Showing 69001 words to 72000 words out of 103469 words
da cin zarafin da tayi har Sauban ya yanke hukuncin nan,cikin muryan kuka Ammi tace"Yanzu fisabilillah da Sauban be yanke saki a tsakanin sa da Akeela ba hakan zai faru? Aida Galadima bazai shiga halin da yake ciki ba,ga lalacewan zumunci"cikin sauri Bodejo tace"
Xahratty CE π₯°
Lallai Alqalami ποΈ yafi takobiπ‘οΈ.
[7/10, 19:53] πππ‘π«π πππ‘π«ππππ²π₯°: π¨π½β𦳠*_GALADIMA FAMILY_* π¨π½βπ¦³
Page: 69/70
____Koda a lokacin Saudan be saki Akeela ba to wallahi sai ya saketa domin bazai zauna da shedaniya ba,yarinyar nan babu alamun shiriya a tattare da ita kuyi la'akari mana,wallahi ko bayan raina saudan bazaiyi rayuwa da alakakai ba"tana kare dadar hakan tanufi corridor din dakinta, Mommy tace"gaskiyan Bodejo ne sam babu lefin Sauban kawai Guggo Laure sai a hankali ne"Mom ta mere baki tace"Hmm kune bakusan halinta ba,itafa nata kawai tasani nata nata ne koba komai a wannan hargitsin ma tanuna"ajiyan zuciya Aunty Maryam ta sauke tace"Ni tun randa aka kawo yarinyar nan naga 'yan uwan mamanta masu budadden ido da ita kanta jikina yayi sanyi,don babu irin kunyar nan ta amare ko miskala zarratin a tattare da ita"Mom tace"Bana tunanin 'yan uwan maimuna ne gaskiya,don maimuna mutumiyar kirki ce,haka 'yan uwanta,itafa yarinyar nan daurin gindi kawai tasamu wajen Guggo,kunsan akanta sai da Guggo taje har gida ta zazzage hajiyan mu kafin bikin su?wai Rammat zata kwace mata Sauban,haka dai akayi maida zance batare da Ummie tayi magana ba, Baba Hasheem ne yashigo yana duban duk wanda ke parlour,don babu yara duk suna waje suna wasa,sai su Nihal tare da iyayen su,duban Mommy yayi yace"hauwa'u kufara shirye shirye,gobe insha Allah Zuhra zata tare a dakinta,domin hukuncin da aka yanke kenan,yanzu Bodejo tayi magana"Mommy zuciyan ta fesss tace"Insha Allah,mutanen parloun cikin tsananin farin ciki suke har Ummie sai dai bata nuna ba fuskan ta kadaran kadahan, Ammi kuwa kaman tayi rawa"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un don Allah kubashi hakuri ni banason auren wallahi banason Yaya ni karatu na zanyi"Zuhra ne ke magana cikin muryan kuka kota ina zufa ne ke tsattsafo mata kamar babu A.C a parloun,duk da mamaki suka tsaya duban ta parloun yayi tsit bakajin komai sai gunjin kukan ta, Mom ce fuska a daure tace"Amma wannan yarinyar anyi ja'irar banza, Kinga wallaphi kikeyaye mu,idan baki son auren mu munaso aikin banza kawai"Mom tayi maganar tana jan tsaki,sosai Zuhra take kuka wanda yasa jikin Ammi yin sanyi,mikewa tayi ta isa ga zuhra ta kamo ta tace"kiyahakuri Zuhra kinga mahaifinki wasiyya yabari na auren ki da son,ki temaka ki aure sa,inaji a jikina ke alkhairi ce agaresa"Ammi tayi maganar tana murmushi Wanda sosai tabama mutanen parloun tausayi, Ummie kuwa a fusace ta taso domin idan bata daki Zuhra ba bazatayi sukuni ba,ganin haka yasa Zuhra fusge hannunta ta nufi dakin da take zama,cikin muryan kuka tace"wallahi banason sa"kamo hannun Ummie Ammi tayi tace"Menene zakiyi haka bilkisou?wai meyasa kina mantawa da zuhra yarinya ce?dole a bita a hankali fa, menene amfanin abinda kike shirin yi? Ummie cikin bacin