Showing 54001 words to 57000 words out of 136570 words
motse yakasa kuma bece mata komai kawai yatsaya yana kallonta sai can kuma yamaida idanun sa tare da azasu akan kyakkyawan hannuta yana kallon su.
Ganin hakan da tayi yasata sakin shi ahankali tare da dan ja baya sannan tace "I'm sorry sir tare da sunkuyar da kanta qasa shikam ya bushe agun ya kasa magana saida kyar ya iya daidaita kansa sannan yakalli Azeema dasai faman cika take tana batsewa nuna ta yayi da yatsan sa yace kinci darajar me daraja amma wlh da sai na canza miki kamanni marar kunya fitsarar riya shasha sha ballagaza....
yana kaiwa nan kawai ya juya yabarta yasan ko ba komai ya rama zagin da tayi mishi yatafi yana tunanin wlh da ba dayar yarinyar nan ba sai ya koya mata hankali, sai ta kirashi da dan iskan da hujja yana qarasa wa wajen motar sa yabude ya shiga yatayar da motar ranshi na mishi quna da shi har yanzu bedena takaicin abun da tace mishi gaba dayama sai yaji ya tsani kansa duk shi yajawa kansa da ya kulasu da be kulasuba da duk hakan bata faru ba bare wannan banzar yarinyar tagaya mishi magana son ranta kuma ya rabu da ita be dauki babban mataki ba haka yaringa tafiya yana ta faman doka tsaki shi kadai.........
Bangaren su Azeema kuwa da ta gama cika da haushi harda kuka wai yazo yaci mata mutunci alhalin shine da laifi amma yayi mata haka Ameesha itama fuskarta da damuwa tace dan Allah kiyi hakuri ki manta da komai shima watakil ranshine ya baci akan zaginshi da kikayi kuma yajiki shiyasa shima yayi miki haka dan ya huce haushin shi tace kuma sai yaringa zagina ni irin haka nayi mishi basai ya rama da abun dana yimishi ba harda cemin fa ballagaza menayi mishi ko yaganni ina yawo da mazane ko ya ganni da wata shiga da bata dace ba Ameesha tace dan Allah kibar wannan maganar yafada ne kawai dan yabata miki rai kinsan daman ramuwar gayya tafi ta gayya zafi shiyasa tun farko nace miki murabu lfy muje kikace kar muje Yanzu gashi nan yazo yabata miki rai yabata mana lokaci dan Allah muje kar Dadda taga mundade,
Janta tayi zuwa inda me kayan miyar yake suna zuwa suka bashi kudin Ameesha ta gaya masa duk abun da suke bukata shikuma yabasu Ameesha tasa hannu ta karba suka juya suka nufi hanyar gida suna tafiya Azeema nacewa wlh in Allah ya yarda sai ya hadu da daidan sa ahanya sai ya hadu da wanda zeci mutun cinsa fiye da yarda yaci mutuncin ta,
Itade Ameesha banda bata hakuri ba abun da take yi mata har suka qaraso gida Azeema bata dena mita ba da sallama suka shiga dadda dake daki ta idar da sallar la'asr ta amsa musu sallamar suna shiga basu je ga shiga dakin ba Ameesha ta wuce ta dauko roba da wuqa da zasu yanka salad din sannan suka shiga daki,
suna shiga Dadda tace sai yanzu Sai kace an aiki bawa garinsu ina kuka tsaya kukuwa?
