Showing 72001 words to 75000 words out of 136570 words
yacika taf da mutane da bayi da jakadu har ma da wasu yaran gidan kowade ya hallara anzagaye gurin ana jiran aga hukun cin da za a yanke.....
Me dorina ne yafara yi musu bayani dalla dalla tunda ga farkon abun da yafaru har qarshe sannan yafadi hukuncin da aka yanke masa harda zancen sauke shi daga shugaban su kowa yayi mamaki jin abun da yayi wadanda kuma suka san halinshi basuyi mamaki ba sai Allah wadai da halinsa dayi mishi Allah ya qara.....alokacin aka fara yimasa bulalansa da narkekiyar bulalar nan da gayya suke yi mishi saida suka farfasa masa jiki dan dukan da sukayi masa ya haura yanda aka sasu dan ko irgawa ma basayi kawai tafkar sa sukeyi su duka biyun sai da suka tabbatar ya ladaf tu da dukan sannan suka rabu dashi.....
Hamza me ya Matso kusa dashi sannaan yace saura nawa kuma hakurin da nace zaka bamu da haka sai ka gaggauta kar mutane su fara tafiya da qyar ya iya daga kai ya kalleshi irin ya tausaya masa mana dame zeji kawar da kansa hamza yayi tare da miqewa yace kai nake jira kana bata min lokaci.
Bayanda ya iya dole ya rarrafa da qyar ya karasa gaban baba yace dan Allah baba kayi hakuri akan abun da na aikata muku banzasake ba""Hamza yace bamuji ba ka daga murya da haka yaqara kokari yadaga muyarsa tare da maimaita abun da yace sannan baba yace Allah yafe mana baki daya daganan ya qara rarrafawa yaje gaban hamza dan bashida qarfin miqewa saboda jikinshi duk ciwo yake mishi yana zuwa gabanshi shima yabashi hakuri kamar yanda yabawa baba shi ko kallon inda yake ma beyiba bare yasa ran ze samu yace ya yafemasa din shiru yayi batare da yabar gaban nasa ba kuma be dagoba ganin haka yasa mutane fara watsewa ko yana fadar albarkacin bakinsa har yazama na ba kowa daga shi sari su hamza da su me dorina.....
Me dorina ne yace suje uwar masarauta nason ganinsu yana gama fada yayi gaba sukuma suka mara mishi baya tafiya sukayi saka barshi tsugunbe agun da yagaji sai kawai yayi kwanciyarsa agun dan baze iya tafiya ba ahalin da yake ciki yanzu...........
'Fulani tafito bayan tafiyar su sai kuma tafara tunanin maganar hajiya sara saida taqara yiwa maganganunta dalla dalla amma ta kasa gano komai abun dade ta iya fahimata shine dole hajiya sara da kwai abun da take nufi amma abun da ta gaya mata bashine gaskiyar abun da yasata tsorata ba lokaci daya harda yarda jaka dole wtakil ko da akwai wata alaqa da ita da tsohon awaje ko kuma de wani abun tagani daban wayarta ta sauka ta kirata amma akace wayar akashe haka taita gwadawa amma bata shiga ba hara gaji ta hakuqara dole tana bukatar ganin hajiya sara tunda ta tafi dade hankalinta ya kwanta amma tund akace mata shugabansu qarya yake musu to hankalinta yaqi kwanciya tarasa wane irin tunani zatayi taga dede amma abun ya faskara gasu a qa'idar su idan mutum yazama bawa a masarautar ba a korarsa saide afita da gawarashi to yanzu yazatayi tana cikin wannan tunanin da ta kasa samun amsa,
Su hamza suka shigo da sallama saboda basuga kowa ba a bakin qofa shiyasa suka shigo kansu tsaye basuyi tsammanin ganinta ba sai kawai suka ganta bata amsa musu ba tajuyo tana fuskantar su duk zubewa sukayi aganta suna qara gaisheta gaba dayansu bawanda ta amsawa daga cikin su saida ta gama qare musu kallo sannan tace suje zata qara nemansu amma basai anmaida su dakin qasa ba kawai kuje kuci gaba da harkar gabanku amma ku zauna cikin shiri koda yaushe zan iya nemanku.