rai tace"Haba haba Ammin yara Zuhra ce yarinyar?hmmm taga ana lallabata ne"Mommy tace"babu maganar lallabo Aunty bilkisou gaskiya ne zuhra yarinya ce,so sai anbita a hankali,cikin bacin rai Ummie tabar apartment din, Mashahuda da Muneefa ne suka shiga bedroom din da Zuhra ta shiga, Aunty muneefa cikin bacin rai ta dubi Zuhra"yarinya ina guje miki ranar nadama,wai kuwa kinsan waye ya Sauban?kin kuwa san yanda mata suka rikece akansa?mata da dama sun mutu a son sa wallahi idan kika auresa keda kanki sai kinyi alfahari da auren",cikin kuka Zuhra tace"nidai bana son sa,meyasa Abbie zai yanke wannan hukuncin?i know Abbie bazai taba zabamin mijin da zai cutar dani ba,sai dai why not zuciya ta takasa amincewa dashi matsayin miji,bazan iya yarje ma batun iyaye nabaaa.....takarisa zancen tana sakin wani irin kuka me tsuma zuciya"meyasa aure na yazo a haka?duban Aunty Mashahuda tayi"Aunty Mashahuda meyasa baza'ayi irin shagulgulan da akayi a naku ba,bikin ku is d best biki a wannan year din"dafa ta Mashahuda tayi tana murmushi tace"bikinku ya fita daban dana kowa,kiyarda cewa rayuwar auren ku ne kukuma zai zama abin kwatance, cuz Allah zai albarkaci aurrn ku trust me"shiru Zuhra tayi tana jan ajiyan zuciya, Laila tayi dariya tare da cewa"Aunt duk fa munafunci ne itama tana son Yaya, amma zuciyar ta takasa yardan mata da haka, Nihal itama dariyar tayi tace"wallahi kuwa hhhhhh"a fusace Zuhra ta dubesu"Ni banson sa bantaba son sa ba,mutum daya naso a duk duniya akan shi nasan menene so,wato ya Shuraim.....Tasss! Karar mari ya sauka akan kumatun Zuhra,huci kawai yakeyi idanuwan nan sunyi jajawur,cikin sauri Mashahuda,muneefa, Laila, Nihal suka bar bedroom din, Sauban kuwa banda rawa babu abinda bakinsa yake masa,cikin muryan tsawa ya nuna Zuhra"ke...kk..kkee da aure na akanki kike fadar kina son wani?yayi maganar yana nufo Zuhra yana huci,girgiza kai Zuhra keyi"A'ah yaya don Allah kayahakuri bazan sakeb......hannu ya dunkule kamar zai kaimata punch,sai kuma yakaima wall din bedroom din,ita kuwa runtse ido tayi jikinta na rawa,juyawa yayi yafita,cikin takunsa wannan karan dai-dai da tafiyar cikin fushi yakeyi.
Mommy ce tashigo dakin cikin sauri,kamo Zuhra tayi"Wai ke bakida hankali ne?sai yaushe zakiyi hankali my Zuhra,kike fadar bakison mutum agaban mahaifiyar sa gatsal haka?cikin kuka tace"Mommy shima fa baya sona"cikin fusata mommy tace"inji uban wa ya fada miki haka? kuka Zuhra ta fashe dashi hankalinta a tashe sai dai takasa furta komai,kukan kawai takeyi,ki tashi kije ki shirya zakije saloon,cikin sanyin jiki ta mike ta fita,babu kowa a palourn na bodejo,kaitsaye apartment din Ummie ta wuce,a palourn kasa ta taras da ita da Taufeeq suna magana,sallama tayi duk suka amsa sannan ta haye stairs,shiryawa tayi cikin riga da straight skirt,harta dau mayafi tasa kome ta tuna?sai kuma tanemo after dress ta dora akan kayan tafita.
Duban ta Ummie tayi"inane zaki haka?cikin sanyin ta tace"Mommy tace nashirya nazo za'a wankin kai"daga mata kai Ummie tayi,hanya ta Kama har takai kofan palour tajuyo cikin raunanniyar murya tace"Ummie ki yafemun"tana karisa fadan haka da sauri ta fice.