Azeema ce tace wlh Dadda wani dan rainin hankali ne yatare mu yaci min mutunci kuma yatafi Allah zesaka min takara sa maganar da kunbura fuska sai kace Dadda ce tayi mata laifin dadda da mamaki take kallon su tare da son qarin bayani dan bata fahimci komai ba,
Ameesha ce ta gayra zama ta bata labarin duk abun da yafaru dadda kwa ita abun ma dariya yabata amma sai tayi qoqarin riqe abarta bata bari ta fito ba saboda yanda taga Azeema tasan ranta yabaci idan kuma tayi mata dariya zata fi jin haushi ma sai kawai tace ayya Allah sarki gaskya be kyauta ba kiyi hakuri Allah ze saka miki kuyi sauri ku gama kuci danni har na ci nawa danaga shiru tunda mungama komai idan kuci sai kuje can gidan din saikiyiwa maman tasu sallama da to Ameesha ta amsa sannan taci gaba da yanka salad din da suka suyo bawanda yaqara cewa komai har tagama taje ta wanko ta dawo sannan taqara komawa ta zubo musu ta kawo komai da zasu bukata harda ruwan sha sannan takalli Azeema tace mata bismillah kai ta girgiza mata alamar baza taci ba hararar ta tayi tace wai ke baza kicire wannan abun aranki ba shi yana can yana uzurin gabansa ya manta dake amma ke zaki tsaya kina sawa kanki damuwa abanza a wofi shiru tayi mata bata ce mata komai ba kuma bata sa hannu a abincin ba,
Saida Dadda tasa baki sannan ta fara cin abincin bawanda yayi magana har suka gama ita kuma dadda nata faman gyangyadi alamar bacci take ji sai Ameesha ta gama kimtsa wajen sannan tayo alwala tacewa Azeema taje tayo tazo suyi Sallah bayan sun idar da sallar ne Ameesha ta sake shirya wa tasa doguwar rigar atamfa da dinki yayi mata das kamar ajikin ta aka dinka shi sai ta dora mayafi akai,
Azeema de na zaune tayi tagumi tana kallon ta har ta gama sannan ta tashi sukayi wa Dadda sallama suka fita a hanya ma de bawan da yace komai saboda Azeema taqicewa komai shiyasa itama taja bakinta tayi shiru suka ci gaba da tafiya sunqun sunqun kamar raquma har suka qarasa gidan dasuka shiga, nan ma de Azeema taqi sakin jikin ta har saida Mama tagane bayan sungama gaisawa da Ameesha sai ta tambayeta me yafaru da Azeema ne nanma de labarin abun da yafaru tabawa mama
Mama tace maganin ki kenan ke meyasa zaki zageshi bayan kinsande ya girme ki gwara da yayi miki hakan ni wlh yayi min daidai,
Azeema jin hakan yasa ta tashi daga gurin ta koma daki dariya Mama tabita da ita tana cewa Allah ya shiryeki sai da tayi shiru sannan Ameesha ta sanar da ita cewa Dadda tana gaida ita kuma tace tana tayaki murna Allah yasanya alkhairi da Ameen mama ta amsa mata sai Ameesha ta dora dagaya mata zasu tashi itama mama batajin dadi ba dajin tashin nasu haka tayi musu fatan alkhari,
bayan sungama kuma itama ta tashi tabi bayan Azeema tana shiga kuma taganta kwance ta kifa kanta tana ta faman kuka da sauri ta qarasa inda take tare da dago ta ta rungumeta tace haba besty wai meye haka ne kikeyi sokike kisawa kanki cuta akan abun da be taka kara ya kar ba,
Azeema tace dole kice haka mana tunda bake aka zaga ba tafada tana kwace jikinta daga jikinta Ameesha itade taga takanta dan ita wlh abun harma yafara bata haushi daman ita Azeema haka take kwata kwata bata iya fushiba zata dade batayi ba amma idan tayi anshiga uku kullum cikin mita take
Dan haka kawai sai tacewa Azeema ke ni wlh nagaji bari inzo intafi gida tunda abunnan yafaru sai baki hakuri nake amma kinki hakura bansan kuma me zan miki ba tana gama fadar haka ta miqe zata fita sai kuma Azeemar tayi saurin ruqota, dakatawa tayi da tafiyar sannan ta juyo tana kallon ta tace wlh inde bazaki dena ba tafiya zanyi.
