Showing 30001 words to 33000 words out of 136570 words
kakewa furairah yanzu me ye laifi akan wani yace yanason ka sonka fa take bakinka ba duk wanda yace yana sonka be kamata kawatsa mata qasa a ido ba kana wulakan tata ni baga laifin yarinyar nan ba tana da hankali ga nutsuwa ga kyau duk wani abu da namiji yake nema tana dasu dan wlh tama fi waccan yarinyar da kake so ka aura dan ni wlh yarinyar nan bata kwanta min ba dan de kawai kana sone kuma mahaifinka ya goya ma baya amma wlh dabazan yarda ka aure ta ba dan sam yarinyar bata da da'a kwata kwata shiru yayi yana ta sauraronta saida tagama sannan yace nifa Ammi wallahi yarinyar ce ni kawai bata kwanta min ba tun lokacin da nafara ganin ta Ammi kinsan hakan nan haka na faruwa sai kaga haduwar ka da mutum ta farko zakagane jinin ku yazo daya a kwai kuma wanda kana haduwa dashi zakaji be maka ba jininku be hadu ba tace hakane itafa yar uwarka ce be kamata kana nuna mata irin qin dakake mata yakamata ka sassauta ka rage ni bance dole sai kaso taba kawai de abun da nake so dakai shine kadan ringa sakar mata fuska intayi maka magana ka bata amsa bakyau wulaknci ko kai akayiwa abun da kake mata zakaji dadi yace a a tace to dan Allah ya arage wannan banzan halin dani banga amfanin sa ba yace to Ammi in Allah ya yarda zan canza daga yau inde har hakan ze faran ta ranki tace yauwa babana haka nake son ji nasan ba halinka bane wulakanta mutane dan murmushi yayi sannan yace yauwa Ammi daman a kwai wata magana danake son muyi dade banyi niyar yimiki ba amma nakasa jure wa tace to wannan wace irin maganace inajinka to fadamin saida yadan yi jimm sannan yace wlh Ammi wata yarinya ce nake so mutai make ta dan tana cikin wani hali kuma tana buqatar taimako wlh tace wacce yariyar ce a ina take bata da iyaye ne yace eh wlh bata da iyaye agurin kakar ta take kuma duk dade bansan asalin labarinsu ba da alama basu da kowa anan sukadai suke rayuwarsu awani gida to kai ya kai kasansu yace agidan su Rasheeda yariyar take aiki tanan muka saba da ita harna nagane wasu abubuwan daga garesu karka ta kuma tana aiki tanayi yan kulle kulle nakayan yara tanakai wa makaranta tasiyar sannan kuma tana kula da yaran makaran tar itace de kamar nani din makarantar tace to yanzu kai yanzu ta ina kakeson mutai maketa yace sonake tadawo gidan nan da zama tace to ita kuma kakar tata kana ganin zata yarda tabayar da ita shiru yayi yakasa bata amsa saida tadan taba shi sannan yasauke ajiyar zuciya yace ai abun sa yasa kenan nagaya miki ke zakije da kanki ki lallabata dan wlh rikitacciyar tsohuwa ce bata da yarda kinga abun da tai min kwa danaje dakaina na tambaye ta nasha tijara da zagi dan wlh da har nayi zuciya ma akan bazan kara wai wayarsu ba amma danayi tunani sainaga be kamata inyiwa yarinyar nan haka saboda tadan saba dani dan da kyar ma tabarni nataho dan catai ai ko kakarta bata barta ba sai tabiyo ni saida nai mata wayo sannan ta rabu dani na taho akan zankoma in dakko ta gashi yau kwana uku kenan amma banje ba duk sai nake jin badadi Ammi tace me kace mata da har tazage ka yace wlh Ammi bawani abu nafada ba kawai rikicine irin nata harda min kuka fa wai zan rabata da jikarta inje insiyar da ita ko in lalata mata jika nan de ya kwashe duk dramar da sukayi da dadda yabata labari aikwa Ammi tasha dariya tace gaskiya kasha tijara nikuma ahaka da kake cewa muje so kake nikuma tayi min duka ko yace Ammi ai ke babba ce bazatai miki abun da tai minba wlh na dade ina tunanin tsohuwar nan tace yanzu yakake so ayi yace kawai kishirya gobe muje amma wlh bazan shiga ba tace aikwa sai ka shiga taya kakeso inshiga nikadai alahalin bata sannni ba kawai shahada zakai mushiga tare inta yarda to in kuma bata yarda ba shikenan kaga ai baza muyi mata dole ba yace hakane Ammi Allah yakaimu goben sai muje Allah yasa tayarda tace Ameen amma zanso inji labarisu gaskiya daga ji akwai wani abun da yafaru da rayuwar su abaya taya za ai ace sukadai suke rayuwa basu da kowa yace wlh nima de abun yana bani mamaki inaso inji suwaye su tace to mubar komai de sai goben kaje ka kwanta dare yayi yace to shikenan saida safe yafada yana tashi tsaye tare da nufar hanyar part din itama ta tashi ta wuce nata sashen kowa yatafi da tunanin yanda zasuje gidan dafatan samaun nasara..........