Sai la'asar suka dawo daga wankin kan,a lokacin ne kuma me henna ke jiranta,abinci taci tayi la'asar sannan Aunty Labeeba da Mommy suka fara yimata dilka,bayan an gama aka mata wankan lalle, fara shiryata cikin wata hadaddiyar net wanda aka mata dinkin wedding gown,blueblack tayi kyau dinkin ya hadu,me make-up tafara zane mata face dinta,light make-up aka mata,tayi balai'n kyau,fito da ita akayi farfajiyan gidan,kanofi ne guda uku,mutane ne zazzaune daga familyn gidan,sai makota da kawayen matan gidan don abune da akayi a kurarren lokaci,anyi decoration din filin sosai,kaitsaye aka kaita wajen rumfarta wanda yayi balai'n haduwa da tsaruwa sai wani walwalin wuta ke tashi ajikin wani rubutu ansa *_HENNA DAY,HAPPY MARRIAGE LIFE, MUHAMMAD TALEEB MUHAMMAD&FATEEMA SADEEQ MUHAMMAD._* Zaunar da ita akayi a hadadden carpet din dake wajen,gefe me lallen ne,aiko nan tashiga yima amarya lalle,sosai kida yafara tashi tare da gudeΒ² na farin ciki,haka me lalle ta cigaba har tagama na kafa ja dana hannu,anfara baki a kafa.....sautin kidan ne ya canza salo,nan Mc ya fara sanarwa"Ga ango nan ga ango nan don Allah a bashi waje,Zuhra kuwa zuciyar ta kaman tayi tsalle tafito,nan kuwa aka saki waqar illela bille illela,lamshi sharahni,sosai kidan ke tashi,ya Sauban ne a gaba cikin wata mahaukaciyar boyel blueblack,sai bakar zanna bukar,kafansa wani hadaddiyar covershoe ne kirar gucci baki,hannunsa dauke da agogon Cartier, yayi bala'in kyau,murmushi yake wanda yakara fito da ainahin kyansa,sosai aka fara tafi da ihu,bayansa abokan sa ne 'yan nan maidugri su biyar sai Taufeeq,Kareem,da Aseef su kuma cikin fararen boyel,kaitsaye wajen Zuhra ya nufo,nanfa yashiga watsa mata daloli,sai da ya watsa mata fin dari,ihu ne kawai ke tashi na mutane,hannu ya mika ya Taufeeq ya saka masa meant na 1000 aiko ballewa yayi yana watsa mata,aiko waje yasake kacamewa da ihu,Suma ya zuba sosa,dukawa yayi dai-dai saitin kunnenta inda kanta ke duke ya fara magana cikin rada tare da kamo hannunta"kinyi kyau matata sosai,am proud of you my beauty"cikin sauri ta dago,don tabbas jitake kamar tana mafarki,a dai-dai nan aka fara daukan su hotuna,waje nasake cika da ihu,nan yaja tawagar abokan sa suka bar wajen,aiko cigabawa akayi, ba'a watse ba sai wajejen 9:30 sannan.
Cikin matsanancin gajiya Zuhra take,lallabawa tayi tanufi bedroom dinta ta rufe sai bacci,sosoai Sauban yaso ganinta amma ina Zuhra tayi bacci.
******
Washegari cigaba akayi da shirye-shirye duk da kuwa botsarewan da Zuhra keyi domin daru sosai tasa kan naqin auren,sai da Baba hasheem ya mata haukaΒ² kana tashiga taitayin ta,karfe biyu akafara walima zuwa la'asar angama duk anwatse sai yarage gidan sai iyasu ahali,da yake Amma ma ta iso tare da matan yayyen Ummie da kannen ta,haka dai aka cigaba, hayaniya ce ta fara tashi,a dalilin shigowan Guggo Laure gidan.