Meqiwa sukayi Baba yana cewa godiya muke Allah qara nisan kwana ko kallonsa batayi ba tana jira taji dayan ma yace ya gode amma sai taji shiru amma bata tanka masa ba ta rabuda shi dan ahalin yanzu bashine agabanta ba...
Shikam daman hamza yana sane yaqi kallon inda take ma ya kada kansa yayi ficewarsa.........
zama tayi kan kujera ta qara daukar wayar ta kira sake gwada kiran hajiya sara amma still no response hakura tayi taci gaba da tunanin mafita...
***********************
____________*ATAKAICE*____________
'Yau kwanan dadda goma cif a gidan su bossay kuma yau ta tashi kuma da rigima wai wlh sai anikaita taga jikarta dan baza ta jure ba ta gaji duk yanda su Ammi sukayi da ita akan ta hakura saura fa kwana biyu amma taki sauraronsu rarrashin duniya amma taki aminta daga qarshe ma hanyar fita ta nufa wai zata tafi da kanta da suka ga haka sai bossay yacewa ammi taje tashirya tazo suje kawai tunda ta nace haka kuwa akayi saida suka yarda sannan ta tsaya kuma taqi zama ta tsaya cak kamar soja har suka qaraso gurinta sannan suka fita tare su su uku
tun ahanya dadda take ta faman masifa wai kawai sunzo sun rabata da jikarta tsawon kwanaki wayasani ma ko sun kasheta sude ba wanda ya kulata sai faman dariya suke mata yanda wai lokaci guda ta tayarwa da mutane hankali sai taje........
Ahaka har suka qaraso asibitin a parking space suka yi parking sannan duk suka fito suka nufi cikin asibitin suna shiga suna qoqarin shiga bangaren da aka kwantar da Ameesha sukaji ance dadda gaba dayan su suka juyo suna kallon wanda yake kiran dadda dukan su basu sanshi ba Ammi da bossay amma ga mamakinsu sai suka ga dadda ta dan saki murmushi tace ashe kaine harkasa na tsorata
saleem ne ya qaraso inda suke yace haba dadda daga kira kuma sai tsorata sai kace a daji kike yagama fada yayin da ya yagama iso wa gurin
tare da miqawa bossay hannu suka gaisa sannan ya gaida Ammi itama fuskar ta da fara'a ta amsa masa"
baya nan yace dadda ina Ameesha sai shekaran jiya Azeema take gaya min wai kun tashi ashede zan qara ganin ku bejira amsar ta ba yaqara dorawa da cewa amma dadda lafiya naganku anan waye bashida lafiya??
Dadda kamar tayi kuka tace Ameeshan ce ai bata da lafiya yau kusan satinta biyu ma akwance anan wai sai likita yadawo zasu duba min jika salon su kasheta....
Saleem yace ya salam me yasameta haka wlh bamu sani ba ai kuma nima anan nake aiki bamu taba haduwa ba tace ai tun ranar da muka kawo ta sai yau muka dawo nazo inga lafiyar tane wlh sai anbude min ita naganta yace to dadda ki kwantar da hankalin ki bari inyi wa wani dr.. magana in Allah ya yarda zezo ya bada umarni ki ganta kar kidamu kinji ceke da jin dadi ta fara washe baki tace kai gaskiya naji dadi Allah yayi maka albarka dan Allah yi sauri kaje kafada mishi ko inzo muje tare yace a'a yi zamanki bari inje yanzu zan dawo yafada yana barin wajen....
Hamdalah su Ammi suka yi tare da sauke ajiyar zuciya sunji dadin zawan wannan yaron dan ba qaramin taimaka musu yayi ba saboda basu san ta inda zasu fara cewa wai sunzo suga Ameesha bayan kuma sungaya musu ba wanda ze ganta sai gashi Allah ya kawo musu dauki.....
kallon Dadda sukayi Ammi tace to Dadda ai sai kizauna ko yanzu hankalin ki ya kwanta bata kula suba tasamu waje ta zauna tare da kawar da kanta sai kace sunyi mata laifi.....,
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER......💅
By
Yaya Azeema 😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
Bismillah.........
