Showing 45001 words to 48000 words out of 136570 words

Chapter 16 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5410

yanda kike so din ba da ke kikeyi min girkin sai yanzu da bukatar ki ta taso ko tace to shikenan karkiyi din danma nace zan taimaka miki wlh sai inta fiyata in rabu dake kuma idan nadawo har yaya bossay yazo baki gama ba to binshi zanyi mubarki ke kadai dan bazan qara kwanan gidan nan ba dadda de bata kulata ba tai ficewar ta dan taga shirmen ta karuwa yake yi kullum bata tsoron gaya mata duk abun da yazo bakinta amma sai ta fita waje kuma bakin yake mutuwa daman ance ido waka rena yace wanda na saba gani tana ganin dadda ta fita kawai sai ta tashi ta dakko bakkon kayan ta ta zazzage ta tafara ware kayan ta da take so tana ware kayan da bata so kayan da ta dauka basufi kala shida ba sai wani sabon hijab dinta da dadda ta siya mata bata wani sashi da yawa ba tsaf ta hada duk wani abu da tasan nata ne kuma zata bukace shi sauran kuma takulle su daban ta ajiye agefe ta ware kayan da zata sa idan bossay yazo masu dan kyau dan kar yan gidan su raina mata hankali dan tasan wasu 'yan gidan masu kudin basu da mutunci saida ta tabbatar kamai is ready ko yanzu yazo sutafi bata da matsala tana gamawa tafito tace dadda dan Allah indan dora ruwan wanka kafin ki dora abun da zaki dafa hararar ta tayi tace ke bafa nason shirme me yake damunkine to wlh kishi ga hankalin ki naga alamar kan ki rawa yake to wlh ki kiyayeni ki fita da ga idona kafin ranki yabaci baki ta turo mata gaba sannan ta koma daki ta qara fito da mayafi a hannun ta dadda tabita da kallo tace gidan ubanwa zaki da farar safiyar nan tace yanzu zan dawo gurin aunty lami zani muyi sallama tana kaiwa nan ta kwasa aguje tafita dan kar dadda ta hanata fita dadda taringa kwala mata kira amma taki tsayawa ta tashi tabiyo ta amma kafin ta fito har ta bace daga qofar gidan komawa tayi ta dakko mayafi itama tabi bayanta tana mita ai wlh bazan barki kishiga gidan nan na fada tana tafiya kamar zata tashi sama har ta qaraso bakin gate din gidan na zuwa ta bubbuga me gadi ya bude ya leko kafin yayi magana ta rigashi tace shiga ciki ka fito min da yarinyar da ta shigo gidan yanzu nan da mamaki baba me gadi yake tambayar ta wace yarinyar shi ba yarinyar da tashigo yanzu tace kamar ya ni zaka renawa hankali yace baba wlh gaskiya nake gaya miki bata zoba tace Ameesha fa nake nufi yace ai nagane wacce kike nema amma wlh bata zo ba da mamaki dadda tace to yarinyar nan ina tayi tace nan zatazo amma shine tayi wani wajen zata zo tasameni wlh sai nayi maganin ta yau zatasan ta rainani dani take zance tana kaiwa nan tayi kwafa tayi gaba tana bambamin bala'i tana wucewa Ameesha dake labe gefen wani gida ta fito tana ta dariya harda kyakyatawa tana bin bayan dadda da gwalo tace ai nasan daman sai kin biyoni shiyasa na buya idan kin koma nashi gidan nasande yanzu baza ki taba dawowa ba dole kijira sai lokacin da naga damar dawowa tana magana ta kwankwasa gidan baba me gadi yazata dadda ce taƙara bugawa ya bude rai abace yace nafa gaya miki wlh yarinyar nan bat....tsayawa yayi da maganar da yakeyi ganin wacce ake neman ce tazo yace ke ina kika je yanzu kakarki tazo ne manki fa dariya ta kuma yi tace rabu da ita baba ai ina kallonku buya nayi yace meyasa to tace wai ita adole bazan qara zuwa gidan nan ba gashi kuma yau zamubar unguwar nan kuma ina so muyi sallama da aunty lami dama sauran 'yan gidan zaro ido yayi yace tashi kuma ina zaku koma tace ni wlh bansan sunan unguwar da zamu koma ba amma de yau zamu tashi yace Allah sarki shikenan yanzu mundena ganinki tace aa wataran idan bossay zezo zan biyo sa sa mugaisa yace to shikenan Allah yasa da gaske kike yafada yana matsa mata tashiga cikin gidan ta qofar brander kitchen tabi tana shiga bata ga kowaba sai ta tsaya tana rarraba ido tana tunanin to kode aunty lamin bata zoba tana tunani kode ta juya ta koma gida kar taje akamata a kitchen din har tajuya danufin fita sai taji anyi gyran murya kasa juyowa tayi saboda bata san dawa zatayi tozali ba har yanzu tana tsaye ita bata tafiba ita bata juyo ba lami dake tsaye abayan ta tana dariya qasa qasa tasan tsorone ya hanata juyowa dan haka sai tasake gyara murya ta kwaikwayi irin muryar matar gidan tace keee da yar tsawa hantar cikin Ameesha ce ta kada tana tunanin shikenan kashinta ya bushe ankamata watakil ma ace mata barauniya tazo sata zuciyar tace ta bata cewa wlh kar ta juya kawai ta kwasa aguje tabar gidan tasande ai baza su taba biyo ta har gida ba inma sunzo dadda zatai maganinsu tana gama ayyana hakan kuwa ta daga qafa zata gudun kawai taji an ruqeta ai kwa saura kadan tasaki fitsari awajen tsabar tsoron da tashiga..........