"Munafukan banza munafukanp wofi,ai dama tun tuni nasan Yaya Bodejo ta tsaneni tatsane jinina, Allah sai ya yimin sakayya tsakanina dakuu"takarisa maganar tana sakin kuka,tsit gidan ya dauka kowa yayi cirko-cirko, Akeela kuwa wajen Zuhra ta nufa tare da nuna ta da yatsa tana huci"matsiyaciya nadawo kanki,'yar iska karuwa kawai,dama tuntuni na fahimci manufar ki akaina kina kokarin rabani da farin cikina karuwa kawai"tayi maganar Cikin karaji,murmushi Zuhra tayi tana duban Akeela"Hmmm Akeela kike da suna ko wane?I don't have time for you cuz ni din nafiki ajiki,kima da kuma mutunci,niba 'yar iska bace,kuma ba karuwa bace,abarshi ma a hakan haka nake,ai gara karuwa da 'yara madigo la'ananniya,domin zunubi da girman madigo ya taka na Zina ya shany....a fusace Akeela tayi kan Zuhra tana cewa"nice kike gayama magana haka?da sauri Zuhra taja baya,aiko wani irin fusgota Akeela tayi tana shirin cacumar ta,jikake tassss! Sauban ne ya sauke wa Akeela lafiyayyun mari har biyu banda huci babu abinda yakeyi gabadaya kamsnnin sa sun rikide,dafe kumatu Akeela tayi tana sakin ihu"Ni ka mara akan wata banziya?nidin matark......daka mata tsawa yayi wanda duk wanda ke wajen sai da ya firgita"point of correction Akeela,you re not my wife,nadatse igiyoyin aure na akanki,sannan koda wasa kada ki kuskura kazantaccen hannunki ya ta6a jikin matata"Guggo Laure ne takariso tare da dauke Sauban da mari"kauu! Magana tafara"baka isa ba Sauban kayi kadan kaci zarafin jinina ina kallo dan iska kawai la'ananne.
Cikin tsananin 6acin rai Baba Hasheem yace"Haba Guggo haba wannan cin zarafin naki yayi yawa,bazaiga la'anta ba,bazaiga la'anta ba Guggo"yayi magana cikin karaji,cigabawa yayi"me Mika miki haka da zafi?kin lalata zumunci,a dalilin ki mahaifin mu nacan kwance da barin jiki, Guggo mungaji da cin zarafin ki"yayi maganar cikin karaji,hannu ya hada waje guda yace"Don Allah Guggo kitafi,muddin ba alkhairi yake kawoki garemu ba so please nd please kidena zuwa kina tayar ma da ahalin mu hankali na rokeki"Guggo Laure kuwa sakin baki tayi tana kallon Baba Hasheem"Hasheem nikake fadawa magana son ranka?ka mance matsayin wa nake a wajenka?kafin yabata answer Aunty Maryam tayi carab cikin muryan kuka tace"Matsayi wani irin matsayi Guggo?kin mance keda kanki kin yanke alaqar dake tsakanin ki da ahalin nan?duk irin soyayyar da Galadima ke miki Amma haka kika rufe ido akan jika kika tozarta sa,duk akan wannan?tayi maganar tana nuna Akeela"meye ribar ahalinmu idan munma Akeela sharri alhalin mudin duk abu daya ne,wallahi Guggo indai shedaniyar yarinyar nan ne watarana sai kinji kunya.
Shiru Guggo Laure tayi da alama jikinta ya danyi sanyi ganin haka yasa Akeela fashewa da kuka"Guggo kinajin su?kina jin irin cin zarafin da suke min?maida dubanta tayi ga Akeela"ke Kuma sai kinsan kin aurar wa kanki masifa da bala'i"tana kare fadar hakan tajuya,da sauri Guggo Laure ta take mata baya tana cewa"Allah ya mana sakayya!
_Hoho Galadima family ko rikici family,nikam zanso naga randa wannan rikicin zai tsaya haka,gadai Sauban da Akeela ga kuma Kuma Zuhra a gefe guda,sannan ga alwashin da Akeela ta dauka akan zuhra._
Xahratty CEπ₯°
Lallai Alqalami ποΈ yafi takobiπ‘οΈ.
