Showing 24001 words to 27000 words out of 136570 words

Chapter 9 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5406

wajen yi mishi addu'a yanzu ma mama na zaune akan sallaya tana azkar kamar yanda ta saba kullum idan tayi sallar asuba sai tayi azkar da karatun qur'ani da addu'o'i bata tashi daga wajen sai wajen qarfe takwas zuwa da rabi sannan take tashi yauma hakance ta kasance tana zaune tanayi Saleem ya shigo cikin shirinsa yazo ya tsugunna cikin ladabi yagaisar da mahaifiyar tasa ta amsa masa ita cike da kulawa tace har ka shirya yace mata eh tace to Allah ubangiji yabaka sa'a ALLAH yasa adace yace Ameen ya mike tare da cewa bari intafi mama kar in makara sunce bakwai tayi min acan tace to shikenan sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya kadan ci wani abunne ko ahaka zaka fita yace a'a Azeema ai tun da asuba ta hada min tea da wainar fulawa tace to shikenan sai ka dawo ka kula de banda shiga abun da ba ruwanka yace to mama yafada tare da fita daga dakin tabi bayansa da kallo tana qara yi mishi addu'ar samun nasara akan aikin da zeje nema yana fita ya hadu da Azeema a falo tana qoqarin shigowa dakin sai ta tsaya suka qara gaisawa itama tai mishi addu'a da adawo lfy yace Allah yasa sannan yayi hanyar fita itakuma taqarasa shiga cikin dakin itama ta gaidar da maman tata sannan ta samu gefen gadon ta tazauna tana jiranta ta qarasa suyi magana tana zaune har bata fita ba har saida tagama sannan ta tashi ta nade sallayar ta ajiye ama zauninta sannan tadawo bakin gadon tace to Azmee gaya min nasan da magana abakinki ko tunda naga kina tajirana zama ta gyara tace kai mama wai dan Allah baza kidena gaya min wannan sunan ba suna na me dadi amma kina bata min(aikam de gaya mata takwarata sunan mu akwai dadi kunsan unique ne ba ako ina akesamu ba kuma ba koya yake cin sunan ba sai wanda yakai karfa kuce nayi san kai gaskiya kawai nafada👌),dan murmushi mama tayi tace ta ina sunan na yake da dadi nikam da asakamin  Azeema gwarama adinga ce min Azmee dan yafi dadi tace wlh mama kema kinsan san da dadi da ba dadi ai da baza kiyarda a rada min ba tace waya gaya miki ai bani nakeso ba babankune yakeso bani ba nikuma kinsan dole inyi duk abun da yakeso taqarasa fadi yayin da taji jikinta duk yayi sanyi itama Azeeman jikinta ne yayi sanyi tace Allah sarki babana Allah yabayyana mana shi aduk inda yake Allah ya kareshi mama tace Ameen duk jikin sai ya mutu gaba daya Azeema ce tai qarfin cewa yauwa mama daman maganar da nake so muyi shine ina so anjima inje gidan su Ameesha sai ta rakani gidan da take aiki sai muroqesu akan suyi mana cigayr baba agidan radio saboda Ameesha ta taba gaya min babban yaron gidan MD ne agidan radio kinga sai mugayawa maman sa ko qaninsa musbahu dan naji yafisu mutunci sai suyi mana hanya zuwa kai rahoton wajensa ko Allah zesa adace asamu labrin sa awani wajen ko  yakikace saida tadan yi jimm sannan tace kina ganin ba matsala kuma zasuyi mana batare da sun bukaci kudi masu yawa ba tace eh to wannanne de wlh bansani ba sai mu tambayesu sai muji ya tsarin yake kinga inzamu iya sai muyi  ko mu jarraba tace to shikenan Allah yakaimu jimawar sai ki kwada zuwa din kijiyo mana Allah yasa zasyi mana danni ina tsoron mutanan nan nake tunda kiban labarin abun da suke yiwa qawar taki tunda basu da mutunci tace in Allah ya yarda ma ba abun daze faru mama kawai muyi addu'ar samun nasara tace to shikenan Allah yashige mana gaba tace Ameen daga nan suka ci gaba da tattaunawar su bayan sungama kuma suka fito falo sukayi breakfasts dake lokaci ya qure basu fito da wuri ba har rana ta fito sosai dan haka kawai suka dora abincin rana saida suka gama tare sannan Azeema tashiga dakinta tafada bandaki tayi sauri tayi wanka tafito ta shiraya shaf shaf  tafito tace wa mama zata tafi mama tace wai har kin shirya kibari mana ayi sallar la'asar sai kitafi yanzu awannan ranar zaki fita tace mama wlh bazan iya jira ba yanzu ma jinake kamar nayi tsuntsu ingani a gidan tafa da tana qara gyara mayafin jikin ta mama tace to abinci fa shima baza kici ba tace wlh aqoshe nake bana jin yunwa kinga bamu dade da cin abinci ba  tace to shikenan sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya kice ina gaisar min da dadda tace zataji tana fadar haka tanufi hanyar fita tafi daga gidan  tana fita tafara sauri kamar kamar zata tashi sama kawai so take ta ganta agidan bata fi 20 minutes ba taqarasa gidan su Ameesha da sallama tashiga dadda ce da take bakin qofar da qaramin gurin da suke girki ta amsa mata sallamar tata da fara'a afuskarta taqarsa inda take ta tsugunna  tace dadda ina wuni dadda tace lafiya qalau Azeema ya gida ya mamanki tace tana nan qalau tace ma ingaishe ki tace ina amsawa kishiga tana ciki daman