Showing 12001 words to 15000 words out of 136570 words

Chapter 5 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5445

ba, a hassale tace mishi yar aikin gidan mufa nake nufi Khadija.

"Ohhh wai baby meesha kike nufi ai sai yanzu nagane ni nama manta munhaɗu yau daman nazo ne zan.....

Beƙara sa zance da yake yiba da qarfi tace "What!!? menaji ka kirata dashi?
shiko saida ya janye wayar da ga kunnen sa yagama dariyarsa ganin yanda tai magana da ƙarfi kuma daman dagangan yai hakan yasan hakan zata faru dan yasan kwata-kwata bata son yarinyar shiya sa yayi mata haka yana gamawa ya mayar da wayar kunne, yace.... "Hello..hello..hello baby wai mekike cewa bafa najinki, tace "Nima ai bana jinka ɗazu amma yanzu ina jinka yace nima haka wataƙil network ne yadauke shiyasa,

"Eh, wataƙil" Daman haka nace me naji kakira sunan yarinyar nan dashi ɗazu? Sake maimai ta mata yayi yace "baby meesha yaƙara faɗa mata batare dajin komai ba,

"Mekake nufi kenan da hakan?

yace "Duk yanda ranki yaraya miki,

Wani ƙaton abu taji yazo mata wuya ya tsaya da ƙyar ta iya cewa "haka ma zakace min? yace..

"To da me kike so in gaya miki kings nifa wallahi bana son wannan ƙorafe ƙorafen naki ke kullum baza ai hirar arziƙi da keba sai kin ce ke kaza ke kaza bana miki kaza wace uwa wace arziƙi to wlh nagaji da jinsu yakamata ki nutsu kisan inda yake miki ciwo da bazan juri irin waɗannan abubuwan naki ba, yana cikin maganar kawai yaji ta sakar mishi kuka, aikwa atake yayi tsaki kawai ya kashe wayar sa.

Tana jinsa haka taƙara fashewa da wani kukan me cin rai tana ayyana abun da zatayiwa yarinyar nan dan a ganinta duk ita taja mata yazo yana yi mata wannan faɗan, sosai taci kukanta ta gaji tayi shiru tana ƙara saƙe saƙen abubuwan da zata yiwa ƴar iskar can gobe, tana kwance tana tunane tunane da guntun hawaye a idon ta a haka har bacci ɓarawo ya sulalo yazo ya ɗauke ta..........
       

*In sha Allah daga yanzu ƙarfe takwas 8:00 daidai na dare zan ringa posting kullum*

sannan kuma indai kuna comment acikin ranar dai indai na samu enough time zaku iya ganin ƙarin wani ako da yaushe*

_Don't forget Pls comment, likes and share_

*My WhatsApp number 08124226526, Pls banda kira*
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#:    💅SARKI SAMEER....💅
                         By
                ❤xeemat..love❤

         🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Edited 🤗😎

                        7&8

*Ameesha*

   Tun wajen ƙarfe 7 nasafe ta tashi ta fara shirwa wajen 7:30 tagama komai ko abinci bata tsaya taci ba ta cewa Dadda idan tadawo taci tai mata sallama ta fita tana tafiya tana karanta
( Allahumma lasahala illa maja'altahu sahala wa'anta taj'alal hazna iza shita sahala)

Da kuma duk addu'ar da tazo bakin ta harta ƙarasa bakin gate ɗin gidan ta buga.

Me gadi ne yazo ya buɗe mata tare da leƙowa, beyima magana ba, tace "Baba barka da safiya ina kwana? Da fara'a ɗaule a fuskar shi ya amsa mata da "lfy ƙalau KHADIJATU. shi haka yake kiranta saboda shine sunan ta na gaskiya,

"Harkin ƙaraso kenan..

Tace "eh, wlh Baba har ma naso in ɗan makara tafaɗa tanasa kai cikin gidan, yamatsa mata tawuce tana ce mishi sai anjima, yace "Allah ya kaimu, a fito lafiya, tace "ameen, sannan ta wuce.