*****************************
**********************
*MASARAUTAR SARKI SAMEER*
Kamar yanda sarki yace hakance tafaru acikin kwanaki ukun da suka wakana yau ce ranar da za a fito dashi
bayan sallar isha'i sarki yabada izinin aje afito dashi bayan kowa ya hallar acikin fadar sukaje suka fito dashi Allah sarki kana ganinshi kasan baqaramar wahala yasha ba dan daman ance wuya bata kisa sai lokacinka yayi dan da tanayi da tuni bawan Allah nan yadade da mutuwa saboda ba qaramar wahala yasha ba dan har rama yayi ga duhu da yaqara yi duk yabi yazama wani irin dashi kamar bashi ba lokacin da aka shigo dashi cikin fadar duk wani me imani inka ganshi sai ka tausaya masa yana shigowa sarki me murabus ne yadago yana kallon sa aranshi yana tunani shiko a ina yasan fuskar bawan Allah nan kamar yasanshi ko kuma me kama dashi yasani oho yakasa tunawa har mutumin yaqaraso ya gurfanar da kansa agaban sarki tare dayin gaisuwa ga sarki sannan yajuya kan duk yan cikin fadar ya gaida su duk yasan da yawan mutanen wajen ya girme su wasu ma ya haifesu amma ahaka ya qasqantar da kansa agaban su yana gaida su wasu suka amsa ba yabo ba fallasa wasu kuma suka amsa a wulakance wasu ma daga ciki ko kallo be ishesuba bare yasamu su amsa koda awulakan ce nan be damuba yayi shiru yana jiran hukunci da zeji saida kowa yayi shiru gun yayi tsitt kamar ba mutane aciki Fulani ce tafara yin gyaran murya kowa kuma ya maida hankalinsa gare ta sannan tafara magana kowade yasan abun da yatara mu anan basai naqara bayaniba dan haka ni matar sarki me murabus kuma uwa ga sarki ma yanzu nayarda da hukuncin da sarki ya yanke da kuma zaman wannan mutumin a masarautar nan kuma daga yau yazama bawa agidan nan daga nan har sanda ze bar duniya ina fatan kowa yaji duk suka jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan ta sannan ta dora da cewa gobe ze fara aiki za a bashi kula da bangaren dabbobi da doku na da basu ruwa da abinci ina fatan kowa yaji inda me magana kuma nabaku minti biyar me magana yayi kowa shiru yayi ba wanda ya iya cewa komai bawai dan basu da abun cewa ba sai dan kawai gudun idan mutum yayi bayarda za ayi ba saide ma yajawo wa kansa wani fadan dan haka bawanda yace komai jinahiru nasu yasa Fulani cewa kowa ze iya tafiya sannan kuma azo adauke sa akaishi bangaren bayi abasa kayan bayi yasaka gobe a nuna mishi yanda zeyi aikin wani bafade da yashigo dazu yace to ranki yadade sannan yakalle sa yace taso muje ko ahankali ya yunqura ya tashi yana tafiya da qar bayan fitar shine sarki me murabus yace yakalli Fulani zeyi magana amma sai ta daga masa hannu alamar bata so yace komai haka kuwa yayi duk wannan abun da suke yi sarki be tsoma musu baki ba bece qala ba daman haka suke inde Fulani na gurin tofa baya cewa komai saboda tun kafin azauna zasu tattauna komai da mahaifiyar sa sai abun da tace za ayi dan sai yazama na ma kamar itace sarkin komai a hannun ta yake ba a isa anyanke hakunci ko wani abun yafaru batare da ansanar da ita ba komai ita take gudanar dashi ba wanda yake da iko acikin masarautar sai da amincewar ta sai yanzu sarki yace mama angama ai zan iya tafiya tace eh nagama zaka iya tafiya sarki ya miqe yafita dagaron sa suka mara masa baya zu sashensa inda iyalain sa suke daman kowa ya watse daga cikin fadar sai yarage daga Fulani sai sarki me murabus sai dayar matar sa me suna *SA'ADATU* wacce ake kira da maman 'yan biyu, maman yan biyu itama mata ce gurin sarki kishiyar Fulani Amma ita halinta ya dan bambamta da na Fulani ita bata dauki duniya da zafi ba mata ce me hanakali da nutsuwa da sanin yakama ta bata shiga kuma abun da ba ruwan ta hasali ma bata da yawan magana bata da surutu kwata kwata komai zataga Fulani nayi bata taba tanka mata saide tabita da ido koda tasan kwa abun da take yi din badede bane saide ma taqara kawar da idonta daga abun da taga tana yi shiyasa ma basa samun matsala da Fulani dan Fulani matace meson a girmamata kuma duk abun da mutum yaga tanayi to ya zuba mata ido batasan ana shiga lamarin ta in ba ita taso hakan ba sai kuma Allah ya hadata da irin wacce take so yanzu made kamar koda yaushe haka maman yan biyu batace komai ba akan al amarin ta sai ta miqe tace ni na wuce sai da safenku sarki kawai yace mata Allah yakaimu sannan tace Ameen tayi ficewarta tabarsu agun sarki ne yace to gimbiya muma ai sai mutafi ko anan zamu kwana ne batace mishi komai ba kawai ta miqe tace muje ko yace to haka ya mike tasashi agaba kamar danta sukabi tabayan qofar inda ze sadasu da nasu part din.................