Dakatar da kukan da take yi tayi sannan tasa hannu tana goge hawayen tace nadena wlh abunne sai nayi qoqarin in manta sai kuma inqara tuna wata maganar tasa maganganun sa sai yawo sukeyi min narasa dalili,
Ameesha tace ki manta kawai gyada mata kai tayi sannan tashiga bathroom ta wanko fuskarta sai ta zauna ta goge fuskar itama Ameeshan zama tayi suna fuskan tar juna tace ko kefa dan Allah wlh har kinyi kyan gani bakya kyau da damuwa bare kuma kuka murmushin dole ta qaqaro ta aza a fuskarta sannan tace ai baza kigane bane amma de yanzu in sha Allah komai ya wuce tace yauwa koke fa..........
Nande da wasa da wasa Ameesha ta shawo kanta sai kuma suka barke da hira kamar ba gobe kiran sallah ne ya katsesu suka ankare wai har lokaci yaja haka dasauri Ameesha ta miqe tana cewa kai besty wai har lokaci yaja haka nayi magariba awaje Allah yasa Dadda kar tamin fada,
Azeema ma tace wlh nima nayi mamaki muyi sallah to sai in rakaki,
Shaf shaf suka idar da sallar sannan suka fito falo mama bata nan daki suka leqa Ameesha tayi mata sallama sannan suka qara fito wa sukayi waje Ameesha tace laa nikam kinga har zantafi bamu hadu da yaya saleem ba Azeema tace wlh kuwa saide ingaya masa idan yadawo niban ma san me yazaunar dashi awaje ba har yakai wannan lokacin tace to shikenan kya gaya masa haka sukai ta hira har suka zo inda zasu rabu sannan sukayi sallama kowa ya nufi hanyar sa,
Ameesha sai sauri takeyi kamar zata tashi sama abu biyu ne suka sata saurin na farko tana tunanin kar dadda tayi mata fada na biyu kuma kar yaya bossay yazo bata nan aikwa adan mintina kadan ta qaraso gida da sallama ta shiga cikin gidan dadda bata waje dan haka kawai tashiga dakin tana shiga taga dadda na lazumi...
Guri ta samu tazauna har Dadda tagama sannan Ameesha tace Dadda kinga nayi dare ko wlh muna daki bamu lura da lokacin ba sai da mukaji kiran sallah Dadda tace to ai shikenan tundade kindawo gida lafya sai a kiyaye gaba kuma.
Tace in sha Allahu Dadda, daganan Dadda ta dora mata da nasiha akan zaman rayuwa sosai kwa nasihar ta shige ta har aka kira sallar isha'i sanna ta tsaya dayi mata alawala Ameesha ta qara yowa tazo tayi sallah itama.....
Abude kamar wasa har goma ta wuce amma shiru kake ji ba labarin zuwan bossay tun Ameesha na hakuri har takasa tace dadda kinga fa har yanzu yaya bossay bezoba anya kuwa zezo tafada fuskarta cike da damuwa
Dadda tace tunda kikaga haka watakil wani uzurin ne ya riqeshi ya hana shi zuwa kije ki kwanta kawai sai gobe idan Allah yakaimu tunda yanzu kinga har shadaya ta kusa bazuwa zeyiba kije ki kwanta,
Da "To" ta amsa mata jikin ta asanyaye ta ta jawo katifar da suka daga dazu ta sauke ta ta dauko zanin ta shimfida da filo sanna ta kwanta tayi luf kamar me bacci ita kadai tasan yanda takeji aranta saboda ta kwallafa rai akan yau zata bar gidan amma sai gashi Allah beyiba haka ta kwanta ta ringa tunani dan bata jin zata iyayin bacci yau.........
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER......💅
By
Yaya Azeema😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
Bismillah.......