[7/12, 00:54] πππ‘π«π πππ‘π«ππππ²π₯°: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs
π¨π½β𦳠*_GALADIMA FAMILY_* π¨π½βπ¦³
Page: 71/72
____Sosai Zuhra ke wani irin kuka me tsuma zuciya,gabadaya sun sake 6ata gidan,bayan sallar magrib aka fito da Zuhra Cikin shigan alfarma na lutfaya Army Green tayi kyau matuka,ita kanta lutfayan daka kalleta kasan nera tayi kuka,kuka takeyi sosai kaitsaye apartment din Bodejo aka nufa da ita inda gabadaya a halin ke a palour a zaune,zaunar da ita akan carpet Mommy tayi kusa da Sauban din,nan Baba Hashim yayi gyaran murya tare da sallama,bayan yayi addu'o'i sannan yace ma Taufeeq yakira su Daddy ta laptop din,aiko lokaci daya sai ga Daddy da Abba sun bayyana.
Anan aka shiga gaishesu,tare da tambayan su jikin Galadima,hadasu da Bodejo akayi suka gaishe ta,bayan sun gama gaisheΒ²n ne kuma Daddy yayi gyaran murya,nan yashiga nasiha,sosai yama Zuhra nasiha me shiga jiki wanda dole yasata cigaba da kuka Saboda tunatar da ita da yasake kan hakkokin miji akan matanshi da abinda idan tayi zata samu zunubi,sosai yayi mata raga-raga da nasiha daga karshe ya damkawa Sauban amanarta,sannan yace idan ya zalunce ta Allah ya isa,shima Abba nan yayi nasa inda shima daga karshe ya damka amanar Zuhra ga Sauban,na karshe Baba hasheem ne yayi nasa,me hade da fadaΒ² don ya lura Zuhra zuma ce sai da wuta a cewar sa,su Daddy nan akayi sallama dasu,cikin tsokana Ummie ta dubi Baba hasheem tace"wallahi da ka hada da duka ina tunanin Zuhra zatafi gane yaren,duk dariya aka Sanya,shima mikewa yayi tare dasu Sauban don zuwa suyi sallah yana cewa"kuyi ku gama mata nasihar da zakuyi mata,don muna dawowa masallaci za'a bashi matansa ya wuce da ita,da to mommy dasu Aunty Maryam suka amsa, Bodejo tace"munafuka munanan daku sanda zasu hade suna kwasar soyayyan su babu meji"dariya palourn akasa, Aunty labeeba tace"yanda kikajin nan Bodejo,nan Ammi tafara mata nasiha,sannan Mommy, Mom, Aunty Maryam, Aunty labeeba,duban Ummie Ammi tayi tace"bilkisou bakice komai ba,dan tamke face Ummie tayi tace"Allah yasa albarka,idan har kika bijerewa umarnin mijinki akan abinda be sabawa mahaliccin ka ban yafe miki ba"tana kaiwa nan tamike ta fice,duk sake da baki suka bita, Zuhra kuwa kuka tasaki.
A hankali aka dinga raguwa a palourn,yarage daga Laila sai Nihal,cikin zolaya Laila tace"Oh mu ko dan siyan bakin nan baza'a bari muyi ba?cab wannan auren manya ne"Nihal tace"Allah yasa Yaya ya jiki,haka suka zauna su Laila na taya ta hira a gefe Bodejo na mata tsiyan kuka gulma takeyi,sai wuraren 10 sannan Sauban ya shiga palour da sallama hannunsa dauke da leda wanda aka RUBUTA Delicious Suya,sannu da zuwa suka fara masa yana amsawa sannan suka mike suka fice,kusa da Bodejo yaje ya zauna yana ajiye mata ledan a gefen ta,murmushi Bodejo tayi tana jawo ledan"me kuma kakawo min ne Saudan?tayi maganar tana bude ledan,cike da farin ciki tace"uhmmm aiko ka kyauta kamar kuwa kasan nagaji da cin wannan farfesun gwanda daka siyomin suyan nan,amma dai na rago ne ba sa ba ko? Sauban dake danne-danne a wayansa yace"Ea na rago ne nasan baki cin na sa ai,keda Amma na siya muku"murmushi Bodejo tayi cikin jin dadi tace"amma kuwa mungode Allah yayi ma auren ku albarka"tayi maganar tana kai