Gudan kar su haɗu da mutanan gidan yasa tabi ta barandar tashiga kitchen da sallamarta lami dake tsaye gaban gas tana preparing ɗin breakfast tajuyo ta amsa mata tana cewa "Hajiya Ameesha sai yanzu, kuma jiya dana dawo bangan ki ba ina kikaje  ina tajiranki baki dawo ba dan sai wajen magriba natafi daga gidannan amma shiru, me yahanaki dawowa ince da lfy ko?

Ƙarasa shiga tai, saida ta ƙaraso inda take, sannan tace "lfy amma ƙalau ba.

Da mamaki Lami take kallon ta tare da cewa "Subhanallahi me yafaru kikace haka? tace kedai bari kawai zan baki labari sai munsamu loƙaci mun zauna yanzu kinga banshigo da wuri ba,

"To shikenan kishiga kifara naki aikin danni harna kusa kammala karin kumallon ba abun dazaki tayani,

"Ok shikenan ta faɗa tanayin gaba dake kullum tana riga Lamin zuwa idan tazo tafara yin nata sai suyi abinci tare tana ɗan tai maka mata da wasu abubuwan saboda bazasu bata girki ba ita kaiɗai tayi yarinta dayawa gashi kuma tana zuwa school shiyasa suka ƙara dame yi musu girki ita kuma tayi share share da goge goge da wankin toilets to tana gamawa sai ta tsaya suyi girkin tare saboda tanason girki arayuwarta komai taga ta dafa sai tayi ƙoƙarin taga ta iyashi zuwa yanzu kwa saidai muce Masha Allah dan ba kallar abuncin da bata iya ba saboda Lami ta gwana ce gurin iya girki.

Har zata fita daga kitchen ɗin sai kuma tadawo da sauri tace "Aunty Lami ina fatan de masu gidan nan basu tashi ba ko dan wlh banaso muhaɗu har inbar gidan nan, "da ɗan rashin fahimta Lami take cewa bangane ba me kikayi da bakyason ku haɗu sai kace yau kika fara aiki" tace ai labarin dazan baki kenan wlh laifi nayi musu jiya"

tace "ke daman ai bakya gajiya dayi musu laifi kullumma cikin laifi kike" tace "kai ai najiya yafi na kullumma dan saida suka lakaɗamin jiki son ransu" tace "tabb kina ruwa kam kishiga kifara kar ki ƙarawa kanki laifi kuma da kike cewa baza ku haɗu ba har kitafi yazaki da gyaran bedrooms ɗinsu da kuma wankin banɗakunan zaro ido tayi tare da ɗora hannunta akai tace nashiga aljanna nayi tsudum tsudum yazanyi dan Allah, danni wlh nama manta dahakan, tace "keki sani kuma kitsaya kita zuba anan harsu sufito suga baki komai ba, kinga sai suƙara maimaita miki abun da suka yimiki jiyan......

Tunkan takai ƙarshen maganar ta da sauri tayi gaba tana faɗin Allah yaƙara kiyayeni dan bana fatan hakan tasake faruwa tana tafiya tana magana har ta ƙarasa cikin falon cikin sauri-sauri tafara gyarawa aɗan ƙan ƙanin loƙaci tagama duk abun daya kamata tayi tana tunanin yanda kuma zata haura upstair ɗin dan tafiso ma sai sunfito waje yin breakfast sai ta salallaɓa taje ta gyara musu tai sauri ta fita batare da sungan taba tana cikin wannan tunanni kawai taji takun takalmi alamun za asauko ƙasa sai tai sauri tashi ge kitchen tana shiga suaki karo da Lami saura ƙiris ta bugeta kayan hannun ta su zub,