35&36
********************
Da wuri Saleem yatashi yafara shirin zuwa wajen aikin da zeje yama gama shiryawa yafito ya gaida mama tana yimishi magana ma akam ya tsaya ya fara karyawa amma yace mata aa baya so yayi late da addu'a ta rakasa har bakin ƙofa,
Azeema ce ta fito da gudu tana cewa yaya wai fita zakayi ina ya qoqari ingma hada maka abun da zakaci dan Allah ka tsaya ya kusafa just give me a few minits dan Allah kaji,
Ɗan murmushi yayi yace "haba auta sokike infara laifi daga zuwa na nafiso inriga kowa zuwa kibari namiki alƙawari koma me kike min ki ajiye min idan nadawo zanci koda ya wuce bata rai tayi tace nifa wlh bazan bari ka zauna da yunwa ba ko ka tsaya ko kuma kaban address din wajen inzo in kawo maka gurin aikin buda baki yayi yace ke rufamin asiri in mutu maza sukaine ba mata ba daga fara zuwa ne sai kawai aga ankawo min abinci kinsan kwa yanda gurin yake da tsaro kiyi hakuri,
Mama ce tace wai ke meye haka din wani sabon kinibibin ne da saunawa yana fita beci abincin ba sai yau zakisashi agaba da shirme kai kuma ka tsaya da tunima ka kusa zuwa, hakan ma da kayi ai ƙara bata loƙacin kake yi ka wuce katafi...
Ɗan murmushi yaqara yi sannan yace Mama ai da sauran loƙaci yanzufa ko bakwai batayi ba zumudine irin nawa kawai amma yanzu tunda tanaso bari injirata ta qarasa idan kuma takai qarfe bakwai da minti goma zan yafi....
Da sauri Azeema tace "na yarda wlh.
Mama tace "Au biye mata din zakayi to nide ba ruwana idan kaje kasamu matsala sai hankalinku ya kwanta ko girgiza kai yayi yace mama in Allah yayarda ma bazamu samu matsalar komai ba in sha Allah kada kai tayi ta koma tazauna tace ai sai kuyi tayi jinjina kai yayi kawai sannan yabi bayan Azeema da tunda taji yace zejirata ta koma kitchen din yana shiga yaganta a tsaye sai faman aiki take da sauri da sauri gyaran murya yayi ta dan juyo ta kalle sa tace laa wai biyo ni kayi ai nama kusa kaje ka jirani a falo kaji yace to sannan yajuya yana ce mata sauran ki minti goma tace kafin lokacin ma ai nagama yace Allah yasa tace amin sannan tadan zuba ƙullin dake gabanta dan tabbatar da man yayi zafi yana zubawa kuwa yayi ƙara cuuwwi nan da nan tafara sakin ƙosai da Sauri da sauri tana gama daidai yanda tasan ze isheshi sai ta kashe gas din ta zuba masa a plate sannan ta dauko cup tazuba mishi kunun gyadar da ta hadashi tundazu tazuba a flax sai yanzu ta tsiyaya mishi daidai yanda tasan ze isheshi sannan ta dora akan faranti tare da cokali sai yar ƙaramar robar sugar ta dora masa duk wannan abun adan ƙanƙanan lokaci tagama komai tafito tace gashi har nagama aide lokacin be cika ba ko?
Ɗaga mata kai yayi sannan yace gsky kinyi sauri me kika yiminne haka akeso sai naci tace idonka yagane maka tunda gashi yanzu zaka gani tana gama fadar haka ta ajiye masa waro ido yayi yace wow gaskiya auta godiya nake kinmin suprise wlh, duk son da nakeyi wa abunnan na dade banci ba bansan meyasa ba kwason yinshi tace wlh nima ina so mama da baba basa sonshi shiyasa bamufiya yinshi ba tace yauwa yaya wai har yanzu basu ƙara kiranka yace wlh basu kiraba tace to anjima idan ka dawo sai ka ƙara gwada kiran su kaji me ake ciki yace nima tunanin danakeyi kenan bari idan nadawo din sai inkira tace hakan yayi tace bari inbarka kaci inje in ƙarasa wancan dan kai kadai nayiwa yanzu yace to sannan yaci gaba da cin abunshi hankali kwance duk saurin da yakeyi hakan besa shi cin abincin da sauri ba ci yake kamar yanda ya saba,
lokacin da yagama bakwai da rabi daidai sannan yatashi ya ƙara gyara jikin shi sannan ya nufi dakin mama da tun dazu tabar falon yana zuwa yayi sallama ta amsa masa sannan ya shiga daga bakin ƙofa yace mama ni nagama zan wuce tace Allah ya kiyaye hanya ALLAH ya tsare hanya yace amin sannan yajuya ya fita da sauri ya dan leƙa kitchen yace wa Azeema shi ya wuce itama da addu'a tabishi sannan ta rakasa har bakin hanya saida taga ya hau napep sannan ta juya ta koma gida.........