suyan bakinta tare da lumshe ido tace"kai naji dadin naman nan sosai,ai ina gaya muku kuda kanku sai kunyi alfahari da auren nan"tana tauna namar tana magana,a kaikaice Zuhra ke zabga mata harara don ta gama ramfo Bodejo santin naman takeyi,mikewa Sauban yayi tare da zura hannayen sa a aljihu,wani mugun faduwar gaba Zuhra taji, shikenan wai dagaske akeyi bin ya Sauban zatayi yau?sai hawaye sharrrr,duban Bodejo yayi"mu zamu wuce sai da safe kici nama lafiya"cikin sauri Bodejo tace"ai ban ba matarka naman ba, Zuhra ungo zo ki amsa"ko kallon ta Zuhra batayi ba tana bin bayan Sauban cikin wani irin kuka, Bodejo tace"Oho dai algunguma anaso ana kaiwa marke(Wai marketπ€£) suna fita ya wani irin fisgota gabadaya tafada jikinsa,face din babu walwala ko kadan yace"Wallahi idan bakiyi min shiru ba sai na baki mamaki,uban waye yace miki nima inason ki da kike damun mutane da kuka?nima ban son ki kakaba min ke akayi"sake fashewa da kuka Zuhra tayi tana toshe bakinta don tabbas taji zafin kalman nasa(su Zuhra Ashe ba dadi,shida kike cemasa bakison sa fa?yafiki jin radadi fa.)
Wucewa yayi haka tabisa har suka fice daga gidan nan securities din suka rufe ko ina,gidan sa ya shiga,gate man din shima yarufe ko ina,kaitsaye apartment dinsa ya nufa,cikin sanyin jiki Zuhra ke binsa,wani mahaukacin kamshi ne ya buge hancin ta, tabbas apartment din ya Sauban aljannan duniya ne don apartment din ya hadu,tamkar don ita akayi shi,gani tayi ya nufi stairs ya haye,samun kujera 1 sitter tayi arakube ta zauna tana lumshe ido a dalilin wani irin sarawa da taji kanta na mata,a haka ta cigaba da zama batare da ta ankare ba bacci yayi awon gaba da ita.
Sakkowan shi kenan sanye da pyjamas masu matukar taushi da tsaruwa bakake,hannun sa dauke da laptop dinsa,ganin ta yayi a kwance,cikin nutsattsiyar muryan shi ya fara magana don tabbatar da tayi bacci ko kuwa"Hey! Hey wake up kada jikinki yayi ciwo,shiru yaga bata motsa ba hakan ya tabbatar masa da tayi bacci,ajiye laptop din yayi yana nufar ta,hannu yakai yana cire mata hannun da tarufe face dinta,sosai tayi masa matukar kyau dama ita me kyau ce,hakan yake fada a ransa always, murmushi yayi yana shafa lips dinta wanda yasake pink a dalilin kukan da tasha yau"Rigimammiya! Yafada yana sakin smile,daukan ta yayi cak like bby yanufi stairs da ita yana cewa"wow ashe tanada nauyi?a haka ya isa da ita parlon ya wuce da ita bedroom dinsa yana kwantar da ita, squeezing face tayi tana dan turo mouth wanda yasa point din ta lomawa,cikin baccin tace"ummm"tana sake yamutse face din,kallon ta kawai yake yi yanajin son ta na sake nunkuwa a zuciyar ta.
Warware mata lutfayan yayi,anan wata gown ta bayyana ganin da yayi kamar gown din bata da nauyi ne yasashi barin matashi yana ja mata duvet din,tare da dai-dai ta mata A.C ya kashe light din ya bar mata bedside dum light,yana fita daga bedroom din,kasa ya sauka ya rufe ko ina tare da kashe fitullu ya haye saman yana rufe shima ko ina,dan balcony dake saman yaje ya zauna yana kunna laptop dinsa gefe daya fresh milk ne sai shawarma,aiki yafara inda yaketa cin karo da sakonni na abokan aikinsa suna masa congrats akan auren sa,wasu Kuma na masa iya shige,yakai wajen karfe 12:30 sannan ya tattara komai ya nufi