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#:   💅SARKI SAMEER....💅
             

               🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

27&28

"Tana gama ayyana hakan kuwa ta daga qafa zata gudun kawai taji an ruqeta saura kadan tasaki futsari tsabar tsoron da ta shiga jin anyi shiru ba taji saukar duka ba kuma ba ayi mara komai ba  yasata juyo wa ahankali ganin ko waye tana dagowa kwa idon ta ya sauka akan lami wata mahaukaciyar ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa kai aunty lami wai daman kece duk kikasa nabi na tsora ta dan wlh kinban tsoro sosai lami dake faman boye dariyar ta sai yanzu tasamu damar yi tace ai nasani shiyasa nayi miki haka tace aikwa kin dau alhakina wlh kinsande yanda nake tsoron mu hadu da masu gidan amma kikai min haka harda boye Murya yanda zanfi tsorata ko dariya ta qara yi tace wlh tsoranki yayi yawa tace ai tsoro wajibi ne saida tagama nutsuwa sannan  tace wai ke sai yau kika ga damar dawowa duk kinbar ni da aiki nikade yanzu komai na gidan nan ni nakeyi katseta tayi da cewa Allah sarki har na tausaya miki Allah yakawo miki dauki danni nan dakike ganina ma daga yau baza ki qara ganin qafata agidan nan ba yanzu ma gurinki nazo muyi sallama saboda barin unguwar nan zamuyi tashi zamuyi yau yau dinnan   lami hannu tadaga sama ta dora akai tace nashiga aljanna nayi tsudum tsudum naqi fitowa kuma bazan fito ba 😂yanzu dan Allah dagaske kike ko da wasa tace wlh da gaske nake tace yanzu bazan qara ganin ki ba ko zakirin ga kawo mana ziyara tace a'a wlh bazan zo ba saide ke kizo tace inda zaku kona yana da nisane da zakice bazaki zo ba ba amana wallahi tace wlh ba nisa mukai ba tace wacce unguwar zaku koma Ameesha tace mata nima bansan sunan unguwar  ba da mamaki lami tackalleta tace kamar ya baki sani ba wai tsaya ma me yafaru zaku tashi matsala kuka samune da gidan da kuke zaune ko wani abunne yafaru da har takai ku ga tashi wlh banji dadi ba Ameesha tace wlh lafiya qalau gidan su bossay zamu koma shida maman sane suka ce mukoma can da zama baki tasaki tana kallon ta saida tagama sannan tace ke dan Allah amma wane bossayn kike nufi tace bossay nawa kika sani tace daya ita kuma ta daga mata kai alamar tabbatar wa tafa hannu tayi tace amma na tayaki murna har yanzu nakasa yarda wai gidan su bossay zaku koma da zama amma fa na taya ki murna dan wlh kakar ki ta yanke saka Ameesha ta bude baki zatai magana kenan suka ji andaka musu wata mahaukaciyar tsawa da ta karade gidan gaba daya saboda safiya ce sai da gidan ya bada sauti Rasheeda ce tsaye abakin qofa da ta fito cikin shirinta na zuwa makaran ta saboda yau da wuri zata fita saboda test zasuyi shigowar ta kenan dan ta dan samu wani abun taci kafin ta fita shine kunne ta yajiye mata maganar da tasa zuciyar ta bugawa da qarfi tana shirin fitowa waje kuma ba komai taji azancen nasuba sai maganar lami ta qarshen da tace wlh har yanzu nakasa yarda wai gidan su bossay zaku koma amma nataya ki murna dan wlh kakarki ta yanke saqa  jin an ambaci abun sonta yasata jin faduwar gaba Qarasowa tayi inda suke ta qara daka musu tsawa dacewa wane bossayn naji kuna magana akai Ameesha da har tafara ruwan hawaye tace aunty dan Allah kiyi hakuri wata tsawar taqara buga mata tace dan ubanki hajuri nace kiban ba tambayarki nake ba amsa zakiban  wuqi wuqi ta farayi da ido takasa magana dan bata san ta yanda ma zata fara yi mata bayani ba suna cikin haka sai ga mom tashigo tana tambayar su me yake faruwa dukan su ba wanda yaba ta amsa saida tace daughter  wai neke faruwa duk tunda natshi nake jin muryar ki daga hannu tayi ta na nuna mata Ameesha da yatsa tana cewa mom wannan munafukar yarinyar ce sai kuma tayi shiru tana hararar Ameesha Mom batai mamakin ganin Ameesha ba saboda da dad yagaya mata zata dawo  aiki to amma abun da yadaure mata kai me yasa yarta haka hartake kunfar baki alahalin kuma jiya da kanta tace ita bata damu da dawowar tata ba amma gashi kuma tazo ta tarar dasu to me ya hadasu bata da wanda ze bata amsa