45&46
***********************
'Saleem na shiga office din dr Shettima yayi nocking daga ciki akace come in tura qofar yayi ya shiga da sallama dauke abakin shi,
Dr shettima ya amsa sannan yace au baka tafi ba kenan?
Yace eh wlh nazo fita na hadu da wata kakata yanzu haka dan Allah inba damuwa taimako zakai mana sai kuma yadan tsagaita dayin maganar dr shettima ya dan gyara zama yana fuskan tarshi sannan yace ina sauraronka fadi abun dakakeso,
Shima gyara zaman yayi sannan ya dora dacewa yanzu wacce na hadu da ita take gaya min ankawo jikarta nan wai har takusan sati biyu amma bansan taƙamaimai abun da yake damun ta ba ance de wai likita ake jira sai yadawo ze yimata aiki ko kansan da zancen?
Dr shettima saida yadanyi jimm sannan yace eh to gasky bansan taba saide tabbas dr.. Jamil yayi min maganar rannan amma banje naganta ba gskiya kuma ansanar da wanda zeyi mata din ai zuwa jibi ze dawo yakusa dawowa,
Amma wane taimako kake nema kai
Saleem yace wallahi kasan ance wai bawanda ze ganta har sai bayan anyi mata aiki to yanzu wajen kwana goma kenan ba wanda yazo din daga cikin su shine sai yau kakarta ta dage wai ita sai sun kawota taga jikarta dan tana tunanin wai ankashe mata jika shiyasa aka hanata ganin ta kasan tsoho da rikice in yadage akan abu sai anbisa ahankali,,yadan tsagaita "sannan ya dora dacewa dan Allah in ba wata matsala ina neman alfarma abarta ta ganta ko zataji dadi ammafa inkana ganin hakan baze haifar da wata matsala ba,,"
Dr shettima yace to bazan ce da da matsala ba kuma bazance ba matsala ba amma de zata iya ganinta sanan kuma kar tayi wani motsi daze haifar da qara suyi ahankali bari nasanar da dr jamil din sai yazo yakaiku,
Saleem yace gaskiya naji dadi godiya nake Allah yabar zumunci Allah saka da alkhairi dr shettima yace bakomai nace maka kadena yimin godiya bakaji ko?
Ɗan murmushi saleem yayi yace yaza ayi kamin abu kuma inqi godiya ai bazan taba yin hakan ba,
Shikuma yace oh hakane to shikenan nikuma sai indena yi maka abu daga yanzu kaga basai ka gode min ba watakil ma saide ka zageni kace wancan mutumin beda mutunci ko,
saleem yayi saurin cewa kai kai haba yaza ayi inzageka ai ko bakamin nasan kamin abaya kaga kwa ai bana ga laifinka ba barema nasan bazaka taba yin hakan ba ai kaidin me mutun ci ne baka wulakanta mutane duk da irin girman da allah yabaka ga kudi ga mukami bakowa bane me irin matsayin ka watakil ko kallon inda nake ma baze yi ba bare har yatsaya ya ringa sauraron duk abun da nazo masa dashi ga taimakon da kakeyimin kaidin na musammune yaqara sa maganar yana fadada murmushin shi tare da kallon shi sai da yayi shiru...