nagaji da ita sai faman rigima take min taqi ta saurareni kije ko zata saurare ki ke tana yar dariya tamike tace to dadda bari inje Ameesha kenan bata gajiya da rigima sai kace yarinya yar qarama tana fada tana tafiya har ta qarasa bakin dakin tayi sallama amma bataji an amsaba dan haka kawai sai tasa kai tashiga ciki tana shiga taganta kwance kan katifar dakin  ta rufe ido kallo daya tai mata tagane baccin qarya take sai ta qarasa gabanta tace dalla malama kitashi ko kuma in dala miki duka irin wanda kikai min ranar nan ai da sauri ta tashi zaune tace wlh kwa da sai na rama tace wlh baki isaba ni da kikaimin kinbarni na rama ne saikece zakice sai kin rama tace eh wlh kinsan ai in akai min abu bana yafiya saina rama tace karkiyi din yauwa dadda tace wai sai rigima kike mata me yafaru ne shiru tayi lokaci guda kuma idon ta ya cicciko da kwala tana shirin yin kuka tace kinga malama ni ba kuka nace kimin ba ki gaya min me yafaru baki ta turo gaba tace to  malama kema infada zaki min kitashi kitafiyar ki kawai tace yi hakuri ni ba fada nake miki ba inajin ki meye saida ta share kwalar da ta zubo mata sannan tafara cemata ba dadda bace ta hanani komawa gidan su Bossay taci mishi mutun ci gashi yatafi yabarni yace ze dawo amma yau wajen kwana uku bashi ba me kama dashi kullum awaje nake yini ina jiran zuwan shi amma shiru gashi kuma nibasan unguwarsu ba bare gidan su kasaqe Azeema tayi tana sauraron zancen ta da bata san inda ya dosaba tace ke nifa kinsani adahu bansan me kike nufi ba ki min bayani yanda zan fahimta mana gyara zama Ameesha tayi sannan tafara yi mata bayanin tun washe garin da ta baro gidansu dazuwan ta gidan su Rasheeda  da yanda mom ta nuna mata da irin zagin da Rasheeda tai mata zuwa marin dadda tai mata da fitowarsu da  haduwar ta da Bossay gaba daya de ta kwashe komai ta gaya mata harzuwa  lokacin da yace mata ze dawo Ashe qarya yake kuma tun ranar taqi kula dadda, dadda tun tana masifar har ta dawo lallashin ta amma taqi kalata dadda kwa ta tattarata ta rabuda da ita tace inta gaji dan kanta tasakko daga fushin da take dan ita de baza ta canza maganar ta ba kuma bawanda ya isa yasata ta yarda  saida tagama bata labarin komai sannan tace tabb babbar matsala kenan ana wata ga wata yanzu kina nufin kindena zuwa gidan su Rasheeda aiki kenan tace eh mana haka de dadda tace amma nibanji hakan zata kasance dan bazan iya hakura ba shiru Azeema tayi tana tunanin yanzu yazatyi da maganar da ta kawota Ameesha ce ta katse mata tunanin ta dacewa besty yade me kike tunani haka ina ta magana bakijina numfashi ta sauke sannan tace hmm  besty bakisan meke faruwa ba ko wlh muna cikin matsala sosai dan yanzu ma abun da yakawoni gurinki kenan kitaima kamin muje gidan aikin naki inroqesu kan suyi mana cigiyar baban mu wlh mun rasa inda yake yau kwana uku kenan amma ba aganshiba be da dawo gida ba kuma har yanzu cikin tashin hankali harda tashi tsaye Ameesha tayi tace  nashiga uku besty kina nufin kice min wai mahaifin kine ya bata me yafaru dashi tafiya yayi ne ko kuma wani waje yaje me nisa kunje police station konkai reporte duk tabi ta rikice sai faman jera mata tambayoyi take Azeema ce tace wlh munkai amma dasuka karbi Case din basu wani dade ba suka sallame mu akan sunyi iya qoqarin su amma basu samu labarin saba dan haka kawai suyi hakuri Allah yabayyanar mana dashi haka muka dawo gida taqarasa fatada murya asanyaye Ameesha tace innalillahi wa inna ilaihi raji un yanzu ya za ayi besty taso muje gidan kawai tafada tana dakko hijabinta tasaka tace besty taso muje tace to amma kina ganin zasu saurare mune tunda kinga yanzu bakya aiki a gidan su kar suyi mana wulakanci tace karki damu zo muje kawai nasan ta inda zamubi bazan bari sugan ma ba zanyiwa auty lami magana sai ta hada mu da yaya musbahu nasan shikadai ne ze saurare mu tace to shikenan muje atare suka fito dadda da haryanzu tana gun tana ta faman yimusu abinci rana taga fitowar su tace ina kuma zaku har Azeema tabudi baki zata gaya mata inda zasu Ameesha tai saurin cewa yanzu zamu dawo gidan wata class mate dinmu da bata da lafiya tace to shikenan sai kun dawo Allah yabata lafiya suka amsa da Ameen suka suna fita Azeema takalli Ameesha tace besty meyasa kikai wa dadda qarya tace inba haka naimata ba kinsan halin dadda nayarda zatai inje ba tace kumafa hakane aikam da kin barni da tuni nafadi gaskiya najawowa kaina yar qaramar dariya Ameesha tayi tace aikamde dadda ai sai addu'a bazata canza ba suna tafiya suna hira su..........
Dadda kwa suna fita itama daman tagama abincin tashiga daki ta dakko mayafinta tace lalle yaran nan wai har ni zasuyiwa wayo bari inbisu inga inda zasu dan banyarda dasuba tana ta sunbatun ta ita kadai tafito tabisu abaya................🙆
  