**********************
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
Kowa yagyara zama domin fahimtar yanda labarin ze kasance
MASOMIN LABARIN masarautar sarki sameer
SARKI SAMEER shine sarki nawajen hamsin da wani abun yagadi sarautar ne awajen baban sa wandan shima gada yayi tundaga sarkin farko sarau tar taringa tafiya harzuwa kansa shima kuma tun kan yamutu yabawa babban dansa sameer kenan sameer yana da qanne hudu kuma duk mazane shine babba shiyasa babansa yabasa sarautar kuma ya yaba da hankalin sa yasan kobayan ransa ze ruqe al'uma zeyi adalci a sarautar sa kuma hakanne yafaru domin yayi adalci sosai iya kacin iyawarsa duk wanda yake awannan lokacin ze yaba da sarautarsa kama daga yan gari yan cikin masarau tar har bayi ma da jaka diyu babu wanda akabari kowa alfahari yake da mulkin sa sarki sameer yana da mata uku uwar gidan sa me suna *KARIMA* karima tana da yaya uku danta na farko shine *MUHAMMAD* na biyu kuma *ALKASIM* na ukunsu kuma *IBRAHIM* sai matar shi ta biyu me suna *ASIYA* itakum tunda suke bata taba Allah be bata haihuwa ba ta ukunsu kuma Amarya agun sa sunan ta *SHAMSIYA* ita kuma yayanta biyu duk mata kuma daya tarasu saura daya me suna *HANNATU* kan matansa duk ahade yake bakajin kansu saide abun da ba a rasaba yau da gobe sai Allah zo muzauna zo musaba daman zama yagaji haka tun yana aiki da qarfin sa har yafara gajiyawa domin tsufa yazo mishi gashi babban dansa da yake so ya dora akan karagar mulkin shi ya nuna mishi baya ra ayin sarautar tun tasowarsa bayaso dan hakama yaroqi me martaba akan shi bazeyi karatu anan ba a Egypt zeyi karatu ba musu kuwa sarki ya amince da qudurinsa yabarsa yatafi acan yayi karatunsa gabadaya lokacin da yadawo yanaso yafara aiki sarki yace be isa ba dole ya karbi mulki ko yana so ko baya so da farkode kin amincewa yayi har saida mahaifiyarsa ta sa baki akan inbe karba ba ransa sai ya baci kuma akace mishi kafin lokaci nadin sarautar yayi suna so yafara aure inkuma bashi da ita zasu zaba aikwa dasauri yace ai yana da ita akace a ina take a Sudan take tun farkon fara karatun sa suka hadu sundade tare kuma iyayen tama sunce zasu bashi yaturo da iyayensa dukan su sunyi farin ciki sosai dajin batun dan nasu dan haka ba bata lokaci akaje aka nemo masa auren ta yakasa wata daya tal sannan suka bayan sundawo ne kuma aka kara ce mishi saifa yayi hakuri dan dole sai yakara da wata matar domin qa idane sarki yakasance da mata biyu yace shi gaskiya bashi da wacce yakeso abar shi da iya wannan ma ta ishe shi suma kuma sukace baza suyarda ba dole yayi hakuri ya amince akace za abashi yar qanwar Asiya kishiyar mamansa kenan yace to beyi musu ba yakaba itama rana daya akasa da na *SABREENA* sunan wacce ze aura kenan ita kuma tabiyun daza a aura mishi itace *MARYMA* rana bata qarya yau kadaura auren Muhammad da matan sa Sabreena da kuma maryama dana din sarautar sa yau yazama ango kuma sarki ba a wani dadeba dayin hakan Allah yayiwa sarki sameer rasuwa kowa yaji mutuwar nan sosai ta girgiza mutane da yawa ahaka har aka dauki kwanaki duk da baya son sarautar hakan be hanashi gudanar da mulkin sa ba cikin adal ci kamar yanda mahaifinshi yake yi dan harma yaso yafi mahaifin nashi komai yana tafiya yanda yakamata.................