Da sauri tamatsa tana cewa "dan Allah aunty Lami yi hakuri wlh ban luraba ne" tace "bawani nan wai ke baza ki nutsu ba sai wani zagaye zagaye kike sai kace wani ne yace kiyi laifin wuce mu koma cikin falon, marairaicewa tayi tace "Dan Allah kibarni inshiga tafiya fa naji alamun wani daga cikinsu zai sauko, tace "sai kuma me dalla wuce muje ungo wannan ruƙemin mukai dinning mujera kan suƙarasa fitowa badan taso ba dan bataso taringa yawan yi mata musu dan haka kawai sai tasa hannu takarɓa tabita abaya suna ƙarasawa suka ga Mom ɗin agurin harta rigasu zuwa tana mamakin meyasa basu jere abincin da wuri ba gashi da wata irin yunwa ta tashi daman tasaba bata wasa da cikin ta shiyasa kullum hawa take kamar anasawa fulawa yis,

Gaban ta sai faɗuwa yake tunda ta hango ta agun ahankli take tafiya kamar munafuka Lami ce ta ajiye na hannuta tanacewa "Hajiya barka da safiya dafatan kin tashi lfy.

Bata jira amsar taba dan tasan daman ba lalle ta amsa mata ba saboda tsabar wulakanci da rashin sanin darajar ɗan adam irin nata sannan tace "Hajiya ina neman afuwa aga farceni rashin gammawa da wuri wlh yar matsala aka samu, "bata kulata ba har saida tagama maganarta, sannan tace mata "Dalla malama rufemin wannan banzan bakin naki kizuba min abinci bayan ɓatan loƙacin dakikai kuma kinzo kina cikani da surutu,

Da sauri ta buɗe tafara zuba mata abun da tadafa sai loƙacin ta lura da bataga flacks ɗin tea ba, juyawa tayi tana kallon Ameesha da ta rakuɓe abayanta tace "bani to tafaɗa tana mika mata hannu, ita kuma tabata tanshirin juyawa, Lami tace "baki iya gaisuwa bane kin wani tsaya sai kace munafuka,

Ameesha runtse ido tayi jin abun da Lami ɗin take mata sai kace bata San halin da take ciki ba meyasa zatai mata wannan tonan siririn ba, saida tagama karanto addu'a acikin ranta sannan ta ɗaga ƙafa da ƙyar taƙarasa gaban yar sukuta, ta tsugunna tace Mom ina wuni itade baza tadena cemata Mom ba dan a ganinta ai tahaifeta tunda ta ajiye manyan 'ya'ya kuma harga Allah gani take intace mata aunty kamar tayi rashin kunya, sannan taƙara da cewa "Dan Allah kiyi haƙuri wlh bazan ƙaraba ta ƙarasa faɗa idon ta na ciccikowa da ƙwalla kawai jira take taji shaƙa amma sai taji shiru kamarma ba mutum agurin ahankali ta ɗaugo ta saci kallon ta taga abuncita take tafama ci kamar ma batasan da zanmata agun ba haka tai ta zama har ta kammala cin abinta ta miƙe zatabar gurin Ameesha taƙa ra cewa kinj Mom dan Allah kiyi hakuri wlh b....

bata ƙasara ba takatse ta da cewa "idan kika ƙara min magana wlh sai na canza miki kamanni agunnan sha sha sha kawai tafaɗa tana barin gurin wani irin mamakine ya rufeta da taga batai mata komai ba ɗoguwar ajiyar zuciya tasauke harda dafe ƙirjinta sannan tamiƙe tana maƙe kafaɗa irin I don't care ɗinnan tunda de ba abun da tai mata ai da sauƙi sai taje tai tayin kunbure kunburen ta ita ba damuwarta bace damuwarta ɗaya shine ace za a taɓa lafiyar jinkin ta shine zata damu tana shiga ta rungume lami ta baya tana cewa "kinga ba abun da taimin.

Lami tace "Allah ya taimake ki, kin tsallake rijiya da baya" tace "wlh kuwa Allah yasade ta haƙura kenan. Tace mata ameen sannan suka cigaba da aikin gabansu.

Rasheeda da tana ɗaki takasa fitowa saboda kukan da tasha jiya yanzu kuma sai ta tashi da ciwon kai dalilin da yahanata fitowa da wuri  kenan da kyar ta iya tashi taje tayi wanka tashirya cikin dogurar riga blue ta ɗaure kanta da mayafinta ta fito saboda yanzu ta ɗanji sauƙi kan nata yadena yimata ciwo saide bata jin daɗin jikin sosai ɗakin Mom ɗin tata tafara shiga ta tarar da ita tana waya.