don't forget pls comment and share it
My WhatsApp number 08124226526
Pls banda kira
*******************************
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER....💅
             By
Yaya Azeema 😎

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


*Allah ubangiji yakaremu daga mugunji mugun gani tsautsayi da asara fatara talauci annuba Allah yakare mu daga sharrin mahassada da masharranta  duk wanda ba alkhairi bane agare mu Allah ya nesanta mu dashi Ameen..........*

             

No Edit🥵

18&19


              ************************
                          *BOSSAY*

Kwance yake akan makeken gadonsa ya qurawa silin ido yana tunani  wata kyakkyawar yarinya ta shigo dakin da gudu sallama babu kan bed din kawai tadosa tafada kansa tana dariya adan zabure ya tashi tare da ruqota yace ke wai meyasa bakyajin magana bana hanaki yimin irin wannan abun ba kishigo min daki da gudu ko sallama babu fuska yarinyar tadan bata tare da turo baki tace yi hakuri nadena ta fada tana qoqarin tashi daga kansa tafita ya riqe ta yace tuba nake my lovely sister yar autar Ammi niban miki fada dan kiji haushi ba qarewa ma bansan namiki ba tace nide kasake ne itafi bazan qara dawo wa ba daman Ammi ce tace kazo muyi dinner yace muje yana fada yasakko da ita shima ya sakko yariqe hannun ta suka fito tana tafaman ciccijewa ita wai sai yasakar mata hannu shikuma yaqi ahaka suka qaraso cikin falon inda yaga dukkan ilahiran mutanen gidan sun hallara wasu ma har sun fara cin nasu abincin suma kujera yaja musu yazauna ita kuma ya dorata akan cinyarshi tare dace wa Ammi barka da dare tace yau ta maida hankalin ta kan abincin da take ci yaran wajen ma duk gaisar dashi sukayi ya amsa musu ba yabo ba fallasa sai ya maida kallon sa ga wani dan saurayi da kana ganin shi kasan qanini shi ne saboda tsananin kamar dasukeyi yace FARUQ gobe idan Allah yakaimu katashi da wuri ka shirya zamu fita yace to yaya Allah ya kaimu din kai kawai yadaga masa sannan yamaida kansa gurin yarinyar da take kanshi yace mimi sauka kije kici abin ciki kinji to tace mishi tare da sauka daga kansa takoma kusa da Ammin ta da tasaba zama ta zauna ta dau spoon ta fara ci dayake daman tun kanta tafi kirawo shi akazuba mata,wata budurwace ta tashi ta matso kusa dashi tace yayana me za azuba maka taji yayi shiru ta qara maimaitawa duk da haka be kulata ba saida Ammi tace wai ba magana akeyiwa *ALIYU* ba (dan Allah adan min uzuri nayi mantuwa inba ku manta ba abaya nace muku sunan shi SALEEM namanta kuma yayan Azeema ne saleem ba Bossay shi asanlin sunan shi kenan ALIYU Aimin afuwa kunsan dan adam ajizine ngd)
sai lokacin ne yace tea kawai nake so yafada tare da hade rai dan arayuwar shi inda wace yatsana bata wuce itaba ba yaso ta ringa shiga harkarsa Ammi ce tace bangane tea kawai zaka sha wai me yake damun kane kwana biyu na lura da kai  kwata kwata baka cin abinci sosai sannan kadena zaman falo kullum kana daki yace Ammi bafa komai tace to naji yanzu ke FURAIRAH zuba mishi koma meye kuma kafin ingama kayi sauri kagama cinyewa zamuyi magana yace nifa Allah Ammi naqoshi tace wlh ranka ze baci agunnan tunda ni sa'ar wasan kace ina magana kanayi min taurin kai ko kaci gaba kar kafasa yace Ammi kiyi hakuri dan Allah idan ranki yabaci banza tayi