************************
*S.A.S SPATIAL HOSPITAL*
lokacin da ya qaraso gurin ƙarfe takwas saura minti biyar Allah ya soshi be makara ba inda suka saba zama idan sunzo shi da sauran jama'ar wajen basu dade ba kwa sai ga Dr.shettima ya iso wajen suna ganinshi kowa yafara gaida shi yana amsawa sannan aka bude masa office dinshi ya shiga ciki yazauna bayan wasu yan mintina kuma ya bukaci su fara shiga
daya bayan daya suka ringa shiga suna fitowa duk wanda yafito kuma sai ya wuce inda zeyi nashi trainning ahaka har akazo kan saleem da fara'a a fuskar shi ya shiga ciki yana shiga kuma ya tsugunna har ƙasa ya gaida shi,
Da mamaki dr...shettima yace "haba abokina da girman ka zaka tsugunna min ina jinma fa ka girme ni amma ka tsugunna min tashi dan Allah kar wani yazo yaganka ai yama dariya yanzu a wannan zamani ko manyama idan za agaidasu ai ba a tsugunnawa yaƙarasa fada yana yar dariya tare da miƙawa saleem hannu alamun suyi musabaha da farko da ƙin yarda yayi saida yaga dr shettima ya dan yi masa hararar wasa yace kai nifa ba ayimin irin wadannan abubuwan ni kowama nawane inzaka saki jikinka ma kasaki dan atare dani zakayi trainning dinka tun jiya ma na riga nagama da file dinka aiki kawai zamu fara idan nagama sallamar mutane akwai wata patient da za a cire mata appendix dan haka sai ka shirya zaka fara ganin yanda ake farke mutum ko antaba yi agaban ka?
yace a'a yaude zan fara gani, jinjina kai dr shettima yayi sannan yace zaka gani yau kuma atsarin aikina saudaya nake koyawa mutum abu saboda bana san wasa idan akan harkar aikine dan haka na dauke ka dan naga alama kammar bazakayi wasa ba kuma na yaba da kwazonka shiyasa dan haka to be a careful ka maida hankali sosai kayi aiki kar kasa wasa aciki,
Saleem yace in sha Allahu zan maida hankali nagode da shawarar ka, yace ba komai ka dauke ni amatsayin yayan ka duk wani abu da baka ganeba ko ya shige maka duhu kasanar dani karkaji komai ni kuma zanyi maka bayani in Allah ya yarda,
Saleem ba ƙaramin dadi yaji ba yace nagode nagode Allah yabiya maka bukatunka yanda ka min kaima Allah yayi maka yace bakomai ai duk yiwa kaine ring din wayar dr shettima ne ya katse musu hirar su duba screen din wayar yayi dan ganin me kiran nashi SAM naga anyi saving dashi akan screen din wani killer smile yasaki tare da saurin dagawa saboda kar wayar ta katse yana dagawa ya kara wayar akunne yana cewa shegen gari sai yau aka tuna dani kullum sai nakiraka amma dan rashin mutunci baka daga wa kuma baza ka kira ni ba ko?
Shiru akayi daga dayan bangaren jin hakan yasashi cewa kaifa matsalata dakai kenan ka kirani kaqi magana kuma nima