dr shettima yace idan kagama zagi nawa sai katashi ka fita kuma kar kasake dawo min office yafada yana nuna mishi qofar fita da hannu shi saleem miqewa yayi yana yar dariya sannan yace tuba nake ayi hakuri yanzu de dan Allah akirashi din inje nasan suna can suna ta jirana,
Dr shettima yace ai nafasa sai kaje kasan yanda zakayi da ita da sauri saleem ya tsugunna a gabansa yace dan Allah kayi hakuri bazan sake fadar komai ba nayi shiru wlh naje nacewa matar nan baza tasamu ganinta ai nashiga uku kataimaka dan Allah nanma de qin amincewa yayi saida qyar saleem ya shawo kansa sannan yadau waya agabansa ya kirashi suka gama magana sannan saleem ya miqe yanzu de bece ya gode ba gudun qara samun matsala sai yamiqe yace mishi yatafi,,
"kai kawai yadaga mishi be kalleshi ba"
gani haka yasa saleem nufar hanyar fita saida yaje dede ze fita dan har ya bude qofa sai kuma yajuyo yana kallonsa yaga shima shi yake kallo"
Sannan ya dan daga murya yace nagode nagode nagode daman ku masu mutunci da kyawawan dabi'u ba kwaso ana yabanku sai kuce wai anzage ku to wallahi ba zagibane mutuncin naka ne yasa ake fada wallah kana da kirki sosai da sosai kaifa na dabanne acikin dari da kyar za asamu biyar irinka kuma wallahi.....
Beqara saba saka makon ganin shi da yayi yataso ze zo wajensa aikwa da wuri yasaki qofara ya fuce duk dahaka yana tafiya yancewa ina qara godiya fa daga nan zan tafi gida sai gobe yana tafiya yana dariya....
Dr.shettima da yayi sauri dan ya cimmasa amma besamu dama ba kawai kwafa yayi yakoma yace ai zaka dawo kasame nine dan kaga ina maka dariya shiyasa ka fara rainani hmmm zakasan nace banaso ka qarayi ka tafi katafi kama maidani abokin wasan ka hakade yayita surutun shi daga qarshe yakoma kan kujerar sa yazauna"....
'Saleem yana dariya ya qarasa gurin su dadda,
Dadda na ganinshi ta miqe tace yawwa yaron kirki muje ko naga kana ta dariya ko ance maka taji sauqi ne kai ya girgiza mata yace a'a dadda ande ce zaku iya shiga dukan kuma amma ba aso ayi motsi me qarfi saboda gudun matsala amma yanzu de wanda ze shiga daku zezo mudan jira shi yana nan zuwa godiya dadda tayi mishi bossay ma yaji dadin jin dukan su zasu shiga dan shima daman yayi missing dinta yana so yaganta yaga halin da take cike,
Ammi ta kalli dadda tace to dadda yanzu hankalinki ya kwanata de ko dadda tace wallahi be kwanta ba harsai na ganta da idon na tabbatar kuma bata mutuba,
Bossay yace waike baza kidena kiramana mutuwa bane to ita bazata mutuba saide in kece zaki mutun,
"Dadda najin haka tayo kansa tace wlh saide kai ka mutu tana fada tana qoqarin kai hannu kanshi....
Ammi tayi saurin riqeta tace haba dan Allah wai anan dinma baza ku saurara manaba tunda muka koma gida kunqi saituwa fadan yau daban na gobe daban yanzu kuma munbar gidan ma baza kuyi hakuri ba ku ko halin da yarinyar nan take ciki be dameku ba za hau yimana fada a asibitin taqarasa maganar tare da sakin dadda sannan tace to kuyi in akazo aka koramu gida kinga sai hankalinki ya kwanta kinzo baki ganta ba ta juya kan bossay tace kaima kuma wallahi na qara jin bakinka awajen nan sai na saba maka tunda ai duk kai kake jawo fadan kasan halinta ba hakura zatayi ba ina lafiya kura bare ta 'ya'yanta baka kulata bama tanayi ina kuma ga ka tsokanota ta qarasa magana cike da jin haushin abun da suke shirin yi,
Bossay ne yace kiyi hakuri Ammi ai duk itace da laifi meyasa kullum bakinta baze fadi alkhairi ba saide kiran mutuwa"
Dadda itama da takaici ya gama cikata tace bazan fada din ba kuma wlh inbaka fita daga idona ba sai munhaura gadon mahaukaciya da kai saide akoreni daga gidan tunda har anfara yimin fada yanzu kamar ni kamar ni da girmana Amina takeyiwa fada ba komai ni najawa kaina ni daga yanzu ma kubarni anan kuyi tafiyar ku bazan sake binku ba bare har wannan ja irin yaron yaringa gaya min magana son ransa taqara sa fada tana matse yar kwalla,
Ammi ce ta ruqota tace kai dan Allah Dadda nifa ba fada nake miki ba amma tunda kince haka kiyi hakuri bazan sake ba,
Saleem de na tsaye yana kallon ikon Allah be tanka musu ba.
