta shiga cewa "kadena min taurin kai ka dena min shishshigi a lamura na sai mu zauna lafiya batare da ka wahala ba saida ta gama faɗar hakan, sannan ta kai hannu saman fuskar shi ta shafasa, tana shafawa kwa yabuɗe idon sa sai tasakar masa murmushi, shima murmushin ya mayar mata dashi tace "Ya da bacci? yanzu kasande ba kyau bacci dab da magariba ko,

Yace "Eh nima wlh bansan ya akai na fara baccin ba kinsan bacci ɓarawo ne shi yazo ya sace ni, ƴar ƙaramar dariya tayi tace lalle yayi ƙoƙari da ya sace sarki guda gaskiya yakama ta a hukun tashi dan yayi babban laifi,

Shima dariyar yayi yace baccin za' a hukunta ko? tace "Eh mana,

Yace "To ayi sauri kar ya gudu in kuma ya haɗa da me hukuncin shima yasace shi kinga shikenan tafaru ta ƙare kenan yaci nasara,

Ba tace komai ba sai dariya datayi wacce iya kacinta baki dan bata kai zuci ba, shima itan yayi yana tashi zaune haka de suka ci gaba da ƴar hirar su kamar basu san da wani abu ba wai shi tsufa,

Kiran sallar da akeyine ya katse musu hirar tasu yatashi ya nufi banɗaki yayo alwalla ya fito yace to kema kije kiyi kafin na dawo muci gaba da hirar mu ko? tace "To" kawai

Shikuma yafita zuwa masallaci yana fita tabi lafiyar gado tai kwanciyar ta alamun bazatai  sallar ba kenan.....

har yaje yayi sallar yadawo bata tashi ba amma yana tambayar ta hartayi sai tace mishi eh tayi be yarda ba amma bashi da damar yin magana saboda sanin halinta dan yasan bata son yin sallah kwatakwata bata dame taba, bece mata komai ba har ya zauna sai kuma yafasa yace mata "Zanje palace (fada)

Sai tace kayi me fa? yace "zan ɗan duba wani abune" tace wane abu ne shi ko ba shida suna, yace "To zanyi maganane da sarki akan batun sabon bawan da kikace ansamu inji aikin da za abashi, tace Bana buƙatar zuwan naka nizan bashi aiki dakaina kazauna kawai anjima ni zanje mutattauna dashi basai kaje ba.

Allah sarki bawan Allah sarki me murabus  haka jiki babu ƙwari yace da ita to sannan yasamu gefanta yazaun tare da zabga uban tagumi da ta lura da hakan tasan yanzu ze fara tunanin nashi da yasaba sai kawai tace "Ƴallaɓai! be ɗago ba yace mata "uhm"

Bata damu ba da yanayin da ta amsa mata ba, tace "Waini kam ya batun waziri ne da matar sa tadawo ne yace mata, "A'a yace min wai iyayen ta sunce bazata dawo ba wai har sai an amince da ƙudirin su sannan zata dawo,

Buɗar bakin ta sai cewa tayi "Lalle kwa zata mutu a gida kenan ko kuma ta auri wani, yace hakan ma baza ta faruba zadai ayi tunani akai za asamu masalaha, tace "To Allah yasa" yace "Ameen"


        ************************

                 *AMEESHA*

Bayan ta maida hankalin ta gareshi yace "Yauwa kinsan me nakeso dake?

Tace "A'a,

Yauwa to daman inaso ince miki kidawo gidan mu dazama zan faɗawa Ammi na halin dakike ciki  nasan zata yarda ni kuma zan ɗauki nauyin karatunki daga nan har kiga ƙarshen biro da takarda kuma ba ruwanki da wani aiki muna da masu aiki yanzu zankai ki wajen, Daddar ki, sai ki gaya mata nasan Itama zataji daɗin hakan ko ya kikace? Yayi maganar yana tsareta da ido, yana jiran yaga reaction ɗin ta,

Shiru tayi na ɗan wani loƙacin bata ce masa komai ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login