Tana ganin ƴar tata  tacewa wanda suke wayar "to shikenan sai kajini sannan ta kashe wayar tana kallon ƴarta ta, sannan tace daughter kin tashi lafiya? sai yanzu kika tashi?

bata amsa mata duka tambayoyin datake mata ba taƙarasa ta zauna akusa da ita tare da ɗora kanta akan kafaɗar tace kawai sai tafashe mata da kukan shagwaɓa, hankali tashe ta ɗago ta daga kan kafarɗar ta tana ruƙe fuskarta tace me kuma yafaru waya taɓa min ke wayajawa kansa bala'i kina dani kike barin damuwa tayi tasiri aranki tafaɗa tana goge mata hawayen ta sannan taƙara rungumeta tana bubuga bayanta sai da tabari kukan nata ya lafa sannan ta ɗago ta tace shalelena gaya min wanda ya ɓata miki rai yanzu muhaura gadon mahaukaciya dashi da sanyin sa safiyar nan zai saka min ke zubar da hawaye takarasa maganar tana tsasttsareta da ido tace kenake saurare!

Cikin shashsheƙar kukan da ta gama tace "Mom wlh Allah akori yarinyar can tabar gidan nan wlh na tsaneta so take ta rabani da babyna" cike da rashin fahimtar inda maganar tata ta dosa tace wai me kike maganane akai? Jiya ba mungama mgana ba gaba ɗaya me kuma ya ƙara dawo da maganar bayan ta wuce,

Cikin jin haushin abun da Bossay yayi mata a daren jiya tafara korawa uwar tata yanda sukai dashi jiya, sai tace da ita "to kuma shine kike wannan damuwar haka ni ai banga wani abun tada hankali awannan maganr ba gaba ɗaya, kinsande ko giyar wake yake sha be isa yafasa aurenki ba kuma muddin ya aure ki, shida kuma auren wata macen saide alahira idan anayi, kuma bama wannan ba ki tuna asalin yarinyar nanfa bata da asali bata da gata bata da galihu ina zatai wata daraja a idonshi barema har yayi tunanin sonta kuma uwarsama baza ta taɓa yarda ba ya auro mata yar talakawa marar asali ba,

Turo mata baki tayi tace "Mom wallahi bakiga a yanda nagansu bane jiya kuma haka mafa yake ce mata wai  baby meesha in basonta yake ba meyasa zena kiranta da hakan?

Mom ta ɗan yi murmushi tana jinjina wannan rigimar ta ɗiyarta, cikin sigar rarrashi da kwantar da hankali tace "kika sani ko dan yaga tayi mishi yarinta ne shiyasa yake cemata haka kinsan wasu idan suka ga ƴar ƙaramar yarin ya suna iya kiranta da baby,

Ƙara turo baki tayi tace "Nima fa baby yake cemin, nufinki nima nayi yarinya da yawa kenan,

Mom tace "A'a ni ban faɗi haka ba, wasu suna iya faɗa wannan ai na soyayya ne ba yanzu naji kema kina cemishi babyn ba kinga shima dole yace miki haka tunda babynce agurinshi gashi kuma yakawo kuɗin auren ki (hmm Allah yakyauta wai uwace take cewa yar ta haka Tabb bakamar Muba kayi zancen sauryi ma agabansu  acima uwa wlh)

"Dan haka kikwantar da hankalinki kawai kinji shalelena babu wani abu a tsakanin su, "kai ta gyaɗa mata Kawai"
Ita kuma taciga ba cewa yanzu kitashi muje kiyi breakfast nasan kinajin yunwa batai mata musu ba ta miƙe suka fita tare amma duk dahaka bataji zata iya barin yarinyar nan ba  hakan nan batare da ta ɗauki ƙwaƙƙwaron mataki ba dan wlh ta tsaneta har cikin ranta take jin tsanarta suna fitowa suka nufi kan dinning taja mata kujera tazauna da kanta tayi serving ɗinta tazauna akusa da ita tana kallon ta har takammala sannan suka dawo falo ta zauna ita kuma Mom tace Mata bari tashiga daga ciki tafito, "Kai ta ɗaga mata kawai ita kuma tawuce sama wayarta ta ɗauka ta fara daddannawa tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya,