dan haka ya ta maida kallon ta ga lami da ta rakube gefe guda tana tsoron kar  adawo kanta  mom ce tace ke lami me yake faruwa yimin baya ni  cike da tsoro tafara yi mata bayanin duka tattauna war da sukayi ita da Ameesha wata uwar shaqa takaiwa wuyan ta tace dan uban wane bossayn kike nufi bade bossay na ba har yanzu bata ce komai ba saboda shaqar da tai mata mom ce tace wai kin tabbatar da shidin take nufi shi me zesa shi yin hakan qara shaqeta tayi tace baza kigaya min ba sai na halakaki agun nan da kyar ta iya bude bakin ta tace eh shi yaya bossayn ki da qarfi tace what! how dare you mom kinji me tace ko mom tace naji meye abun tada hankali aciki kinsande dad dinki na gida idan kika bari yazo yasame ki ahaka baza kiji da dadi ba kuma zaki gayawa aya zakinta dan haka nide ba ruwana jiki magayi tana gama fadar haka tai ficewar ta daman so take tasamu damar rama abun da tayi mata jiya kuma ta rama dan kwa Rasheeda ba karamin shaqa tayi ba ganin yanda mom din tata ta nuna bata damu da ita ba hasala ta qayi tana kallon Ameesha tace to wlh yau sai kin gaya min alakar ki da shi da har kika samu damar komawa gidan su gaya min shegiya munafuka me kama da 'ya'yan  aljanu fada min ko kuma in kasheki kowa ma ya huta ko kuma maular da kikasaba kikaje gidan su yar matsiyata kawai to wlh baki isaba ba inda zaki fita daga cikin gidan nan dan acikin store zan sakaki in qulle daga nan ki mutu aciki inga uban da ze tsaya miki banza shegiya yar gidan shegiya tana gama fadar haka ta fara kokarin janta Ameesha tayi saurin katse ta cikin shashekar kuka tace nifa wlh aunty da wasa nake mata ba gidan su bossay za mukoma bafa a unguwar sune de gidan dazamu koma shima kuma aikatau zamuje saboda dadda tace bazan qara zuwa aiki nan gidan ba shine nikuma bazan iya zama ba aiki ba shine nafito ko zan samu wani gidan su dauke ni saida naje wajen gida biyar amma bansamu ba ina kan hanyar komawa gida sai na hadu da wata qawata yar makaran tar mu itama aikatau take yi sai nagaya mata tace inzo muje unguwar da take aiki bazan rasaba zan iya samu haka tayi mana kudin mota muka je shine muna zuwa muka tsaya muna tunanin inda zamu fara shiga saiga yaya bossay ya fito yana fitowa na gaida shi yake tambayata me muka zo yi unguwarsu nace ai bansa ma nan unguwar suba sai yanzu daga nande mukai mishi bayanin aiki nake nema sai ya nuna mana wani gida yace mushiga gidan su abokin shine  yaji suna neman me aiki mushiga muce shi ya turo mu mukai mishi godiya ni tunda ga ranar ma ban qara ganin shiba  ba har yau  bayan munshiga gidanne kuma suka ga nayi qarama sukace min ina iyaye na suke nace musu banda su ni da kakata muke zaune shine suka ce inzo da kakar tawa suyi magana da ita danaje gida nagayawa dadd.....bata qarasa ba ta daga mata hannu tace dalla malama yimin shiru sai wani yimin dogon jawabi kike sai kace na tambayeki  tana gama fada ta kama kunnen ta da qarfi taja tace Allah ya taimakeki amma wlh wlh kinji na rantse koda wasa nakama ki da shi na lahira sai yafi ki jin dadi duk wani abu da kikasan zesa ku hada hanya karki bari hakan tafaru kar kiga ba unguwa daya muke ba duk wani motsun ki da zakiyi acikin unguwar za asanar dani dan zansa asaka miki ido a ringa min bincike akanki dan haka ki kiyaye ni nidin nan da kike gani ba kanwar lasa bace duk yanda kike tunani na na wuce haka tana gama fadar haka ta turata gefe tare