08124226526
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
By
Yaya Azeema😎
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Allah ya gafarta mana ya yafeman kurakuranmu wanda mukasani da wanda ma bamu saniba Allah ya shige mana gaba aduk kanin al amuran mu yabamu yanda zamuyi Ameen..........*
Bismillah......
18&20
**************************
'Tunda yake zaune da matansa be taba jin kan matansa ba suna zaman lafiya da juna har sukai wajen shekara biyu amma gaba dayansu bawanda Allah yabawa ciki ko batan wata bawanda yataba yi dan har mahaifiyar shi Karima tafara yi mishi maganar ko ze kara aure ne amma sai yace mata tayi hakuri sukara hakuri zuwa nan gaba ko Allah zesa wata daga cikin su tasamu bata takura mishi ba ta rabu da shi ta cigaba da zuba musu ido ahakade har suka qara daukan lokacin kwatsa saiga amaryar sa SABREENA da ciki saboda lokacin da akayi aure duk da yafi sonta amma bada ita yafara kasance wa ba, saboda ita ba aranar aka kawota ba shiyasa yafara kasance wa da MARYAMA amatsayin itace uwar gida kenan,
Abun ba a magana saboda tsabar murnar da ahalin masarautar nan suke dan har wata yar walima aka hada na farin cikin samun cikin kowa sai nan da nan akeyi da gimbiya sabreena sarki kwa har wata soyayya yake kara nuna mata wacce bata taba ganin irinta har wajen kishiyar ta ma tana samun kulawa haka wajen surukar tama har kishiyo yin surukar tama ba abarsu abaya ba saboda wannan cikin idan Allah yaraya shi shi ze zama magajin sarki domin anyi scanning anga namiji ne kuma ana fatan Allah yasa hakan ta kasance a haka akai ta rainon cikin har Allah yasa ta sauka lafiya ranar suna yaro yaci sunan baban sarki Muhammad aka saka mishi sameer,
Yaron yana cikin wata na daya kenan wani gagarumin abu ya afko musu sunshiga tashin hankali marar musaltuwa sama ko qasa annemi yaro an rasa itade gimbiya sabreena bayan tayi mishi wanka ta kwantar da shi akan gado tashiga bandaki domin tayi wanka fito warta ke da wuya taga ba yaro da farko de bata kawo komai a ranta ba saboda tayi tunani ko sarki ne yashigo dakin yafita dashi ko kuma gimbiya MARYAMA tashigo ne bata jiba oho tana ta tunani har tagama shiryawa tafito tana fitowa kuma bata ga kowa ba afalo jakadiyar ta KANDE tashiga kwalawa kira amma itama taji shiru bataji ta amsa ba saida takirata wajen sau uku sannan tashigo falon da sauri tace gimbiya gani na danje wajen balaraba ne kiyi hakuri na fita bansanar dake ba tace ba komai daman tambayar ki zanyi ko wani yashigo dakina ne lokacin da na shiga wanka banga Annur ba, (shine sunan da suke kiran sameer dashi) "kuma gashi kema kince bakya nan yanzu kije kitambayo min bangaren gimbiya MARYAMA ko ta shigo sannan inkin fita kafin ki wuce kigayawa Salisu yaje fada yagani ko yana can tace to sannan ta fita.
da sauri sauri taje ta tambayo akace mata baya can tana hanyar shigowa bangaren ta hadu da salisu shima yadawo yace mata shima yaje ance baya can tana shiga ta sanar da gimbiya cewa duk sun duba ance ba a ganshi ba,
Nande aka shiga cigiya sarki ma yabaro fada domin jin yanda akayi aka rasa yaron acikin masarautar nan yana zuwa yatambayi yanda akai gimbiya duk tagaya mishi yanda akai kafin kace me magana ta zagaya har wajen gari kowa hankalin sa ya tashi neman sa ake lungu da sako amma babu shi babu labarin sa gimbiya Sabreena tasha kuka dan har kwantar da ita akayi agadon asibinti saboda tsaban shiga tashin hankali sai da qyar sarki yake rarrasheta dan shima dauriya kawai yake amma ba karamin tashin hankali ya shiga ba gimbiya maryama ma tasha nata kukan kamar itace ta haifi dan kowade