Ameesha data gama bawa Lami labarin abun da yafaru jiya cike da tausaya mata tace Allah sarki gaskiya kinji jiki sannufa, tace "hmm jin jiki ai ba kaɗan ba, amma ni tunda yau basuyi mini komai ba ma da sauƙi,
tace "aikam de kinga kitashi kije kar ki fusatata tayo kanki tunda daman haushinki take ji, miƙewa tayi tare da cewa "Wallahi kam bare inje ingyaro bedrooms ɗin inzo intafi gida dan wlh wani bikin yayar ƙawarmu akeyi inje inshiraya dawuri kar loƙaci ya ƙure min gashi sai naje gurin telama na karɓo ankona, tana gama maganar kuma bata jira cewar taba tafice.....

Tana dab daza ta haura upstairs ɗin taji ance "Keee..! zonan ita kwakwata ma bata lura da ita ba cike da zulumin me kuma zatai mata tajuyo tadawo gaban ta kai ƙasa tare da cewa "Aunty gani ina kwana?

Bata amsa mata ba kawai sai ji tayi ta kamo kunnnan ta da ƙarfi tancewa ke marar kunya ko? marar mutunci kirasa da wanda zaki tsaya kina wa dariya sai babyna to inaso inga ya miki cewa yafi ƙarfin ki nesa ba kusaba hanyar jirgi daban ta mota daban ki fita daga har karsa, ba sa'anki bane yatara komai ya fiki ta ko ina kama daga da komai kin san da hakan, ɗan dakatawa tayi tana ƙara murɗe mata kunne kamar zata cire mata shi, sannan ta ci gaba da cewa....

"Kyau,Gayu,Dukiya,asali,Arzuƙi,ilimi babu abun da yarasa ke koma gaya min me kike dashi waye ubanki marar asali yar tsintuwa kawai waya sanima ko uwarki ayawan ta zubar tasameki ayawan gantalinta nabin maza dan da alama baki kama da 'ya'yan sunna ba daga ganin ki kinfi kama da 'ya'yan shegu tasakar mata kunne tana karasawa da cewa ƴar titi kawai yar bakin kasuwa shegiya ƴar shegiya ke shegiya uwarki ma shegiy......

bata ƙarasa faɗar abun da tai niya ba sakamakon jin wani haɗaɗɗun maruka har biyu akan kyakkyawar fuskarta da saida taga star, tare da ɗaukewar ji da gani na wucin gadi, kafin ta dawo hayyacin ta, dafe fuskar ta tayi tare da ɗagowa dan tabbabtar da abun dataji da gaske ne ko kuma mafarki take in da gaske ne wane mahalukin ne yau yajawo kansa ruwan dafa kan sa........
 

    *Karku bari a baku labarin wannan littafin me salo iri iri daban daban kubiyoni domin jin yanda wasan ze fara meyeke wakana acikin masarautar sarki sameer kuma waye ya zabgawa RASHEEDA maruka? kuma da gaskene AMEESHA ƴar shegiya ce kamar yanda Rasheeda ta faɗa? kuci gaba da bibiya ta, muje zuwa amsar ku na nan gaba.......*


Don't forget pls comment, likes and share

My WhatsApp number is 08124226526
Pls banda kira 
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#:   💅SARKI SAMEER.....💅
            By
Yaya Azeema 😎

            🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
       
No Edit🥵

11&12

Cikin tsanani mamaki da yagama cika zuciyarsa wata kon Rasheeda da kuma hajiya sadaiya ita tana tuna nin me hadawo da mijinta a irin wannan lokacin da safe kuma ma be sanar da ita kwasam sai ganinshi sukayi itama Rasheeda na tuna nin me yadawo da abbanta yau bata saniba kode mom daman  tasan da dawarta sa amma  bata gaya mataba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login