da ficewa daga kitchen din dan tama manta abun da yakawota kitchen din Ameesha zubewa tayi awajen tana sauke ajiyar zuciya lami dake makale gefe guda taje ta dakko mata gorar ruwa ta kawo mata tana bata kwa ta karba ta bude tunda tadaga bata ajiye ba saida ta shanye tas sannan ta ajiye robar aqasa lami ce ta tsugunna agaban ta tana yi mata sannu kai kawai ta daga mata saida ta dan samu nutsuwa sannan ta mike tace aunty lami saduwar alkhairi lami tace muje in rakaki tare suka fito saida suka dan yi nesa da wajen kitchen lami da abun ya daure mata kai to me yasa tayi mata qarya tace agidan su bossay zata zauna alahalin tasan qarya take yi kasa daurewa de tayi tace wai nikam intambaye ki me yasa kikai min qarya da kikace agidan su zaku zauna yanzu kuma ga abun da kika gaya wa Rasheeda saida Ameesha taja wani lokaci kamar ma baza ta bata amsa ba sai kuma tace duk abun da kikaji nagaya musu qarya nake wanda nagaya miki ne gaskiya lami kasake tayi kamar wata sokuwa tace wai kina nufin duk wannan uban labarin da kika bayar qirqirq kikayi ba gaskiya bane tace mata eh tace gaskiya na jinjina miki zubaida kin iya tsara labari kamar gidan radio Ameesha tace ko kece kika ga ana shirin rabaki da duniya akaiki barzahu sai kinyi irin wacce tafi tawa lami tace rabani ina ni ina iya wannan qaryar ai tayi yawa fada fa kike tayi bawanda zece zancen ki akwai karya aciki Ameesha tace ni dan Allah kibar ni da abun da yake damuna da jikin zanji ko kuma da surutun ki lami tace nidin kuma yau ake gayawa haka lalle manya sunji shaqa bata kulata ba tayi gaba har de suka qaraso bakin gate din sannan sukayi sallama lami ta dawo ciki ita kuma tafita dan ko baba me gadi batayiwa sallama ba ta wuce ta tafi abin ta saida ta fito ta qara fashewa da kuka tana tunani wai ita kam me tayiwa aunty Rasheeda ba da bata sonta kwata kwata bata qaunar ta ta tsaneta arayuwar ta  duk sanda zasu hadu sai taci zalinta ko kuma tayi mata zagin wulakanci da cin mutun ci yanzu yazatayi idan kuma tagane qarya ta shirya mata gashi kuma tace zata sa ayi mata bincike in aka gaya mata ga agidan datake fa yazatayi wata zuciyar ce tace mata sai ki zamanki basai kin fito ba bare ma aganki agaya mata bashike nan ba tana wannan tunanin har  ta qaraso qofar gidan su sai kuma abun da tayiwa dadda ya fado mata ashe fa dadda batace taje ba tafita gashi kuma taje ta jawowa kanta wulakanci Allah yasa de dadda kartayi mata fada sadaf sadaf tayi ta leka cikin gidan sai taga ba kowa dan haka sai tashiga da sallama ciki ciki da inba akusa da ita kake ba baza kataba jin me tace ba tana shiga saiga dadda tafito daga bandaki sai kawai ta tsaya bata shiga dakin da take shirin shiga ba dadda tunda taga fuskar ta tasan tasha kuka dan haka tace daga gidan uban wa kike kasa bata amsa tayi tana wasa da yatsun hannuta dadda tace wai ba magana nake miki ba dagowa tayi zatai magana dadda naganin fuskar ta kawa sai ta fashe da dariya saida tayi me isarta sannan tace Allah yaqara ya qara qarawa wanda beji bari ba ai bayaji hoho ba tana kaiwa nan tayi gaba abunta tana qara yi mata dariya ganin haka yasa Ameesha zaman dirshen agurin   harda bubbuga qafafu aqasa me yasa dadda zatai mata haka me makon ta rarrasheta amma kawai sai takama yi mata dariya haka ta ringa kuka me sauti dadda da tundazu tana jinta bata kulata ba sai yanzu da kukan ya isheta tafito Ameesha baji fitowar dadda ba kawai sai jin saukar doruna tayi agadan bayan ta aikwa wata mahaikaciyar qara tasaki da kwanciya agun tana burgima dadda sake dagawa tayi ta qara tsula mata bulalar tana cewa uban wani ya aikeki saida nace karkije kidawo amma kika ki da na biki abayama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login