Bossay ya bude baki zaiyi magana kenan saiga dr jamil ya qaraso gurin su da sallama tare da mikawa saleem hannu sukayi musabaha sanna ya miqawa bossay shima suka gaisa yagaida Ammi da dadda, Ammi ce kawai ta amsa amma banda dadda da har yanzu bata dawo daidai ba taki sakin ranta,
Bayan nan dr jamil yace musu bismillah su shiga su ganta sai lokacin dadda ta dan saki ranta, gaba yayi suka bishi abaya har bakin qofar da take a kwance ahankali ya shiga tura qafar tare da saka qafa cikin dakin saida yagama shiga sannan suma suka shigo gaba dayan su mayar da qofar yayi ya rufe sannan ya qara nufar wata qofa dake ciki inda ze sadasu da ainahin inda take kwance suna shiga suka ganta kwance an daura mata wasu na'u'ro'ri da suke taimaka mata wajen kare duk abun da zesa ta farka kuma kullum ana zuwa aduba lafiyar ta,
Dadda naganin ta ta fashe da kuka saide tasa hannu ta toshe ba ajin sautin sosai ganin haka yasa dadda kamata ta fito da ita waje suma basu dade ba dr.. yace musu suzo su fita suma saleem ne yafara juyawa cike da tausayin yarinyar ya tausaya mata matuqa ganin halin da take ciki yana so yaji me yasame ta amma ba halin yin hakan yaji daga baya idan komai ya daidai ta,
Dr. Jamil ne yasake yiwa bossay magana da yatafi duniyar tunani firgit yayi yadawo cikin hankalinsa da ya bar gangar jikinsa azahirance inka kalleshi zakace Ameesha yake kallo amma a badene abun ba haka yakeba,
Cike da rashin kwarin jiki yajuyo yabiyo bayan dr. jamil suka fito tare suna fitowa Ammi tacewa bossay su wuce gida kawai haka kuwa sukayi basu wani bata lokaci ba sukayiwa dr jamil godiya tare da yi masa sallama,
Tare suka fito da saleem inde shima yayi nasa wajen yakama hanyar fita bossay yace yazo suje suyi dropping dinshi amma sai yace mishi a'a ya gode ba yanda suka iya dashi dole suka rabu dashi yatafi suma suka shiga mota bossay yaja suka fita daga hospital har zuwa lokacin dadda bata dena kuka ba tun Ammi na rarrashinta har tagaji tadena shikam bossay daman ko kallon inda take beyi ba bare ya kulata ahaka har suka qarasa gida suna qarasawa lokacin ana kiran sallar magrib bossay nayin parking suka fito tare suka shiga suna shiga kowa yakama gabansa amma banda Dadda da tayi zamanta a falo tana cigaba da kukanta ba jimawa Bossay yafito ya dauro alwallarsa ze wuce masallaci ta gabanta yazo ya wuce be kulata ba yayi ficewar sa yana fita ba dadewa faruq shima yafito da shirin wucewa masallacin sai yaci karo da dadda tana kuka,
Da sauri ya qarasa kusa da ita tare da ruqo hannun ta yana cewa ya salam dadda me yasameki kike kuka ko ance muku ta mutune dadda ta jinjina masa kai alamar a'a yace to meyasaki kuka nanma shirun tayi mishi bata bashi amsaba yace dan Allah dadda ki gayamin wlh duk kinsa hankalina yatashi,.....
Shikuma hakan nan jininsu ya hadu da dadda tunda tazo gidan bazaka taba jin