mishi ganin haka shima be qara cewa komai ba yaja bakin shi yayi shiru har furaira ta zuba masa jalouf din shinkafa da taji kayan hadi tana daukar ido ga wani uban qamshi da takeyi ta dora masa pape checking akai sannan ta  tara masa gaban sa ba yarda ya iya haka yadauki spoon yafara turawa kamar mecin magani AYSHA ce tafara tashi tare da cewa Ammi saida safe zanje inkwanta Ammi tace tun yanzu tace eh wlh bacci nake ji gashi kuma gobe da wuri zan fita dan  8 nake da lecture tace shikenan Allah ya tashemo lafiya tace Ameen sannan ta wuce  dakin su bayan tafiyarta ne bada dadewa ba Bossay yace wa Ammi yagama tace to yajirata a falo dasauri kwa yatashi yabar gun daman jinsa yake kamar aka qaya bayaso yaga sun tsaya inuwa daya da furairah kan kujera yazauna yayi zaman sa tare da ciro wayar sa yafara daddannawa yana tafiya kwa itama furaira ta miqe daman danshi take zaune agun itama saida safe tayiwa Ammi ta wuce saida tafara zuwa falon taje kusa da Bossay tace ya ALIYU saida safe ko inda take be kalla ba bare tasa ran ze amsa mata inda sabo ta daman tasaba dan haka abun baya damunta murmushi kawai tayi ta wuce saida yaji tafiyar ta sannan yadago yabita da wata muguwar harara yace banza marar zuciya kawai ai ta korar ka daga guri amma kana qara nanewa mutane yafada yanajan wani wawan tsakin mimi ce takara so gurin ita da YASMIN da ta ruqo hannun ta zasu tafi nasu dakin su kwana suma saida Mimi taje kusa dashi ta rungume sa tace good night yaya Bossay yace good night tare da dan kamo kuma tunta tayi yar dariya sannan suka wuce suma sai yarage daga shi sai Ammi dan faruq ma tuni yatafi part din shi badade wa Ammi ta qaraso falon itama zaman tayi kusa da kujerar da take kusa dashi sannan ta kira sunan shi hankalin sa ya tattaro yamaida gareta tare da amsa kiran da tai mishi tace daman magana zan maka akan abun da kakewa furairah yanzu me ye laifi akan wani yace yanason ka sonka fa take bakinka ba duk wanda yace yana sonka be kamata kawatsa mata qasa a ido ba kana wulakan tata ni baga laifin yarinyar nan ba tana da hankali ga nutsuwa ga kyau duk wani abu da namiji  yake nema tana dasu dan wlh tama fi waccan yarinyar da kake so ka aura dan ni wlh yarinyar nan bata kwanta min ba dan de kawai kana sone kuma mahaifinka ya goya ma baya amma wlh dabazan yarda ka aure ta ba dan sam yarinyar bata da da'a kwata kwata shiru yayi yana ta sauraronta saida tagama sannan yace nifa Ammi wallahi yarinyar ce ni kawai bata kwanta min ba tun lokacin da nafara ganin ta Ammi kinsan hakan nan haka na faruwa sai kaga haduwar ka da mutum ta farko zakagane jinin ku yazo daya a kwai kuma wanda kana haduwa dashi zakaji be maka ba jininku be hadu ba tace hakane itafa yar uwarka ce be kamata kana nuna mata irin qin dakake mata yakamata ka sassauta ka rage ni bance dole sai kaso taba kawai de abun da nake so dakai shine kadan ringa sakar mata fuska intayi maka magana ka bata amsa bakyau wulaknci ko kai akayiwa abun da kake mata zakaji dadi yace a a tace to dan Allah ya arage wannan banzan halin dani banga amfanin sa ba yace to Ammi in Allah ya yarda zan canza daga yau inde har hakan ze faran ta ranki tace yauwa babana haka nake son ji nasan ba halinka bane wulakanta mutane dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login